CHAPTER 13 DAKIN AZABA
BABI NA GOMA SHA UKU
ƊAKIN AZABA, A CIKIN GIDAN HAJIYA BARA'ATU
Izzatu, ta buɗe idonta da ƙyar, ta ga wasu giza gizai haɗi da yana-yana sun haɗu sun samar da wata ƙwarya-ƙwaryar gajimare. Ta ƙyafta idanuwanta da suka yi mata nauyi. Take ta ga haske kamar yanzu ne gari ya waye.
Kwance take rigingine bisa wani ƙaramin gadon ƙarfe, fuskarta tana kallon sama, yayin da ta ji kamar a na kwaɗa mata guduma a kai. Nan take ta tuno inda take. Wato gidan Hajiya Bara'atu. Ta yunƙura za ta tashi sai ta ji ƙafarta ɗaure da wani murtukeken igiya an haɗa da gado.
Ta ji gaba ɗaya ma jikinta ciwo yake mata. Ta saki nannauyar ajiyar zuciya ta yi jarumtar tashi zaune haɗi da buɗe ido sosai, sai ta ga ba a falon Hajiya Bara'atu take ba, nan yafi kama da BQ. Ta tambayi kanta 'Me ya sa na kawo kai na ga halaka?
Oh! Ni Izzatu, yau na shiga uku, na taka sawun ɓarawo, wai ma me ya sanya ni bin tafarkin shaiɗan? Me ya kai ni shiga ayarin masu shashanci da mata? Da na bi gargaɗi da nasihar mahaifiyata, da tuni na yi aurena, da tuni ina da 'ya'yana....’
"Ai in dai ba ki faɗi gaskiya ba, to sai dai ki haifi 'ya'yan a kiyama" inji Hajiya Bara'atu. Sam! Izzatu ba ta san maganar da ta yi a zuciyarta ya fito fili ba. Hajiya Bara'atu, ta durƙusa kusa da ita, ta faska ma ta mari.
"Ba ki azabtu ba har yanzu, azabar da aka gana maki bai shigeki ba, to yau kuwa za ki ɗanɗana kuɗarki, amma kuma idan kika yi wa kanki ƙiyamul laili kika faɗa mini inda kika aje kayan Surayya Mustafa, to zan 'yanta ki wata ƙilama ki zamo ɗaya daga cikin 'yan gatana."
Hawaye ya gangaroma Izzatu a kunci, ta cije laɓɓanta haɗi da girgiza kai. tana ji a jikinta koda za a yi ƙuli-ƙulin kubura da ita, ba za ta yi gigin faɗa masu cewa kayan Surayya Mustafa yana gidan Ramla ba, don ba ta san abin da za su yi wa Ramlan ba. Cikin alamun gajiya Izzatu ke faɗin. "Na rantse ban san komai game Surayya Mustafa ba balle kayanta, sunan dai ɗakinmu ɗaya ne, amma kusan zaman 'yan marina mu ke yi, kowa da inda ya sa gabansa."
Hajiya Bara'atu ta kalli Izzatu a ɗage, sam ba su faɗa mata sun san ta ba da wasiƙa a ajema Surayya ba, ba su sanar da ita cewa wasiƙar tana hannunsu ba. Izzatu ba ta san cewa sun san kayan Surayyan yana wajenta ba, ƙila shi ya sa ta kafe akan babu komai na Surayya a wajenta.
Hajiya Bara'atu, ta samu kujerar roba ta zauna tana fuskanta Izzatu ta ce, "Kin san ƙarya kala kala ne. To gara ki faɗi baƙar ƙarya, domin farar ƙarya, kan sa a harbo jirgin maƙaryaci da sauri, kuma ba za ki taɓa layance mun ba." Izzatu, ta fashe da kuka, "Wallahi babu ƙarya a duk abin da na faɗa maku..."
