Chapter 4 : page 4
by @zeeyabour20
WANI SO
NA ZEE YABOUR
FREE PAGE 04
Yamma lik'is Jameel ya dawo daga office, kai tsaye gida ya nufa, K'ofar shiga yaci karo da Batul ta d'ame cikin jeans da top wacce iyakacin ta ciki, kanta sanye da d'ankwali, gashin attach da ta saka ya zuba gadon bayanta, gefe ta d'an matsa tace "Welcome Bro", Ya mata nodding kai da cewa "Sai ina?", "Gidansu Esther (itace bestfrnd d'inta kowa ya sansu tare)", "Ok sai kin dawo", Tace "Ok bro", Ya shige ciki ba tare da ya damu da shigar dake jikin ta ba,
Zaune ya tarar da mahaifiyar su, itama sanye cikin english gown, kanta da yasha attach babu d'ankwali, ta maida dukkan hankalinta wurin kallon tv, Khairat na gefenta jefi-jefi suna magana kan series d'in da suke kallo,
"JAMEEL an dawo", "Yes Mum, sannu da hutawa", Ya fad'a daga tsaye, "Yawwa, ga abincin ka can kan dining table", "Na k'oshi sai anjima", "Alright", Ya juya da zumar fita, Ta dakatar dashi da cewa "Ka k'i kawo mun Jauhar, almost a week ina bin ka", Murmushi yayi na jin dad'in yadda ta damu da wanda yake so yace "Gobe In Shaa Allah zan kawo miki ita", "Ina jira saura ka kawo mun wani excuse", Yayi dariya yace "Gobe zaki ga daughter in-law d'inki", Ya fice ba tare da ya jira amsarta ba,
*********************
Tana zaune falo suna hira tare dasu Airah, akai akai tana duba agogo taga ko lokacin dawowar Jameel gida yayi ta kira sa, bata son kiranshi yana office ta hana masa aikin dake gabansa, Ganin bakwai saura tana da tabbacin ya koma gida, ta mik'e ta nufi d'aki ta kira sa,
Fitowar sa wanka kenan yana tsane jikinsa da towel kiran Jauhar ya shigo wayarsa, Ya d'auka yana karawa kunne, "Ina fatan ka dawo gida lafiya?", "Lafiya lau babyna, kema ina fatan kina lafiya?", "A'ah" ta fad'a tana yin k'asa da murya, "What's wrog meke damun ki?", Ya tambaya cikin kulawa, "Missing d'in ka", Ajiyar zuciya ya sauke Yace "Har kinsa gabana ya fad'i, na d'auka wani abu ya samar mun ke", Tayi dariya tace "Lafiyar ruhi ce ta tab'o, bata jiki ba", "Anjima zanzo, dan ni kaina idona sun k'wadaitu da son ganinki", "Allah ya kawo mun kai lafiya", "Amin", Kiran sallar magrib da suka soma ji yasa tace "Zanje nayi sallah", "Ki mana addu'a sosaai kinji nurul qalb", "Kai ma kayi mana Allah ya barmu tare", Yayi smilling yace "Zanyi, I love you soo much", Ya k'arasa da mata blowing kiss ta mayar masa, Tana kashe wayar ta shiga band'aki alwala.
Jameel sai da ya gama shirin sa cikin wando three-quarter wanda ya d'an wuce gwiwar sa da kad'an sai riga armless, ya fesa turaruka masu k'amshi, ya taje gashin kansa da ya tara, Ya gabatar da sallar magrib wacce minti biyar yayi yawa ya kammala ya mik'e da sauri, Ya d'auki mukullin motar sa da waya ya fita.
*********************
Had'add'en wurin hutawa ne wanda aka masa ado da kujeru masu tebura, daga tsaruwar sa da had'uwar sa zai tabbatar maka na masu hannu da shuni ne, Samari da yan' mata ne kewaye da wurin kowa yana sharholiyar sa mafi akasari kayan maye suke sha, babban tebur mai cin mutum shida su Jameel ke zaune, sai yan' mata guda biyu wanda suka d'auka matsayin k'awayen su, kowannensu rik'e da pot na shisha suna zuk'a, Jameel yafi so gwanancewa har ta hanci yake hurawa cike da son burgewa, cikin k'ank'anin lokaci ya gama yace a k'aro masa wani flavor, Yana jin wayarsa na vibrating yak'i d'auka sanin Jauhar ce, baya so ta fuskanci wani abu.
*********************
Jauhar kira biyu ta masa bai d'auka ba, zuciyarta ta bata akwai uzurin da ya hana sa, text message ta tsara masa ta tura, Jin k'arar message ya fiddo wayar ya duba, "Lokuta da dama na kan zauna shiru ina mamakin soyayyar da nake maka, anya kana jin abunda nake ji akan ka kuwa, soyayyarka tamun nisa da mugun kamu, pls kada ka cutar da zuciyata JAMEEL ba zan iya d'auka ba, Kai ne mahad'in rayuwata, ka zama wani babban jigo na rayuwata", Murmushi yayi tare da jin sonta na ratsa shi, soyayyar da take nuna masa da kula ka k'ara sa yaji yayi dace, ga uwa uba tana da kamun kai, baya son matar sa ta kasance mai rawar kai saboda tsananin kishin sa, Wayar ya mayar aljihu sai ya koma gida zai mata reply ya kirata.
