CHAPTER 6 : 06
by @zeeyabour20
Yau asabar ranar hutu ga ma'aikata da yan' makaranta, Hayaniyar su Aira har d'akin Jauhar wacce ke shirya kayan da zata tafi dasu zaria gobe, Ta shirya komai tsaf cikin akwati, Kana ta mik'e ta saka hijab jalbab, ta d'auki k'aramar jakarta ta rataya, ta fito, A d'aki ta sami Yaya deeja ta sanar da ita zata je shopping mall siyayyar tsaraba, kamar yadda ta saba, duk zuwa sai ta kaiwa iyayenta da yan' gidansu tsaraba, "Kina da kud'i ne?" Yaya deeja ta tambayeta, Kai ta mata nodding tace "Eh", Bedside drawer ta jawo ta zaro bandir na 200 tace "Gashi ki k'ara", Hannu biyu tasa ta mata godiya, ta fita,
"Aunty zan bi ki" Cewar Airah, "Ki sameni mota, amma kiyi sauri", Ta k'arasa tana nufar k'ofar fita,
Farfajiyar gidan taga motar da suke fita a fake, ba tare da tunanin komai ba, ta bud'e murfin baya ta shiga, ta rufe k'ofa tana gyara zama, K'amshin turaren da ta soma shak'a ya sata saurin kallon gefenta, JUNAID ne zaune cikin shigar suit da suka matuk'ar yi masa kyau, kansa sunkunye k'asa yana danna waya, babu wata alama da ta nuna cewar yasan da shigowarta motar, Ganin haka ta soma k'ok'arin bud'e motar ta fita, tasa k'afarta d'aya waje taji muryar Baba direba yace "Ai tare zamuje, na ajiye shi, sai na wuce dake", Kafin tayi magana Airah ta bud'e murfij gaba ta shiga tana cewa "Maama tace muyi sauri mu dawo", Jauhar ji tayi tamkar tace ta fasa fitar sai dai kuma bata so ya zargi saboda shine, Hakan yasa ta maido k'afarta d'aya cikin motar, ta rufe k'ofar tare da mannewa jikinta, gaba d'aya tana jin ta a takure, Zaman Junaid kusa ta da ita tamkar zaman abunda tafi tsoro ne, dan ko motsi mai k'arfi ta kasa,
Baba direba yaja motar, suna hawa titi, Kiran Jameel ya shigo wayarta, ba zata iya share kiran sa ba, Hakan yasa ta d'auka tana kai dubanta ga JUNAID taga gaba d'aya hankalinsa baya kanta, Ta soma magana "Hello My babe", "Na'am my love", Ta fad'a murya k'asa k'asa ta yadda Junaid ba zai ji ba, sai dai karaf a kunnen sa dan Allah yayi masa masifar ji, but yanayin sa zaka rantse da Allah bai ji komai ba, "Kina mota ne?", "Eh", "Zuwa ina?", "Shopping mall kasan gobe ne zuwa na zaria", "Shine baki fad'a mun zaki fita ba", "Am sorry i was carried away", "Ok ki kular mun da kanki kinji", "I will In Shaa Allah", "Ina sonki sosai babe", "Nima ina sonka sosai", Ya mata blowing kiss ya kashe wayar, Dubanta ta k'ara kaiwa ga JUNAID, ya lumshe ido yana cizon labb'ansa na k'asa, hakan ya sake bata tabbacin bai ji wayar tasu ba, Ta maida kallonta kan window, zuciyarta cunkushe da soyayyar JAMEEL.
