CHAPTER 11 NA CI DANBEN KUTURU
BABI NA GOMA SHA ƊAYA
GIDAN YANMAKARANTA
A tsawon kwana biyu, su Ado Gombe sun yi matuƙar ƙoƙarin ganin sun gano ainahin dangin Surayya Mustafa. Amma har yau Talata da suke bisa hanyar zuwa gidan 'yan makaranta. ba su ko samu wani wanda ya ce ya santa ko ya taɓa ganinta ba. Sun je FCE zaria babu wani gamsashshen bayani game da ita.
Da har sun yi shawarar buga hotunan Surayya a kafafen yaɗa labaru. To sai suka fasa saboda yin hakan ƙila ya zaburar da makashin nata ya kauce daga inda tsautsayi zai sa a kama shi.
Hadiza, ta yi fakin a ƙofar gidan, a tare suka fito daga cikin motar ita da Ado Gombe. Suka bar motar tasu a nan waje suka isa kai tsaye zuwa ɓarayin 'Hajiya Ma'u. Sun isketa tana karin kumallo da kakkauran shayi da Soyayyar dankalin turawa da ƙwai.
Bayan sun yi sallama ta amsa haɗi da ba su izinin shiga. Suka haɗa baki gaba ɗaya wajen gaishe da ita. "Barka da war haka Hajiya." Hadiza ta nuna kanta ta ce, "Sunana Hadiza, Abokin tafiyata kuma Ado Gombe. "Hajiya Ma'u ta kallesu cike da neman ƙarin bayani, ba ta yi magana ba har sai da ta haɗiye wainar ƙwan da ta cika mata baki. Ta ce, "Ban gane ku ba, daga ina? zuwa Ina?"
Hadiza ta ce, "Ranar da na zo bakya nan, shi ya sa ba za ki gane ni ba, na zo satin da ya wuce neman wata 'yar hayarki, da ban same ta ba, na ce zan dawo wani lokaci, to shi ne yau na ƙara dawowa."
"To, yanzu za ki iya zuwa ki ganta. Amma maza basa shigar mini ɓarayin 'yan haya saboda kariya daga wasu mugayen mutane."
"Na sani Hajiya." Hadiza ta faɗi tana kallon Ado Gombe da yadda ya haɗe fuska kamar zai kwarma ihu. ta ci gaba, "Ban Sani ba ko za ki taimaka mana da... "
"Na taimaka na kira maku ita?” Hajiya Ma'u ta faɗi a ɗan fusace. Fahimtar hakan ya sa Hadiza ta yi saurin katseta. "A'a, Hajiya, wane mu mu ce za mu aikeki, abin da nake son faɗi shi ne, tambayarki za mu yi game da ita."
"Wace ce za ki yi mini tambaya game da ita?"
"Surayya Mustafa."
"Ok, to ina zuwa." Ta miƙe a ƙuntace ta isa cikin ɗaki ta ɗauko ƙaton littafin da take ɗaukar sunayen 'yan hayar gidanta. Ta dawo ta buɗe wasu shafuka kana ta ɗago kai ta kalli su Hadiza ta ce, "Surayya Mustafa ta bar gidan nan kusan sati uku ke nan, yanzu wata ce a ɗakin nata..."
"Amma Hajiya, a wancan satin da na zo na haɗu da wata ƙawar Surayyan."
"Idan Izzatu kike nufi? Ita ma ta tashi yau kusan sati biyu ke nan."
"A'a, ba Izzatu nake nufi ba, Ni wacce na haɗu da ita, ta ce mini sunanta Sajida..."
"To wai wa kike son gani cikin Sajida; Izzatu; da Surayya?”
"Da za mu ga Sajidar ma ya wadatar." Inji Ado Gombe. Hajiya ta ɗauki wayarta ta kira mai gadi, minti ɗaya kacal ya iso yana faɗin, "A yi mun afuwa Hajiya, na zaga kama ruwa ne da yake yau na tashi da atini."
"Allah ya sauwaƙe, dama Sajida za ka kira mini a sama ɗaki na 22." Mai gadi ya bi su Ado Gombe da kallo, ta ke ya shaida Hadiza, yana murmushi ya ke faɗin, "Sajida ba ta a gidan nan, rabon da na ganta tun ranar da kuka haɗu Hajiya." Ya nuna Hadiza.
Hadiza cike da mamaki ta ke faɗin, "Bayan rabuwarmu ne ta tafi ko?"
"Ai kuwa, a ranar da kuka haɗu, ita ma a wannan ranar Talata ta tafi, har yau ba ta dawo ba." Hajiya Ma'u ta ce tana kallon mai gadi, "To kuma kayanta fa? Wata bar ma wa? Ni fa ba na son irin haka wallahi." Mai gadi ya ce, "Ni kaina ban san lokacin da ta zo ta ɗauki kayanta ba, duk da yake dama ba wasu kaya ne mai yawa ta zo da su ba."
