Mugun gani

Chapter 4

by @sadiyanasir



A haka Sakina tacigaba da Rainon cikinta har yakai watan haihuwa, cikin ikon Allah kuwa Sakina ta haifi Yarinya Mace kyakykyawa mai kama da Abdul_Salam, Alhaji Bashir yayi farin ciki sosai da wannan karuwa daya samu, domin son Yara A jininshi yake.


Nan su Hajiya Mairo Aka shiga shagalin ya bikin Suna zata kasance, Yan_Uwan Sakina kuwa haka suka tare A gidanta, kowa sai Gyara kanshi yake da Abinci masu kyau da Kyal_kyalin Duniya.


Kwana Bakwai cif, Alhaji Bashir ya rada wa Yarinya sunan Mahaifiyar Sakina, Itace ta zabi hakan shi kuma ya biye mata, za'ana kiranta da Iman.


Tunda Iman ta fara wayo, kullum Abdul yana Side dinsu, shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Abdul da Iman, hakan kuwa ba karamin bakin ciki yasa Sakina ciki ba, Babu yanda ta iyane data hana Abdul Shigowa Side din nata.


Ganin Iman din itama tana Kaunar 'Dan_uwan nata yasa Sakina ta dan rage wasu Abin, domin tana Kaunar Iman, bata son bacin Ranta, Sai dai tunda Abdul ya fara daukar Iman yana zuwa da ita Side dinsu! Sakina takasa Jurewa, shiyasa ta fito fili ta gwada wa Hajiya Salma bata son wannan Mu'amala.


Bakaramin Mamaki Hajiya Salma taji ba, ganin da Gaske Sakina bata Kaunar zuwar Iman wajensu, Akwai Ranar da Abdul yaje ya daukota Sakina bata saniba ta shiga wanka, hakan yasa data fito tazo Side din tayiwa Abdul dukan tsiya.


Sabida Al'ajabin Abinda Sakina tayi yasa har Salma ta fada wa Alhaji Bashir Abinda ya faru.


Hakuri ya bata Akan komai lokaci ne, Karta damu watarana sai Labari, Yaranta da tsananin Kishi ke damun Sakina.


Haka Rayuwa tacigaba da kasancewa tsakanin Salma da Sakina, Abin dai babu dadi, domim zaman doya da manja su keyi, tun Alhaji na ganin lefin Sakina harya daina, sabida Iya makirci, ga kuma tsayin daka da Alhaji Ali keyi Akanta.


 A wannan ya nayi Aka sake buga gangar siyasa, cikin Ikon Allah kuwa Alhaji Bashir ya sake lashe zabe A karo na biyu, murna sosai Iyalan nashi sukayi, ga Arziki tafi gaban nada, babu Abinda za'ace sai godiya.


A cikin wannan yanayi Sakina ta sake samin ciki, nan ma saida suka sake rikici da Ali sosai Akan mummunar Kudirin shi, yakaima ko Magana basuyi, kowa ta kansa keyi, domin Sakina tace idan har ta haifi Na miji babu wanda ya isa ya kashe, domin Arzikin Alhaji Bashir kara yawaita yake, babu yanda za'ayi tayi wa kanta keta.


Sakina nada cikin wata biyar Hajiya Salma itama ta sake samun ciki, murna kam kamar Alhaji zai zauce, domin yana tsananin kaunar Hajiya Salma, tun cikin Hajiya Salma na wata hudu yayi girma domin za kace ta shiga wata bakwai ne.


A wannan lokacin Sakina ta sake haihuwa, Da ikon Allah kuwa ta haifi Yaro na Miji, Tashin hankali da ba'ayi mishi Rana, nanfa Aka shiga takun saka tsakanin Sakina da Alhaji Ali, domin ya dau Alwashin dole Sakina ta kashe wannan Yaron, sabida Alkawari ta dauka tun farko.


Ita kuwa haka ta kekeshe tace babu wanda ya isa ya kashe mata Yaro, Ana jibi suna Alhaji Ali yazo Gidan cikin Dare shida Hajiya Mairo.


Alhaji Bashir yana jikin windon dakinshi yana tunanin Rayuwa yaga Mace ta fito daga ta bangaren Sakina ta wuce da Jariri kanta lullube da mayafi tayi ta baya wajen Flowers, A kidime ya sauko ya nufi side din Sakina hankali tashe.


Ganin kofar A bude yasa ya kutsa kai ciki, jin kananan hayaniya ta cikin dakin Sakina ya sashi nufar wajen da gaggawa, Tsayawa yayi Cak saka_makon jin Muryar Alhaji Ali shida Sakina suna Magana cikin yanayi na fada, A hankali ya karasa kofar dakin gamida kasa kunnuwarsa, nan yaci gaba da jin zantukan da sukeyi A tsakani.


