9&10
MANUFA
NA
AMINA ABUBAKAR YANDOMA
(Meenat A Yandoma)
ArewaBooks:- Meenat_A_Yandoma
Wattpad:- Meenat_A_Yandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
*LITTAFIN MANUFA LITTAFIN KUƊI NE AKAN NAIRA 300 KACAL! ZA KI TURO KUDIN TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 AMINA ABUBAKAR U.B.A BANK.KO KATIN MTN NA 300 TA WANNAN NUMBER *** SAI KI TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER ****
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*****
*****
*AMATULLAH RAHUSA DATA*
*DATA SERVICES AT APPORDABLE PRICES*
*MTN*
500MB-150
1GB-280
2GB-550
3GB-780
5GB-1290
10GB-2500
*AIRTEL*
500MB-180
1GB-400
2GB-620
5GB-1600
10GB-3100
*GLO*
500MB-200
1GB-400
2GB-600
3GB-800
5GB-1600
10GB-3100
*9MOBILE*
500MB-500
1.5GB-1200
2GB-1400
3GB-1600
*Validity 30days*
Checkbalance codes
*MTN* *460*260#
*AIRTEL* *140#
*GLO* *127*0#
*9MOBILE* *228#
*VIA THIS ACCOUNT*
8160508316. Jamila Bello Abubakar. Opay bank
*** for call or whatsapp
LAST FREE PAGE
*PAGE 9️⃣&1️⃣0️⃣*
...Ihu Zinatu take kurmawa ganin yadda ake janta. Ba'a jefar da ita ko ina ba sai tsakar gidan kanta ya bugu da kasa. Da kyar ta Mike tana share hawayen wahala, mutane ta gani tsattsaye saman kanta sun sha fararen kaya fsukokinsu fari tas! Jada baya ta rika yi tana ganin wasu taurari na Mata shawagi. Ganin yadda suka sakata a tsakiya suna kewaya ta hannuwansu dauke da wata tsoka jini na zuba a jikinta. Lokaci daya taji kanta ya sara mata yanke jiki tayi a wurin.Yazid kuwa a hanyar shi ta dawowa yana tsaka da tafiya ya ji an dafa kafadarshi ta baya. Tsaida Driven din da yake yi yayi tare da juyawa amma wayam babu kowa. Doguwar ajiyar zuciya ya sauke tare da cigaba da tuka motar hankali shi duk ya koma ga Zinatu ganin yadda yake jin gabanshi na faduwa.
A gigice ya taka birki, amma ina sai da ya kai ma tsohuwar karo da motar shi. A rikice ya fito tare da sallallami yana dubawa yaga tsohuwace kwance tana numfarfashi. Gabas da yamma duk ya duba bai ga kowa ba sakamakon dare daya fara yi. Kama hannun tsohuwar yayi ya sakata mota ya fizgi motar da gudu.
"nan zan sauka"
Tsohuwar ta fada.
Juwuyowa yayi nan yaga wayam babu tsohuwar babu dalili ta. Gaban shine ya yi mummuna faduwa cike da zullumi abinda zai biyo baya. "anya kuwa wannan matar mutum ce?"
Ganin cikin jeji yake ya saka shi barin wurin a guje.
Jin gidan shuru ya tabbatar mashi Zinatu tayi barci. Kwance ya isketa saman kujera, me aiki ya kwala a kira ta kawo mashi abinci. Bude idanun da Zinatu zata yi taga Yazid tsaye shi da me aiki a kanta. Wata irin kara ta kwala tare darirrike Yazid.
"Ba mutum bace ka kore ta daga gidan nan. Kashe ni zasu yi."
Cike da mamaki 'Yar aikin da Yazid ke kallon ta.
Ganin da gaske take ya saka Yazid yace me aikin tabar wurin.
"Zinatu! Ki dawo cikin hayyacinki. mekeshirin faruwa dake haka? Anya kuwa kece."?
"Ba zaka gane ba domin ba kai ake firgitarwa a cikin gidan nan ba. Sai ranar da ka tarar da gawata sannan zaka fahimci cewar ana tsoratar dani."
"Ga jikkar ka yanzu wata tsohuwa tace a kawo maka."
Me aikin ta kara sa maganar tare da miko ma shi Jikkar.
"Tsohuwar tana ina?"
"Yanzu ta fice daga gidan, tana bani bata tsaya ba."
"OK. Jeki kawai."
"Yazid! Wace ce tsohuwa?"
Dafe kan shi yayi tare dayin Jim! Nan ya kwashe kaf abinda ya faru tsakanin shi da tsohuwar nan ya fada mata.
