WANI SO

CHAPTER 9: 09

by @zeeyabour20

Meenal har Jameel ya k'araso wurin bata san dashi ba, saboda nisan tunanin da ta tafi, "Am sorry i keep you waiting", Ta tsinci muryar sa, Sai a lokacin ta juyo tana duban sa, lokaci d'aya taji zazzafan kishin sa na sake shigar ta, ba zata tab'a iya rasa shi ba, zuciyar ta ta kwad'aitu da son zama abokin rayuwar sa, Gira ya d'aga mata alamar ya dai, Murmushin k'arfin hali tayi tace "Na gaji sosai ne, ina son hutawa", "Ayyah Sannu ko", Ya fad'a yana mik'a mata hannu ta basa wayar shi, "Na manta ma wata ta kira, na fad'a mata ba ka kusa", Wani kallo ya jefe mata da cewa "Meyasa kika yi picking", Sanin ba kowa bace sai Jauhar, Meenal da kallon mamaki tabi sa tace "Na d'auka mum ce shine na d'auka mu gaisa sai naji ba ita ba ce", Goshin sa ya dafe sanin ta kira masa ruwa, bai san ta ina zai fara da Jauhar ba, "Tana da kishi sosai ko, kana tsoro ta maka fitina", Meenal ta fad'a tana duban sa, zuciyar ta cike da k'unar ganin damuwa a kan fuskar sa, ashe akwai wacce yake so sosai haka, Basar da zancen yayi da ce mata "Sai da safe", Ya wuce, Meenal bayan sa tabi da kallo cike da takaici a zahiri ta furta "Ko wacece sai na raba ku, its a promise, kai nawa ne JAMEEL",



***********************


Jauhar ta kasa ko k'wakk'waran motsi sai faman ajiyar zuciya take, tana jin zafi sosai a jikin ta kamar mai hucin zazzab'i, K'arar kiran Jameel yasa ta d'auki wayar, Tare da karawa a kunne, "Babyn Jam...." , Tayi saurin katse sa da cewa "Wacece ta d'auki wayar ka?", Numfashi mai nauyi yaja yace "Budurwar Ahmad ce", "Menene had'in ka da ita da har zata karb'i wayar ka", "Mun fita tare dashi da ita ne, sai muka bar ta a mota, mun shiga wani shopping mall, kinsan waya ta da tasa iri d'aya ce, ta d'auka shi ake kira shiyasa ta d'auka, da muka dawo motar baki ga masifar da ta mishi ba, sai da na fahimtar da ita ai waya ta ce", Ajiyar zuciya mai k'arfi ta sauke tace "Ban tab'a sanin ina kishin ka haka ba sai yau JAMEEL, cikin lokaci kad'an na rasa natsuwa ta", Jameel sanyi yaji ya ratsa zuciyar sa na nasarar shawo kan ta a zahiri yace "Ya kamata zuwa yanzu ki cire duk wani zargi a kaina, ki sa tabbacin cewa Jameel mallakin Jauhar ne ita kad'ai", "Na yarda da kai Jameel, kawai kishi ne da bani da control a kan sa", "Na fahimce ki Babyna, matuk'ar akwai so to da kishi, ni kaina ina masifar kishin ki, shiyasa na k'osa na mallake ki ta yadda zaki zama k'ark'ashin kulawa ta nayi ma sauran maza k'walele", Dariya tayi yana jiyo sautin ta waya, "Kinsan me?", Tace "A'ah", "Gobe idan sun je, nace su rok'a a saka wata d'aya", "Bai yi sauri ba kuwa", "Na d'auka ma zaki ce yayi yawa, ashe baki matsu muyi aure ba", Ta nisa tace "Ba kaina nake dubawa, idan nice ban k'i a d'aura aure gobe ba, Su Bappa nake tunanin ko zasu amince", "Zasu yarda ma In shaa Allah", "Allah yasa", Yace "Amin ki zama matata, mallaki na ni kad'ai", Tayi murmushi tace "Kai ma ka zama mallakina", "Mu fara gina sabuwar rayuwar soyayya, saura kuma kunya tasa ki kasa sake mun jikin ki nayi yadda nake so", Runtse ido tayi tamkar tana gaban sa, "Uhmm a wayar ma kunya", "Ba zan hana ka duk wani hakk'in ka dake kaina ba", "Yawwa babyn jameel haka nake son ji", Tace "Uhmm", "Na shigo gida, will call u back", "Ok take care", "I will", 


Ta kashe wayar tana jin sanyi a zuciyar ta da k'ara tabbatar da girman soyayyar ta a zuciyar Jameel, tana ba kan ta tabbacin ita kad'ai ce muradin ran sa.



