ALAQAR MU!

Chapter 5

by @hafsatouamjad2

💋_ALAQAR MU_💋

         ~Our destiny ~


©️®️```Hafsatouamjad``` 


Chapter 05 .


*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_nfection_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_


_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****



Daga can bangaren Ammah ta mike hankalin ta atashe tace “What “? 

“Yes Ammah I mean it I love her “

Katseshi Ammah Tayi cikeda fargaba tace “What are you saying Hammad ? Asmah kanwar ka kake cewa kana so zaka aura are you insane ? “

“Ammah kin fini sani ai kinsan Akwai aure tsakanina da Asmah mesa baza ki bari na aureta ba “?

“Shut up my friend “

Ammah ta doka mishi tsawa tace “Look ka hadomin kan ‘yayana ku dawo gida ,in nasan haka ze faru bazan barka ka kebance da ita ba tunda har kana darsa wani abu a ranka game da ita ,kanaso ka sakata confusions ne “?

Bata kara bari yayi magana ba ta katse kiran bayan ta kara jaddada masa gobe su taho gida if not zega other side dinta .

Wulla wayar yayi akan gado yana baya da sumar kanshi ,jijiyoyin kanshi sun mimikke rike kanshi yayi yanajin kamar yayi kuka . Ya dade a atsaye bakin glasses din dakin ya kurawa Guri daya ido , 


Ammah tana katse kiran ta kira wayar yusuf yana daga wa tace “Yusuf kaje ka samar muku ticket gobe ku dawo gida “

“Lafiya kuwa Ammah “?

“Do as I say “

“Okay Ammah ,Amman please meke faruwa Naji hankalin ki atashe did something bad happened “?

“Babu komai kawai inason ganin yarinya tane “

Sauke numfshi yai yace “Ammah you scared me “

Itama ajiyar zuciya tayi tace “Take Care “

Yana sauke wayar ya fito daga dakin , dakin Hammad ya nufa a zaune ya ganshi a gefen gado rike da kanshi ,karawa yayi da sauri yana riko shi yace “Lafiya kuwa Ya Hammad “?

Girgiza masa kai kawai yayi be iya magana ba .

Taimaka mishi yayi yace Toh ya kwanta ya huta ,beyi musu ba ya kwanta akan gadon yana Lumshe idanun shi . 


Yana fitowa Airport ya nufa seda ya tabbatar ya samar musu ticket din sannan ya dawo time din Magrib ya kusa , seda yayi sallah a masallacin hotel din sannan ya hau ,dakin Asmah ya shiga ya fada mata gobe zasu wuce Ammah ta kira ,dage girarta tayi tana cewa “Ya Yusuf banyi tsaraba ba fah ni gaskiya karmu tafi “.

Zama yayi yana tallafo fuskanta yace “Asmah so kike Ammah tayi fushi damu “?

Girgiza kanta tayi ,yace “Toh gara mu tafi din next time zamu dawo , Yanzu ki shirya semuje ki siyo abunda kikeso “.

Murmushi tayi ta tashi da sauri ta wuce toilet shikuma ya fita .


A bangaren Ammah kuwa hankalin ta yayi balain tashi ,bazata bari wannan abun ya faru ba tasan halin Hammad yanada xuciya muddin yace zeyi abu babu makawa se yayi ita kuwa bazata bari hakan ya faru ba batason suyi wani abunda ze sakawa Asmah shakku aranta akan ta.

Tunani take tayi ta kama wannan ta saki wannan ,Tunowa da Noorain da tayi yasa da sauri ta dauki wayarta tayi dialing number shi ,daga can bangaren Noorain yace “Ammah barka da yamma “

“Barka Noorain ya aiki “?

“Alhamdullilah “

Shiru tayi tana nazari aranta ,batada wani zabin daya wuce shi ,shi kadai ya rage hope dinta .

“Ammah wani abu kikeso “?

“Inason ganin ka please “.

Da sauri ya tashi yace “Toh Ammah gani nan “.

Hankalin sa ya tashi ayanayin dayaji muryan Ammah . 

  Daman yana gida shiyasa be dauki 10minutes ba ya shigo gidan ,tana zaune a parlour tayi shiru da alama tunani Take .

  Da sallama ya shigo cikin parlour Ammah ta dago tana amsa mishi ,Da faraaa a fuskanta .

  A Dan nesa da ita ya zauna yana Dan yin kasa da kanshi 

Kallon shi Ammah ta farayi tun daga kan kafar shi ,har tsakiyar kwantacciyar sumarshi , Kamilallen mutum me cike da Haiba da nasaba ,ayanda Ammah Take kallon shi tunani Take a shekarun sa dinan Anya bazata tauye shi ba ? Dan tabbas tasan Noorain kadan ya rage yakai 40years shin ze iya mingling da Asmah Yar shekara 16 ? 

Sauke numfashi tayi tana bawa kanta hope Dan bataso ta sare .

“Noorain Alfarma nake nema awurinka “

Da sauri Noorain ya dago yace “Ammah ai kinfi karfin ki nemi alfarma awurina kawai umarni zaki bani “.

Murmushi tayi najin dadin kalamansa tace 

“Inaso na baka auren Asmah Noorain , na bincika banga wanda ya dace da Asmah ba Sakai ,inason rayuwar yarinta ta inganta banso na barta acikin tunani ko damuwa kai kasan abunda ya sameta abunda yasa na zabeka kenan ,Asmah yarinya ce kamilalliya wallahi bata ta’amalli da mutanen banza Kaddarara ce taxo ahaka ,kayi min Alfarma nan ,sanann banso bikin ku ya wuce wata daya “.