**********************
JUNAID aka fara saukewa wani company na oil and gas, motar sa da yazo da ita garin ta samu matsala, hakan yasa Baba direba ya kawo sa, Yana fita motar, Jauhar ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya tana jin tamkar an rabata da k'aya, Tuni ta sake suna hira da Airah wacce itama a takure take ganin Uncle JUNAID, Siyayya sosai tayi, Gwaggo da Bappa duk tafi kashe musu kud'i, sauran kishiyoyin Gwaggo turaruka da sabulu ta siyan musu, sai k'annenta da suke Baba d'aya su uku ta siyan musu kayan k'walama, suka koma gida, a falon suka baje suna hira da Yaya deeja da Inna ladi (dattijuwar mata dake aiki gidan, tun haihuwar Airah, sun saba da ita sosai, haka ba zaka ce yar' aiki bace, yadda suka sake mata),
********************
A daren JAMEEL yazo suyi sallama, Kamar ko da yaushe Jauhar ta chab'a ado ta fito tana rambad'a k'amshi, "Sarauniyar ado da kyawu", Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, "Sannu da zuwa muradin zuciyata" Ta fad'a tana masa murmushin dake narkar dashi, Yace "Yanzu tafiya zakiyi ki bar ni", "Sati d'aya kawai zanyi", "A wurin ba kawai bane, dan zanji tamkar shekara ne", "Ni kaina zanyi su ne cike da kewa da begenka, amma zuciyoyinmu ai suna tare da juna", Kai ya mata nodding yace "Ina jin wannan shine zuwa na k'arshe da zakiyi ba tare da igiyar aurena a kanki ba", Murmushi tayi tace "Allah ya tabbatar mana", "Amin Amin kina dawowa zan turo magabata na, ban da ma zakije zaria ai da jibi zasu zo", "Me zai hana, tunda ko sunzo ba ganina zasu yi ba, ina cikin gida", "A'ah zasu buk'aci ganin ki na tabbata", "Tunda zaria zanje ai sai suzo ko", "Gidan yayarki zasu zo ai ba zaria ba", Da mamaki ta d'ago ta kalle sa tace "Tushena, gidan iyayena ai can ya kamata su je", "A'ah ki bari su zo nan d'in, gudun surutu da tsegumi", "Ban fahimta ba", Ta fad'a tana kallon sa, "Kinsan yadda yan'uwa suke, za'a je ana tsegumin ban d'auko yar' babban gida ba", Kallo
mai cike da mamako had'i da takaici ta masa tace "Ina ce yar' babban gida itace yar' mutunci gidan dattako", "Hakane amma kinsan wasu na duba kud'i, nasan irin dangina zasu duba wannan",
Ranta taji ya b'aci lokaci d'aya, take yanayinta ya canza, Ganin hakan Jameel yace "Ban zata zaki kasa fahimta ta ba, har kiji haushi akan wannan maganar, a zatona ke mai fahimta ta ce, kinsan halina, kinsan ban damu da yanayin gidan ku ba, kawai bana son abunda zai sa su raina ki ne, kizo cikin dangi suna miki wani kallo, zuciyata ba zata d'auka ba", Zuciyarta taji ta dan' yi sanyi haka bata son b'acin ran Jameel ko kad'an, Ta numfasa tace "Ba komai na fahimta, su zo nan d'in", "Yawwa My baby", K'asan zuciyarsa yana murnar amincewarta, dalilin da ya bata sam ba haka bane, dan buk'atar kansa ya fad'a, sam baya so a raina sa, itama kyawunta ya k'ara jawo hankalinsa gareta da sai yar' wani hamshak'i zai aura, Jameel kalaman soyayya ya cigaba da yi mata wanda yayi nasarar goge duk wani b'acin rai da shakku akan sa, Sai goma na dare suka rabu, ta shige cikin gida, tana zuwa d'aki, ruwa ta watsa ta saka kayan bacci, tabi lafiyar gado.
*******************
Jameel yana barin gidansu JAUHAR, joint d'insu ya nufa, To his suprise yaga Meenal ta tsuke cikin wando da riga iya gwiwa, kanta d'aure da scarf, "Hy Handsome" Ta fad'a tana k'arasowa wurin ta, Murmushi ya mata yace "What's up", "In the sky" Ta fad'a tana dariya, shima yayi dariyar, Tebur d'aya suka zauna tare da ita, dan kujera ta d'auko tayi joining d'insu, Suna shan shisha itama gwana ce, flavor iri d'aya tace a bata da na JAMEEL, sai shishhigi masa take tana jan sa hira, Ya sake da ita sosai, wanda hakan ba k'aramin dad'i yake mata ba, tana jin ta samu shiga wurin sa, ba da jimawa ba zasu fara soyayya, Pass 12 suka mik'e kowa ya nufi motar sa, Motar da Meenal tazo da ita, ba k'aramin tafiya tayi da Jameel ba kasancewar sa mayen mota, haka kuma ya k'ara tabbatar masa ta fito gidan daula, "Motar ki ta had'u fah" Ya fad'a, "Thank you" Ta fad'a cikin jin dad'i, Yace "Bye" yana shigewa motar sa, tabi sa da kallo cike da soyayyarsa.
