CHAPTER 8 : 08
by @zeeyabour20
Sautin sifiku(speakers) ke tashi na kad'e kad'e da wakok'i, Jameel tuni yayi saurin fitowa daga motar, kid'an na tsuma shi, Meenal ta kalle sa da murmushi, a zuciyarta tace "Jameel ba dai son kid'a ba", Ta fito motar tana bin bayan sa, A tare suka jera shiga hall d'in, layi suka tarar wanda sai ka nuna gate pass kafin ka wuce, Kowane saurayi sak'ale da hannun budurwar sa, Meenal shu'umin murmushi tayi tana k'ara matsowa kusa dashi, ta sak'ala hannunta a nashi, Saurin dubanta yayi ta sakar masa murmushi tare da d'aga masa girar sama, Kasa cewa komai yayi ya mayar mata da murmushin, Meenal dad'i taji a ranta, tana k'ara matse hannun sa, yayin da take jin zazzafar k'aunar sa na shigar ta, k'aunar da bata jin zata iya rayuwa ba tare dashi ba,
Shigar su hall d'in yaja hankulan mutane da dama, ciki hadda abokan sa da suka riga shi zuwa, Hafeez yace "Wa nake gani kamar Jameel rik'e da hannun Meenal", Sauran suka kai dubansu da cewa "Shine wallahi", Ahmad yace "Kar dai ya fara soyayya da yarinyar nan", Fahad yace "Haba kamar baku san irin son da yake yiwa Jauhar ba, ai bana jin akwai macen da zata d'auke masa hankali", Hafeez yace "Hakane, duba da Jameel mutum ne mai sakewa sosai especially da mata, so ba abun mamaki bane idan an gansu da meenal", Ahmad yace "Exactly, kawai yanayin nasu ne kamar saurayi da budurwa", Kafin wani ya bada amsa Jameel ya k'araso wurin, "Hey what's up guys", Ya fad'a yana zama kan kujera, "Meye had'in ka da babe d'in ko anyi ma Jauhar rival ne", Ahmad ya tambaye sa cikin zolaya, Jameel harara ya watsa masa ya nuna zuciyar sa da cewa "My heart belongs to only Jauhar, Meenal is just a friend", "JJ na mata", Jameel yace "Na Jauhar dai, sauran kawai ana good time ne", "Allah dai ya kaimu auren ka da Jauhar, ranar till dawn zamuyi" Cewar Hafeez, Sukayi dariya had'i da shewa.
****************
"K'awata haka kika samu shiga wurin Jameel", Cewar Hussy zuciyarta cike da bak'in cikin dama itace, Meenal tayi murmushi tana tauna chewing gum tace "Ai na dad'e da samun gurbi a zuciyar sa, zazzafar soyayya ke gudana tsakanin mu", Hussy k'ok'arin b'oye bak'in cikinta tayi da cewa "Ke mai sa'a ce gaskiya", Meenal tace "K'warai" ta tauna chewing gum yayi k'ara, Sauran k'awayenta biyu basu tanka ba, sai hararar gefen ido da suke bin ta dashi mai cike da hassada, da ganin ta k'wace saurayin da suka dad'e kowaccen su na hari.
******************
Jauhar washegari bata wuni gida ba, gidajen yayyenta dake garin ta kai musu ziyara, sai yamma lik'is ta dawo gida, Kamar kullum mutanen gidansu na k'ark'ashin bishiya sunna hira, Ta gaishe su ta shige ciki, Zamanta ba jimawa Gwaggo ta shigo,
"Tun d'azu Bappa ke neme ki, yace idan kin dawo muje tare" Cewar Gwaggo, Jauhar ta tashi daga kwancen da take kan kujera tace "Toh", Mayafin data dawo dashi, ta yafa ta mik'e, A tare suka fito da Gwaggo,
Cikin ladabi ta gaishe da Bappa, Ya amsa da far'a yana cewa "Autan gwaggo", Tayi murmushi ta zauna k'asan carpet, Gwaggo ta zauna kujerar kusa dashi, Remote ya d'auka ya kashe tv'n dake aiki, Yayi gyaran murya yace "D'azu Kabeeru ya kira yake sanar dani iyayen yaron dake neman Jauhar sun kira sa, kan cewar zasu zo neman aure da saka rana", Jauhar farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta har murmushi na sub'uce mata, Bappa da Gwaggo sun lura da yanayin ta, hakan ya k'ara shaida musu tana son sa, Gwaggo tace "Mashaa Allahu", "Sai dai sun nuna cewar gidan Kabeeru zasu je", Gwaggo ta girgiza kai da cewa "Ga tushen ta, asalinta gidan mahaifinta ai nan ya dace suzo, kamar yadda aka nemi na kowa", Bappa yace "Nima tunanin da nayi kenan, gidansu ya kamata azo", Jauhar tuna yadda sukayi da Jameel tayi saurin cewa "Ina ganin kamar idan aka zo nan ba'ayi wa Yaya Kabeer kara ba, duba da shi ya rik'eni tun ina k'arama",
Bappa da Gwaggo sunyi mamakin maganarta, basu zaci zatayi saurin saka baki ba, ko zamanta birni yasa ta haka dan sam ba tarbiyar su bace, duka yaran da akayi wa aure gidan babu mai saka kansa maganar auren sa har ayi a gama, itama ya kira ta ne ya tabbatar tana son auren Jameel, dan baya yiwa yaran sa auren dole, wanda kake so shi zai aura maka, matuk'ar mutumin kirki ne.
