Chapter 5
by @sadiyanasir
Shuru-shuru har tsawan kwana Uku babu labarin Salma, Police kuwa bincike sukeyi sosai don gano wanda yayi wannan Mummunar Aikin, da yawan Jama'ah sunfi Alakanta wannan Al'amari Akan Abokan Siyasar Alhaji Bashir ne.
A yayin da wasu ke tunanin sune suka sace Hajiya Salma, domin A cewarsu babu yanda za'ayi Ace haka kawai Salma ta kashe Alhaji Bashir da Matarsa kuma tabar Gidan ba tare data dauki 'Danta ko Dukiyar Alhaji Bashir ba, Shiyasa suke ganin wannan Kadai Hujja ce da zaisa A fahimci Hajiya Salma bata da Hanu cikin wannan Mummunar Aikin.
Ba karamin tashin Hankali Ahalin Salma suka shiga Akan wannan Al'amariba, Addu'a suka shigayi da saukar Alqur'Ani Akan Ubangiji ya baiyanata ko A mace ko A Raye.
Acikin wannan yanayi Alhaji Bashir da Sakina suka cika kwana 40, Nan Alhaji Ali ya dauki Abdul_Salam ya mai dashi Cikin iyalanshi, Babu yanda Yan_uwan Salma ba suyi dashi Akan Yabar musu shiba Amma Sam Mutumin nan yaki Amincewa, ganin sun takura yasa yashiga ya fita har sai da ya rufe bakinsu kif.
Haka zalika duk wasu kadarori na Alhaji Bashir daya Mallaka haka Alhaji Ali ya hada kansu gaba daya yaci gaba da juyawa hankali kwance babu tsoron Allah.
Ba karamin dukiya Alhaji Bashir ya Mutu yabar wa Abdul da Iman ba, Amma haka Alhaji Ali ya raba kashi Uku yaba Hajiya Mairo kashi daya shikuma ya rike biyu.
A haka Rayuwa tacigaba da kasancewa Duniya tayiwa Alhaji Ali dadi shida Iyalanshi.
Bayan shekara Biyar da Mutuwar Alhaji Bashir, Alhaji Ali ya gawurta ya zama Babban Attajiri, yana daga cikin Masu fada Aji A garin Bauchi.
Duk irin wadakar da yake da Dukiyar Marayu, babu wanda yake iya tunkararshi Akan Abinda yake bai dace ba, domin har Kasar Senigal ya tafi Akayi Mungun Asiri, Har Jaki sai da Aka birne A cikin Kasa domin A toshe bakin Jama'ah Akan tofa koda Kalma daya ce Akan Abinda ya shafi dukiyar Alhaji Bashir da Yaranshi.
Sabida tsanar da Alhaji Ali yayi wa Abdul hakan yasa baya iya kwatanta Adalci A tsakaninshi da Yaran daya Haifa, ko Kaya ne idan ya siyo na Abdul ba'a banbance shi data Yaran Aikin Hajiya Mairo, sun mayar dashi tamkar Almajiri A gidan, hakan yasa shima yaja jiki dasu domin Yaran Alhaji Ali suna nuna mishi Banbanci A fili, shiyasa bayida Abokiyar hira Sai Inna Mariya.
Inna Mariya Dattijuwa ce Mai kirki da sanin ya kamata, 'Yar Asalin Jihar Gombe ce, Aiki ne ya kawota gidan Alhaji Ali tun Mairo tana Amarya, sabida sanin Halin Hajiya Mairo shiyasa tasha Maganin zama da ita, hakan yasa suke tare har tsawan wannan lokacin.
Inna Mariya tana Kaunar Abdul domin Yaron yana bata tausayi Hasalima ji take tamkar 'Dan data haifa, Ba karamin Janshi tayi A jiki ba, domin har kayanshi A dakin Inna Mariya yake, hakan kuwa ba karamin Dadi Hajiya Mairo keji ba, domin ya nema wa kanshi mafita daya nemi dai_dai da Rayuwar shi.