Da karfi yace Innalillahi wa'inna ilaihi Raju'um... jin irin Munanan Maganganu da Ali yakeyi, Hakuri yake ba Sakina Akan dauka mata Jariri da yayi domin Aje A Kashe, A razane gaba daya suka nufi kofar dakin, Muryar na Rawa Alhaji Bashir ya nuna Ali da yatsa, Amma ya kasa cewa komai.


Ganin haka yasa Alhaji Ali Nufar Kichen A guje ya dauko wani karfe ya buga wa Alhaji Bashir Akai, take ya fadi ko shurawa baiyiba.


Karan Ihun Mace su kaji ta bayan windo, A kidime Alhaji Ali yayi hanyar waje, Amma ina ko walkiyar Mutum bai ganiba, Hankali tashe yadawo dakin Sakina, tana tsaye kamar gunki tama rasa Abinyi, banda Karkarwa babu Abinda jikinta keyi, Babban tashin hankali ta shiga domin Ali ya kure mata tunani.


Kota Kanta baiyiba ya nufi Inda Alhaji Bashir yake kwance magashiyan ko Motsi ba yayi, Pillow ya dauka ya sake danne kanshi har saida ya tabbatar yabar Duniya.


Security kuwa tunda su kaji Ihun Mace suka firgita kowa ya mike yashiga lalume, Amma ba suga ko Alamar Mutum ba, Ganin Security sun nufo wajen Dakin Sakina yasa Alhaji Ali kashe duk Kwan lantarki dake dakin, Babu yanda za'ayi kayi tunanin Akwai Mutumin dake motsi A wajen.


Sai da suka shafe kusan Hour suna bincike kafin wajen yayi shuru, da Alama dai ba suga kowaba, ganin haka yasa Alhaji Ali daukar Gawar Alhaji Bashir cak A wuya ya nufo waje dashi, cikin hikima da rufin Asirin Ubangiji yasamu nasarar Shiga dakin Barcin shi ya Ajiye Gawar A Qasa ba tare da Securities sun ganshi ba.


Dakin Sakina ya dawo ya sameta yanda ya barta, bata iya motsa ko yar yatsar Kafarta, Ganin haka yasa ya dau waya ya kira Hajiya Mairo, Ringin daya ta dauka, nan yake sanar da ita Abinda ya faru, ba karamin kidima tayi da wannan Al'amarin ba.


Nan tacigaba da kwantar mishi da hankali Akan ya jirata karya fita A gidan Idan gari ya waye za tazo da Motor, ta yanda baza'a gane ba tare suka shigo gidan ba, cikin yarda da Maganarta ya katse wayar ya cigaba da safa da marwa A dakin.


Duk da sanyin AC dake tashi A dakin bai hanashi hanashi gumiba, Frige ya nufa ya dauko Ruwa mai sanyi tare da watsa wa Sakina A fuska, cikin firgita ta fara sammabatu kamar tababbiya, tana tsine wa Alhaji Ali.


Ganin zata tara mishi jama'a yasa ya wanke ta da gigitaccen mari da sai da taga walkiyar Wuta, A take ta dawo hayyacinta, wani irin kukan kunci ta fashe dashi da karfin gaske.


Gaba daya Abinda ya faru ya dawo mata sabo fil, Kichen ta shiga da gudun gaske ta dauko wuka tayi kan Alhaji Ali cike da zafin Nama, ganin haka yasa yayi kukan kura ya cafke hanunta tare da gwara mata Kai A garu.


Tsit kake ji, take ta sulale ta fadi A kasa sumammiya, cikin wannan ya nayi Akayi kiran Assalatu, Nan take Aka fara dirin zuwa Masallaci, har Aka idar da Sallah A masallacin kofar gidan Alhaji Bashir ba A ganshi ya fito ba, kowa da Abinda yake sakawa cikin zuciyar shi, Masu tunanin bayi da lafiya sunfi yawa, Domin Alhaji Bashir Mutum ne mai tsayar da Ibada, baya wasa da bin Jam'ih matukar ba ciwo yake ba.


Ganin har karfe takwas Alhaji Bashir bai bude kofar side dinshi ba, yasa Securties din dake kula da wannan bangaren suka nufi farfajiyar Gidan domin neman mafita, Sabida babu irin bugun kofar da basu yiba Amma shuru kamar babu Bil'adama.


Side din Hajiya Salma suka fara shiga domin su sanar da ita mai yake faruwa, Mamaki dauke Akan Fuskarsu ganin ko ina Abude, hakan yasa suka kutsa kai ciki, Amma babu inda basu dubaba Allah baisa sunganta ba.


Fitowarsu tayi dai_dai da shigowar Motar Hajiya Mairo cikin Gidan, da sauri tayi parking ta fito ganin sun nufi Side din Sakina, cikin daga murya ta dakatar dasu, cike da girmamawa suka tsaya.


