CHAPTER 3 : page 3
by @zeeyabour20
WANI SO
NA ZEE YABOUR
FREE PAGE 03
K'arar alarm na wayarta, yasa ta janye bargon da ta rufa dashi a hankali, ta bud'e idonta wanda suka mata nauyi saboda bacci da bai ishe ta ba, wayar ta d'auka kan bedside drawer ta kashe, kana ta zuro k'afafunta k'asa tare da mik'ewa ta shiga band'aki,
Mintuna kad'an ta fito ta gabatar da sallar asuba, tayi karatun qur'ani, bata koma bacci ba, duk da baccin dake damunta, sanin masoyin nata zai zo, kar ta kwanta bacci mai nauyi ya d'auketa, tana da tabbaci bakwai zuwa takwas zai zo shine lokacin da yake fitowa zuwa office,
Kitchen ta shiga, ta kamawa yan' aikin gidan had'a breakfast, da abincin yan' makaranta, Tana kammalawa ta fito falo, Yaran Yaya deeja su biyar(Airah, Adeel, Hayyimat, Muhsin, Noor) suka soma gaisheta tana amsawa, kowannensu sanye da uniform, Agogon dake manne bangon falon ta kalla, bakwai da minti biyar, D'aki ta koma kai tsaye ta shiga band'aki, tayi wanka tare da brush, Ta fito ta zauna kan dressing mirror ta shafe jikinta da cream na products d'in aljism, wanda ke k'arawa fatar ta kyau da shek'i, Oil perfumes masu dad'i da sanyin k'amshi tabi lungu da sak'o na jikinta dasu, kafin ta mik'e ta nufi wadrobe d'in ta, doguwar riga ta abaya ta d'auko ta saka, ta yane kanta zuwa wuya da k'aramin mayafin abayar, Tayi kyau sosai zaka rantse balarabiya ce, Wayarta ta soma k'ara, a zaton ta shine har tana saurin d'auka, Ganin sunan Yaya Jummai na yawo kan screen, tayi mamakin kiran na safe, sanin bata kiranta a irin wannan lokacin, Ta d'auka tana karawa a kunne,
"Assalamu alaikum Yaya ina kwana?", "Lafiya lau Jauhar", "Yasu Haulat?", "Duk lafiya lau an tafi makaranta", "Allah ya bada sa'a", "Amin", Ta numfasa tace "Jiya da daddare Deeja ke sanar dani kince ba zaki cigaba da jami'a ba, ina ta alla alla safiya tayi na kira ki, shin hakane?", "Eh Yaya" Jauhar ta fad'a kai tsaye, "Kina ganin anya kin wa kanki adalchi kuwa, karatun nan shi kowa ke yi fah yanzu, mu kanmu da ba zamanin ku ba munyi NCE, amma ke kin samu damar da za'a saka ki makaranta mai kyau da tsada wacce da yawa ke son samu basu samu ba, kada kiyi wasa da damar ki Jauhar", Shiru ta dan' yi kafin tace "Jameel ne ya nuna baya so, wai aure ba zai tafi tare da karatu ba", Yaya Jummai tsaki taja tace "Nasan ruwa baya tsami k'asa banza yadda na sanki da son karatu, ba zaki k'i jami'a ba, ashe shi ya canza miki ra'ayi, toh saurareni da kyau kiji, Namiji da kike gani ba dan' goyo bane, duk da cewar ba'a taro an zama d'aya ba, Amma babu ta inda aure yake hana karatu, matan aure dubu nawa ne a jami'a, kuma ina da tabbaci a kanki Shima yana da akan tarbiyar ki jami'a ba zata kawo matsala ga aurenki ba, Dan haka yana da wani dalilin sa amma ba wannan ba, kada ki bari soyayya ta rufe miki ido ki dawo dana sani daga baya, Yaron da bai san wahalar ki ko d'aya, rana tsaka yace zai dakatar dake karatu, Shin kina ganin Kabir(Mijin Yaya deeja) kin masa adalchi kenan, yasha d'awainiyar karatun ki dan ganin kin amfana dashi lokaci d'aya ki watsa masa k'asa a ido kice ba zaki cigaba ba, maza ki canza shawara", "Toh In Shaa Allah", Ta fad'a rai babu dad'i, "Yawwa ki sake tunani, sai anjima" Ta kashe wayar,
Jauhar ajiyar zuciya ta sauke, tana k'ok'arin watsar da zantukan Yaya Jummai, tasan dama ba wani son alak'ar ta da Jameel take ba, kuma ita a ganinta rashin karatu ba matsala bane indai zatayi aure ta samu kulawa, kwanciyar hankali da soyayya wanda take da tabbacin samun wurin JAMEEL, Da tunanin haka ta mik'e ta fito falo, tana duba agogo ganin har kusan k'arfe takwas bai zo ba, dining area ta nufa, ta zuba chips sai ruwan lipton wanda yasha cinnamon tana ci a natse tare da sipping shayin kad'an kad'an saboda zafin sa.