Sake rikicewa tayi da kyar ya shawo kanta ta fuskance shi.
"Je ki dauko mani Fruits domin ban iya cin abinci. In na gama sai muyi maganar."
"Ka taso muje tare, don gaskiya bani iya zuwa ni daya."
A tare suka dauko Fruit din tana yanka masu suna sha.
"Maganin da Boka ya ba mu shi nike so ki dauko mu turarashi a yau. Ina fata baki manta sharaɗin maganin ba dan kada a kuskura ayi atishawa."
"Ban manta ba amma tsoro nike ji."
"Ki fidda tsoron komai a zuciyar ki domin wannan ita kadai ce hanya guda daya tilo da muke da ita."
Maganin suka dauko tare da turara shi. Hayaƙin shi ya turnuke falon har ta kai Zinatu tishawa ta kufce Mata. A kiɗime Yazid ya kalle ta, kafin ta ankara Yazid da idanu wa shi suka kada suka yi jajur ya sha keta sun fara kokawa. Cikin rashin sa'a Zinatu ta fizgo wukar da suka yanka Fruit tana kokarin buga ma Yazid ita. Fizge wukar yayi tare da kuma mata ita a ciki. Firgitacciyar kara ta saki saida gidan yayi amsa Kuwwa sannan ta yanke jiki ta fadi jini na ambaliya...
... Kamar a mafarki Junaid tsintar kansa yayi a wani ƙasurgumjn jeji me dogayen bishiyoyi ga matsananciyar duhuwa. Sunan shi yaji ana kira, sautin ya rika bi domin ya kai ga me kiran Sunan shi. Daf da wani wawakeken rami ya ganshi ga wata mace tsaye tasha baƙaƙen kaya fuskarta gashi ya rufe ta.
"Junaid! Kayi kuskure taba abinda nike masifa so wanda saboda shi 'ya' ya na casa'in da biyu na cinye. Zan ladaftar da kai ta yadda ko da gaba bazaka sake tunkarar inda Muradina yake ba."
"Wace ce ke? Mi kike nema a wurin?"
Tuntsurewa tayi da dariyar data hadda sama jejin girgiza.
"Ni wuta ce kowa ya taɓani sai na ƙona shi. Ban gayyato ka wurin nan ba donmu tsaya muna surutai marasa amfani. Don haka yanzu ne lokacin da ya kamata ka girbi abinda ka shuka."
Nuna shi tayi a hannu sai ga wani hayaƙi ya fito tare da shiga cikin jikin Junaid. Wata iri karkarwa ya fara yi kafin ya yanke jiki ya fada cikin ramin.
Bayan safiya tayi har suka gama kalaci Junaid bai fito ba. A zaton su ko ramuwar barci ce yake kasancewar yau Weekend ne, sai da suka ga har wurin sha daya shuru. HAJIYA da kanta taje dakin domin tayar dashi.
Kwance yake idanunahi sun kalli sama ga wani farin abu ya biyo ma shi ta gefen baki. Gaban Momy ne ya fadi sakamakon hango Junaid da tayi.
"Junaid! Lafiyarka kuwa baka tashi ba har yanzu?"
Shuru bai farka ba.
Sake magana tayi tare da girgiza Junaid amma shuru bai motsa a. Salati ta fara tare da tafa hannuwa tana me fashewa da kuka. Shugowar Daddy kenan ya jiyo kukan ta.
Ganin Junaid da yayi a wannan halin ba kara min tayar ma shi da hankali ya yi ba. Domin Junaid Ɗan ƙanwar shi ne da suka rasa rayuwarsu ita da mijinta sanadin hatsarin jirgin sama. A gaggauce ya kira likitan shi.
Babu jimawa sai ga Family Doctor din ya iso.
Duk wani bincike daya kamata yayi ma shi yayi amma bai ga komai ba don haka ya umurci Alhaji da suje Asibiti zai fi.
Minah na cikin daki ta rika jiyo hayaniya da kyar ta lallaɓa ta fito sakamakon kanta da taji yana mata ciwo. Ganin Junaid a wannan hali ya Sakata yin kan shi tana tambayar abinda ya same shi.
Basu bi ta kanta ba suka nufi Asibiti.
Duk wani bincike sunyi amma basu ga komai ba, hasalima lafiya lau suke ganin komi. To amma Mike damunshi da har irin wannan ciwo zai kama shi da karancin shekaru shi?
Ɗaya daga cikin likitocin ne ya kira Mahaifin Minah office.
"Alhaji ina tunanin ciwon Ɗanku bana asibiti bane. Abinda zai fi shine ku je dashi gida ko zuwa gobe ne ku nemi Malam addini su duba shi."