******************
Jauhar tunda ta tashi sallar asuba bata koma ba, tafiyar safe zasu yi, dan Baba direba juyowa zai yi ba can zai kwana ba, Bakwai da rabi ta fito cikin shirinta tsaf, Turkish riga ce a jikinta, sai mayafi tayi rolling zuwa wuyanta dashi, Ta fito tana k'amshin turarenta mai sanyi, Masu aikin gidan suka fitar mata da kaya, Tun daren jiya sukayi sallama da Yaya deeja, sanin da safe ba lallai su had'u ba,
A harabar gidan ta hango JUNAID jingine da bango, ya hard'e hannayensa biyu, jikinsa sanye da jallabiya wanda ke nuni da cewa ba fita zai yi ba, ga dukkan alamu bacci ma ya tashi, "Toh me yake yi anan?", Ta tambayi kanta, Wata zuciyar tace "Ina ruwanki", Ta tab'e baki ta k'arasa mota ta shiga, Suka gaisa da Baba direba yaja motar, ta turawa Jameel text ta wuce, sanin yanzu bai isa tashi bacci ba.
**************************
Tafiyar minti arba'in da biyar ta kawo su garin ZAZZAU, Motar Baba direba na parking bakin madaidaicin su gidan su, mai d'auke da k'aramar k'ofa shiga, Yara wanda jikokin gidan suna wasa a wajen, suka soma ihu da fad'in "Aunty Jauhar, Aunty Jauhar", Murmushi tayi ta bud'e murfin motar ta fito, suka dabaibayeta suna mata oyoyo, Manyan cikinsu suka shiga da kayan ciki, Tayi ma Baba direba godiya tare da sallama, Ta nufi cikin gidan nasu, ba wani babban gida ne sosai, gidan da ne, tsakar gida ne mai d'auke da k'aton bishiya wanda anan suke shan iska, sai d'akunan matan su uku, kowacce ciki da falo, sai b'angaren Bappa shima ciki da falo, sai wasu d'akuna guda biyu can ta baya wanda nan samarin gidan ke zama, babban kitchen mai murahu a tsakar gidan, wanda yanzu suna da camping gas, Yaran gwaggo sunzo canza musu gida, Bappa yak'i a cewar sa yafi sabawa da nan d'in, komai na hidima basu rasa a gidan ba, dan Yaran gidan na taimakawa,
D'akin Inna ta fara shiga, ta tarar da ita tana sallah, ta shiga d'akin, Har k'asa ta duk'a ta gaisheta, Ta amsa da sakin fuska tana bin kayan jikinta da kallo cike da hassada, ganin ga yar'ta Bintu sa'ar Jauhar bata samu gata irin nata ba, "Ina Bintu?", "Ta tafi koyon d'inki, kinsan ta shiga makarantar koyo", "Ok Allah ya bada sa'a", Ta amsa da "Amin", Jauhar ta mik'e ta fita.
******************
Gwaggo dake zaune kan sallaya tana lazimi, jin fad'uwar Jauhar tayi jikinta, "Oyoyo Auta, sannu da zuwa sannu da zuwa", "Yawwa Gwaggo na", Ta fad'a tana d'aura kanta kan kafad'ar Gwaggo, "Ya kika baro mutan can?", "Kowa lafiya lau", "Toh madallah Auta", "Bappa yana nan", "Yanzu ya fita gona", Tace "Toh" tana mik'ewa ta nufi wurin kulolin abinci wanda take da tabbacin nata ne, Kular farfesun kaza ta fara bud'ewa tace "Gwaggo duk ni akayi ma", "To wa zan ma idan bake ba Auta, kinsan nama ba damu na yayi ba", "Allah Sarki Gwaggo na, sannu nasa ki aiki", "Ba komai Auta, ke dai zauna kici ki k'oshi", Zama tayi ta tank'washe k'afa ta soma cin naman kazar, sai taci mai isar ta, ta ajiye saura,
Wayarta taji na k'ara, wanda Jameel ne, ta d'auka tana shigewa d'akin Gwaggo, "Nurul qalb ya hanya?", "Ai har mun isa", "Kunyi sauri, ko da yake babu nisa", "Eh babu", "Toh sannu, ina gaishe da Gwaggo", "Zata ji", "Nima yanzu na tashi daga bacci", "Kayi mafarkina", "Yes my love kema kinsan kullum sai nayi", "Bani labari toh", "Munyi aure muna having romance", Shiru tayi jin kunyar zancen sa, "Sarkin kunya, bara na shiga toilet, will call you later", "Ok bye love you", "Love you too", Ya kashe wayar.
OUM MUHRIZ