Hadiza da Ado suka kalli juna. Ado Adamu, ya aje numfashi. Ya ce, "Yanzu ina za mu ga Izzatu tunda Sajida ta yi layar zana?" Hajiya Ma'u ta ba shi amsa, "Ina kuwa muka san inda Izzatu ta koma, kawai hanya mafi sauƙi ku je makarantarsu, KASU."
"Kayan Surayya ma yana wurin Izzatun. Kuma har ma wasiƙa ta bari aba Surayya duk ranar da ta dawo. Ina ganin adireshin inda za a sameta ta rubuta a wasiƙar. To amma na ba Sajida wasiƙar." inji mai gadi.
"Ka ba Sajida wasiƙar?" Ado ya tambaya a ɗokance. "Eh, na ba ta ne saboda ita ƙawar Surayya ce, ta kuma ba ni tabbacin za ta ba ta."
"Tabɗijan, to yanzu ina za mu ga ita Sajidar? Hadiza ta buƙata." Hajiya Ma'u ta ce, "Ba mu san inda za ku ganta ba itama, sai dai ku bar wasiƙa ko lambar waya idan ta zo a ba ta." Mai gadi, ya yi saurin katseta, "Ina kyautata zaton Sajida za ta dawo, domin ta ba ni wayarta na kai ma ta gyara, to ban amso ma ta ba kun ga kuwa dole ta dawo don wayar mai tsada ce."
Cikin rawa baki Hadiza ta ce, "Shin ina ne ka kai mata gyaran wayar?"
"A maƙarfi plaza ne..."
"To mun gode, koma bakin aikinka mai gadi." Hajiya Ma'u ta faɗi haɗi da daddanna waya, da alamun ƙosawa a tattare da ita.
Bayan ta kanga wayar a kunni ta yi magana da mai napep a kan ya zo ya kaita anguwa. Ta juyo ga su Hadiza ta ce, "To ina ganin iya taimakon da zan iya yi maku ke nan, domin duk mutanen da kuke nema sun tashi daga gidan nan, ni ma yanzu anguwa za ni sai bayan sati zan dawo."
Ado da Hadiza suka yi ɗan shiru zuwa can kowannen su ya fiddo da I.d card ɗinsa na shaidar aiki sannan suka haɗa baki gaba ɗaya wajen faɗin. "Ya kamata tun farko mu faɗa maki mu su wane ne, mun zaci ba za ki bamu haɗin kai ne ɗari bisa ɗari, shi ya sa ba mu nuna maki cewa mu (CID OFFICER'S) ba ne wato ‘yansandan farin kaya. Mu na neman duk wanda yake da masaniya ko bayani game da Surayya Mustafa."
Take fuskar Hajiya Ma'u ta sauya daga kyakkyawar yanayi zuwa hazo-hazo, murya a shaƙe take faɗi. "Allah sarki, ban san daga hukumar bincike kuke ba. To amma ku yi haƙuri, kun ga dai babu ko ɗaya daga cikin matan da kuke nema. Ina zaton babu wata gudunmawa da zan iya ba ku kuma."
Hadiza ta yi murmushi, "Bayan mu masu bincike, da Sajida ƙawar bogi. Babu wasu da suka taɓa zuwa neman Surayya?"
"A'a, gaskiya babu."
"kin tabbatar?" Ado Gombe ya tambaye ta haɗi da ƙura ma ta ido ko zai gano wani abu. Sai ya ce, "Ki rantse ba ki ɓoye mana wani abu ba?”
"A'a, zan yi maku ƙarya ne? Ƙarya fa linzamin shaiɗan ce..."
"Ƙwarai kuwa, kuma ƙarya fure take ba ta 'ya'ya." in ji Hadiza ta ci gaba da faɗi tana kallon abokin aikinta. "Gombe, ya kamata mu yi tozali da bakaninken da aka ba gyaran wayar Sajida."
"Ni ma hakance na raya yanzu a raina. "Suka kalli Hajiya Ma'u gaba ɗayansu, inda Hadiza ta tsareta da ido ta ce, "Hajiya muna neman alfarmarki, muna son mai gadi ya zo ya kaimu wajen mai Gyaran wayar."
Da ganin yanayin Hajiyar, ta ƙosa su bar ta ta huta, don haka cikin ƙosawa ta ce, "Wani lokacin fa, mai gadi shagiri girbau ne"
"Me kike nufi, Hajiya?" Ado ya tambayeta.
"Bai san ainahin gaskiyar batu ba sai ya yi ruwa da tsaki, ina nufin ya faye katsalandan da faɗi ba a tambaye shi ba ko kuma ya kwashe ba a kasa da shi ba..."
"Ai kuwa mun kasa da shi sai dai idan ke ce za ki hana shi ya kwashe, ko ki yi ma bakinsa asurka." Hadiza ta faɗi tana kallon Ado. “To shi ke nan, ga fili ga mai doki nan." Ta ƙarishe da ɗaure fuska haɗi da ci gaba da shan shayinta wanda ya riga ya zama ruwan sanyi.
