WANI SO

Chapter 2 :02

by @zeeyabour20

WANI SO


NA ZEE YABOUR


FREE PAGE 02


Zuciyarta ke k'ok'arin k'aryata mata Sumy sanin Jameel da irin girman soyayyar da yake nuna mata, amma ta kasa samun natsuwa kishi ke nuk'urk'usar zuciyarta, Tana yi wa Jameel zazzafar k'auna wanda ta haddasa kishin sa mai tsanani a zuciyarta, Idonta ta runtse tana k'ok'arin tausar zuciyarta da son kawar da zancen Sumy, abun yaci tura ta kasa jurewa, idonta ba abunda suke hango mata sai Jameel tare da mata, Ta bud'e idonta tare da jawo wayarta dake kan gado, Ta danna kiransa, 



K'arar kid'e kid'e ya hana Jameel jin ringing na wayar sa, Hankalinsa gaba d'aya na kan rawar da suke tare da yan' matan amarya, wuri ya kacame ana ta tafi da ihu, kai ka rantse club suke, da yawa mutane sun watse sun bar su, Jameel dan' son rawa da chashewa ne shiyasa duk dinner bata wuce sa ba, sai idan ba'a gayyace sa ba, hatta birthday party na abokansa yana zuwa, Jameel na da son rayuwar papa (high life) komai na manya yake da son burgewa, 



Kira biyar tayi masa bai d'auka ba, Jikinta yayi matuk'ar sanyi, zuciyarta ta karaya tana bata tabbacin zancen Sumy ganin yau ce rana ta farko tun had'uwar su ta masa kiran da ya wuce biyu bai d'auka ba, Wayar ta ajiye gefe, ta kwantar da kanta kan pillow, ta runtse ido tana sauraren bugun zuciyarta, yayin take k'ok'arin karewa kanta Jameel d'in ta hanyar sawa ranta akwai uzurin da ya hana sa d'aukar wayar ta, babu macen da zata d'auki hankalinsa, 



********************


Jameel basu bar wurin ba sai sha biyu na dare, kowannen su ya nufi gidansu kasancewar babu mai aure cikin su, Horn d'aya securities suka bud'e makeken gate na gidan, sanin shi kad'ai ne bai dawo ba cikin mutanen gidan haka babu mai kawo ziyara a irin wannan lokaci, 


Yasa kan motar sa cikin farfajiyar gidan wanda tsayawa fad'a muku had'uwa da girman gidan zai d'auki lokaci, Parking space ya ajiye motar sa, Ya nufi sashen Mahaifiyar sa sanin bata isa bacci ba, 


*********************

Tantsamamen falo ne da ya wadatu da kayan alatu da more rayuwa, Dattijuwar mace ce kishingid'e kan kujera tana kallon tv, sanye take da doguwar riga ta tsadadden material mai adon duwatsu, Yan' matan biyu na kwance kan carpet idonsu kan tv suna kallo, Da sallama ya shigo wanda ta maido hankalinsu gare sa, Suka amsa, "Yaya Jameel sannu da zuwa", Cewar Yan' matan a tare, "Yawwa" Ya amsa yana k'arasawa cikin falon, "Mummy barka da dare", "Barka ka dai, yau hala anje Dinner ko party", Murmushi yayi yace "Dinner abokina muka je", "Allah ya nuna mana taka kai ma, muyi rawa da juyi", Yayi dariya yana amsawa da "Amin", Jauhar ta fad'o masa a rai, tun d'azu bai ji daga gareta ba, Hannu yasa aljihu ya zaro wayar sa, "Ya salam" Ya furta ganin ta masa missed calls har biyar, ya tabbata tana cikin damuwar rashin ji daga gare sa, Mummy ta katse tunaninsa da cewa "Lafiya?", "Jauhar tamun missed calls ban lura ba", Murmushi Mummy tayi tace "Ai sai ka kira kayi lallashi ko", Ya mik'e yana cewa "Sai da safe Mummy", "Za'a je asha soyayya dai", Yayi dariya yana ficewa falon, Akwai shak'uwa da sakewa sosai tsakanin Mummy da yaranta, kasancewar rayuwar turawa da boko da ta tsaga jikin su, sam bata takurawa yaranta abunda suke so shi zasu yi, suna da cikakken yan'cin kansu, haka Mahaifinsu Alhaji Sule Bako shima rayuwar tasa ta turai ce, a tak'aice dai rayuwar turai da boko ke gudana a gidan, 


Jameel yana shekara biyar a duniya suka koma America da zama a lokacin Alhaji Sule yana matsayin ambassador, har ya kammala shekarun da aka d'ibar masa basu dawo ba, zaman garin ya masa dad'i ya soma business d'insa a can wanda yake samun kud'i bana wasa ba, Basira(Mummy) a can ta haifi Batool da Khairat daga su ta tsayar da haihuwar a cewarta yara uku sun isheta, Alhaji Sule shima ya goya mata baya kasancewar rayuwar turan ta soma shiga jikin sa, Haka yaron suka taso cikin rayuwa irin ta turai, wanda hausa ma bata kama bakin su ba, Karatun islamiyya basa wani yi, malami ne ke zuwa yana koya musu shima bai gwanance ba, hakan yasa suka taso babu ilimin addini sai boko, Wayewa iya wayewa sun yi ta, haka gayu ba'a bar su a baya ba, Shekararsu goma sha biyar america suka dawo nigeria, a lokacin Jameel yana shekara ashirin ya soma jami'a hakan yasa bada shi suka dawo ba, Batool na Ss1 Khairat na js2, 


Ko da suka dawo nigeria al'adunsu da d'abi'unsu sun bambamta da na hausa fulani, zaka rantse ba haifaffun garin kaduna bane k'auyen soba, A makaranta basa huld'a da kowa sai wayayyu wanda mafi yawa christians ne, su suke ganin sunyi daidai da wayewar su sauran gidadawa ne a cewar su.