************************
Tana gama rubuta masa text d'in, ta ajiyewarta ta shiga toilet ta watsa ruwa ta saka riga mara nauyi wacce ta zauna d'ass a jikinta, hula ta saka, ta fesa turare mai sanyin k'amshi, sai wet lipstick saboda gudun bushewar baki, Falo ta fito tana fad'in "Aira an fara program d'in?", Turus tayi ganin wanda bata tsammaci gani ba, a take yanayin fuskarta ya canza, "Ina wuni?", Ta fad'a murya k'asa, Sai da ya d'auki seconds kafin ya amsa da "Lafiya" ba tare da ya kalleta ba, Kallonsa tayi cikin takaicin halinsa na mugun miskilanci, a zuciyarta tace "Matar sa ta boni, ko ya zaman su zai kasance", Ta juya ta koma d'aki cikin rashin jin dad'in zuwan sa, sam tasu ba zata zo d'aya ba, dan a gidan ma har gara kowa da ita, yafi rashin sake mata sam, ko kallo bata ishe sa ba, ban da tazarar shekarun da ya bata, ba abunda zai sa ta rik'a gaishe sa, amsarwa wulak'ancin da yake mata na matuk'ar ci mata zuciya, fatan ta Allah yasa ba jimawa zai yi ba, bata son had'uwar su wuri d'aya ko kad'an,
Tun shigowar sa falon, yaran gidan gaishe sa kad'ai sukayi suka watse zuwa d'akunan su, baya sake musu sam bare yayi wasa dasu, hakan yasa suke tsoron sa da shakkar sa.
Miskili ne da ya amsa sunan sa miskili, wanda ke da matuk'ar wahalar mu'amala, zaku zauna dashi har ku tashi ba tare da yayi wata magana ba, hatta mahaifiyar da ta haife sa baya doguwar hira da ita, tun yana yaro haka yake, farkon tashin sa an d'auka bebe ne dan har asibiti aka kai sa, baya sharing matsalolin sa da kowa, bashi da amini, mutum ne shi mai matuk'ar zurfin ciki wanda duk iya k'wakk'wafin ka baka isa jin cikin sa ba, idan kaji abunda ya shafesa toh wanda ya kama dole ne, K'ani ne a wurin Mijin Yaya Deeja, uwar su d'aya uban su d'aya, Sai dai halinsu ya bambamta nesa ba kusa ba, Mijin Yaya Deeja yana da sakewa sosai da son mutane, Sab'anin JUNAID MAINA da kullum he is isolated, zama dashi nada wahala kafin ka fahimce sa, Da yawa mutane sun d'auki halinsa na miskilanci wulak'anci, sukan ce kyau da dukiyar dake garesa yasa yake ganin kowa ba komai ba,
Asalinsu fulanin Cameron ne, wanda aiki ya kawo mahaifinsu Alhaji Mamman Maina zama abuja, sana'ar man fetur yake wanda ya kawo masa mak'udan kud'i bana wasa ba, Kabeer da Junaid su kad'ai ne yaransa maza, sauran mata ne su hud'u, hakan yasa ya sakar musu ragamar komai, tun suna yi tare da shi har kowannen su ya soma nashi individual, JUNAID mutum ne mai zafin nema wanda yasan ciwon kansa, lokaci kad'an ya kud'ance Allah yasa masa albarka, hakan yasa ya raba hannu a kasuwanci daban daban, cikin shekaru kad'an ya tara dukiya bata wasa ba, Shekarunsa talatin a duniya amma a irin dukiya da manyancen sa zaka rantse yaba arba'in baya, sai dai k'irar jikinsa da zaka kalla ta tabbatar maka bai yi shekarun ba,
Wani conference ya kawo sa kaduna, duk lokacin da abu ya kawosa garin, gidan yayansa yake sauka, baya kama hotel, wanda sauran garuruwa baya sauka ko'ina sai hotel, kowa ya d'auki hakan saboda kusancin dake tsakanin sa da Yayan nasa ne.
