WANI SO

Chapte 1: page 1

by @zeeyabour20

WANI SO


NA ZEE YABOUR


FREE PAGE 01


Kyakkyawar budurwa ce mai kimanin shekaru sha tara zaune kan stool na madaidacin madubin d'aki, shak'e yake da kayan ado da shafa kala kala, ta shafa wannan ta guga wancan, wanda hakan ke nuni yar' gayu ce mai son ado da tsafta, ta share kusan minti talatin zaune bakin madubin,


"Jauhar shirin ne baki gama ba har yanzu, ko ganin gwamna zaki ai sai haka" Cewar Matashiya wacce ba zata gaza shekaru talatin da biyar ba, Ta d'an sunkuyar da kanta alamar jin kunya tana murmushi, Kumatun ta suka lotsa dimple d'inta dake k'ara k'awata fuskarta ya bayyana, Yaya deeja tace "Ko da yake wannan so da ake yiwa Jameel ai yafi ganin gwamna", Murmushin ta sake yi ba tare da ta kalli Yaya deeja ba, 


"Ni dai shawarar da nake baki ko da yaushe itace ki sassauta son da kike mishi, ban ce kar ki so shi ba, amma WANI SO idan yayi yawa ya kan zama cuta", Kanta tayi nodding tace "In Shaa Allahu Yaya", Ta juya ta fita, Jauhar ta mik'e ta k'ara kallon kanta a madubi, tayi murmushi ganin tayi kyau sosai, ita kanta tasan kyakkyawa ce sosai jinin hausa fulani, haka komai ta saka kyau yake mata, Shigar da tayi zaka rantse gidan biki zata ko wani gagarumin taro, 


Wayarta k'irar iphone 11 ta soma k'ara, daga sautin kiran ta gane mai kiran kasancewar ta bambamta nasa da na kowa, Bata yi yunk'urin d'auka ba sanin kiran na nufin yazo, Mayafinta madaidaci ta yafa kan kafad'a, Ta fito d'akin tana tafiyarta mai cike da natsuwa,


"Aunty gaskiya kina ji da Uncle J" Cewar Airah dake zaune tana kallo itace babbar yarinyar Yaya deeja, "Kowa dai ya gane soyayyar da ake wa Jameel", Cewar wata dattijuwa da bazata gaza shekaru arba'in da biyar ba, Jauhar murmushi tayi ta wuce ba tare da tace komai ba,




************************


Namiji ne da ya amsa sunan sa namiji, wanda kallo d'aya zaka masa kasa shi jerin maza ajin farko, ko ba'a fad'a maka ba, fatar jikinsa kad'ai ta isa shaida maka dan' hutu ne wanda ya jik'u da naira, 


Zaune yake a falon bak'i dake waje, Riga da wando ne jikinsa, kasancewar sa dan' boko mai son shiga irin ta turai, k'amshin turare mai dad'i ke fita daga jikinsa, hannunsa rik'e da waya k'irar 13pro max yana dannawa, 



Da sallama ta tura k'ofar falon ta shiga, Wayarsa ya ajiye gefe ya maida dukkan hankalin sa wurinta, Murmushi yake jifanta dashi, had'i da kallo wanda ke rikita tunanin ta, Har ta k'araso ta zauna kujerar kusa dashi bai d'auke idonsa daga gareta ba,



"Kyakkyawa wacce kullum kyawonta ke k'ara bayyana, mai cikar baiwa da sura, gaskiyaa dole na k'ara godiya ga Allah da ya bani masoyiya irin ki, tabbas ke zinari ce mai wuyar samu, wanda idan an same ta ake tattali gudun kar ya salwanta saboda tsadar sa", Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, Dariya tayi mai cike da farin ciki had'i da shauk'i tace "Ina fatan kazo lafiya, kuma su Mummy na lafiya?", "Ko da ace ban zo lafiya ba, ganinki kad'ai ya isa wadatar dani dukkan lafiya, Su Mummy kuma lafiya lau na bar su", "Naji dad'in jin haka, kamar yadda ganin ka yasa zuciyata sanyi ta wadatu da farin ciki", 


"Jauhar" Ya kira sunanta cikin sigar da shi kad'ai ke fad'a, Ta amsa da "Na'am" Tana bin sa da kallo mai cike da soyayya, sam kasa danne soyayyarta take idan tana gabansa, mantawa take da wani aji na ya' mace, burinta a ko da yaushe ta isar da sak'on zuciyarta zuwa gare shi, ta bayyana masa zazzafar k'aunar da take masa, ta nuna masa soyayyar da ba zai yi marmarin wata ya' mace ba, 