Sabida Shakuwar da Sukayi, har Idan Inna Mariya zata tafi Gombe tare suke zuwa da Abdul su kwana Biyu, yariga ya saba dasu ji yake tamkar 'yan_uwanshi na Jini, wani zubin idan zasu dawo Bauchi har Kuka yakeyi.
Alhaji Ali kuwa Makarantar Kudi ya nema wa Yaranshi duka, ciki harda Iman, domin Umurnin Hajiya Mairo ce.
Wani Abin takaicin har Driver Aka nema musu domin zuwa Makaranta, sabanin Abdul dake Makarantar Gefen Gidansu ta Govnoty, A haka Rayuwa tacigaba da kasancewa har Abdul ya Kammala Makarantar gaba da Primary cikin kunci da Maraici da Rashin 'Yanci, da yardan Ubangiji kuwa yaci jarabawa yanda ya kamata.
Da taimakon Hajiya Mairo ya samu ya fara zuwa Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, tayi hakan ne sabida ganin Abdul ya fara girma karya zargeta A matsayin bata Kaunarshi, Har shopping tayi mishi ta kama mishi daki, nan ya soma zuwa Makaranta yanda ya kamata, A lokacin Iman tana Aji Biyu A secondary, sabida Mungun turba da Hajiya Mairo ta daura Iman Akai yasa sam bata Kaunar Abdul A matsayinshi na Dan Uwanta.
Tunda Abdul ya koma Makaranta ya maida Hankalinshi Akan Abinda ya kawoshi, wani lokaci yayita kewar Inna Mariya, Amma daya tuna irin Rayuwar da yake A wannan Gidan sai yaji sam baya Kaunar zuwa.
Abdul bayida Abokai sai Amini guda daya da suka hadu A sanadin Karatu, wato Mannir, Abota sosai sukeyi da Mannir domin tasu tazo daya, Mannir Mahaifinshi yana da wadata dai_dai gwargodo, don haka Abdul bai shiga Matsin Rayuwa ba, duk da Hajiya Mairo kan taimaka mishi lokaci zuwa Lokaci.
Mannir dan Katagum ne Karatu ya kawoshi Bauchi, Su Uku ne A wajen Mahaifinsu, Mahaifiyarsu tajima da Rasuwa, Saka_makon Mummunan ciwon data samu bayan Haihuwar Autar su Mannir, shiyasa Mahaifinsu yake Kaunar Autarsu domin tayi tashin Maraici, sabida dalilinta har Aure ya kasa.
Kullum idan Abdul da Mannir suna hira, Mannir kan dauko mishi hiran 'Yan_uwanshi, sabanin Abdul dake rasa shi mai zaice game da nashi 'yan_uwan, wani zubin idan suna hiran gidansu Mannir! haka kawai yake tsintar Kanshi da son ganin wannan Autar tasu mai suna Zaliha.
A haka har suka Kammala Aji daya suka doshi ta biyu, Watarana suna Gida suna hutu bayan sun kammala Exams, Abdul yana zaune A dakin Inna Mariya suna zancensu da baya karewa, 'Yar wayarshi ce tayi kara, da hanzari ya dauka ganin Number Mannir ne, Cike da Murna ya dauka suka Gaisa, nan Mannir yake sheda mishi gasu A Garin Bauchi shida Abba da Kannenshi sun shigo ziyara, shine ya rokeshi su biya Gidansu Abdul zumunci ya karu.
Murna sosai Abdul yayi tare kwatanta mishi gidan, Kasar Zuciyar shi kuwa damuwa ya shiga domin bai san wata irin tarba Alhaji Ali da Iyalanshi zasuyi musu ba.
Ganin yanayin damuwar daya shiga yasa Inna Mariya tambayarshi mai yake faruwa, nan ya zaiyana mata komai, Murmushi tayi sannan ta bashi Karfin Guewa Akan ya tashi yaje ya sanar wa Hajiya Mairo Maganar.