"Auta yaushe kika zama mara kunya", Cewar Gwaggo tana duban ta, Bappa yace "Ba'a saurin saka baki a magana irin wannan kin ji ko", Jauhar ta d'aga kai sama da cewa "Toh" ita kanta taji kunya, bata san me ya shige ta tayi saurin magana, ko dan gudun b'acin ran Jameel, bata son jayayya dashi tunda ya nuna inda yake so aje neman auren ta, Bappa ya katse tunanin ta da cewa "Maganar taki abun dubawa ce, kina da gaskiya, ya kamata ayi wa Kabeer kara, dan yanzu matsayin ya' kike a wurinsa", Gwaggo ta jinjina kai tace "Hakane, kuma ya rik'e ta tsakani da Allah tamkar yar' da ya haifa ta cikin sa", "K'warai da gaske, zan kira sa nace ya basu damar zuwa gidan sa", "Hakan yayi, Allah yasa a k'ulla alkhairi", Bappa ya amsa da "Amin zaku iya tafiya",
************************
Dattijuwar mata ce mai kimanin shekaru sittin zaune kan carpet, bayanta jingine da kujera, ta mik'e kafafunta kyakkyawar budurwa yar' shekara ashirin na mata tausa, sanyin ac ta ko'ina yana ratsa falon wanda aka narkawa dukiya kai kace ba za'a mutu ba, kujerun falon wanda royal ne kad'ai sun ishe ka kallo, "Danna mun nan" Ta fad'a tana nuna wurin gwiwar ta, Budurwar ta cigaba da danna mata, tana jera mata sannu, "Yawwa yar' albarka"
"Ummi dole k'afafu suyi ciwo, sanyin nan da kike sha yayi yawa", Cewar Junaid yana k'arasowa cikin falon ya d'auki remote ya rage ac, Budurwar ta kai dubanta gare sa tace "Ina kwana Yaya?", "Lafiya" Ya amsa kamar dole ba tare da ya kalleta ba,
"Zafin nan ai dole sai da ac", Ummi ta fad'a, "Ina kwana?" Ya gaisheta dan baya son maganar tayi tsawo, "Lafiya lau", Bai sake cewa komai ba, ya zauna ya fiddo wayarsa yana dannawa,
"Anisa kawo masa abincin sa", Ummi ta fad'a sanin bai cika zama kan dining table cin abinci ba, Aneesa ta amsa da "Toh" tana mik'ewa cikin rawar jiki, Allah yasa mata masifar son JUNAID, wanda bai san tana yi ba, idan za'a tsare sa ba zai ce ga kamaninta ba, Cikin mintuna kad'an ta dawo d'auke da tray na abinci, ta ajiye gaban sa, Zata fara serving d'in sa ya dakatar da ita da hannu, Rai babu dad'i ta mik'e tana komawa kan kujera,
Junaid sai da ya k'ara kusan minti goma, kana ya ajiye wayar sa gefe, Yayi serving kan sa kunun gyad'a da k'osai(his favorite, bai k'i kullum da safe a masa su ba), Ya soma ci a natse, Aneesa duk wani motsin sa akan idon ta tana jin tamkar ta tashi ta rungume sa tsabar so, komai nasa burge ta yake, addu'ar ta da fatan ta Allah yasa ita ce macen da zata yi nasarar mallakar zuciyar sa,
Ummi ganin ya kusa gamawa, ta kai dubant a ga Aneesa, ta mata alamar ta tafi d'aki, Aneesa ta mik'e ba musu, tana addu'ar Allah yasa maganar ta Ummi zata sake yi masa, da fatan samun nasara a kansa wannan karon,
Kofin ya ajiye, da zumar tashi, Ummi tace "Zauna muyi magana", Hankalin sa ya mayar kan mahaifiyar tasa, Ta numfasa tace "Girma kake Junaid, ka mallaki komai na dukiya, ina so kasan cika da kamalar mutum ita ce aure, kana da arzik'in da zaka iya auren macen har hud'u, amma na rasa dalilin da duk sanda za'a d'auko maka maganar aure sai ka kauce, shin auren baya cikin tsarin ka ne ko meye damuwar", Shiru yayi rashin sanin amsar bata, "Kayi shiru kai nake saurare", "Ba wani dalili Ummi", "Ai dama nasan mugun zurfin cikin ka ba zai bari kayi magana ba, toh bara kaji na gaji da ganin ka haka, aure hud'u ina nema maka wurin yan'uwa da abokan arzik'i kana watsa mun k'asa a ido, yanzu Aneesa itama da na d'auko tun daga cameroon kana neman watsa mun k'asa a ido, shin so kake mu zura maka ido ka zama tuzuru",