"Maƙaryaciyar banza. Kin san Allah? Wallahi ba ni da tausayi ko na ɗigon ƙwayan zarra, abin da aka yi maki zuwanki gidana, ba komai ba ne idan a ka kwatanta da abin da na yo maki tanadi yanzu, don wallahi sai na shayar da ke maɗaukakin mamaki. Ina kika kai kayan Surayya Mustafa?"
"Don darajan iyaye da kakanni ki yi haƙuri, wallahi ban san komai ba game da Surayya Mustafa. Inda na sani kwarankwatsa da na faɗa maki."
Hajiya Bara'atu ta miƙe a fusace, ta isa ga soket ɗin jikin bango ta jona dutsen guga na nepa 'yan mintoci kaɗan ya ɗauki zafi rau! A kusa da ita akwai wata 'yar roba mai ɗan faɗi, a cikin robar akwai ruwa, sai ta saka dutsen gugan a ciki, ji kuke cuuuuu! Ta fidddo da shi yana turiri, ruwan kansa turiri ya ke yi. Ta nufo Izzatu da dutsen gadan gadan.
Izzatu ta tashi da sauri tana maƙyarƙyata. "Wayyo Hajiya ki yi mini rai, ba kyau azabtar da bawa da wuta, Allah ne kaɗai mai ikon yin haka." Hakan da ta faɗi sai ya sake tunzura Hajiyar. "To, koki faɗi gaskiya ko kuma in ɗora wannan dutsen a kyauyawar fuskanki ta yadda mutane zasu kasa gane ki, kin ga batun ƙwalisa da kwalliya ta ƙare."
Ta aje dutsen gugan a ƙasa. Ta isa gaban Izzatu ta wanka ma ta mari. "Za ki faɗi gaskiya ko a'a? Wannan itace tambayar ƙarshe da zan yi maki, wallahi Allah idan ba ki faɗi inda kika ɓoye kayan Surayya Mustafa, ba sai na goge fuskarki da dutsen guga kamar yadda ake goge kaya."
Ta wancakalar da Izzatu ta koma ta ɗauki dutsen gugan ta sake nufo Izzatu gadan-gadan. Da Izzatu ta tabbatar lallai ba shakka idan ba ta faɗi inda kayan suke ba, Hajiya za ta iya nasa ma ta dutsen a fuska, don tun zuwanta gidan ta fuskanci Hajiyar ba ta da imani, ba ta da tausayi. Ai kuwa ba ta yi aune ba ta ji hucin zafin wuta a kuncinta. cikin kiɗima take faɗin.
"Dakata ki ji Hajiya."
"Yawwa koke fa? Ai gara ki jefar da ƙwallon mangwaro ki huta da ƙuda. Muddin kika faɗi inda kika ɓoye kayan Surayya kin sha a wajena. Ko da yake ba zance ɗari bisa ɗari kin sha ba har sai mun je mun ɗauko kayan." Nan take ta kwatanta ma ta gidan Ramla.
Bayan ta gama sai Hajiyar ta isa gaban soket ta kashe haɗi da zare wayar dutsen gugan ta ce, "Zan aika a ɗauko mun kayan. Idan sun dawo, to sai a kwanceki ki kama gabanki idan kin so ki ci gaba da shiga sharo ba shanu."
Hajiya Bara'atu ƙasurgumar muguwa ce, mare ɗigon imani balle tausayi, idan ta aikata wani ta'addacin, za ku rantse da Allah ba mace ta aikata ba. Ko da yake an ce zama da maɗaukin kanwa yana kawo farin kai. Wata ƙila hakan ce ta sa Hajiya Bara'atu ta iya salo-salo na horar da mai laifi don samun bayanin da ta ke nema. Saboda an ce ta taɓa yin saurayi soja, kafin su rabu da juna, ya sha gasa ta, da azabtar da ita da nau’ikan horo, shi ya sa ta gwanance a fagen iya horar da duk wanda ya yi rashin nasarar shiga huruminta.