WANI SO

CHAPTER 5 : page 5

by @zeeyabour20

WANI SO


NA ZEE YABOUR


FREE PAGE 05



Tana komawa d'akin ta watsar da lamarin JUNAID, band'aki ta shiga tayi brush da wanka, ta shirya cikin atamfa fitted gown, bata tsayawa shafa komai a fuskarta ba, ta fito falo yin breakfast, Sauran kunun gyad'a da akayi ma Junaid ta sha, itama tana so sosai, Shi kad'ai ta sha, ta zauna falon tana kallo, wanda fin rabi tunanin yadda zata sanar da Yaya deeja zuwanta gidansu Jameel take, Zamanta da kusan minti talatin Yaya deeja ta fito, "Jauhar kina nan", "Eh Yaya", Ta k'araso falon tana zama kujerar kusa da Jauhar, Ta nisa tace "Kinga da ko catering school kin amince kin shiga, ai da kin rage zaman kad'aici", Murmushi tayi tace "Yaya ai duk abincin da ya kamata na koya, na koya a wurin ki, a ganina babu buk'atar shiga catering school", "Jauhar kenan banda abun ki, dole akwai abubuwan da ni kaina ban san su ba balle na koya miki, kuma ko kin iya ai sai ki k'ara gwanancewa", Murmushi kawai tayi, dan sun tab'a maganar da Jameel ya nuna baya so, hakan yasa tun lokacin abun ya fita kanta,



Yaya deeja ta katse shiru ta da cewa "Yanzu shekara d'aya fah kenan da kammala makarantar ki, kina zaune gida, babu abunda kika k'aru dashi, ko islamiyyar nan kin k'i shiga, auren ma shiru bai turo ba, a yadda kuke soyayya ban zata a d'auki tsawon lokaci haka ba kuyi aure ba", Kanta ta sunkuyar k'asa tace "Yau yace zai zo ya d'aukeni na gaishe da Maman sa", "Kece ma zaki je gaishe da mahaifiyar sa kenan, naji kunyar jin zancen nan a bakin ki, a zatona zakiyi tunani da hankalinki na ganin rashin dacewar hakan, wane kallo kike so mahaifiyar tasa ta miki, na mara kamun kai ko me", "A'ah Yaya, ita tace ya kawoni ta k'osa ta ganni wai", "Idan ta k'osa su turo a saka rana ayi aure, sai tayi ta ganinki har ta gaji, amma ba yanzu da ko rana ba'a tsayar ba",



Jauhar k'asan zuciyarta tasan gaskiya Yaya deeja ke fad'a mata, ita kanta tana jin kunyar zuwa gidan nasu, sai dai bata son b'acin ransa, bata son wani abu da zai sa yaga laifinta komai k'ank'antar sa, lokaci d'aya taji mood d'inta ya canza, Yaya deeja ta lura da sauyin ta amma ta basar, ba zata bari soyayyar Jameel tasa K'anwar tata ta rasa ajin ta na ya' mace ba, Tashi tayi ta shige d'aki da tunanin hanyar da zata bi, Idea ta fad'o mata, Ta kira Sumy, bayan sun gaisa, ta rok'eta Dan Allah ta kira Yaya Deeja tace zata rakata wani wuri, Tace "Toh" ba tare da ta tambayeta dalilin hakan ba, sanin tabbas fitar tana da alak'a da Jameel, shi kad'ai Jauhar zatayi haka a kansa,



Tana kashe wayar Sumy na Jameel na shigowa, "Hasken idaniyata ina fatan kina lafiya?", "Ina lafiya kamar yadda kake lafiya", "Taya kika san lafiyata", Numfashi taja tace "Naji a jikina", Dariya yayi yace "A kullum soyayyarki sabuwa take zame mun", "Ka cancanci soyayyata JAMEEL", "Na tanadar miki zazzafar k'auna had'i da kulawa a gidan auren mu", Sanyi taji na ratsa zuciyarta tace "Allah ya nuna mana lokaci", "Amin Amin, bayan la'asar zanzo na d'auke ki", "Sai kazo", "Ok ki kular mun da kanki Nurul qalb", "Kai ma ka kular mun da kanka", "I will", Ya k'arasa da mata blowing kiss, Ta kashe wayar tana ajiyar zuciya mai cike da k'aunar sa.



