Mugun gani

Chapter 14

by @sadiyanasir



Mayafi ta yafa dan karami Akan doguwar Rigarta ta fito, A Kichen ta samu Ummi da Fadila suna kokarin hada Breakfast, karasawa tayi ta durkusa "Barka da safiya Ummi da fatan kin tashi lafiya?"


"Alhmdullah Sadiya, ya karfin Jiki kuma?"


"Ummi Alhmdullah yanzu bana jin komai" Juyowa Fadila tayi "Barka da Safiya Aunty Sady! ya karfin Jiki?"


"Alhmdullah Qanwata jiki Akwai Sauki"


"Masha Allah Sadiya ina zuwa haka? naga kamar shirin fita kikayi?" 'Dan sunkuyar da Kai Kasa tayi "Ummi Sadiq ne yazo shine zanje wajenshi A waje" murmushi Ummi tayi toshikenan Adawo lafiya"


Fita tayi da sauri sabida karta bata mishi lokaci, Ummi ce ta dubi Fadila "Yaran nan Suna Kaunar Junansu Fadila, na tabbata Sadiya ta sanar mishi da zancen da Abbanku yayi jiya ne, shiyasa kikaga yayi sammako haka" Murmushi Fadila tayi "Ba Abin Mamaki bane Ummi, don Aunty Sady tana Girmama Soyayyar Sadiq dinnan"


"Hakane! Allah ya tabbatar Mana da Alkairin dake ciki"


"Ameen ya Rabbil Alamin Ummi".


Sadiq kuwa tun daga nesa ya hango Sadiya tana taku cikin Nutsuwa, gashi kayan Jikinta sun Amsheta "Masha Allah" Ya Ambata A fili, da Irin Baiwar da Ubangiji ya mishi! na samu Mace Kyakykyawa Mai hankali da Nutsuwa irin Sadiya, Idanuwarshi ya zuba Mata yana Mai tsananin Jin Dadi gami da Nishadi.


Cigaba da kare Mata Kallo kawai yake cike da So da Kauna. 


Sadiya kuwa irin Kallon da Sadiq yake Mata! yasa Gaba daya taji Qafafuwarta ba zawu iya daukarta ba, Hakan yasa ta tsaya Cak, domin ba zata iya cigaba da tafiyarba, gaba daya kunya ce ta lullubeta.


Sadiq Kuwa Ganin haka yasa ya saki wata Irin Murmushi! dashi Kadai yasan Ma'anarsa, take Beauty Point dinshi suka fara lotsawa A hankali, Nan danan Sirrin Kyawun da Ubangiji ya mishi suka Fara baiyana, Iska mai Sanyi ya furzar tare da Qarasawa inda take da Azama.


Durkusawa yayi A gabanta Idanunshi cikin Nata."Barka da Safiya ya Sahibal Khalbi! Kuma Amarya A Gidan Abubakar Sadiq Kasim, Hakika duk Wanda Ubangiji ya mishi Baiwa da Samunki Matsayin Abokiyar Rayuwa! to ba karamin Rahma yayi Mishi ba, ya zama dole ya kara gode Masa da wannan Ni'imar, Sadiya kin riga kin zama Ni, duk wani Abinda zanyi To kina Makale cikin Zuciya ta.


Mikewa yayi ya tsaya daf da Ita har yana iya jiyo Yanayin Numfashinta, Ajiyar Zuciya ya sauke tare da zaga yawa ta baya daf da Kunnuwarta, Cikin wata irin siga ya cigaba da Magana, Hakika Muryarki Kadai idan Naji takan Haifarmun da Farin ciki Mai yawa, Tabbas Ke Rayuwata ce Sadiya, kisa A Zuciyarki duk Rintsi duk Wuya kina Makale A Zuciya ta.


Ina Sonki Sadiya, Ina Sonki, Wannan Kalmar ba zata daina Fitowa daga Bakina ba har sai Ranar da Qasa ta danneni" Rufe idanu Sadiya tayi cike da Jin kunya ga wani Bakon Yanayi da take jin Kanta Lokaci Guda, Tabbas Irin Soyayyar da Sadiq yake Gwada mata ta daban ce.


Kuma Samun Dan Soyayya Mai bawa Soyayya Hakkinta yanda ya kamata Kamar Sadiq sai An tona Qasa.


Dawowa yayi ya tsaya A gabanta Fuskarshi dauke da Murmushi, Waya ya fito dashi cikin Aljihun shi yayi Dialling Number Ammie, Ta jima tana Ringin kafin ta dauka.


Cike da ladabi kamar wanda yake gabanta yace "Ammie na kin tashi lafiya? ya Gidan yasu Haneep?" daga bangarenta ta Amsa mishi da "lafiya kalau Sadiq ya Aikin dai? ko ba'a fita bane?"