*****************************


JUNAID yau kwata kwata bai lek'a sashen Ummi ba gudun ta masa zancen auren Aneesa, bai san amsar bata ba, dan ya kasa samun hanyar bijirewa auren, ko abinci bai je ci ba, Snacks da lemo ya wuni ci, dama shi ba gwanin cin abinci ba ne, 



K'ananun kaya ne jikin sa, riga sleeveless sai gajeren wando, k'afafun sa sanye da slippers shoe, yana zaune kan kujerun hutawa dake k'aramin balcony d'in sa na d'aki, Iska mai dad'i yake shak'a, wanda yafi son sa akan na AC a cewar sa yafi bada lafiya, in dai zai wuni cikin AC sai mura ta kama sa, sam Ac baya shafa masa lafiya, Hakan yasa lokuta da dama nan ne wurin zaman sa, Takardu yake dubawa na meeting da zasu yi gobe kan business na gas, gefen sa ruwan kanumfari ne yake sha wanda baya rabuwa dasu, saboda lafiyar jikin sa, Wayar sa tayi k'ara ya kai duban sa kan screen, YAYA KB yayi appearing, A natse ya kai hannun sa kan stool dake gefen sa ya d'auki wayar, yana karawa a kunne,



"Assalamu alaikum", Ya fad'a cikin husky voice d'in sa, "Wa alaikassalam JUNAID barka da dare", "Ya aiki Yaya?", "Alhamdulillah, dama maganar zuwa na gobe meeting i can't make it, masu neman auren JAUHAR zasu zo", Shiru yayi na d'an lokaci kafin yace "Ok no problem", Kabeer yace "Yawwa, nasan tunda you are there, ba wani problem ba ne", "Eh" Junaid ya fad'a a dak'ile, "Sai anjima", Cewar Kabeer ya kashe wayar,



JUNAID ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idon sa, kana ya bud'e su, Ya mik'e ya shiga cikin gida, Kai tsaye band'aki ya nufa, Yayi alwala, Ya fito ya shimfid'a darduma ya soma gabatar da nafilfili, idan yayi sujada yana dad'ewa kafin ya d'ago, (BAWA NA SAMUN KUSANCI SOSAI DA UBANGIJIN SA YAYIN SUJADA, KUMA ANA KARB'AR ADDU'A YAYIN SUJADA).



************************


Yaya Deeja yau tun tashin ta, take faman aikin abincin masu zuwa neman auren Jauhar, abinci kala uku aka musu bayan snacks da nau'i'kan lemo, Ana kiran sallar azahar suka kammala komai akai kai falon Kabeer, Yaya Deeja ta nufi d'aki dan huce gajiya, Missed calls na Yaya Jummai ta tarar a wayar ta, tabi kiran, Bugu d'aya ta d'auka,



"Ina kika bar wayar ina ta kira shiru" Cewar Yaya Jummai, "Ina kitchen had'a girkin bak'in yau", Yaya Jummai ta numfasa tace "Jauhar dai ta nace sai wannan yaro, ni ban san meyasa sam hankali na bai kwanta da shi ba", Yaya deeja tace "Ni kai na ba wani son alak'ar su nake ba, duba da irin son da take masa yayi yawa", "Shi ne abun takaicin ai, gaba d'aya ta susuce a kan sa, ko wane motsi nata Jameel, hatta makaranta ace a kan sa zata bar ta, wane irin so ne wannan", Yaya deeja tace "Jauhar nayi wa Jameel WANI SO, sai dai kawai mu bi ta da addu'a, da yi musu fatan zaman lafiya", "Shine kawai, idan sun zo kya sanar dani yadda aka yi", "In Shaa Allahu", "Sai anjima ki gaida su Airah", "Zasu ji",



***********************


K'annen mahaifin Jameel su biyu, da yayyen mahaifiyar sa su biyu suka zo, kamar yadda suka buk'aci nan da wata d'aya an amince, Sun ji dad'in tarbar da suka samu, suka tafi suna yabawa, Kaya sosai suka kawo kwalayen su alawa da biscuit d'ari, lemuka sai goro k'warya goma, da kud'i dubu d'ari biyu, Ko gida ba'a shigo dasu ba, Yaya Kabeer yace a wuce dasu zaria,




