Mugun gani

Chapter 10

by @sadiyanasir



Jiki na Rawa Manu ya mike ya nufi dakin shi, Juyowa Sadiq yayi gefen da Ammie take, gaba daya idanuwanta sun kada sunyi jazur "Kiyi hakuri Ammie insha Allah komai zai gyaru, Mu gode wa Allah da Abin baiyi nisaba, Ammie irin Rayuwar da Ake fama dashi kenan Ako ina, Musamman idan Yara suka hadu da gurbatattun Abokai.


Ki kwantar da hankalinki insha Allah Doctor's zasu shawo kan Matsalar ba tare da Ankai Ruwa rana ba"


"Sadiq dole na zubda hawaye! A lokacin da Manu ya kamata yayi hankali yasan Mutuncin Kanshi! A lokacin ne kuma zai koma Ruwa, Shiba Karatun ba shiba Sana'ar ba, Amma Ubangiji yana gani, bakuma zan gushe dayin Addu'a ba Allah ya shiryamin ku gaba daya"


"Ameen ya rabbi Ammie, ya kamata kije ki kwanta ki huta, kinga dare ta tsala"

"Hakane Sadiq, mikewa tayi, To saida safe insha Allah zamuyi Maganar Haneepha" 


"Ba komai Ammie Allah yakaimu da Rai" sai da yaga shigar Ummi daki kafin ya dau Abinda zai dauka ya nufi 'Dakin shi, Wayarshi ya dauko, kama Kai yayi ganin tarin Miss calls kusan rabi da kwata ta Sadiya ce, cike da zumudi ya dauka yakara kiran Number, kusan sau Uku yana kira bata daukaba "Allah Sarki Honney Allah ya baki lafiya, na tabbata kinyi barci A wannan lokaci"


Har ya danna kiran Number Zuby da yaga miss call dinta sai kuma ya fasa, tsaki yayi ya haye gado, mintuna kadan Barci mai dadi yayi Awon gaba dashi.


Washe gari da safe bayan sun karya ya kada Kan Manu sukayi Asibiti, Sosai Doctor yayi bin cike sannan ya basu Magani da shawarwari da idan Manu yayi Anfani dashi zai sami maganin matsalarshi, sosai Sadiq da Doctor suka ja mishi kunne tare da sanar dashi illar shan Miyagun Kwayoyi, sai wajen karfe Sha_daya kafin suka dawo Gida.


Parking din Motor yayi tare da kiran Sunan Manu da Kakkausar Murya "Kana jina ko? Wallahi wannan ya zama karo na farko da Karshe da zanzo garinnan na sami Mummunar labari Akanka, wai kai bakasan ka girma bane? Akwai Matasa kamanka wanda yanzu haka suke da Iyalai fa, to wallahi ya kamata kasan Kagirma.


Ka sake jiki baka daga Goma ya zama Ashirin, takamarka wai kayi Deploma, Aikin da ba'a samu yanzu, Gaka Gabjeje mai Karfi A jika Amma ba zaka mori jikin kaba, ka zauna kana biyewa Yaran da suke da Gata, ta kamarka komai ina yimaka ko? to wallahi ka farga na rantse da Allah.


Muna shiga Gida ka gaggauta neman Gafarar Ammie, wallahi idan ka Mutu A haka ina sanar dakai babu Abinda zai hana A jefaka A wuta, rashin sanin Girman Mahaifiya A gareka shiyasa kake sakaci da Al'amarin, to wallahi kaji tsoron Allah na sake fadama Wawa kawai"


"Kayi hakuri Yaya Insha Allah zan gyara, ba zaka sake samuna da laifi Makamancin wannan ba, nayi maka Alkawari, Batun sana'a kuma insha Allah zan koma wajen Babba mai gyaran Machine! dama can ninaki"


"Yauwa ko kaifa Kanina, da wannan sana'ar da kake Rainawa zakana faranta wa Mahaifiyarka fiye da yanda baka zato, kuma Ubangiji yayita sa maka Albarka kenan, Allah yasa Mudace, wuce muje ko" Fita sukayi A Motar suka nufi cikin Gidan.

 

A daki suka sami Ammie, har Qasa Manu ya durkusa "Dun Allah Ammie kiyi hakuri kiyafeni Abinda nayi miki, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, wancan dinma sharrin shaidan ne, wallahi bazan sake mu'amala da David ba, nayi miki Alkawari, kiyafemun Kunci da takaici dana sakaki Dun Allah" Kuka ya fashe dashi Sosai.


"Ba komai Manu ina kan yi maka Addu'a Allah ya Ganar dakai, hakika nashiga taskun Rayuwa, da tsananin bacin Rai, na ganin irin Rayuwar daka 'Dauka wa Kanka, Amma Ance mai nema baya Rasawa, na tabbata Akwana A tashi Ubangiji zai Amsamin Addu'ata, Allah ya shiryeka.