"Aiki Alhmdullah Ammie na! yanzu na 'dau hanya! na tsaya Gidansu Sadiya zan dubata saina wuce"


"Ikon Allah da farar safiya haka Sadiq? ba zaka barta tayi Aikin Gida ba?"


"Ammie Albishir tayimin mai dadi yasa na kasa wucewa Office ba tare da nazo naganta kuma nakiraki A gabanta na shaida miki wannan Albishir da tayimin Mai Dadi, Na tabbata zakiyi farin ciki kamar yanda na kwana dashi Daren Jiya"


"Kai Ai ka iya tsara zance, ina jinka fadamin wani irin Albishir ce tayi maka haka?"


"Ammie zancen da mukayi dake kafin na dawo Bauchi, Abbanta jiya yace idan da Gaske nake ina da Niyyar bidar Aurenta ya bani dama, duk lokacin dana Shirya na Turo A tsayar da Magana , kinga kuwa labari ce mai dadi, kuma na Tabbata zai Faranta miki Rai"


Murmushi tayi "Tabbas Wannan Labarin tayimin Dadi, bazan Misalta maka irin Dadin da naji A yanzu ba, Zamanka Babu Mata yana damuna Sadiq, Ina tayaka Murna, Ubangiji yasa Muna Raye za'ayi, Allah yasa Abokiyar Arzikinka ce"


"Ameen ya Rabbil Alamina Ammie nah, Shiyasa na kasa Hakuri nayi Sammako don Nazo na ganta na kara jin Dadi"


"Kai dai Sadiq dad'i na dakai Baka jin kunyata, sabida idonka ya rufe da Soyayya har nima baza'a barni ba?"


Dariya yayi "Ammie kenan to Ai duk Duniya babu wacce ta cancanta taji mai yake damuna mai kyau ko Akasin haka bayan Ke, bani da Aminiya sama dake duk Duniyar nan, Ina Sonki Ammie"


Murmushi tayi cike da Jin dadi "Hakane Sadiq nima Ina sonka, Allah yayi Maka Albarka, ya karemun Kai daga Sharrin Mutum da Aljann"


"Ameen Ammie na, Nagode Miki saina dawo zan kiraki Mukarasa Magana"


"Shikenan saina Jika" Kashe wayar Yayi Idanunshi suna Kan na Sadiya "Amarya na Gajiyar dake da tsayuwa Ko? ki gafarceni, zamu iya karasawa Mu zauna"


"Huhm Bakomai Baby Kawuce haka A zuciyata, Qasar Bishiyar Gidansu suka nufa suka zauna suna Fuskantar Juna, Baby Anya kayi Break kuwa? irin wannan Fitowar bai kamata Ace ka Karya ba"


"To ina zan iya cin Abincin, lalle kin dauki wannan Al'amarin da sauki, to bari kiji Barci A Daren Jiya Gagarata tayi Sadiyati" Dariya sukayi gaba daya.


Fadila kuwa suna tsaka da Aiki ita da Ummi kiran wayar Muktar ta shigo, Ta naji har tayi Ringin ta tsinke bata d'a gaba, Gaba daya Kunyar Ummi takeji, Musamman da tasan yana Hanyar Zuwa Gidan su, ga kuma zancen da Ummin tayi Akan Aunty Sady, Wayarce ta sake shigowa, Cike da Mamaki Ummi ta dubeta.


"Fadila kinaji Ana kiranki A waya ba zaki dauka ba, lafiyanki kuwa? ".


"Ummi Muktar ne, Haka yakemin! da Safe sai yakirani yacemin yana kofar Gidan mu zai ganni kafin ya wuce Office, kinga kuma ina Aiki yanzu, gashi Aunty Sady tana waje babu wacce zata tayaki, shiyasa naqi 'Dagawa! idan yaji shiru zai koma"


"Haba Fadila Ai baza'ayi hakaba, ta yaya za'ayi Mutum ya taso yazo kuma ki barshi ya koma, Aiki Ai Anriga Anci karfi, maza jeki saurareshi, bakyau wulakanta Mutane kinji?" tsame hanunta tayi cikin Ruwa cike da Kunya ta dauki wayar Ta fito waje.


  "Hello Yaya Muktar?"


"Haba Gimbiya Fadila saura kiris kisani Kuka, kinsan irin takaicin da na keji idan nakira wayarki baki da gaba? Please Fadila ta kirinka tausayamin"


"Yaya Muktar Ina gaban Ummi shiyasa ban daukaba, Amma kayi hakuri ka iso ne?"


"Ki daina Bani hakuri, bakya lefi A wajena, Kuma Ai Ummi Uwata ce babu laifi idan kin Amsa wayata A gabanta, kin manta nan gaba kadan zan zamo Mijinki? toki fito gani A kofar Gidan, naga Babu Baba Mai_gadi A wajen"


"Okey to shikenan gani zuwa Insha Allah, inaga ya fita ne" dakinta ta nufa tasa Hijabi Babba har Kasa ta fito ta dauki Key din Karamin Palon Abba, tun daga fitowarta idonta ya sauka Akan na Sadiq da Sadiya, Kare mishi Kallo tayi kafin taja wata doguwar tsaki "Shifa wannan Guy din ya dauka wani Burge Mutane keyi ne? Yana wani ji da Kai sabida yana jin Kanshi Kyakykyawa ko?" Harara ta bishi dashi ta wuce Abinda Zuciyarta Cike da Bakin ciki! na Ganin Aunty Sady ba tayi dacen Miji ba.