Tun kafin tayi magana suka shaida mata wannan zance, A razane ta dubesu kamar bata san da Abinda ya faruba, nan tayi musu da bara Akan suje su gwada Balle kofar bari Alhaji Ali ya karaso.


Haka suka koma inda Alhaji Bashir yake, ita kuwa da gaggawa ta kutsa Kai cikin dakin Sakina, ganin halin da Mijinta ya shiga ya sata neman waje ta zauna tare da zuba mishi idanu, gaba daya lokaci guda ya fita hayyacin shi.


Murmushin Mugunta tayi ta dubi Sakina dake kwance A Kasa sumammiya, ta jima tana kallonta kafin ta maida hankalinta wajen mijinta.


Nan ta saka masa muguwar shawara data saba, Akan ya dau wuka ya Cakka wa Sakina itama ta Mutu, idan yaso Ace Salma ce ta kashe su, yanda babu wanda zai fahimci da hanun su ciki, Amma idan suka bar Sakina A Raye zata iya tona musu Asiri.


Cike da jin dadin kalmar Mairo ya mike ya dauki wukar da Sakina ta dauko babu imani A tare dashi ya daba mata A kahon Zuciya, Cikin 2minute ya saita nutsuwarshi suka bar dakin ba tare da kowa ya saniba.


Da hanzari suka nufi side din Alhaji Bashir nan suka sami Securities Hankalinsu A tashe ganin Gawar Alhaji Bashir A kasa, nan danan Alhaji Ali ya nufi kan Gawar yana mai wani irin kukan Munafuci gwanin ban tausayi, ganin kidimewar da Yayi yasa suka fara tunanin A kira Police domin su shiga lamarin.


Gaban Alhaji Ali ne ya fadi jin kalmar da Securities suka fada, da sauri ya dago idanunshi ya dubi Hajiya Mairo, ganin ko inkula da tayi da maganar ya sashi maida kanshi bisa kirjin Alhaji Bashir yana mai wani irin Kuka.


Hajiya Mairo ita ta basu karfin Gwiwa Akan su kira Police domin baza'a bar wannan wulakanci A banza ba, nan ta tura securities da su shiga side din Matan Alhaji domin su kirasu su gane wa idanunsu Abinda yake faruwa.


Nan danan kuwa suka Aiwatar da Umurninta, da hanzari suka dawo suka shaida mata cewar basu ga Matan Alhaji ba, Amma sunga Abdul_salam yana barci A dakinshi har yanzu bai tashiba, Nan fuskar Hajiya Mairo ya sake nuna Alamun tashin hankali, da hanzari tace Securities su biyota, haka suka kutsa kai dakin Salma, da hanzari ta karasa gadon Abdul ta rungumeshi, ta kara fashewa da Sabon Kuka.


Abdul bai fahimci Komaiba, A lokacin yana da Shekara 7 A duniya, Amma ganin ya nayin Hajiya Mairo kawai yasha Jinin jikinshi.


Kamo Hanunshi tayi suka fito, yana ta wai_waye baiga Ummin shiba, haka suka nufi side din Hajiya Sakina, Amma wayam basuga kowa ba, dama Iman tana wajen Hajiya Mairo tun Ranar da Sakina ta Haihu, domin Abar mai jego tadan huta.


Zama tayi dirshan Akan kujera ta cigaba da risgar Kuka Abin tausayi, tana mai Magana da karfi Akan ina Yar_uwarta ta shiga, haka ta daga hankali har sai da Police suka shigo Gidan.


Bincike sosai Aka cigaba dayi, nan Aka samu Gawar Sakina A wani daki dake cikin Side dinta, kwance magashiyar Jini yana zuba A jikinta, da gudun gaske Hajiya Mairo ta fada jikin Sakina tana mai wani irin Kuka, hakan yasa Police jin haushi domin zata basu matsala wajen binciken wanda ya cakka mata wukar, saka_makon takai jikinta kan wukar, dole Shatin hannayenta za'agani.


Cikin yanayi na tashin hankali ta budi baki tace Ina Salma? inhar ba'aga Salma A gidan nanba to tabbas itace ta Aikata wannan Mummunan lefin, domin tuntuni kishi yana damunta zata Aikata fiye da haka.


Kafin kace meye Jama'a sun cika gidan makil, nan Akaita Artabu da Jami'an tsaro Akan A jinkirta Sallar Gawarsu sabida su karisa bincike, Amma Imam na Babban Masallaci dashi da mai Martaba Sarki haka suka hana domin A samu A sada Alhaji Bashir da Gidan shi na gaskiya.


Nan Aka wankesu Aka nufi dasu Makabarta, idan kunga irin Kukan da Ali yake yi saikun tausaya mishi, wadansu harda zubda kwalla sabida tausayi, Alhali duk wannan Abin na Munafurci ne...



  Sadiya Nasir Dan