"Ina sonki sosai Jauhar", Ya fad'a yana saka idonsa cikin nata, "Ina k'aunar ka Yaya Jameel", "Allah ya nuna mun ranar auren mu", Ta amsa da "Amin", "Matso kiji", Kanta ta d'an rankwafo saitin bakin sa, "Can't wait to have our first night together", Saurin janye kanta tayi, tana juyawa gefe saboda kunyar zancen nasa, Dariya yayi yace "Sarkin kunya, Soon zan cire kunyar", "Ni dai ka daina mun irin maganar nan", Ta k'arasa cikin shagwab'a, "Am sorry babyn jameel na daina" Ya kama kunnen biyu, Murmushi tayi tace "Ya wuce" Sam bata iya fushi dashi, girman soyayyar sa ba zai bari tayi fushi dashi na tsawon mintuna ba, "Shiyasa nake k'ara sonki akwai hak'uri", Murmushi tayi sanin babu wanda take tolerating ta shanye b'acin ranta akan sa face shi, "Murmushin nan ba k'aramin kyau yake k'ara miki ba", "Kamar yadda naka ke k'ara k'awata mun fuskar ka", Ya bude baki da zumar magana kira ya shigo wayar sa, Tamkar zai share ya kai dubansa ganin Hafeez amininsa ne mai kiran, Ya danna receive "Haba JJ ya zaka bar mu muna ta jira", Wayar ya d'an matsar daga kunnen sa ya duba lokaci, "Am sorry bansan haka lokaci yaja ba, kasan idan ina tare da Nurul qalb bana tuna komai", "Sannu baban soyayya, mu dai kayi sauri", "On my way", Ya fad'a yana kashe wayar,



Jauhar kallonsa take fuska marairaice, Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ba ke kad'ai ce baki son rabuwa dani ba, ni kaina ban k'i na kwana a nan ina kallon kyakkyawar fuskar ki ba, ina sauraren muryar ki da tafi mun komai dad'in saurare", Zuciyarta taji tayi sanyi da jin kalaman sa ta numfasa tace "Ina zaku je, da ba zaka iya fasawa ba", Ta fad'a sanin lokuta da dama ya kan bar guraren zuwan sa, ya kashe lokaci tare da ita, "Babu abunda ya kai mun ke muhimmanci bayan iyayena, kawai biki ne na abokina wanda ya dace na halarta, na masa kara", Jauhar ta jinjina kai cike da gamsuwa duk da k'asan zuciyarta tafi son ya zauna tare da ita, A zahiri tace "Ka kular mun da kanka, pleasee kada ka kalli kowacce mace", Dariya yayi yace "Wacce mace zan kalla bayan ke kad'ai nake wa kallon ya' mace", Murmushi tayi cike da jin dad'in furucin sa, Ya mik'e yace "Bara na tafi sai munyi waya", Har ya kai k'ofa ya jiyo muryarta "Ina sonka sosai nurul qalb", Ya juyo ya mata blowing kiss yace "MUKULLIN ZUCIYATA kece", "Kai kuma mahad'in rayuwata", Kisses ya sake mata blowing ya fice da saurin, sanin tsaf zantukan ta zasu kashe masa jiki su hana sa tafiya da wuri.



***********************


"Uban soyayya tun d'azu ka shanya mu", Cewar Ahmad rai b'ace, "Kuyi hak'uri am here ai", Cewar Jameel, "Ai na d'auka ba zaka je ba" Cewar Fahad, Wata irin dariya Jameel yayi yace "Kai ma fad'a kake, kafi kowa sanin waye Jameel", Ahmad yace "JJ da son party ka tab'a ganin anyi Dinner bai je ba, sai idan ba'a gayyace sa ba", "K'ara tuna masa dai" Jameel ya fad'a ya shige band'aki, Ya watsa ruwa, Ya fito ya shirya cikin suit irin na abokansa wanda anko suka yi, Duk da saurin da suke sai da ya tabbatar ya shirya tsaf ta yadda babu mai raina sa a wurin, Convoy na motoci hud'u suka yi, duk layin da suka wuce sai an bi su da kallo, had'uwar motocin da yadda suke tuk'in tamkar zasu tashi sama ke jan hankulan mutane,


Jameel, Hafeez, Ahmad da Fahad aminan juna kenan, wanda tun sakandire suke tare har zuwa jami'a, k'asar america sukayi karatun su, kuma dukkansu course d'aya suka karanta Engineering, sanadin abokantakar su iyayensu ke shiri, wanda kowannensu babanshi ya jik'u da naira, akwai kyakkyawar mu'amala da fahimta tsakanin su, tsaftacen zama ke gudana tsakanin aminan hud'u.