Abu na gaba, Dun Allah ka rike Maraicinka Manu, kaji tsoron Allah, kana tuna duniya ba'a tabbata cikinta, Yau kayi Abu mai kyau ma ya kakare bare kuma? to yakamata kana tunani"


"Insha Allah Ammie nayi miki Alkawari, kuma zakiga canji daga yanzu"


"Masha Allah naji dadin jin haka Allah ya maka Albarka"


"Ameen suka Amsa gaba daya, Magani Sadiq ya miko mishi "gashi kaje dashi idan kasha don kanka in kuma kaki shikenan, Shi duniya Ai tafi Gabaruwa iya Gima, Allah ya shiryeka" karba yayi "nagode Yaya" ficewa yayi ya koma 'Dakin shi cike da Nadamar Abinda ya faru dashi.


Zama Sadiq yayi gefen Ammie tare da Kallonta "Ammie kin bukaci ganina Akan Maganar Haneepha yanzu ya kike So Ayi da zancen?"


"Eh to Sadiq ya kamata kaje ka sanar wa Baffanku, yasan Abinda Ake ciki, ya baka Rana da Yaron nan zaije wajensu Gaisuwa, tunda Allah yasa sun dai_daita kansu shikenan, fatan da zamuyi Allah ya basu zaman lafiya"


"Alright babu matsala insha Allah daza ran nabar Nan can Bayan Fadar zan wuce ko zan sami Baffa lamido A Gida".


"Shikenan ba matsala, ka tabbatar komai ya tafi dai_dai Sadiq, sai dazu na Bude sakon dake cikin bocket, daga inane haka?" Murmushi Sadiq yayi Ammie daga wajen Sadiya ce tace in kawo wa Ammie! kuma ince tana gaisheki"


Murmushi Ammie tayi "Masha Allah gaskiya Nagode, Allah yayi Albarka! Nikan Sadiq tunda kun fahimci juna da Yarinyar nan meye zai hana A fara zancen Auren nan, nifa bana son dogon nema"


"Wallahi Ammie Matsalar ba daga ni bane, kin san bata da koshin lafiya, to kullum tunanin Iyayenta kar suyi nisa da ita, Amma kafin nazo din nan mun sake maganar da ita, tacemin zatayi nazari kuma insha Allah komai zai zo cikin sauki, nidai Addu'arki nake nema Ammie"


"Allah Sarki Sadiq kullum ina yimaka Addu'a Ubangiji ya hadaka da Abokiyar zama ta gari"


"Ameen ya rabbi Ammie, banji duriyar Haneep ba"


"Kamance yau Akwai Makaranta, sai karfe Biyu zasu tashi"


"Ok hakane na mance, ni barin wuce wajen Baffa Lamido daga nan zanyi Gidan Jaddi musha hira, Nasan yanzu haka tana tsumayena, don nabi wajenta kafin na shigo Gida"


"Allah Sarki! idan kaje kace ina gaisheta ko" Mikewa yayi ya dau Makullin Motor "Za taji insha Allah" Yana fita Kai tsaye Bayan Fada ya nufa, A kofar Gida ya sami Baffa Lamido yana tsaye shida wani, da Alama Abokin kasuwanci ne, durkusawa yayi har Kasa ya gaidasu.


"Sannu Sadiq Allah yamaka Albarka saukan yaushe?" sosa kai yayi "Ameen Baffa jiya nazo"


"Ato masha Allah ina ce kowa lafiya ko? ya Aikin kuma?"


"Alhmdullah Baffa lafiya kalau, barin shiga na jiraka nazo wajen kane"


"Eyya to bakomai gani shigowa insha Allah" cikin Gidan ya nufa! Nan yagaida Matan Baffan nashi sannan ya zauna A Palonshi yana dakon jiran shi, bai dau lokaci ba yashigo Gidan.


Sake sabon gaisuwa sukayi sannan Baffa ya dubi Sadiq "Ina jinka Allah dai yasa lafiya"


"Alhmdullah Baffa, dama na zone Akan zancen Haneepha! Akwai wani Yaro dake zuwa wajenta, toya matsa Akan yana so ya turo Magabatansa Ayi magana, shiyasa nazo na sanar dakai domin Asan Abinyi"


"Kai Masha Allah Abu yayi kyau, inace Kasan Yaron? kuma kayi bincike Akansa"


"Eh Baffa, Yaro Herwa_gana ne, kuma Mahaifinsa sanannen Mutum ne, Batun Hali gaskiya bayi da Matsala, Amma sanin dai_dai sai Ubangiji"


"To masha Allah hakan yayi, nidai daga wajena babu matsala idan sun shirya ko Gobe suzo, Allah ya sanya Alkairi"


"Ameen ya rabbi Baffa"


"Kai kuma naka sai yaushe ne? zaman bashi da Anfani Sadiq, kana da Aiki ka sami rufin Asiri to Abinda ya kamace ka Ajiye iyali"


Sunkuyar dakai yayi Qasa "hakane Baffa! insha Allah nan bada jimawaba zan fito da matar Aure"


"Yauwa Yaro shine magana" sun jima suna hira kafin Sadiq ya mike, kudi ya ciro masu dama ya Ajiye wa Baffa, sosai yayi godiya tare dasa masa Albarka.