Jiki A sanyaye ya nufi side din, A rakube ya zauna ya sanar da ita, ta jima tana kallonshi kafin ta sanar dashi bakomai Allah ya kawosu lafiya, A take fuskar Abdul ta nuna tsantsar Farin ciki.
Bayan isowarsu Abban Mannir, Abdul ya musu iso zuwa wajen Hajiya Mairo, da Mamaki yaga ta tanadar musu komai na tarba yanda ya kamata, har cikin Ran shi yaji dadin yanda ta karbesu, bayan sun gaisa ne take shaida musu Alhaji baya Gari.
Tun shigowarsu Gidan Idanun Abdul ke kan Kanwarsu Mannir wato Zaliha, haka kawai ya tsinci Kanshi da Kaunar Yarinyar Farat daya, har suka kammala suka fito Abdul bai daina kallonta ba, duk kyau da yake gani ta Mannir Ashe ko kafar Kanwarsu bai kaiba, bayan sun gama gaisawa sukayi Sallama dasu suka fito.
Har sai da sukaga kulewarsu kafin Abdul suka koma Gida shida Inna Mariya.
Abu kamar wasa Zaliha ta fara yawo A cikin Kwa_kwalwar Abdul, Kullum idan ya zauna shi kadai bayi da lokaci sai na tunanin Zaliha, A haka Aka koma Makaranta, kasancewar bashi da wata shamaki shida Mannir ya sashi zaiyana mishi komai da yake cikin zuciyarshi, sosai Mannir yayi Murna tare da shaida mishi Ai bata kula kowa, don haka yana da damar tusa Kanshi gareta.
Sanin da yayi wa Abdul na Mutumin Kirki ya sashi Kiran Baban su ya shaida mishi wannan zance, Yayi farin ciki ta bangarenshi, domin tun ganin Abdul da yayi ya kwanta mishi A Rai, Uwa Uba kuma jin irin tarihin Rayuwar shi.
Da taimakon Mannir Abdul ya samu yaje garin Azare domin ganawa da Zaliha, cikin Ikon Allah kuwa Aka sami fahimta cikin sauki, domin Zaliha ta Amince sabida yabon da Yayan Nata yake Akan Abdul, bayan sun dawo Abdul ke sanar wa Inna Mariya.
Shawari ta bashi Akan kawai ya sanar wa Hajiya Mairo wannan zancen, Nan take ya tunkari Hajiya Mairo da wannan Magana, Hakuri ta bashi Akan za tayi bincike duk Abinda Ake ciki zata sanar dashi, Hajiya Mairo kuwa sai da tasa Akayi Mata duba sosai Akan wannan Hadin, daga Karshe bincika ya nuna cewa koda Anyi babu Abinda zai faru, ta kwantar da Hankalinta, nan tasa Aka sake bincika Mata waye Mahaifinsu Mannir da irin dukiyar dake dashi.
Ganin sun fishi dukiya nesa ba kusaba yasa tayi Gaggawar sanar wa Alhaji Akan ya Amince kawai da wannan Hadin suje can su karata.
Shikuma baya wasa da zancen Hajiya Mairo, hakan yasa ya Amince Akasa kankanin Lokaci dun gudanar da hidimar Bikin.
Sabida Kissa da Makirci irinta Hajiya Mairo da Aljihunta ta sayawa Abdul Gida Mai kyau da zasu zauna da Amarya.
Kayan lefe kuwa na gani na fada ta hada mishi, wanda sai da fuskar Alhaji Ali ta kasa don bakin ciki, Amma dake yasan Hajiya Mairo ba tayin komai sai da dalili hakan yasa ya danne zuciyarshi idan Ankwana biyu yasan da kanya zata sanar dashi Kudurinta.
Ranar da za'akai Kayan lefe harda Hajiya Mairo ciki, sunga tarba sosai domin suma ba'a barsu A bayaba wajen zubar da dukiya, An hadasu da tsaraba na gani na fada, Ahaka suka dawo gida kowa da Abinda yake fada.
