CHAPTER 10
by @zeeyabour20
Rai babu dad'i ya iso gida, Kai tsaye b'angaren Ummi ya shiga, Aneesa kad'ai ya tarar a falon, Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, ganin sa ba k'aramin natsuwa ya saukar mata a zuciya ba, "Yaya Ina wuni?", "Lafiya" Ya amsa a dak'ile ba tare da ya kai duban sa gare ta, Idon ta k'yam a kan shi tana jin tamkar ta bud'e zuciyar sa ta saka mishi son ta, tana mishi WANI SO da Allah kad'ai yasan adadin sa,
Junaid sam bai san tana yi ba, tuni ya lula duniyar tunani, Kusan minti goma suna haka, Kana ta mik'e tace "Bara na fad'awa Ummi", Bai amsa ta ba balle ya nuna yasan tayi maganar, Bata damu da rashin amsawar sa ba sanin halin sa,
Shigar ta da minti biyar Ummi ta fito, Aneesa bakin corridor ta lab'e dan jin me zasu tattauna, wanda zuciyar ta ke bata a kanta ne,
"JUNAID ka shigo", Ummi ta katse masa tunani tana zama kujerar kusa da shi, Ya numfasa yace "Barka da rana Ummi", "Barka ka dai, da ban buk'aci ganin ka ba za ka zo ba kenan", Shiru yayi bai ce komai ba, Ta cigaba da cewa "Saboda na maka zancen auren Aneesa shi ne ka daina shigowa kwana biyu, kafi so a zura maka ido a k'yale ka babu aure", "Ummi nufi ne na Allah, idan lokaci yayi zan yi", "Baka da niyyar aure JUNAID, girma kake k'arawa shekarun ka na ja, duk wata nagarta da kyawo da ake
nema a wurin ya' mace Aneesa tana da su, meyasa ba zaka amincewa auren ta ba?", "Ba ita zuciya ta ke so ba", Ummi tace "Wacece zuciyar ta ka ke so, idan kana da ita sai ka fad'i ayi aure mana", Shiru yayi bai sake cewa komai ba, "JUNAID" ta kira sunan sa in a serious tune, "Na'am" Ya amsa cikin sanyin murya,
"Ka fad'a mun menene damuwar ka, ina da tabbacin akwai abunda ke damun ka, ni ce mahaifiyar ka wacce tafi kowa son farin cikin ka, ka ajiye zurfin ciki ka sanar dani matsalar ka, ko ban magance maka ba zan ba ka shawara a matsayina na wacce ta kawo ka duniya", Idon sa ya lumshe yace "Ba komai Ummi", "Shikenan tun da ka zab'i b'oye damuwar ka, amma ina so ka sani ba zan tab'a samun natsuwa da farin ciki ba har sai naga ka ajiye iyali, na ba ka sati d'aya ka sake tunani kan auren Aneesa",
"Yaushe Abee zai dawo?", Ya tambaya yana son kawar da zancen, "Gobe In Shaa Allah", Ummi ta fad'a duk da tasan yace ne dan kawar da zancen amma ba zai rasa sanin ranar dawowar sa ba, akwai sakewa sosai tsakanin su da mahaifin su, "Allah ya kawo shi lafiya", "Amin, ga abincin ka nan", Ya amsa da "Toh", "Aneesa zo ki kawo masa abinci",
Aneesa dake lab'e tayi saurin cewa "Toh" Rai a jagule ta fito, jin zantukan JUNAID ya d'aga hankalin ta, bata son rasa shi, ta k'wallafawa ran ta shi, Jiki sanyaye ta d'auko tray na abincin ta ajiye gaban sa, ta koma ciki, bata son Ummi ta fuskanci sauyin yanayi a tare da ita.
