Chapter 12
by @sadiyanasir
Ta 'bangaren Sadiq kuwa kamar yanda yayi Alkawari, sai da yaga komai ya kammala tsakanin Hanifa da Saurayinta, har Sadaki sun bayar tare ta tsayar da lokacin Aure nanda wata 5, kafin hankalinshi ya kwanta, 04:00pm ya kammala shiri tsaf ya dauko Jakarshi ya fito, A Palo ya sami Manu yana zaune hanunshi rike da Cup, Ganin Sadiq yasa yayi saurin mikewa fuska dauke da Murmushi.
"Barka Yaya har zaka wuce kenan?" zama yayi A daya daga cikin kujerun "Eh Manu insha Allah tafiya zanyi, Ina Ammie?"
"Ta shiga Wanka"
"Okey to yayi kyau. Manu... ya Ambata, dago ido yayi ya dubeshi, bai jira Amsar shiba ya cigaba da Magana, Manu ina so na jawo hankalin ka na kuma kara yi maka nasiha da kaji tsoron Allah, duk Abinda zakayi karka dubi idanun Jama'ah ka duba Mahaliccinka.
Kwana biyu da nayi A Garin nan har kiba kayi sabida kaurace wa Miyagun kwayoyi da kayi, to dun Allah kar daga bayan don baka ganin idona kaci gaba da sha, wallahi cutar da Kanka zaka yi, Ina so yanda kayi min Alkawari ka zama mai cikawa koda bayan idona"
"Insha Allah Yaya! naji kuma zaka sameni mai cika Alkawari ko bayan idonka bazan koma Shan Abinda na dai naba"
"Yauwa Manu Allah yayi maka Albarka" Ameen su kaji Muryar Ammie ta Amsa, Ashe tana bayansu basu saniba, duk maganar da sukayi A kunnenta ne, murmushi suka saki mata A tare, ita dinma mayar musu tayi ta zago ta zauna A gefen Manu.
"Kaji dai Abinda Yayan naka ya fada maka ko? gyara kayanka bai zamowa sauke muraba, Kuma duk Abinda kaga Yayi maka Soyayyace ta jawo haka, duk wanda kaga ya damu da Rayuwarka to Masoyinka ne, Allah ya muku Albarka, Ameen suka Amsa A tare. Sadiq har Anfito kenan? na dau ka fasa ne"
"Aa Ammie yanzu zan tafi, Ina so na wuce Gidan Jaddi inyi mata Sallama! Sai na kama hanya"
"Eyya Sadiq wato ba zaka bar tafiyar Dare ba? kai sam baka da lokacin hawa Hanya sai Yamma liss?"
"Ammie ba komai insha Allah lafiya zan isa, tafiyar tafimun dadi ne, ke dai kawai Addu'a zaki yimin Allah ya kaini lafiya" mikewa yayi ya dauki Jakarsa, Hanu Manu yasa ya karbeshi ya fita waje "Sadiq".Ammie ta Ambata, da wowa yayi ya zauna ya fuskance ta "Na'am Ammie".
"Sadiq zaka kai tsawon wani lokaci kafin ka sake zuwa ?"
"Eh to Ammie gaskiya zan kai kwana 30 Nan gaba"
"Yauwa to Dun Allah Sadiq ku sake zan tawa da Yarinyar nan Sadiya Akan Maganar Auren ku, ina so ka dawomin da magana mai dadi, ina so idan lokacin bikin Hanifa yayi ya zama 'Yan_Uwana su koma da Ranar da zasu dawo domin naka"
"Huhm shikenan Ammie na! insha Allah nayi miki Alkawari, Allah ya tabbatar mana da Alkairi"
"Ameen ya rabbi, shikenan ka tashi lokaci yana kara kurewa, Allah ya tsare maka hanya ya kuma Albarkace A duk inda kake"
"Ameen ya rabbil Alamina Ammie" har kofa ta rakoshi, ita da Manu haka suka cigaba da daga mishi hanu harya kule A layin.
