Mugun gani

Chapter 11

by @sadiyanasir



"Haba Sweet, nakira wayarka har na gaji baka daukaba, pls karinka tausaya wa Zuciya ta mana? ina son kasancewa dakai fiye da yanda kake zato Sweet, Bazan iya misalta maka irin tsananin missing dinka dana keyi ba Sweet"


"Zuby... ya Ambata Murya A shake.

Na'am ta Amsa da wata irin firgitacciyar Muryar da Sai da Sadiq ya furzar da wata iska mai zafi " gani A Gombe Zuby, gashi munyi nisa da Juna, ina cikin yanayin da nake Bukatar Taimakonki A Yanzu, duk wata kan tsiya kin sani Zuby, gashi kinsa Arba da Abinda ya rikitamin tunani cikin Sakonki ta watsap"


"Woow Sweet... to meye A ciki? Inhar kana da bukatar ganina A Yau! Aiba Abin daga hankali bane, Gombe da Bauchi Ai babu nisa, yanzu sai na hau Motor na taho, Kaga zamu kwana muna Faranta wa Juna, Nida Kai duk mu sami Nutsuwa"


"Huhm Zuby kenan, duk Girmar bukatar da nake dashi A gareki ba xan iya cewa kizo Gombe ba, karfa ki manta Mahaifata kenan, Babban Al'amarin ma idan kinzo na Ajiyeki Aina? kin san ko A Bauchi bana harkar Hottel! bare Nan Gombe"


"Oh Sweet yanzu kana nufin haka zamu hakura da Juna Alhali dukanmu muna da Muradin Juna? Haba Sweet kayi Nazari mana"


"Zuby kenan, Ni dai yanzu Abinda nake bukata dake, ko ince Alfarmar da zakimin, Kiyi wa Allah kisan Hikimar da zakimin na samu Nutsuwa A halin da nake ciki, Zuby na sanki babu wasa Cikin hidimarki, kiyi Abinda zai kwantar min da hankali kafin na dawo na fanshe wannan Muguntar da kikamin yau"


Dariya Sosai Zuby tayi irinta Yan tasha "An gama Sweet, ka bani 10mnt zan koma d'aki sai muyi Video Call, Tunda ka yarda nice Nutsuwarka toka gama yimin komai, kuma zakayi Alfahari da Sabon Salon da zaka samu A Yau"


"Okey... yace tare da kashe wayar ya daurab Kanshi saman steary, tare da dafa cikin shiy dake juya mishi Ahankali. Bai wani dauki lokaci ba kiran Zuby ya sake shigowa wayar, jiki na Rawa ya dauka tare da Ajiyewa yanda zai na ganinta cikin sauki, sun dau Akalla kusan Hour Guda suna saba wa Ubangiji (Wa'iyazu Billah) kafin Sadiq ya dawo cikin Nutsuwarshi, Ajiyar Zuciya ya sauke mai karfi tare da Godewa Zuby bisa taimakon da tayi.


Murmushi tayi "Bakomai Sweet, na fada maka kai nawa ne, baka da shamaki dani, A duk lokacin da kake da muradina 'Kofa A bude take, yanzu ka samu ka karasa Gida! sai munyi magana Anjima"


"Shikenan Zuby zakiga Tukuici Anjima! Nagode sosai" Kashe wayar yayi tare da Jingina A jikin kujera, lumshe idanu yayi, take Zuciyar shi tafara tunano mishi Sahibar Ranshi Sady, tare da tsine wa Zuciyar shi dake biye wa Zuby, shi kanshi yasan baya kyauta wa Sady, Amma rashin yin Auren su shiya janyo mishi shiga wannan Hali, wani iska mai zafi ya furzar yayi Key wa Motar ya dau hanya.


Bayan Sallah Isha'i kamar kullum suna zaune suna hira shida Ammie da Yara ya dubi Hanifa "Dazu naje na sami Baffa Lamido Akan Maganarki da Yaron dake zuwa wajenki, Ina so kiyi mishi Magana kice A Gidanku Ance idan sun shirya suzo zanyi musu jagora zuwa wajen Baffan A tsadai Rana kafin nakoma Bauchi, ba naso nakoma ba tare dana kammala da wannan matsalarba"


Murmushi Hanifa tayi ba tace komaiba, Ammie ce ta dubeshi "Shikenan bakomai Sadiq, za'ayi yanda kake so, dama Yaro mu yake jira, tunda Kullum shike Magana Akai, Allah yasa zamu kai lokacin Muna Raye"


"Ameen ya Rabbil Alamina Ammie na, Sadiq ya Amsa tare da Kallon Hanifa, shikenan jeki dama Abinda yasa na kiraki kenan, Yauwa Ina Manu? yau dinma ya fita ne?"