*********************
Iyayen Jameel sun ji dad'in jin irin tarbar da aka ma su Shu'aibu, a zaton su KABEER MAINA shine mahaifin Jauhar, dan sam basu tsawwalawa bincike ba, son kawai bi abun da yaron su ke so, da kuma jin gidan da take su ma masu kud'i ne hakan yasa basu tsaya wani bincike ba,
"Irin auren da nake so yara na suyi kenan" Cewar Daddy, Mummy tace "Shi ya dace da su ai, me ake da tsiya", "Wallahi babu, ko dan fita kunyar abokai ba zan yarda yarana su d'auko aure gidan talauci ba", Cewar Daddy, "Raini za su ja mana ai, zamanin nan k'warya ta bi k'warya kawai, hanyar jirgi daban na mota na daban", Daddy yace "Tabbas", "Allah ya kawo na su Batul haka", Daddy ya amsa da "Amin",
**********************
Jauhar ranar da ta cika sati d'aya, Baba direba yazo d'aukar ta, Yan' gidan su har waje suka mata rakiya, Ta tafi cike da kewar iyayen ta tun ba Gwaggo ba, haka ma ta bar Gwaggon da kewar ta,
Ana gab da magriba suka iso gidan, Yaran Yaya Deeja da gudu suka fito suna mata oyoyo, Ta rungume su kana suka shiga cikin gida,
"Mutan zazzau, amaryar jibi" Cewar Yaya Deeja cikin sigar zolaya, Murmushi tayi tace "Yaya ina wuni?", "Lafiya lau, Ya hanya?", "Alhamdulillah", "Kin baro Gwaggo da kewa", Tayi dariya tana wucewa d'aki,
Wayarta ta fito cikin jaka, ta turawa Jameel text sun iso, Kana ta shiga band'aki, ta watsa ruwa, Ta fito ta shafa oil perfumes masu k'amshi, ta saka turkey gown, wacce ta zauna d'as a jikin ta, Kwanciya tayi ta huce gajiya bata salla hakan yasa har akayi sallar magrib bata mik'e ba,
Ganin shiru Jameel bai yi replying message d'in ta ba, kuma bai kira ta ba, yasa ta kira sa, Call waiting yana ta waya da wata friend d'in shi Nussy tun suna secondary school, hira tayi dad'i bai ji shigowar kiran Jauhar ba, Wayar ta kashe ta ajiye gefe da tunanin ko wacce waya yake mai muhimmanci ce sosai shiyasa bai d'auki kiran ta ba,
Bayan kusan minti talatin da kiran ta, Suka gama waya da Nussy, Ganin text da kiran Jauhar yayi saurin dialing number ta,
Jauhar wacce bacci ya soma d'auka sam bata ji kiran nasa ba har ya tsinke, "OMG Allah yasa ba fushi tayi ba", Ya fad'a yana tashi tsaye, bakin wadrobe d'in sa yaje ya canza kaya, Riga armless ya saka da wando three quarter, Ya gyara gashin kan sa, Ya fesa turaruka kusan kala uku, Ya fito yana k'amshi,
Mota ya shiga zuwa gidan su Jauhar, sam baya son tana fushi da shi, yana gudun rasa ta matsayin matar sa dan ta had'a duk wasu qualities da yake so wurin mace, Yana ganin kiran Meenal na shigowa yak'i d'auka, baya son taja sa da hira,
Meenal ganin bai d'auka ba, ta ajiye wayar gefe tana jin zuciyar ta na zafi dan tuni ta raya yana tare da Jauhar ne, Tun ranar da ta gano yana da budurwa take k'ok'arin cusa kan ta wurin sa, da shigo masa da sababbin salo da kisisina, dan ta d'auki alwashin cire Jauhar a zuciyar sa, tayi nata sabon dashen.
**********************
Jameel wayar Jauhar ya sake kira da addu'ar Allah yasa ta d'auka, Yaci sa'a yana kira cikin bacci taji kiran ta d'auka, "Nazo ina guest falo", "Ok" Ta fad'a tana kashe wayar, sai da ta sake sabon shiri ta fito.
"Naji sanyi da natsuwa a zuciya ta wanda na kwana biyu ban ji ba, saboda rashin tozali da kyakkyawar fuskar ki", Jameel ya fad'a yana bin ta kallo mai cike da so, "Zuciya ta a kullum cikin bugawa take na bege da kewar ka, ganin ka yanzu ya sa ta samu cikakkiyar natsuwa", Yayi murmushi yace "Sai dai naga ki dan' yi bak'i kuma kin rame da alama zaria bata amshe ki ba", "Gashi tun zuwa na ban yi wani aiki na wahala da zai saka ni canji ba", "Kin san fah fatar ki kalar yan' hutu ce, rashin cin abinci mai kyau da shiga ac kad'ai zai iya a samu sauyi a fatar ki", Maganar tasa taci ta bambamra k'wai, Tace "In dai abinci ne bani da matsalar hakan, sai dai Ac kuma ba na jin zai zama illa ga fata ta duba da Ac ma bai cika ba da lafiya ba", Murmushin gefen baki yayi yace "Haka dai kika ce, amma bara kiga kwana biyu zaki dawo normal, sai ma mun yi aure zaki ga chanji sosai a tare da fatar ki, dan ba k'aramin hutu zaki samu ba, ga uwa uba mu'amalar aure itama tana k'ara lafiya",
Nauyin zancen nasa taji hakan yasa ta basar da cewa "Tun zuwa na Zaria ko sau d'aya baka tab'a cewa na ba ka Gwaggo ku gaisa ba, haka ban tab'a ji an ce ka kira Bappa ba", "Ban da abun ki Babyn Jameel ko fah aure nan ba'a yi balle na soma gaisuwar surukai", "Ai ba sai anyi aure ba, in dai kana neman yarinya ya kamata kana gaishe da iyayen ta time to time", "Ok naji, yanzu dai fad'a mun irin missing d'ina da kika yi", Ya k'arasa yana jifanta da kallo cikin k'wayar idon ta, lokaci d'aya ya saukar mata da kasala had'i da zazzafar k'aunar sa, "Ke nake saurare babyna", "Baki yayi kad'an wurin furta kewar ka da nayi, kwanaki bakwai da nayi ba tare da na gan ka tamkar watanni bakwai ne a wurina, idanu na kullum cikin kwad'aituwa su ke da son ganin ka", Hannun ta taji ya kamo, karon farko tsawon shekara d'aya da had'uwar su yayi hakan.......
OUM MUHRIZ