"Doctor nima nayi tunanin haka. In sha Allah zuwa gobe in dai naga babu abinda ya canza zamu mayar da shi gida."
Junaid kuwa a hankali ya fara bude idanuwan shi da suka yi ma shi nauyi. Firgigit ya karasa bude su sakamakon ganin Minah da yayi zaune saman kujera tana me sakar ma shi murmushi ga wata sharɓeɓiyar wuƙa a hannun ta.
" Mina! Mi kika zo yi a wurin nan? Mi zaki yi da wuka?"
"Naji suna raɗe-raɗin zasu kira malamai shine nazo in ka rasa ka domin bani son ka tashi bare kaci gaba da kawo mani turjiya a cikin lamurana."
Ganin da gaske take ya saka shi dirowa daga zaman Gadon ya nufi kofar fita. Kofar ta rufe ya kasa koda girgizata. Kara ya saki sakamakon jin an luma ma shi wukar ta baya ta bullo ta gaba...
... Jin hannuwan Jariri sun shaƙota ya Sakata sakin ihu Tana ƙoƙarin jefar da yaron amma ina ba rikon wasa ba yayi mata. Tim! Taji yaron ya fado kasa, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon jinjiri mara kyawun halitta. Mikewa tayi zata ruga ganin jinjiri ya biyo ta a guje tankar yadda ƙadangare ke gudu. Jin taci karo da mutum ya Sakata fasa wata sabuwar ƙarar domin a tunani ta shine taci karo da shi.
"Lafiyarki kuwa Latifa?"
"Ba lafiya Aljani. Ga shi nan a baya na, ka rabani da gidan nan Latif"
"Aljani kuma? Latifaaa! Kin cika tsorata shi yasa kullum a firgice ki ke."
"Da gaske nike Latif ka leka dakin can zaka ga jariri daya riƙe mani wuya."
Ko da ya leka dakin baiga komi ba sai wani ƙaramin Teddy na wasa da Latifa ta siya ta aje ma Unborn din ta.
Dariya yake hannun shi rike da Teddy. "Abun wasan Unborn fane ya tsorata ki."
"Da gaske kake baka ga komi ba?"
"Da gaske mana. Kema dake ganin tsoro ne kika sama ranki."
"Jaririfa na gani yana kirana Mahaifiyarshi. Mi yasa in na fada maka abu baka yadda ne?"
"Babu abinda zai hanani yadda kece dai kawai kina sakama ranki tsoro amma ni na san gidan nan babu wani abun tsoro."
Ganin zata tayar da hankalinta kauda maganar yayi.
An kwan biyu kullum in Latif ya tafi wurin aiki Latifa bata zaman gidan sai dai ta shige gidan makwafciyarta.
Zaune suke suna fira ita da makwafciyarta tata wadda ita ma amarya ce kusan lokaci daya aka kawo su. Tsoro ne ya kama Farida jin irin abubuwan da Latifa ke gani a cikin gida ta.
Ƙarar bugun Get suka ji.
"Latifa gidan ki fane ake bugu."
"ina ga Latif ne ya dawo tun da har magariba tayi."
Ko da ta fito bata ga kowa ba amma ga gidan a bude yake.
Wasu yara da ta gani zasu wuce masallaci ne ta tambaya sunga wanda ya bude gidan ta?
"Wani mutum ne ya shiga yanzu."
Da sauri ta shige gidan gudun kada Latif yayi fushi. "
Sai dai babu motar lafit a harabar gidan. Amma sai wata zuciya tace mata kila wurin aiki ya baro motar. Kutsa kai tayi cikin falon nan tayi arba dashi ya juya baya ya dora kafa ɗaya bisa daya.
"Daga ina kike? Kuma da izinin wa kika fita?"
Muryar taji kamar bata mijin ta ba. Don haka kasa magana tayi sai da taji an dauke ta da wani bahagon Mari daya Sakata ganin taurari suna mata shawagi. Kuka ta saki tare da dafe kumci ta, dagowar da zata yi ganin shi tayi tsaye a gaban ta ga wani rafkeken kai da ido kwaya daya tal! A tsakiyar goshi. Kofa ta nufa a guje zata fice, sai dai kafin ta kai ga kofar ji kake garam! Kofar ta rufe kanta da ƙarfi...
FREE PAGES SUN KARA ME BUKATAR JIN YADDA ZATA KAYA TA TURO KUDIN TA A WANNAN ACC DIN 2294023532 U.B.A BANK AMINA ABUBAKAR. YAN NIGER MASU BUKATA KU TURO KATIN AITEL KUNDAUKI PHOTON SHI KU TUROMANI TA WANNAN NUMBER ***