Shekararsu takwas yanzu nigeria amma babu abunda ya canza daga d'abi'un su, Ga iyayensu dake k'ara k'arfafa musu gwiwa, wanda suke ganin hakan matsayin yan'cin kai, Iyayen Alhaji Sule sun rasu hakan yasa babu mai tsawata masa kan tarbiyar da ya d'aura yaransa, Amma Mummy mahaifiyarta na raye tana k'ok'arin lurar da ita da nuna mata rashin dacewar hakan amma sam bata d'auka, hakan yasa ta zuba mata ido.


**********************


Jameel yana shiga d'akin sa, wanka ya fara yi, Ya sake pyjamas d'in sa, Ya kwanta kan gado ta yadda zai ji dad'in waya da masoyiyar sa, Numberta da yayi saving da Nurul qalb yayi dialing,



Jauhar na kwance d'aki, kwata kwata yau bata fita falo hirar dare ba, damuwa da tunanin rashin ji daga Jameel sun dabaibaye zuciyarta, Wayarta na soma k'ara tayi saurin d'auka, kiran sa take jira tun d'azu, ganin shine ta d'auka tare da sauke ajiyar zuciya, 


"Am sorry babyn jameel, nayi laifi yau a yafe mun, pls kar ki hukuntani kinsan zuciyata mai rauni ce a kanki ba zata iya d'aukar fushin ki ko na second d'aya ba", Ya fad'a cikin sigar lallashi wanda hakan ke narkar da zuciyarta, "Baka yi laifin da zanyi fushi da kai ba, sai da ina son sanin mai ya hana ka d'aukar wayata", Numfashi yaja yace "Ina wurin Dinner abokina da na fad'a miki zanje, k'arar kid'e kid'e ta hana ni jin kiran", "Kayi rawa da yan' matan ko", Ta tambaya cikin sanyin muryarta dake kashe masa jiki, Dariya yayi yace "Babyn jameel sarkin kishi, kishin ya motsa ko", Tace "Uhmm", "Ki kwantar da hankalin ki, am all yours, kin riga kinyi dashe a zuciyata da babu mai yin sa, zuciyar Jameel mallakin Jauhar ce ita kad'ai", Murmushi tayi wanda ya jiyo sautin ta waya, Yace "Na so murmushin nan a fili ne aka mun shi", "Kamar yadda naso ace ina kallon kyakkyawar fuskar ka", "Gobe early in the morning zanzo na gan ki", "Har kasa naji tamkar na jawo daren zuwa wayewar gari", "Kiyi tozali da ruhin ki ko", Kai tayi nodding tamkar tana gabansa tace "Eh kai ma kayi tozali da ruhin ka", "Ina sonki Jauhar so mai tsanani", "Kowane bugun zuciyata yana tafiya ne tare da son ka", "Kamar yadda fitar numfashina ke tafiya tare da zazzafar k'aunar ki", Shiru tayi saboda zuciyarta dake harbawa akan tsananin son sa, "Babyna kin fara bacci ne", "A'ah" Ta fad'a cikin sanyin murya, "Ba wani bacci kika fara, ki kwanta kinji, kiyi mafarkina gobe idan nazo ki bani labari", Ta amsa da "Toh kai ma kayi nawa", "I will, Gudnyt" Ya mata blowing kiss ya kashe, Wayar ta ajiye gefe, ta matse pillow kan k'irjinta ta lumshe ido tana jin ta cikin shauk'i na soyayya.



*******************


Minal tunda suka bar wurin dinner take zancen Jameel, har k'awayenta suka soma gajiya da ita, dan kowaccen su tana son samun matsayi a gun sa, Bata bar wurin ba sai da ta samu number sa wurin Ahmad, haka sai da tayi k'ok'arin shafar jikinsa ta yadda k'amshin turaren sa ya gauraya a kayanta, Tana dawowa gida taaa shige d'akinta ta cire kayanta, daidai saitin wurin turarensa ta saka a hancinta tana shak'a yayin da take jin zazzafar k'aunar sa na shigar ta, "Sai na mallake ka Jameel, ban tab'a jin soyayyar wani da' namiji kamar kai ba", Tayi murmushi tana sake hasko fuskar sa da irin rawar da sukayi a wurin, tana ganin ba zata sha wahalar shawo kansa ba, dan yana da sakewa.




MINAL KUWA ZATA SAMU SHIGA WURIN JAMEEL A YADDA YAKE IKIRARIN JAUHAR KADAI CE MURADIN RANSA?


DA YADDA ITA KANTA JAUHAR KE DA TABBACIN BA MACEN DA ZATA JA RAAYINSA?



OUM MUHRIZ