*********************


Duka ilahirin gidan suna zaune tsakar gida, yara suka soma shigowa da kwalaye, Gwaggo da Jauhar suna gani suka san daga ina suke, sab'anin sauran mutanen gidan dake zancen zuci daga ina, Jauhar kanta tayi mamakin yawan su, Inna ce ta kasa dauriya tace "Wai kayan nan na meye?, daga ina?", Gwaggo tace "Neman auren Jauhar, yau sun je gidan Kabeeru", "Neman auren Jauhar sai dai mu ji daga sama" Cewar Mama cike da hassada, 


Gwaggo tace "Ai neman auren ne, ba aure ba, dama na jira su zo ne a tabbatar, sai a sanar da kowa", Mama ta tab'e baki tace "A can kaduna aka nemi auren nata kenan", Gwaggo tace "Eh", Inna tayi caraf tace "Tabb Ikon Allah, wane irin neman aure ne wannan ba za'a nema gidan su yarinya ba sai kalan gida, gidan mijin Yaya mace, ba ma gidan yayan ta namiji ba", Mama tace "Shi ne abunda na gani", Gwaggo tace "Idan da kara ai gidan kabeeru ya dace, tun da shi ya rik'e ta tun tana k'arama, kuma ya d'auke ta tamkar yar' cikin sa", "Ko meye dai da gidan uba ake ado, na tabbata ba komai yasa aka je can ba, sai dan gudun tushe an saba da rayuwar birni ta yan' k'arya", 



Gwaggo shiru tayi tana mik'ewa ta shiga d'aki ganin suna son mayar da maganar wani abu daban, Inna ta juya kan Jauhar tace "Ke kiyi wa kan ki fad'a wallahi, ace kina gudun gidan ku, wanda zaki aura kina b'oye masa tushen ki, to ki sani dai ba'a gina rayuwar aure kan k'arya", Cikin sanyin murya da rashin jin dad'in zantukan Inna tace "Wallahi Inna ba haka bane, komai talauci da rashi na ahali na bazan guje su ba, haka nasan da uba ake ado, babu dalilin da zai sa na guji a zo gidan mu neman aure na", Inna ta tab'e baki tace "Uhmm toh naji", Mama itama ta gwatsina fuska, Jauhar ta mik'e jiki sanyaye, rai jagule ta shige d'akin Gwaggo,


********************


"Kada zancen su ya dame ki kinji, duk nasan ba su kad'ai zasu kawo hakan ba, amma Allah yaga zuciyar mu da dalilin yin haka" Cewar Gwaggo cikin sigar lallashi, Jauhar ta d'aga kai sama tare da kwanciya kan cinyar Gwaggo, ta lumshe ido, tunanin Jameel da yau ta k'ara shaida ta kusa zama mallakin sa, yasa zuciyar ta yin sanyi, ta saki murmushi ba tare da ta sani ba.



**********************


"JUNAID ya shigo yau?" Ummi ke tambayar Aneesa dake zaune falo tana kallo wanda fin rabi ba kallon take ba, tunanin JUNAID da rashin shigowar sa ke damun ta, Ummi ta jinjina kai tana komawa d'aki ta d'auki waya ta soma kiran sa, Fitowar su daga meeting kenan wanda fin rabi bai san me aka tattauna ba dan hankalin sa baya kan su, yayi nisa wurin tunani da damuwar dake cin zuciyar sa, Vibrating yaji na wayar sa a aljihun gaban rigar sa, Ya fiddo, ganin Ummi ce mai kiran yaja numfashi ya d'auka,



"Ummi ina wuni?", "Lafiya lau, kana ina ne?", "Yanzu muka fito meeting", "Ka zo gida yanzu ina son ganin ka", Ya amsa da "Toh",


Rai a jagule ya shiga mota sanin neman me take masa, abu d'aya ya sani shi ne ba zai tab'a amincewa auren Aneesa ba, baya son zama da' mara biyayya amma akan aure baya jin zai yi biyayya, dan auren wata ba k'aramin cutarwa ne gare sa da ita wanda zai aurar.



OUM MUHRIZ