Ammah ta karasa hawaye na tarar Mata a idanunta .

Wani sanyi da farin ciki ne ya ziyarci zuciyan sa, be taba tunanin ze mallaki Asmah ma cikin sauki haka ba , mene ne na neman Alfarma ai shi yakamta ya nemi wannan alfarmar besan tukwicin da zeyiwa Ammah dashi ba ,Mafarkin Momyn shi ze tabbata kullum adduarta Allah ya fito mishi da Matar aure karya mutu beyi aure ba ,karya mutu bataga Jikokin abun kaunarta ba .

Jin yayi shiru yasa jikin Ammah yayi sanyi tace “bazan maka dole ba Noorain In baka sonta please karka takura kanka ,tunda kai ba yaro bane “.

Ahankali yace “Ammah babu alfarmar da zaki nema awurina naki miki sede idan banida dama ne,Inason Asmah ,sabida Asmah abun so ce ga kowa kuma kowa zeyi fatan ya sameta amatsayin Matar aure na amince Allah ya sanya alkhairin sa “.


Wani kayataccen murmushi Ammah ta saki bata taba tunanin Noorain ze amince da wuri haka ba .

“Thank you Noorain Allah yayi maka albarka nagode “.

Da Amin ya amsa yana mikewa yace “Mu kwana Lafiya Ammah “

“Toh Nagode Noorain ,gobe Asmah zata dawo “

“Allah ya kaimu “

Duk yanda Noorain yake da zurfin ciki amman seda farin cikin ya bayyana a fuskan sa , Yana shiga gidan part din Momy ya nufa suna zaune itada da Nabila suna lissafin kayan da Uncle governor ya kawo wanda zaa rabawa masu karamin karfi , Da sallama ya shiga parlour fuskan shi ke Waye da Murmushi , amsa sallamar Momy tayi tana kallon fuskan shi tace “Noorain ko de an maka albishir ....”

Katseta yayi yace “Momy yau de Burin ki ya cika “


Zama tayi akan kujeran dake facing nashi tace “Ka samu Matar aure “?

Gyada mata kai yai yana fadada faraarshi .

“Allahu akbar “.

Momy ta fada tana sujjada ,dagowa tayi tana cewa “Allah na gode maka daka cikamin burina Alhamdullilah ya Allah “

Nabila ma dake zaune Murmushi take tace “Finally tuzuru ze zama ango “

Kallonta yayi yana balla Mata harara tayi ksa da kanta tana dariya . 

“A ina ka samomin zankadedeiyar Amarya ,wait wata mace ce ma tayi nasarar yin awon gaba da zuciyar tuzuru”.

Murmushi yayi yace “Ammah ai kuna kusa ma kin Santa “

Gyada kai tayi tana cewa wacece ? 

“Asmah ce Momy ta gidan Uncle USMAN “.

Tuni duk wata faraa dake fuskan Momy ta dauke dif tai kicincikin darai . Kallonta Noorain yayi yace “Momy yanaga kamar bakiyi farin ciki ba “?

“Baze yiwu ba ,auren ka da Asmah baze yiwu ba Noorain muddin Ina raye bazata aureta ba Wallahi ,ka rasa wadda zaka daukko min Kaf cikin matan duniya se wannan yarinyar da bata da gata batada Asali ,Yarinyar shegiya ita zaka daukkomin “?

A zabure Noorain ya dago kanshi jin kalaman da Momy take bin Asmah dashi ,lokaci daya yaji ranshi ya baci hankalin shi ya tashi ,duk wadannan magan ganun menene amfanin su .? 

Nabila ita kanta maganganun sun mata nauyi kwata kwata bataji dadin maganganun Momy ba .

Be gama farfadowa daga Wada can maganganun ba ya tsinkayi muryan Momy tana cewa “Kodan mun damu kayi aure yasa ka zabo mana mara nasaba Noorain ? Banda mutuwar zuciya ma Ina kai ina wannan Yar yarinyar sa’ar Nabila Ina zaka kaita ? Me zata maka ,so kake ka jawomin magana ko Toh Wallahi baka isaba karka saka wannan maganar ma aranka ka hakura da Asmah ka nemi wata koma wacece zan aura maka amman Banda Mara asali tsintacciya “.


Innalilahi wainilaihi rajiun yaketa maimaitawa a ranshi . 

Kwata kwata ya kasa magana zuciyar shi kawai take tafasa , kanshi ya rike da yake sara mishi yanata addua aranshi 

Dakyar ya iya bude bakin shi yace “Momy ni Asmah nakeso muddin kika rabani da ita nima zaki rasani “


“Sede kuwa na rasaka Noorain dadai na barka ka aureta Wallahi ,shima wanda yace ze auretan bagashinan ya fasa saboda yayi bincike ya gano abunda suke boyewa sekaine shugaban marasa zuciya na duniya kowa yana gudunta kai zaka debo mana ita Toh Wallahi ahir Dinka ,ka fita idona in rufe “.


Tana gama magana ta wucewa ta ta barshi a parlour .Nabila binshi kawai take da ido ya bata tausayi ba kadan Momy bata kyautawa akan son zuciyarta babu abunda bazatayi ba .



Littafin Alaqar mu na kudi ne it’s just 500 Vip posting sau biyu arana 1k babu tsada Yar uwa ki siya kar abarki abaya salon labarin na musanman ne domin Karin bayani ku tuntubeni ta *** ina maraba da masu sharhi .