WANI SO

CHAPTER 7 : 07

by @zeeyabour20


Yamma ce sakala, rana ta fad'i, fin rabin mutanen gidan suna zaune k'ark'ashin bishiya, wasu na zaune kan kujerun tsugunno, wasu kan tabarma, wasu na kwance, K'ananum yara suna daga gefe suna wasa, Hira ake mai cike da nishad'i, zaka rantse da Allah zaman soyayya, k'auna da amana ne tsakanin kishiyoyin uku da yaran su, babu wata alama da zata nuna maka akwai zazzafan kishi wanda ya rikid'e ya zama hassada a zuciyoyin wasu daga ciki,



Jauhar na kusa da Gwaggo tana cin awara, wayarta na hannunta tana chatting da masoyinta, Inna tace "Wannan waya dai tana d'auke miki hankali da waya, tun zamanki wurin nan kike tab'awa, ki ajiye ki huta mana", Ta k'arasa tana bin wayar da kallo wanda ko ba'a fad'a maka ba kasan mai tsada ce, Jauhar murmushi tayi ta ajiye wayar gefe, Inna tace "Yawwa ko kefa, amma tun d'azu kan abu d'aya", "Ai dama yaran birnin nan haka suke da waya, kullum suna kanta ko sallah sai kiga basa tashi suyi, sai anci sa'a wasu daga cikin su ke had'a salloli" Cewar Mama, Inna tace "Shiyasa aurensu ke yawan mutuwa dan sam basa tattalin miji ko yaushe ana kan waya", Gwaggo tuni ta d'ago habaici ne suke yadawa amma tayi tamkar bata fahimta ba tace "Allah dai ya shirya mana zuri'a", Suka amsa da "Amin",


Jauhar kuwa awara ta cigaba da ci abun ta, ba tare da ta fahimci ina maganganun nasu suka dosa ba, Shigowar Bappa yasa hankalin kowa ya koma kansa, suna gaishe sa yana amsawa, Ya kai dubansa ga Jauhar da cewa "Autan gwaggo(haka yake kiranta) yaushe aka zo?", Da murmushi tace "D'azu Bappa", "Ya kika baro su Hadiza da yaranta", "Duk lafiya lau suna gaishe ku", "Toh madallah" Ya k'arasa b'angaren sa, Mama ta tashi tabi bayan shi yau girkinta ne, Kiran sallar magrib kowa ya watse zuwa sallah, a tsakar gida Jauhar tayi alwala kana ta shiga ciki.




************************


"Kina ganin Jameel bai yi k'arami da aure ba kuwa", Cewar Daddy(Mahaifin Jameel), "Haba dear(duk da sun manyata bata daina kiransa da haka ba), Jameel ne yayi k'arami da aure he is 27 fah, idan baiyi aure yanzu ba yaushe zai yi" Cewar Mummy, Daddy yaja numfashi yace "Akwai abunda nake hange, ina ganin kamar har yanzu Jameel bai san ya rayuwar aure take ba, akwai k'uruciya a lamuran sa", "Am sure Jameel zai kula da matar sa, saboda yana sonta sosai, kuma tunda ya nuna yana son auren ai gara a mishi", "It's Ok tunda kin ce haka, sai a saka ranar zuwa gidansu iyayen yarinyar", Hugging d'inshi tayi da cewa "Naji dad'i", Murmushi yayi yace "Soyayyar mu bata tsufa", Tace "K'warai", 


Ya nisa yace "Amma yar' gidan waye?, a wane gida take?", "Naji kamar yace Kabeer Maina", Daddy ya girgiza kai yace "Good, dan bana son harkar k'arata", "Ni kaina banson wlh my dear, gara ayi abu na harkar girma", Daddy ya jinjina kai yace "Tabbas, so zanyi magana dasu Shu'aibu ranar da suke free sai aje a saka rana kawai", "Ok Allah ya kaimu", Ya amsa da "Amin", Yana maida hankalin sa kan kallon news.