*********************


Sumy ta kira Yaya deeja ta rok'eta Jauhar zata rakata unguwa, ba tare da ta kawo komai ranta ta amince, wanda hakan yayi ma Jauhar dad'i sosai, Tana idar da sallar la'asar, ta sake wanka, ta shirya cikin tsadadden lace d'inta red mai touches black, yana cikin kayan sallar da mijin Yaya deeja ya mata, Light makeup tayi wanda ta k'ara fiddo kyawunta, pink lips da ta shafa ya k'ara k'awata labb'an ta, turare masu sanyin k'amshi marasa hawa kai ta fesa, ta yafa mayafinta da ya shiga da kayan, bata d'auki jaka ba sai wayarta,



Taji dad'in rashin ganin kowa a falo gudun surutu, ko Yaya deeja ta zargi wani abu, Da sauri ta nufi k'ofar fita, Jin tayi kacib'us da mutum wanda k'iris ya rage k'irjinsu ya had'e, tayi saurin kai dubanta, Yau ce rana ta farko da idonta ya had'u da na JUNAID take kallon k'wayar cikin idon sa shima ya kalli nata, Fad'uwar gaba taji tayi saurin ja baya, Kafin tayi wani k'wakk'waran motsi ya rab'a gefenta ya wuce, Ajiyar zuciya ta sauke, k'amshin turaren sa da ya gauraye wurin na ziyartar k'of'ofin hancin ta, Saurin ficewa tayi a zuciyarta tana blaming d'insa na kaurar tasu, "Mutum kamar baya ganin gaban sa" Ta fad'a, 


Napep ta shiga ta kaita gidansu Sumy, Ta gaisa da mutanen gidan ta shiga d'akin Sumy wacce ke kwance, ganin Jauhar ta mik'e zaune da fad'in "Sai ina?, nasan dai tafiyar nada alak'a da Jameel", "Babu ruwanki", Cewar Jauhar tana k'ok'arin kawar da zancen, Sumy ta tab'e baki tace "Mu dai mun k'osa mu gwangwanje", "Very soon" cewar Jauhar, Sumy k'awarta ce tun js1 suna shiru, duk da bambamci na halayyar su, Sumy nada surutu sosai bata gani tayi shiru sab'anin Jauhar da ba ko yaushe take son magana ba, haka bata shiga abunda bai shafe ta ba, 



Tun fitowar ta ta masa text ya sameta gidansu Sumy, Yana fitowa gidansu Sumy ya nufa, Horn d'in motar sa kad'ai taji ta gane shine, Tayi ma Sumy sallama ta fito,



Murfin gaban motar ta bud'e ta shiga, "OMG kin had'u babe, kinga kyan da kika yi kamar a sace ki a gudu, gaskiya ke kyakkyawa ce, am even out of words", Murmushi tayi wanda ke k'ara mata kyau, "Gaskiya i can't wait any longer, next week zan aiko a sa rana", Farin ciki mara misaltuwa taji ya ziyarci zuciyarta har ta kasa b'oyewa sai da ya bayyana kan fuskarta, "Kina murna ko", Ta masa nodding kai, "Bazan iya jure rasa ki ba Jauhar, samun mace mai kyawun ki nada wahala, irinku ake cewa na gaban mota", Dariya tayi tace "Ka daina fasa mun kai", "Ba fasa miki kai ba sai zallar gaskiya", Tayi murmushi, "Ina sonki wallahi, kin had'a komai da nake so a wurin mace", "Nima ka had'a komai da nake so wurin namiji", "Really" Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, Kanta ta kawar gefe cikin kunya.





*********************


"Sorry JUNAID na bar ka kana jira", Cewar Yaya deeja, "Ba komai" Ya furta ba tare da ya kalleta ba, Zata iya fad'ar sau nawa a iya saninta dashi ya kalleta, suma duka da k'wakk'waran dalili, bata tab'a ganin miskili irin sa ba, da godewa Allah da halayyar sa ba d'aya da Kabeer ba, da tasha wahalar sa, Da tunanin haka ta k'araso falon ta mik'a masa takardun da yazo karb'a, Kabeer ya manta ya fitar masa dasu, kuma yana buk'atar su hakan yasa yazo karb'a, Ko seconds ashirin bai k'ara ba ya nufi hanyar fita, daidai k'ofar shigowa ya tsaya kamar mai tunanin wani abu, kana ya fice, 



Da sauri drivern sa ya taso ya bud'e masa mazaunin baya ya shiga ya zauna, tare da kwantar da kansa kan kujera, ya lumshe ido tamkar mai bacci, but a zahiri tunani kala kala ne a zuciyar sa (Wanda alkaalmin zee yabour bai gano su ba🤪 watakila sai zuwa gaba zan hasko muku zuciyar JUNAID)



********************


Jauhar girma da tsaruwar gidansu Jameel kad'ai ya isa shaida mata masu kud'i ne, Kanta sunkuye k'asa suka shiga falon Mummy, Batul da Khairat a tare suka taso suka rungumeta da fad'in "Oyoyo in-law", "Kuyi hankali dai kar ku karya mun ita", Cewar Jameel, "Bro babu kara", Cewar Batul, Sukayi dariya har Mummy, Hannunta suka ja zuwa cikin falon, tana k'ok'arin zama k'asa, Mummy tayi saurin cewa "Zauna kan kujera mana, feel free you are at home", A kunyace Jauhar ta zauna tana sunkuyar da kanta k'asa cikin ladabi tace "Ina wuni?", "Lafiya lau, ya gida?", "Lafiya lau" Ta amsa, "Sai yau dai na ganki, ashe a fili ma daughter nawa tafi kyau", "I swear mum, camera na rage mata kyau", Cewar Khairat, Batul tace "Exactly", Jameel ya kalli Mummy yace "Na iya zab'e ko", "Yes my son, she is so beautufil and presentable ba inda ba za'a shiga da ita ba", Zancen Mummy yaso ba Jauhar mamaki, ta zaci tarbiyarta zata duba ba kyawo ba, wani b'angare na zuciyarta yayi saurin kwab'ar ta, bata son sakawa kanta negative tunani akan wani da ya danganci masoyin nata,