Jaddi tana zaune tana Karatun Alqur'ani Sadiq yayi sallama ya shigo, Billy dake tsaye tana goge TV! ta Amsa fuska dauke da Murmushi "Ah_Ah Qanwata idanunki kenan?" dan sunkuyar da kai Qasa tayi "barka da zuwa Yaya Sadiq" zama yayi A gefen Jaddi "yauwa barka Billy kwana biyu ya karatu?"
"Alhmdullah Yaya Sadiq Ana tabawa" to masha Allah Ubangiji ya bada sa'ah"
"Ameen". ta Amsa ta wuce Kichen ta dauko mishi Ruwan sanyi, Jaddi kuwa tana kai Aya ta rufe Alqur'ani ta juyo ta dubeshi "Mai Gidan ya naganka da jaka kuma?"
"Jaddi zan koma wajen Aiki shine nazo kiyi min Addu'a"
"Wato Sadiq tafiyar Dare kai kake So ne? idan zaka shigo Garin nan da Dare haka zalika in zaka koma? to Allah ya kyauta" kama hanunta yayi ya daura A fuskarshi "Haba Jaddi na, insha Allah lafiya kalau zan isa"
"To shikenan Ubangiji ya kaika Lafiya" Mkewa yayi ya dauki Jakarshi ya Rataya "Na barki lafiya Jaddi! ba kice na gayar da Kishiyarki taki ba?" Hararanshi tayi "kaji dashi dai Angon Karya, kullum sai cika baki Ankasa cimma gashi"
Kada Kai kawai yayi ya fice A Gidan, sai dai ya dau Hanya sosai kafin ya kira Sadiya A waya, Ringin din wayarta shiya tasheta daga barcin Gajiyar da take, Murya A shake ta dauka "Baby ya kake?"
Parking din Motor yayi A gefen Hanya jin Muryar Sadiya ba A yanda yayi zato ba "Diyatee lafiya kalau nake, baki da lafiya ne naji muryarki haka?" gyara zama tayi "lafiya lau Baby barci nake shi yasa kaji haka"
"Eyya banji dadi dana katse miki barci ba sorry Diyatee"
"Laa Yaya Sadiq Ai lokacin Sallah ta gabato ya zama dole na tashi"
"Hakane to ina hanya, kamar yanda nace miki zan taso yau, ina neman Addu'arki"
"Allah sarki Allah ya dawo dakai lafiya, ina yi maka fatan Alkairi"
"Nagode Diyatee, Gobe insha Allah da safe kafin na wuce Office zan shigo na dubaki, kinga zanyi shigowar Dare babu hali na zo"
"Hakane to babu laifi Allah yakaimu goben saika iso"
"Ameen ya Rabbi Diyatee Ina sonki ina Alfahari dake" kashe wayar sukayi gaba daya kowanne fuskarsa dauke da Murmushi.
Mikewa tayi ta shiga daki ta gabatar da Sallar Magarib, Fadila ce ta bude dakin da Sallama ta shigo, zama tayi gefen Gado "Barka Aunty na kin samu tashi? dazu na duba Palo na ganki A shimfide kina barci"
"Na tashi Qanwata ya kike kema?"
"Lafiya lau, Aunty Sadi ban san wani irin missing dinku zanyi idan nabar Qasarnan ba, Allah sai da Abin yazo gaf nake jin wani iri" nade Abin Sallar tayi ta hayo gadon ta dubi Fadila "Qanwata kenan, dama kewa ta zama dole dukan mu zamuyi, Amma karatun naki Akwai mahimmanci, dun Allah kar kije kisa damuwa A Ranki ki kasa Abinda ya kaiki"
"Insha Allahu Aunty Sady" hira suka cigaba dayi har Aka kira Sallar Isha'ih, fita Fadila tayi A dakin tayi nata dakin, Misscall Uku ta samu na Muktar, Murmushi tayi "Yaya Muktar kenan zumudi kenan?" Ta fada A fili gami da daukar Wayar ta kiran Number, kamar mai jira ya dauka "Haba Gimbiya Fadila ina kika shiga kinsa na fara zubda kwallah?" Dariya tayi "Yaya Muktar kenan"
"Wato ba zaki can zamin suna ba? Maryama haka zamuyi Auren kina cemin wani Yaya? gaskiya bazan Amince ba" kama baki tayi kamar yana ganinta "Ni Maryam, yanzu wani suna kake so na kiraka dashi?"