********************
Jameel bacci sosai yayi na gajiyar jiya, bai tashi ba sai bakwai saura, band'aki ya shiga kai tsaye, ya tub'e kayansa ya jefa laundary basket, yayi wanka, kana yayi brush da alwala ya fito, Sai da ya gama shirin sa tsaf cikin k'ananun kaya jeans and t-shirt wanda ta fiddo k'irar jikinsa har ana ganin shape na nonon sa da suka taso kasancewar sa k'arfaffan namiji, Ya gabatar da sallah raka'a biyu, ya karanta azkar na sallame sallah sharp sharp ya mik'e, Ya d'auki mukullin motar sa da waya, missed calls yaga sunyi appearing kan screen na wayar, "Nurul qalb am sorry i keep u waiting" Ya fad'a yana unlocking wayar, sai dai ga mamakin sa bak'uwar lamba ce, bai bi kiran ba, Ya fito d'akin cikin sauri.
*******************
Jauhar ganin kiran Jameel wanda ke bata tabbacin yazo, ta ajiye breakfast d'in ba dan ta k'oshi ba, ganin masoyin nata yafi mata komai, tana ganinsa tasan zata nemi yunwar ta rasa.
************
Jingine yake jikin motar sa bai shiga falon ba sauri yake kar ya k'ara b'ata lokaci ya makara zuwa office, Tun kafin ta k'araso yake bin ta da kallo mai cike da so yana mata murmushi, itama tana mayar sa yayin da shigar sa ta matuk'ar burgeta,
"You look awesome" Ya fad'a yana had'a yatsun sa biyu wurin nuna mata had'uwar da tayi, Murmushi tayi tace "Shigar ka tamun kyau, sai dai naso ni kad'ai akayi ma na gani", "Taki ce ai ke kad'ai", Kai ta girgiza tace "A'ah office zaka je yan' mata su gani" Ta k'arasa cikin shagwab'a, "Bara naje gida na canza toh", "A'ah sai nasa ka makara ai", "Ba laifi bane hakan, indai zai faranta ranki", "Bazan zama mai son kai ba, ka tafi haka, ko sun kalla k'walelensu kai d'in mallakin Jauhar ne", "Tabbas kece mahad'in rayuwata, idan babu ke babu Jameel", Tayi murmushin jin dad'i tace "Ina sonka sosai", "Nafi sonki", "Ba wani kowa nashi ya sani", Ya fad'a yana kafeta da kallon dake kashe mata dukkan gabb'an jiki, Numfashi ta d'an ja tace "Na tambaye ka", "Yes" Ya fad'a yana d'aga mata gira, "Zaka amince na cigaba da karatuna idan har zan kiyaye maka kaina da igiyar auren ka" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina ce mun gama maganar nan, meyasa kika d'aukota yanzu", "Uhmm kawai dai", "Kawai dai me?" Ya k'arasa yana kafeta da ido,
Tayi shiru rashin sanin abun ce masa, Ya katse shirun ta yayi da cewa "Hankalina ba zai tab'a kwanciya ba matuk'ar kina jami'a, ba wai ban yarda da tarbiyanki ba a'ah, kawai zuciyata bata ra'ayin matata tayi jami'a, dukkan wata kulawa da buk'atun ki zan d'auke miki Jauhar kada kiyi shakku a kaina, pls kada ki sake zuwar mun da zancen nan", Kai ta masa nodding cikin gamsuwa da zancen sa tace "In Shaa Allah", "Ina sonki sosai, yadda kike bin ra'aayina tun kafin auren mu, nasa naji ba k'aramin dace nayi ba", Murmushi tayi tace "Nima nayi dace da samun ka", "Allah ya nuna mun ranar da zaki zama matata", "Amin Ya Allah", Agogon dake d'aure wutsiyar hannun sa ya kalla yaga 8:30, "Bana son daina kallon kyakkywar fuskar nan", Ya fad'a cikin wani salo, Marairaice fuska tayi itama tana jifan sa da nata salon kallon, wanda ke narkar da zuciyarsa fagen k'aunarta, Idonta ta d'an kawar daga kallonsa bata son hana masa tafiya office, dan taga yanayinsa tsaf zai iya shantakewa a wurinta, "I love you soo much Jauhar", "I love you more" Ta fad'a ba tare da kalle sa ba, Ya juya ya nufi motar sa, idonta na kansa har ya shige, ta sauke ajiyar zuciya cike da k'aunar sa ta shige gida.