******************


"Gasu nan wallahi, sun zo" Cewar wata matashiyar budurwa da ta matse cikin d'inkin anko ta, Yan' mata kusan su biyar dake zagaye da teburin d'in suka mayar da hankalinsu kan k'ofar shigowa, 


A tare suka jero suna takun su mai cike da isa da burgewa, ko ba'a fad'a maka ba daga kallo zaka san suna lokacin tashen su na samarta ka, Haka kowannensu ba baya ba wurin kyau da naira,


"Jameel duk yafi so had'uwa" Cewar Minal, Sauran suka ce "Eh wallahi", Minal tace "Kaya iri d'aya suke sawa lokuta da dama amma sai kaga Jameel ya fita daban, shigar tasa tafi burgewa", "Exactly" Suka fad'a a tare, "Idan ka samu miji irinshi ai ka more", "Bari kawai kawas", Sukayi shewa kowacce a zuciyarta ta na nasawa kanta zama mata ga d'aya daga cikin su tun ba Jameel ba wanda shine star,



Har suka isa kujerun da aka tanadar musu na musamman, hankalin yan' matan na kansu, bama su kad'ai ba, mata da yawa samarin sun tafi da zuciyar su, kama daga wanda suka jima da sanin su kasancewar sunyi sunan cikin garin KADUNA, har ga wanda yau ce ranar farko ta ganin su.



Biki yayi biki, Maza da mata ana ta chashewa, Yan'matan Amarya ne a farfajiyar wurin suna chashewa, kowacce na son nuna bajintar ta ta hanyar rawa, Jameel ya fara mik'ewa sauran suka mik'e suna nufar farfajiyar suka soma zuba ruwan dollars, ai tuni wurin ya d'auki ihu da tafi, Jameel shine kan gaba wurin rawa da watsin dollars, Minal nata k'ok'arin matsowa kusa dashi, bai matsa ba sai ma biye mata da yayi suna rawa yana mata lik'i.



************************


Jauhar tunda ta koma cikin gida take kwance d'aki, tana faman juyi kan gado, tunanin Jameel da zantukansa na yau sun hana zuciyarta sakat, ta rasa wani irin so take masa, wanda lokuta da dama bugun zuciyarta kan sauya a duk da take tunanin sa ko tayi tozali dashi, Wayarta ta d'auka da zumar shiga chats d'insu ta karanta wanda hakan ke k'ara jefata cikin shauk'i, Jameel ba baya ba wurin iya tsara kalaman soyayya masu kwantar da hankali da tsuduma zuciyar wanda ake ma fagen k'auna, Kiran k'awarta sumayya ya shigo wayar, Tamkar zata share dan bata son duk wani abu da zai mata shamaki ga barin tunanin Jameel, ta d'auka tare da karawa a kunne,



"Sumy ya gida?", "Wallahi ina wurin biki ma", "Allah sarki toh ya kike?", "Lafiya lau, dama Jameel na gani suna ta chashewa da k'awayen amarya, yana musu lik'in dollars", K'irjinta yayi mugun dokawa, tare da jin abu ya tsaya mata tsakanin mak'oshi da zuciya, "Hello" Sumy ta fad'a jin shiru, Da k'yar ta iya cewa "Ina zuwa Sumy ana kirana", Ta kashe wayar, Sumy tabi wayar da kallo tace "Uwar kishi da so, yadda take fad'in soyayyar su zaka rantse mace bata ishe sa kallo ba, amma kaga kamar zai shige jikin wancan", Ta tab'e baki ta jefa wayar jaka.




ANYA JAMEEL YANA YIWA JAUHAR IRIN SON DA TAKE MISHI? JAMEEL YA CANCANCI SOYAYYAR JAUHAR HAKA?


KU BIYONI CIKIN LITTAFIN WANI SO DAN SAMUN AMSAR TAMBAYOYIN KU




OUM MUHRIZ