"Na baki Assignment daga nan zuwa Jibi ki nemo kinji?"
"To shikenan bakomai"
"Yauwa Maryamata ya Alkawarin mu? da fatan kinyi nazarin?" Zama tayi sosai "Yaya Muktar munyi Magana da Ummi tace babu matsala zaka iya tunkarar Abba, Amma dun Allah yaya Muktar karka sakani cikin Maganar kaji? kace ra'ayinka ne yasa kake so A tsayar da Magana! ni ban ma saniba" Dariya Muktar yayi "Haba Gimbiya Maryam sai kace ni Yaro? karki damu kinji bazanyi Abinda zai bata ranki ba kinji, ke dai kawai idan Abba ya tambayeki Muna tare Amsarki Eh, hakan shi zai saukaka Al'amarin"
"To shikenan bakomai Yaya Muktar" ina Aunty nah?"
"Lafiyanta kalau ina bakin hanya ban karasa Gidanba, na fiso ingama da Habibiyata tukun"
"Yaya Muktar kenan" hiransu suka cigaba dayi cike daso da Kauna har sai da Fadila taji kiran da Ummi take kwala mata kafin sukayi sallama da Muktar ta mike ta nufi waje.
Sadiq kuwa tun yana Inkil ya kira wayar Zuby, kusan 3 miss_calls kafin ta daga, murya A shake, da Alama tayi Mankas da kayan Maye "wayene kai?" ta Ambata, tsaki yayi "Mahaukaciya kinje kinsha Abinda ya dameki ko? ke kam ba zaki taba hankaliba Wawiya kina ina?"
'Dan murmushi tayi da Alama ta gane mai Maganar "ina Birnin Madina dazu na tafi" tsaki yayi ya kashe wayarshi, domin idan ya biye Zuby haka zata cigaba dayi mishi tanbele don tayi matukar Nisa, Ajiyar wayar yayi A gefe ya cigaba da Tuki, A kofar wani karamin Masallaci yayi parking ya fito! gamida daura Alola ya shiga domin sauke farali.
Ya jima A ciki yana lazimi yana shan iskan Fan, sai wajen karfe takwas da Rabi kafin ya fito daga cikin Masallaci, nanma Masu gadin Masallacin ne suke da bukatar Kullewa, yana shiga Motor ya kira Number Sadiya don ya shaida mata cewar ya iso, kusan 2miss_calls bata daga ba yasa ya tura mata sakon cewar ya iso gari.
Sai da ya biya ya siya Nama A kasuwar wunti kafin ya wuce Gida, A palo ya Ajiye Jakarshi ya jibgu Akan kujera yaci Naman shi ya koshi tam kafin ya mike ya nufi ciki don ya watsa Ruwa ko zai rage Gajiya, tun baiyi nisa da fara wanka ba yaji wayarshi tana ruri Alamar shigowar kira, sai da ya fito yasa kaya masu sauki ya dauki jakar systerm dinshi ya fito palo kafin ya dauki wayar.
Kiran Sadiya ya gani, Murmushi yayi ya kara bin kiran, suna zaune dasu Ummi A palo Abba yana musu hira kiran wayar Sadiq ya shigo, dan fakaitar idonsu tayi ta fice ta koma daki domin Amsawa, Murmushi Alhaji Abdul_salam yayi domin ya fahimci Saurayinta Sadiq ne ya Kira, duban Fadila yayi "Kije kice wa Auntyn naki idan ta idar da wayar tazo ina son ganinku gaba daya" mikewa Fadila tayi da sauri domin zuwa isar da sakon da Abba.
A zaune ta sameta A jikin Mirro tana wayarta cikin kwanciyar Hankali, haka kawai ta tsinci kanta da tsananin jin haushi, domin ta tabbata da wannan Sadiq din take waya, Allah ya gani sam Fadila bata kaunar Sadiya da Sadiq, Amma ya zatayi Abinda Auntyn nata take so kenan, ya zama dole ta goyi bayanta ko dan lalurar da take damunta, ganin wayar tasu bata da lokacin yankewa yasa tayi gyaran Murya.