**********************


"Dama yau ne zaka koma, ba gobe kuna da meeting da manager Basako oil ba", Cewar Kabeer, JUNAID ya numfasa yace "Eh, someone will represent me", "Amma meyasa ba zakayi hak'urin jibi ka tafi ba, tunda ba wani muhimmin abu zakayi abuja ba, ina ganin zuwa da kanka yafi wani ya wakilce ka", Kai ya girgizawa Kabeer alamar a'ah, yana duba agogon dake d'aure wutsiyar hannun sa, Yace "Flight d'ina is 2pm", "Ok Safe" Cewar Kabeer, Junaid ya masa nodding kai yana ficewa daga falon, bai yiwa Deeja sallama ba, dama ba al'adar sa bace yi mata, bata sanin ranar zuwan sa haka bata sanin ranar tafiyar sa, sam babu wata doguwar alak'a tsakanin su, idan ba an fad'a maka ba, ka gansu tare zaka rantse ba k'anin mijinta bane, zaka ce ma basu san juna ba saboda rashin sakewa irin ta JUNAID.



*********************


Jauhar na kwance kan cinyar Gwaggo, suna hira mai cike da k'auna ta tsakanin uwa da ya', Wayarta tayi vibrating alamar shigowar text, Ta d'auka ta duba ganin Jameel ne ta saki murmushin farin ciki,


"I can't wait to have you my side baby, am longing to kiss ur soft lips", Saurin kifa wayar tayi kan k'irjinta, ta runtse ido tamkar tana gabansa, kwanakin nan Jameel yana mata wasu maganganu wanda a da ba haka yake ba, ko k'osawar suyi aure ke sa shi haka, ita kam yana sata kunya, 


"Lafiya kika damtse ido", Cewar Gwaggo, "Bacci na fara ji", "Toh tashi kije d'aki ki kwanta", Ta amsa da "Toh" tana tashi ta shige d'aki, dama bata son Jameel ya kirata a gaban Gwaggo,



*************


Jameel dake kwance d'aki yana jiran reply na Jauhar yaji shiru, Ya danna kiranta, Bugu biyu ta d'auka, Tare da yin shiru, "Babyna kunyar ce ta hana ki magana", Tace "Uhmm" tana sake jin wata kunyar tamkar tana gabansa, "Anya kunyar nan taki zata bari muyi soyayya bayan aure", "Na tanadar maka zazzafar k'auna bayan auren mu, fatana Allah ya nuna mana lokaci", "Da gaske Nurul qalb", "Yes Babyn Jauhar", "Har kinsa naji sanyi da dad'i a zuciyata, da ina cikin fargaba", Dariya tayi tace "Ka daina shakku akan komai my love", "Na daina my babe", Taja numfashi tace "Ina sonka so mai tsanani son da bansa adadin sa", Kwanciyar ya gyara tare da k'ara jawo pillow jikinsa yace "Babu abunda nake so kamar naji ki a kusa dani, ina jin kamar ace pillow da nake rungume dashi kece", Duk da taji kunyar zancen sa, gudun kar yaji babu dad'i ta danne kunyar tace "Lokaci na zuwa da zamu kasance da kuna ko da yaushe", "Can't wait my baby", "Nima hakan", "Really" Ya fad'a cike da murna, Tace "Yes", "Allah yasa ki iya juriya dani daren farko, dan bazan sassauta miki", Dan k'ok'arin danne kunyarta ta kasa tace "Uhmm", "Kada kiga laifina Jauhar, soyayyarki ke sani jin haka game dake", "Nasani" Ta fad'a zuciyarta na bata tabbacin zancen sa, Jin shigowar Ahmad yasa yace mata "Yana zuwa, zai k'ara kiran ta", Tace "Toh" Ta kashe,



Bai d'auki wayar Ahmad ba, sanin yana kiran sa ne zasu je wani party na budurwar abokin su, Shiryawa yayi cikin crazy trouser da polo t-shirt, ya taje gashin kansa, yabi jikinsa da turaruka masu hawa kai sosai, Ya d'auki mukullin motar sa ya fito,



Yana shiga mota kiran Meenal ya shigo, "Hello handsome", "Yes girly", "Please ku zaku biyo ka d'aukeni battery mota ta yayo running down", "Ok kina ta wurin ina ne", "Malali", "Ok on my way", Yayi hanging up, Meenal murnushin farin ciki tayi ba abunda ya samu motar ta, tana son kawai suje wurin tare ne, k'awayen dake wurin su k'ara shaida saurayinta ne kamar yadda ta soma fad'a musu, Shima Jameel yaji dad'in zasu je tare, kasancewar ta babban yarinya idan an gansu tare gp d'insa zai k'ara hawa, duk da babu soyayyarta ko d'igo a zuciyar sa, amma yana son harka da classy babes, yaran masu hannu da shuni.




HMMMM JAMEEL, JUNAID, JAUHAR, MEENAL🤔



OUM MUHRIZ