*********************
Sha biyu na dare Jameel ya koma gida, sai da yayi shirin bacci, Ya kira Jauhar wacce tun d'azu kiran nasa take jira,
Muryarsa yayi k'asa kamar wanda ya tashi bacci Yace "My baby kin kira ina bacci, na dawo na gaji sosai, so i slept off", "Ai gara da kayi baccin ka huta", Ta fad'a, "Naji dad'in baccin coz cike yake da mafarkan ki", "Really" Ta fad'a cikin jin dad'i, "Yes babyna, kinsan mafarkin me nayi", "A'ah", "Wai munyi aure, kina kwance kan cinyata ina shafa gashin kanki, kina mun shagwab'a", Wani bak'on yanayi taji a tare da ita, tana sauraren yadda bugun zuciyarta ya canza lokaci d'aya, "Kinyi shiru ko mafarkin bai miki dad'i ba", Tace "Uhmm", "Gaskiya zanyi magana azo a tsayar da rana na gaji da zaman gwauranci", Murmushi tayi wanda har ta cikin waya yana jiyo sautin, "Kema kin k'osa muyi aure ko", "Na k'osa dai na kasance tare da kai ko da yaushe", "Ki rik'a kwana a k'irjina ko ina jin d'umin jikin ki", "Uhmm" tace sabodaa kunyar zancen sa, "Sarkin kunya da munyi aure zan cire ta", "Uhmm" ta sake cewa, "Yawwa ki shirya gobe zanzo muje ki gaishe da Mummy, tana son ganin ki", "Amma sai nake ganin rashin dacewar haka, a al'adar bahaushe da kunya naje gidan surukai ba tare da an d'aura aure ba",
Dariya yayi yace "Matsalar hausawan mu kenan basu waye ba, America is very common, ko ba tare dani ba, mace alone zata iya zuwa", "Nan a nigeria muke arewa, bai dace ba, ina jin kunya", "My mum tace tana son ganin ki kice ba zaki ba Jauhar" Kafin ta bashi amsa ya kashe wayar, Zuciyarta ta doka ganin ta b'ata masa rai, Da sauri tabi kiran ya d'auka, "Am sorry don't misunderstand me, zanje gobe kazo ka d'auke ni", "That's why i love you", "I love you too amma pls bana so kana saurin fushi dani", "Na daina my princess", Suka cigaba da hirar soyayyar su wanda ke tsunduma su cikin fagen k'aunar juna, Jameel ya fara rigata bacci, bata kashe wayar ba sai ma kwanciya tayi ta runtsee ido tana sauraren saukar numfashin sa, zuciyarta na k'ara tsuduma zazzafar k'aunar sa, baccin da ya soma d'aukarta yasa ta kashe wayar tayi bacci.
******************
Knocking k'ofar ta ya tashe ta nauyayyen baccin da take, tunda tayi sallar asuba ta koma, bata fito taya yan' aikin gidan had'a breakfast ba saboda baccin da yaci k'arfinta, Bargo ta yaye, ta tashi ta bud'e k'ofa, Yaya deeja ce,
"Ina kwana?", "Lafiya lau", "Sorry na tashe ki kina bacci", Murmushi tayi, "Dama breakfast d'in JUNAID zaki mik'a masa, duk sun tafi school, kuma ba son yan' aiki yake su kai masa ba", Zuciyarta taji babu dad'i lokaci d'aya amma babu damar yi ma Yaya deeja musu, hakan yasa ta amsa da "Toh", "Yawwa kiyi sauri pls", Hijab kad'ai ta zura kan rigar baccin dake jikinta,
Kitchen ta shiga ta d'auki tray na breakfast d'in sa, nasa daban ake masa kasancewar ba komai yake ci ba, Rai a jagule ta nufi guest room, nan yake sauka duk lokacin da yazo, Bakin k'ofar ta tsaya tana knocking,
Ya gama shirin sa kenan cikin shadda wagambari light blue wanda ta karb'i chocolate skin fatar sa sosai, JUNAID ba fari bane haka ba bak'i ba, kalar fatar sa mai kyau ce sosai wacce ta had'u da hutu, kwantaccen gashin sa na fulani, wanda aka masa askin low cut, ya kwanta luf yana shek'i zaka rantse oil ya shafa masa, hannun sa d'aure da agogo designer na kamfanin calvin klein, Zama yayi bakin gado kana ya furta "Yes"
Jauhar dake tsaye waje zuciyarta kamar zata fashe saboda takaicin jiran da ya barta, ta murd'a k'ofar d'akin ta shiga, k'amshin turarensa mai dad'i ya ziyarci k'ofofin hancin ta, dan' toshe hanci tayi dan hawa mata kai ya soma, turaren JAMEEL kad'ai ke mata dad'in shak'a, tebur dake tsakiyar d'akin ta ajiye, Tace "Ina kwana?", Ko alamar shigowarta bai nuna ba balle ya amsa gaisuwarta wacce tayi murya k'asan mak'oshi kamar wacce ake ma dole, A ranta tace "Kada Allah yasa ka amsa", Ta juya ta fice, Muryarsa taji yace "The door" Saboda takaici ma ta manta bata rufe ba, wani haushi ya bata da irin maganar sa, ba zai ce ta rufe k'ofa sai dai yace "The door, mutum sai shegen miskilanci da girman kai", Ta rufe k'ofar ta fice cikin takaici, inda sabo ya kamata ta saba da halayyar sa dan tun saninta dashi haka yake, bai tab'a canzawa ba.
OUM MUHRIZ