Mai gadi kuwa dama kamar jira yake yi a kira shi, ƙila kuma ya maƙale a ba bakin ƙofa ne, don a nan kiran sunansa ya afko kamar an jeho shi. Cikin sauri Hadiza ta rufar ma sa da tambayar, "Za ka iya kaimu wajen wanda ka kai gyaran wayar Sajida?"
"Eh, zan kai ku mana, amma sai idan Hajiya..." Ya ka sa ƙarasawa, sai ya ɓige da kallon ɓangaren da Hajiya Ma'u ke zaune. Hadiza da Ado suka bi Hajiyar da kallo su ga ko za ta yi masa magana da ido ko wata alamar da za ta hana shi ya yi masu rakiya.
Mai gadi da ya lura suna kallonta sai ya samu ƙwarin gwiwwar ci gaba da faɗin, "Idan Hajiya ta amince zan rakaku mana." Jin ana ma ta kallon ƙurulla ya sa ta ce.” Ba matsala mai gadi, kana iya rakasu ba ni da kayan zafi.. "
"Yawwa, mun gode sosai Hajiya da wannan karamci da haɗin kan da kika ba mu, in shaa Allah ba zai daɗe ba. "Su uku suka shiga mota, Ado Gombe ke tuƙawa Hadiza zaune a gaba yayin da ɗan rako Mai gadi ke baya. 'Yan mintoci su ka isa maƙarfi plaza, cikin sa'a su ka sami Najib yana tsaka da aiki, ga wayoyi nan da ya yi masu tsirara ana ta gyarawa. A teburin nasa mutane ne kusan biyar suka yi ma sa ƙawanya suna jiran a gama masu gyara a basu wayarsu.
Najib, ya ƙware wajen gyara ko wace irin waya babba ce ko ƙarama. Shi ya sa kodayaushe za ku ga ana yi ma sa layi, wani zubin kuma ya kan yi wasan ɓuya da masu waya musamman idan ya saɓa alƙawari. Suka ɗan keɓe da shi.
Bayan ya ji batunsu na son sanin inda za su sami ganin Sajida, cike da mamaki yake faɗin. "Ai ta zo nan da daddaren ranar Talata ta amshi wayarta." mamaki ya kama mai gadi, "Ka na nufin ta zo nan ranar Talata ta amshi wayar? To amma ai a ranar mun yi maganar wayar da ita, ba ta nuna za ta zo ta amshi wayar da kanta ba, tunda har kuɗin mota ta ba ni. Kuma tun lokacin ban sake ganinta a gidan 'yan makaranta ba."
Najib ya kalli mai gadi wani iri, "Na ji ka ce ba ka ƙara ganinta a gidan 'yan makaranta ba, shin me ya kaita gidan 'yan makaranta? Na san Sajida fiye da shekara a nan garin, ta kan kawo mun gyaran wayarta Da na ƙawayenta, idan kuma canjin waya za ta yi, ni take ba tsohuwar nata na siyar sai ta yi ciko a siya ma ta wata. To ko dai ba Sajidar da nake magana kuke nema ba?"
Ado ya katse shi, "Kwatanta mana Sajidar da ta zo ta amshi waya." Najib ya kwatanta masu, sai Ado ya kalli Hadiza ya ce, "Kamannun ta ne ya kwatanta?" Ta gyaɗa kai tana faɗin, "Ita ce wallahi, amma Malam Najib ina kake ganin za mu Same ta?"
Ya ce, "Wallahi idan nace ga anguwar da take ko garin da take na yi ƙarya, ni dai tana kawo mun gyaran waya, ta kan kuma canza idan ta ga sabon shigowa. To amma a wannan karon da ta zo ta amshi wayar, na ji tana waya da ƙawarta, inda take faɗa ma ta maganar fatin da za su je Abuja ranar sha huɗu ga watan biyu (14/2/2018) wato ranar masoya ta duniya, nan take ya faɗa masu sunan wurin da ya ji Sajida na kwatantawa ƙawar tata. Suka yi sallama da Najib, suka ɗauko mai gadi sai gida, da za su rabu suka yi masa babbar kyauta da farare bugun Abuja haɗi da neman guntsa masu idan Izzatu ko Sajidan wata ta sake dawowa.
A mota Hadiza ke faɗin, "Ka ga kuwa Ado Gombe, Sajida ce lamba ɗaya cikin jerin mutanen da za mu zarga, ta yi baki biyu wajen gabatar mun da kanta a lokacin da muka fara haɗuwa ranar Talata a gidan 'yan makaranta, ban da haka jikina ya ba ni cewa bincike ko bin diddigi ya kawo ta har ta kama ɗakin haya a gidan. Amma koma mene ne? Za ta zo hannu a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗan kada."