Ajiyar numfashi ya sauke yace "Kiyi hak'uri Ummi","Hak'urin me zaka bani, abu d'aya ne ka amincewa auren Aneesa", A razane ya kalle ta yana girgiza kai, "Meye da Aneesa, kyawo dai Allah ya bata, kuma jinin ka ce kar ka manta yar' kanina ce, haka addini da tarbiya duka tana dasu, to me kake nema a wurin mace", Idonsa ya d'an runtse kad'an ya bud'e su yace "Dan Allah Ummi ki bani lokaci", "Idan kana da damuwa ne, ka fito ka gaya mun Junaid, zurfin ciki babu inda zai kai ka", Iskar baki ya d'an fusgar yace "Sai anjima Ummi", Yayi saurin mik'ewa ya fita, Ummi tabi bayansa da kallo cike da takaicin zurfin ciki da taurin rai irin nasa, ita kam wannan karon ba zata bari taji kunya ba, Yan' mata hud'u tana kawowa gidan da sunan auren Junaid, sai magana tayi nisa ya rusa ta, Aneesa itace ta biyar yanzu da ta kawo ko yana so ko baya so wannan karon sai ta aura masa ita.
**********************
JUNAID kan kujerar falonsa ya kwanta, yana dafe kansa dake ciwo wanda maganar Ummi ta haddasa masa, sam baya son maganar aure, babu shi a tsarin sa yanzu, baya son Ummi na tursasa masa auren wata, sanin bazai tab'a k'aunar ta ba, tuni ya dad'e da rufe zuciyarsa ta yadda babu soyayyar wata ya' mace da zata shiga, duk wanda Ummi zata aura masa wahala zata yi dan ba zata tab'a samun soyayyar sa da kulawa ba, yana gudun hakk'in ta ya kamasa, hakan ke k'ara sa baya sha'awar auren da Ummi ke masa tayi, tunanin sa yadda zai bijirewa auren Aneesa da ta tado dashi, ya runtse idonsa yana sauraren bugun zuciyar sa mai cunkushe da damuwa, wacce ya kasa sanar da kowa saboda zurfin ciki irin nasa.
*********************
Jauhar tun bayan isha'i take kiran wayar Jameel ta kasa samu, ta damu sosai na rashin ji daga gare sa, har bacci ya d'auketa a falon,
Ta b'angaren Jameel yana joint d'insu na shan shisha, Meenal na gefen sa ta k'ak'abe tamkar zata shige jikinsa, flight mode ya saka wayar kar Jauhar ta kira ta fahimci wani abu, Sha biyu saura suka mik'e zuwa gida, Meenal ta mik'e tana duba wayarta bata gani ba, Jameel ta kalla tace "Please ara mun wayar ka na kira", Da gangan ta b'oye wayar dan tana son ganin sunan da ya mata saving ne, Ya zaro wayar sa aljihu ya mik'a mata da cewa "Ina zuwa baro na k'arbo chips a ciki am hungry", Tace "Ok",
Tana cire wayar flight mode, kiran Jauhar ya shigo, farkawar ta kenan, ta sake kiran sa, Ganin sunan NURUL QALB na yawo kan screen d'insa k'irjinta yayi mugun dokawa, "Kar dai yana da budurwa" Wani b'angare na zuciyarta yayi saurin cewa "No, bashi da ita, k'ila maman sa ce", Receive ta danna dan kawar da zargi,
"My baby ina ka shiga yau, ina fatan kana lafiya" Cewar Jauhar cikin shagwab'a, Meenal wani abu taji ya soki zuciyarta cike da takaici tace "Mai wayar baya kusa", Ta kashe, tana cizon labb'an k'asa.
Jauhar mummuna fad'uwar gaba taji, ta kawar da wayar gefe tana duba sunan ko ba number sa ta kira ba, ganin tabbas shine, tuni jikinta ya d'auki b'ari ta saki wayar kan kujera, Tana da tabbacin ba Batul ko Khairat ba ce, "Wacece?" shine abunda zuciyarta ke nanata mata, Kanta na juya mata, wutar kishi na ruruwa a zuciyar ta.
OUM MUHRIZ