Abdul kuwa ya sake sosai da Hajiya Mairo, sabida yanda tayi ruwa da tsaki Akan hidimarshi yasa ya fara mancewa da irin ukubar daya fuskanta daga wajenta, har shawari yakanzo suyif kuma ta bashi hadin Kai,
duk da Inna Mariya takan jashi gefe tace yanayi Ahankali, domin tasan Hajiya Mairo ciki da waje.
Yaran Alhaji Ali kuwa tunda Aka shiga satin biki! suka bar kasar, domin A cewarsu ba suga mai zasu zauna suyi A bikin wannan Matsiyaci ba.
Hakan ya mishi zafi Amma ya daure domin bayi da bakin Magana tunda ba 'yanci yake dashi A gidan ba, kwanci tashi Asaran Mai Rai, A haka Aka fara gudanar da Hidimar Bikin Abdul da Zaliha.
Alhmdullah Biki yayi kyau babu Abinda za'ace sai godiya wa Ubangiji Mahalicci, tsabar kissar Hajiya Mairo da kanta ta rakasu Gidan da zasuyi Rayuwar Aure, sosai tayi musu fada kafin ta koma Gidanta.
Bayan Biki da Sati guda Abdul ya koma Makaranta yacigaba da Karatu, Amma zuwa yake ya dawo sabida Zaliha, ita kuwa Zaliha ta cigaba da sana'arta ta saka kayan Fulani tana Sai dawa.
Watarana tana zaune tayi kewar Inna Mariya dake tana yawan kawo mata ziya, waya ta dauka ta kira Abdul yana Aji ta sanar dashi, Fatan A isa lafiya yayi mata, hakan yasa ta shirya ta nufi Gidan, Sosai Inna Mariya tayi farin cikin ganin Zaliha, da kanta tayi mata jagora zuwa cikin Gidan domin gaisawa da Surukanta.
A palo ta samesu gaba daya, Irin tarban data samu wajen Hajiya Mairo da Iyalanta yasa tasha jinin Jikinta sosai, shiyasa da Inna Mariya ta mike itama ta rufa mata baya zuwa dakinta, Sun jima suna hira kafin Zaliha ta sako mata zancen Hajiya Mairo.
Bata boye komaiba, Inna Mariya ta sanar da ita kaf Abinda yake Faruwa, har irin wadakar da suke da Dukiyar Abdul, sosai Zaliha tayi kuka domin ta tausayawa Rayuwar Mijin nata, tare da Addu'ar Allah yaji kan Mahaifanshi.
Nan ta kudurta A Ranta insha Allah saita taimaki Mijinta wajen kwato Dukiyar shi! ko da hakan zaiyi Sanadiyyar Mutuwarta.
Ganin irin yanayin data shiga, ga kuma irin Alwashin data dauka, yasa Inna Mariya ja mata kunne sosai, Akan ta rufa Mata Asiri kar wani yasan wannan zance, daga bisani ta tunasar da ita irin Illar da Hajiya Mairo take dashi, inda Abun mai sauki ne da Abdul bai tsinci kanshi A haka ba.
Don haka taja mata Kunne Sosai Akan tabi komai A sannu kafin ta jawo wa kanta Masifar da bata san ranar Fita ba.
Tun Ranar da taje Gidan bata sake sha'awar sake zuwa ba, ko Abdul yace suje takan kawo mishi uzuri, da yake yasan irin Gidan nasu shiyasa baya takura mata Akan taje dole, Amma babu irin tambayar da baiyi mata Akan ta sanar dashi ko da wani Abubu Amma fir taki.
Ahaka Rayuwa tacigaba da kasancewa har Aurensu yakai shekara guda, A wannan lokacin Allah yaba Zaliha Ciki.
Murna sosai sukayi tare da gode wa Allah da kyautar daya musu, xama suke na rufin Asiri, domin baka sanin sunci ko basu ciba haka suka cigaba da Rainon cikin har yakai wata Tara...