"Aunty Sady idan kin gama wayar Abba yana kiranmu A palo, zanje daki ki yimin Magana idan kin gama" kad'a Kai Sadiya tayi Alamar to, jawo mata kofar tayi ta wuce dakinta ta zauna, tunani ta soma ko meye dalilin da yasa Abba yake kiransu Oho? ko dai Muktar ya sameshi ne Akan Maganar nan? ko kuma Akan maganar karatu ne? haka tayita saka da war_wara bata da wanda zai bata Amsar Tambayarta.
Sadiq kuwa tunda Fadila ta fara magana harta gama haka kawai yaji Gabanshi yana mummunar faduwa, shiyasa ya kadaita wayar dayi mata wayon taje taji kiran da Abba yake mata, sallama sukayi Akan sai da safe sabida ya gaji zaiyi barci, Ajiye wayar yayi A gefe ya kura wa Slim idanu, gaba daya kasala da faduwar gaba ne suke Addabarshi A lokaci guda.
Sadiya kuwa dakin Fadila ta nufa ta bude tana zaune tayi tagumi "Ke Fadila lafiyanki kuwa?" Ajiyar zuciya ta sauke "Lafiya kalau Aunty Sady meye kika gani?"
"Okey shikenan tunda lafiya muje ko na gama" mikewa tayi suka nufi palo cikin takun nustuwa, durkusawa sukayi A gaban Abba gamida sunkuyar da Kai.
Kallonsu yayi daya bayan daya yana mai cike da jin dadi da Allah ya hada mishi Kan yaranshi, Uwa Uba Ubangiji ya bashi Aron Rai suka girma A hanunshi ba tare dasun dandani tacin da Maraici ke dashi ba.
"Allah ya muku Albarka" kalmar data fara fitowa daga bakinshi kenan "Ameen suka Amsa gaba daya, Duban Sadiya yayi dakyau "Yar Gidan Abba ya jikin naki dai?" dariya tayi domin tana Kaunar wannan sunan da Abba yake kiranta dashi "da sauki Abba"
"To Alhmdullah, Hajiya Zali dake da iyalanki ina so ku bani Aron kunnuwarku domin nayi wata yar Magana daku, Dazu wani Bawan Allah ya sameni da Magana Akan yaga Fadila yana so kuma da Aure, ya fadamin ya samu damar da sukayi Magana har suka fahimci Juna, Amma Fadila ta gwada mishi Karatu ne A gabanta, nace mishi tabbas hakane Amma karatu baya hana Aure, matukar Ansamu Mijin.
Shin Fadila kinsan da wannan zancen?" Shuru tayi gaba daya zufa ta keto mata duk da sanyin da Dakin ke fitarwa, Ummi ce tayi caraf ta Amsa "Fadila ko shine Mutumin da yazo ranar nace miki ki fita?" Murya na Rawa tace Ehhh Ummi shine"
Murmushi Abban yayi "To ya rokeni Akan yana so ya turo Magabatan shi A tsayar da Magana idan Allah yasa Fadila Matarshi ce tana dawowa daga Makaranta Ayi biki, ya fadamin Allah bai bashi Haihuwa ba tsawon wasu shekaru Masu yawa, na kuma yi mishi Addu'a Allah ya bashi Masu Albarka.
To Fadila ina so ki nutsu nace mishi yazo Gida ku zanta da ganan zuwa Jibi, ki sani Aure ba Abune na wasa ba, idan hankalinki ya kwanta dashi ki sanar mishi dacewa ya turo iyayen nashi" To Fadila tace gamida kara sunkuyar da Kai.
"To 'Yar Gidan Abba ya muke ciki ne? dazu dai da Alama Surukin nawa ne ya kiraki A waya, to ina so inji ya kuke ciki dashi? idan kina Son shi basai kawai musha biki ba? koda nanda Wata Uku ne"
Rasssssss haka Fadila taji gabanta yayi wani Mummunar Sarawa...