******************
Yana tada motarsa ya hau titi, lambar d'azu ta k'ara kiransa yayi receiving yana connecting da bluetooth na wayarsa, "Hello Handsome" Ya tsinci muryar mace wacce kamar an shak'e kaza tsabar k'ank'antar ta, "Hello" Ya amsa, "It's Minal" Ta fad'a tana sake sanyaya murya, "Ohh ya gida?", "Lafiya lau, ya gajiyar jiya, nasan ka kwana da ciwon jiki", "Not that much, am use to", "Oh wow", "Yeah" Ya fad'a, "Ok i just call to say hi", "Thank you ki gaida mutanen gida", "Olryt take care", Ta kashe wayar,
Jameel bai damu yasan ina ta samu number sa ko dalilin kiran sa, ya saba da kiran mata kala kala, wani lokaci ma shi ke karb'ar number su idan sun had'u a wurare da sunan friendship, yana huld'a da mata kala kala, tun daga wanda sukayi school, amma mutum d'aya yaba zuciyar sa JAUHAR, ita kad'ai yake jin soyayyarta haka ita yake burin samu matsayin mata, duk da yasan zafin kishinta da yadda bata son kowacce mace ta rab'e sa hakan bai sa yayi avoiding mata ba, sai dai yana k'ok'arin b'oye mata da nuna mata baya mu'amala kowacce iri da mace indai ba wurin aikinsu ba, saboda gudun b'acin ranta, Amma shi b'angarensa kowanne namiji baya so tayi mu'amala dashi hakan yasa yace baya son tayi jami'a gudun duk abunda zai had'ata wata doguwar mu'amala da wani, yana kishinta sosai baya son kowane da' namiji ya rab'e ta.
*****************
Tana komawa d'aki ta cire abayar ta saka k'aramar riga ta shan iska kasancewar lokaci ne na zafi, Su Airah basu dawo school ba ko ta fita bata da abokin hira, wayarta ta d'auka ta kira mahaifiyarta, bugu biyu ta d'auka, "Auta shalele ina shirin kiran ki" Dariya tayi tace "Gwaggo ina kwana?", "Lafiya lau, Ya kuke dasu Deeja?", "Kowa lafiya", "Toh madallah", "Ya Bappa dasu Inna?", "K'alau suke" Cewar Gwaggo, "K'arshen satin nan zanzo In Shaa Allah", "Toh Allah ya yarda", "Amin Gwaggo, kiyi mun awara", "Toh Auta, kina da sauran yaji ko nasa a daka miki", "Ya kusa k'arewa", "Bara anjima na aika gidan Tabawa, sai me kike so?, "Sai nazo Gwaggo", "Allah ya kawo mun ke lafiya", "Amin", "Allah yayi miki albarka", "Amin gwaggo", "Sai anjima naji Bappa na kira", "Toh sai anjima" Ta kashe tana murmushi, Gwaggo naji da ita sosai kasancewarta Auta, kuma bata tashi wurinta ba, tun tana shekara shida ta koma hannun Yaya Deeja lokacin aurenta aka bata ita, dan akwai shak'uwa sosai tsakanin su, hatta sunanta Deeja ta rok'a aka saka mata jauhar.
Gwaggo su goma ta haifa, Kasimu, Jafaru, Jummai, Deeja, Yusuf, Bello,Umar, Harira, Basiru sai Jauhar, Mahaifinsu Malam Sani(Bappa) haifaffen garin Zaria ne cikin city unguwar liman, yana da rufin asiri sa, ba za'a kira sa talaka ba, haka ba za'a kira sa mai kud'i ba, sana'ar noma yake, Matan sa uku Gwaggo itace uwargida, sai Hajaru(Inna) yaranta biyar sai Atika( Mama) yaranta biyar, suna zaman lafiya daidai gwargwado, sai dai mafi akasari gidan kishiyoyi ba'a rabasa da gutsiri tsoma, hassada da bak'in ciki suma a gidan ana tab'awa, Sauk'i d'aya yanzu tsufa yazo, yaran duk sun girma da yawa sunyi aure, Gwaggo yaranta sunfi kowa kud'i a gidan, har matan Allah ya musu suturar aure masu kud'i, kuma duka suna zaman lafiya, wanda hakan ke tab'a zuciyoyin kishiyoyinta da wasu yaran gidan, sai dai babu yadda zasu yi da hukuncin ubangiji, Auren Jauhar yanzu shi ya tsokale musu ido ganin ba'a nan ta tashi ba, cewar su idonta ya bud'e da birni, zasu so ganin wanda zata aura,
Jameel basu dad'ewa da had'uwa ba ya gabatar da kansa ga iyayenta, sai dai ba'a tsayar da ranar auren su ba, Duk bin k'wakkwafin yan gidan sun kasa sanin wa take tare dashi, a tunanin su ma bata da tsayayye, da yawansu kan ce ai ba zatayi auren wuri ba, tunda idonta ya bud'e da birni, Gwaggo kullum fatan ta da addu'arta Jauhar ta samu farin ciki da kwanciyar hankali a gidan aurenta, kamar yadda sauran yan' uwanta suka samu.
OUM MUHRIZ