Yana barin wajen ya nufi wajen Jaddi, tana zaune tayi mishi kunun tsamiya tana jiran shi, cike da So da kauna ta tarbeshi "Sannu da zuwa Maigidan" kama hanunta yayi suka karisa kujeran.


"Sannu Jaddi, da fatan kina lafiya?"


"Lafiya lau! Sadiq shine baka zo da wuri ba, dazu kawunka yazo nake sanar dashi kazo, Gashi nayi maka kunun tsamiya tun dazu"


"Wallahi Jaddi nadan fita da safe ne ko Gida banjeba, batun jikarki ce ta samu Mijin Aure shine naje sanar wa Baffanmu Akan za'azo neman Aure"


Tafa hanu Jaddi tayi "kai nayi murma matuka Sadiq, Allah ya nuna mana, ya kamata Ayi tare da naka, ina so naga na tara zuriya tunda ni Allah bai bani da yawa ba"


"Huhm Jaddi kenan, to ba gashi Biyu kyautar Ubangiji da kika samu sai tara miki zuriya sukeyi ba, Ammie yaranta Hudu, kawu Hassan Yaran shi Shida, tome kika rasa? gashi kuma suna kan Aurar da Yaransu suna kan haihuwa, kinga 'Yan biyu sun jawo miki zuriya da Yawa"


Daga hanu Jaddi tayi sama "Allah nagode maka, Kwarai kuwa Sadiq ina Alfahari da hakan, Allah ya Albarkaci zuriyata Alfarman Manzo S.A.W"


"Ameen ya rabbi" Kichen ya shiga ya dauko kunun tsamiyar ya dawo gefenta ya zauna.


"Kinga Anfanin Billy kenan, kin kama kin koreta, da yanzu ita zata kawomin, ke dai Allah ya shiryeki Jaddi" 


"Ungo naka nace, Ancema ba zata dawo bane? ko An fadama Aiki yana damuna ne?"


"Allah ya baki hakuri me yayi zafi? daga fadin gaskiya, yanzu dai ba wannan ba, wayar shi ya dauko ya kira number Sadiya, dauka tayi tare da turo baki kamar yana ganinta "Baby wato kamance dani yau ko? Miss call nawa nayi maka kashareni, sai yanzu da Rana tsaka zaka nemeni?"


"Kiyi hakuri Honney zanyi miki bayanin meye ya tsayar dani kigafarceni, yanzu ga Jaddi ku gaisa" Mika mata wayar yayi "wato har wani horn Ake ce miki? kinbi kin rikemin Mijina, gashi nace ya kawoki A samu Ayi Auren sai shuru"


Dariya Sadiya tayi "karki damu Jaddi insha Allah kamar yanzu ne, kiyita mana Addu'ah"


"Ina kanyi Sadiya Allah ya tabbatar mana da Alkairi" sun kai minti Uku suna hiran barkwanci kafin sukayi Sallama.


Nan sukaciga da hira shida Jaddi, A unguwar yayi Sallar Azahar da la'asar sannan ya mata sallama ya fito, sai da yayi nisa da tafiya kafin yayi parking A gefen Hanya, wayarshi ya dauko ganin Ana kira, tsaki yayi ya kara A kunne " Kaifa Dan iska ne wallahi, ba zaka kira Mutum ku gaisa haka kawai ba sai Akan zancen Mata, yanzu meye zubyn tace maka Babanta?"


Dariya Khalil yayi "ni kenan bani da zance saita zuby, A nawa kenan zatana biyana ina yimata fadanci, na jika shuru ne kawai nace barin kira mu gaisa, dazu naje Bank dinku baka nan, shine nace barin ta baka A waya"


"Sorry wallahi gani A Gombe, nazo ganin gida Amma Monday zan dawo kayi hakuri"


"Alrigt ba komai karka damu, yanzu ya 'Yan_Matan naka suke?" tsaki Sadiq yayi "Dan iska ba zaka canza haliba wallahi, kaga zan kiraka Anjima ina tuki"


Dariya Khalil yayi "Shikenan ba matsaka saina jika Angon Zuby" kashe wayar yayi baice dashi komaiba, Watsap dinshi ya shiga domin yaga ko Masoyiyar shi tabar mishi sakon Masoya, Murmushi yayi ganin Abinda yake zato hakane.


Duba sakon yarin kayi yana dariya yana Mayar mata cike da kaunarta A zuciya, sai da yagama kafin ya shiga Number Zuby, Fitsararrun Pictures ya fara Artabu dasu, A hankali suka fara budewa.


"Oh my God ya Ambata A fili, ganin zuby tana neman sashi ya rasa lissafinshi, gashi yana wata Uwa Duniya, take gumi ya fara karyo mishi, idanunshi Akan Pictures din! yana karewa Kirjinta Kallo, tuni yafara rasa tunaninshi, ganin wani Lalataccen Video data turo mishi, Numberta yakira ringin daya ta dauka.


Cikin Murya irinta yaudara ta soma Magana...




 Sadiya Nasir Dan