"Ku taso muci abinci, let's have dinner together", Cewar Mummy tana kamo hannun Jauhar, Kunya da nauyinta yasa ta kasa musa mata, Kujerar kusa da ita tace Jauhar d'in ta zauna, Batul tayi serving d'insu, daga yanayin abincin su ta k'ara tabbatar da rayuwar turai suke gudanarwa, Sai da aka yi sallar magrib, Jameel yace ta tashi su tafi, K'atuwar leda mai shak'e da kaya, Mummy ta mik'awa Jameel tace ya bata, Haka Batul da khairat kowaccen su sai da ta bata k'aramar gift bag, Taji dad'in yadda suka tarbeta da nuna mata soyayya, hakan yasa bata duba rashin tarbiyar da ta gani a tare dasu ba, wanda sam bata addinin musulunci ba ce,



*******************


A cikin motar suna tafiya babu abunda ke tashi sai sautin wak'ar kiss daniel, Jameel yana bi yana girgiza kai, jefi jefi yana kallon Jauhar yana mata blowing kiss ta mayar masa da murmushi, Kiran waya ya katse wakar wanda connecting bluetooth na motar yayi da wayar sa, Ya danna receive, "Hello handsome" Ya tsinci muryar Meenal, bai yi saving numberta hakan yasaa bai d'auka ita bace, Kallonsa ya kai kan Jauhar, wacce k'irjinta yayi mummunan dokawa, yanayinta ya sauya lokaci d'aya, "Hello handsome baka ji ne", "Wrong number" Ya fad'a yana kashe wayar ya saka flight mode, 


"Babyna" Ya furta cikin sigar lallashi, "Uhmm" Ta amsa ba yabo ba fallasa, "Kinsan ba halina bane waya da mata ko", Tayi shiru k'irjinta na zafi, "Wrong number ce, idan na santa ai zaki ga suna yayi appearing ko", Numfashi taja tace "Hakane, ba zanyi saurin judging d'in ka ba, tsawon shekara d'aya muna tare da kai, ban tab'a kama ka da cin amana ko yi mun k'arya ba, so na yarda da kai", "Shiyasa nake sonki babyna", "Jameel" Ta kira sunan sa, "Na'am", "Dan Allah kada kaci amanata, zuciyata ta amince da kai, na baka dukkan yarda da amana", Ta fad'a murya marairaice, "Bazan tab'a cin amanarki ba Jauhar, ke kad'ai zuciyar Jameel ke so, yau kad'ai ya isa zama shaida gare ki, idan ban d'auke ki da muhimmanci ba, my family ba zasu d'auke ki haka ba", Kai ta masa nodding cike da gamsuwa dashi, "Ba da jimawa zaki zama matata, wanda zaki k'ara tabbatar da soyayyar Jameel gare ki", Murmushi tayi tana jin sanyi a zuciyarta,



Har suka kawo gida yana mata kalamai masu dad'in saurara, da tsunduma zuciya fagen k'auna, Bakin gate na gidan ya ajiyeta, ta shiga ciki da kaya nik'i nik'i, sai a k'ofar shiga gabanta ya fad'i tunanin me zata cewa Yaya deeje ina ta samu kayan, Addu'arta Allah yasa bata falon ba, Sai dai tana shiga sukayi ido hud'u, Idon Yaya deeja ya sauka kan kayan da ta shigo dasu, Jiki sanyaye ta shigo, Ta gaisheta, Ta amsa da cewa "Ina kika samu kaya", "Jameel ne ya kawo mun", "Jameel kuma ba tare da Sumy kuka fita ba", "Eh daga can yaje ya d'auko ni", Kallon tsaf Yaya deeja tabi ta dashi tace "Na hanaki zuwa gidansu shine kika b'ullo ta wata hanya kika je ko", Kai ta girgiza tace "Ban je gidan su ba, a gidansu Sumy ya sameni shine ya d'auko ni", "Naji, akan me zaki shiga motar sa ya dawo dake gida, daga yau ya zama na farko na k'arshe, idan anyi auren ku ya d'auke ki ku tafi birnin sin ma, amma ban da yanzu", Hak'uri taba Yaya deeja, ta shige d'aki tana hamdala da bata gano gidansu Jameel taje ba,



Kaya barkatai Mummy ta had'a mata masu kyau da tsada, hadda takalmi da mayafi, Batul da Khairat designer turaruka suka bata, Sosai taji dad'i a zuciyarta tana jin tayi dacen dangin miji.



MUNA MIKI FATAN HAKA JAUHAR👌🏻



OUM MUHRIZ