"Aa Yaya Manu yana daki, Zazzabi ke damunshi tunda Yamma"

"Eyya Allah ya sawaka, Maganin da Aka bashi ne, Insha Allah A hankali zai war_ware Matukar yabi Abinda Likita yace, Allah kuma ya shirya mana shi" Ameen suka Amsa gaba daya.


Sai da ya cika cikin shi tam da Abinci suka taba hiran Office da Ammie kafin yayi haramar zuwa Barci, lokacin karfe Tara, yana shiga daki yayi shirin Barci ya hau Katifarshi suka cigaba da Hira shida Sahibar Ranshi Sadiya.


'Bangaren su Fadila kuwa! washe Gari da hantsi suna zaune ita da Ummi suna hira ta dauko mata Maganar Muktar "Fadila baki bani labari ya kukayi da bakon naki ba?" Murmushi Fadila tayi ta sunkuyar da Kanta Kasa "Ummi cewa yayi yana So ya Aure ni idan kun Amince, shine nace mishi ni Karatu zani yanzu haka, Amma yayi hakuri bazan iya ce mishi komai game da Bukatarshi ba har sai nazo nayi shawari da Gida"


"To in banda ke Fadila karatu Ai baya hana Aure, suma Mazan sun gane yanzu Ilimi shine Gishirin Rayuwa"

 "Ummi yana da Mata kuma ba Yaro bane fa, kinga nayi Qarama da zama da Kishiya A shekaru na, ni wallahi tsoron da nakeyi kenan" karasa Maganar tayi tare da Turo Baki.


Ajiyar zuciya Ummi ta sauke "Bakomai Fadila duk wanda yace Allah to ya gama komai, bazan zafafa wannan Al'amari ba, domin bamu san meye Ubangiji ya shirya Akaiba, nima kaina ina tausayin Qaramar Yarinya dake Ace zaki zauna da kishiya, kuma Yaranshi nawa?"


"Ummi Har yanzu Allah bai bashi haihuwa ba, sun dau shekaru Akallah Goma sha... da Matarshi Amma shuru" Kallonta Sosai Ummi tayi "toke kina jin zaki iya Auren shi? ya fada miki matsalar daga ina take?"


"Aa Ummi kawai iya Abinda yace dani kenan"


"Shikenan ba laifi kiyita neman zabin Allah, Kuma A hankali ki tambayashi sun taba zuwa Asibiti sabida wannan Matsalar? Allah ya wuce mana gaba"


"Amin ya rabbi Ummi nah... A cikin kwana Hudu Abba ya gama duk wasu cike_cike daya kamata Yayi Akan Fitar Fadila Kasar Waje, wannan Abu ba karamin dadi yayi wa Fadila ba, bata dauka Abba zai daukaki Abin haka ba, duba da yanda taga yadau zafi daga Farko.


Waya kuwa sosai sukeyi ita da Muktar, yanda yake mata Soyayya Abin har kunya yake bata, Musamman idan taga Photon shi yanda yake ba Yaro ba, wani zubin har Kukan shagwaba yake yimata Abin dai sai wanda yaji... yau suna waya dashi! Muktar ya dauko mata wata Magana.


"Maryama ta ina so kiyimin wata Alfarma mana Dun Allah" Murmushi tayi "bakomai Yaya Muktar ina sauraronka"


"Yauwa Allah yayi miki Albarka, kinga saura Kwana 10 kibar Kasar nan, Maryama ta shekara Uku zakiyi kafin ki dawo Nigeria, Dun Allah ki bani dama nazo na sami Abba Akan Maganata dake, idan ba hakaba Fadila zan shiga wani irin yanayi, Zuciya ta tana sakamin kamar Rasaki zabyi, Dun Allah kinji?


Shuru tayi kamar wacce Kwai ya fashewa A ciki, kinyi shuru ba kice komaiba?"


"Yaya Muktar wallahi nima ina son haka, Amma tunanin da nake shine idan har ka shigo da wannan Maganar Abba bazai barni naje karatun ba, cewa zaiyi Aure zai yimin, kaga kenan na rasa wani farin ciki dana jima ina shiryawa"


"Maryam Fadila kenan, Maganar da zanzo muyi da Abba babu Abinda zaisa ya shafi Karatun ki, nifa ba Yaro bane, Fadila idan ban so Abinda zai saki Farin_ciki ba meye zanso? Ai cikar Burinki shine mini zaman lafiya da Kwanciyar hankali, nidai kawai ina so Abba yasan da zamata, kuma Ummi tasan da gaske nakeyi, please Fadila ki duba zance na kinji?"


"Huhm Yaya Muktar kenan, ba komai zamu zanta da Ummi Akan wannan Maganar, duk yanda mukayi da ita zuwa dare zan kiraka A waya in shaida Maka Anjima"


"Yauwa Amarya ta ina godiya da kulawa" haka suka cigaba da hira cike da Kaunar Juna.


Bayan sun kammala wayar, mikewa tayi domin taje ta isar wa Ummi sakon Muktar, A Harabar Gidan ta sameta ita da Manager ta Resturant dinta, da Alama suna zantawa Akan kudi ne, ganin haka yasa takoma Palo zaman jiran shigowarta, takai Akallah 40mnt tana zaune kafin Ummi tayi Sallama ta shigo "Fadila hutawa kikeyi ne?" murmushi tadanyi "Eh Ummi, nemanki nake dana leka waje sai naga kinyi bako"


"To Allah yasa dai lafiya?

Zama Ummin tayi tare da fuskantar fuskar Fadilan, Ina jinki" Saita nutsuwarta tayi ta dubi Ummi "Dama Muktar ne ya rokeni wata Alfarma, shine nace yayi hakuri idan nayi shawari dake zan sanar mishi zuwa Dare, Alfarmar da Muktar ya roka A gareta shita zai yana wa Ummi, bata rage koda Kalma daya ba cikin Maganar da sukayi.


Murmushi Ummi tayi "to Ai wannan ba wani Abu bane Fadila, Muktar da gaskiya yake sonki shiyasa komai yakeyi yanda Addini ya tanadar, bakomai kice mishi ya sami Abban naku, Amma koda wasa karya Gwada cewar da Yawunki A cikin Maganar, idan kin fada mishi haka yasan meye nufina"


"To shikenan Ummi, Nikan ina Aunty na? yau fa ban sata cikin idanuwata ba"


"To kina daki kina kulle sai ki shafe 2hours! ta ina zaku hadu? Gobe Sadiq din nata xai dawo, shine taje Ayimata Kunshi" kama baki Fadila tayi "Iko Sai Allah, har dasu Kunshi? lalle da gaske takeyi Ummi, ni damuwata! yanda Aunty Sady take Kaunar wannan Sadiq din, Allah yasa haka shima yake Sonta, nidai Addu'a nakeyi kenan Har A Sallah, Allah yasa ya sota yanda take kaunarshi dinnan, kar yazo ya Aure mana Aunty gashi bata da lafiya yaje yasa ta A jalala"


"Insha Allah zata sami farin ciki, Sadiq yana kaunar Sadiya domin ni shai dace, ya jima yana takurata Akan zancen Auren su, Abbanki kuma tausayinta yake, kamar yanda kike tunani, baya son Abinda zai taba lafiyarta, sabida shi yasan wahalar da muka sha tun Sadiya tana Yarinya, Amma dole daga karshe hakuri zaiyi tunda ba tabbata za tayi A Gida ba, dole itama zata so taga Jininta suna yawo A tsakar Gida"


"Hakane Ummi! to Allah ya kara mata lafiya, yasa Sadiq din yazama sanyin idaniya A gareta, zaton da Nake yi mishi Allah yasa ya bani kunya"


"Amin ya Rabbil Alamina Fadila ta"


Sai yamma liss kafin Sadiya ta dawo, gaba daya idan ka ganta ta jigata, Jakarta ta Ajiye A kan kujera, ita kuma ta Shimfida A Kan Capet sai barci, daga Fadila har Ummi babu wanda yaji motsin shigowarta, wajen karfe Shida Abba ya shigo, jin karar Motar shi yasa Ummi Mikewa da sauri domin tarbo shi.


Kama baki tayi ganin Sadiya A shimfide A kasa sai sharar Barci take "Yanzu dama Yarinyar nan ta dawo? nayita kiran wayarta baya shiga? duk tabi ta tashi hankali na, tunanina idan Abbansu ya tambayeni ince meye?" Allah ya kyauta ta Ambata ta wuce Abinta...


 


 SADIYA NASIR DAN