Ko Kallon inda suke bata sake yiba ta nufi jikin Gate din Gidan. 


Sadiq kuwa tun Fitowarta Idanunshi suka sauka Akanta, irin Kallon da yaga tana mishi yasa yasha Jinin jikin shi, gaba 'Daya ya rasa maiyasa Yarinyar ta Tsaneshi, Tun haduwarsu na Farko A Duniya, Gashi irin Alamun da take nunawa ya gane sam bata Kaunarshi da Sadiyati, Ajiyar Zuciya ya sauke mai Karfi ya mayar da Kanshi Qasa, duk sai yana jin Babu dadi.


Bude Kofa tayi sukayi ido biyu da Muktar! Murmushi ta sake mishi, take yaji wani irin Nutsuwa ta shigeshi, matsa mishi tayi A hanya ya shigo cikin Gidan, Tafiya ta fara, ganin bayi da Niyyar binta yasa ta juyo "Yaya Muktar Muje mana"


"Zo yace da ita, A hankali ta dawo inda yake, Haba Gimbiya sai kace wani ba Muktar dinki ba? kin wani yi gaba, gaskiya tare zamu taka zuwa Ciki, tunda babu Abba da Ummi" Kallonshi tayi kamar tace dashi tana jin kunya, Amma meye ta tuna oho, yasa ta saki Murmushi "Muje to"


Jerawa sukayi suna tafiya Fadila tana mishi Magana cike da Shagwaba, Ba karamin Rikidewa Muktar yayi ba, domin bata taba yi mishi irin wannan Salon ba, Sai da suka iso gab dasu Sadiq Muktar ya dubeta "Fadila Naga Auntyn mu bari mu gaisa ko?"


"Okey Muje toh" Karasawa sukayi, Murmushi Sadiya tayi ganin Muktar, ita sam Kunyar Mutumin takeji, da Sauri baki harna Rawa tace Antashi lafiya" Sai A sannan Sadiq ya dago Kai


"Lafiya Auntyn mu ya Karfin Jiki kuma?"


"Alhmdullah jiki Akwai Sauki Nagode Sosai" Mika wa Sadiq Hanun yayi "Barka dai 'Dan_Uwa" Kamar bashi da Lafiya ya Amsa A takaice da "Barka dai".


Wani bakin ciki ne ya turnuke Fadila, to wannan meye yake takama dashi ne haka? shegen Girman Kai, Fuska A turnuke tace "Yaya Muktar Muje zaka Makara fa?"


Kallonta Sadiq yayi, Ganin irin Mugun Kallon da tayi mishi yasa yayi saurin sauke Kanshi Kasa, Sallama Muktar yayi Musu suka Karisa Ciki.


Sadiya ce ta lura da Yana yinshi "Lafiya Kuwa Baby? naga duk jikinka yayi Sanyi Meye ne?"


"Huhm Sadiya bazan boye miki ba, na rasa meyasa Fadila Sam bata Kaunata, ko har yanzu tana tuno Abinda ya wuce Shekara da shekaru ne? Yarinya Sam bata da Mantuwa, keda nayi miki tsiwarma Kin hakura kin sake Amma banda Fadila?"


"Baby Kenan Karka damu Yanayinta ne haka, kuma Fadila tana Sonka kaine baka lura da hakanba, Abinda yasa nace haka, Fadila bata boye Abinda yake Ranta, na tabbata inda hakane data fadi A Kunnuwata naji, So Please ka watsar da wannan Maganar"


Murmushi yayi "Ya wuce Diyati, Mikewa Yayi "shikenan ki koma Gida kinga na fara Makara, insha Allah zamuyi waya Anjima" Kallonshi tayi "Baby ni sam Yanayinka bai munba, 'Yar dariyar daka sabamin dinma yau ban samu halin hakaba? Ko Akwai wani Abune? ni dai nasan ba haka kazo Gidan nanba"


Dariya yayi "To Hajiya Sady gashi nayi miki Dariya, idan kina so infasa zuwa Office in zauna inyi miki Hira ina dariya shikenan yanzu zan cika Aiki"


"A'A ni bance ba, maza jeka Allah ya bada sa'a, ta ina zan katse mana hanyar Halak dinmu? bayan dashi Muke Gadara. Mikewa itama tayi suka jera, har Jikin Motarshi ta rakashi tana daga mishi hanu, Sai da ya tabbatar ta shiga Gida kafin yayi Key wa Motar ya dau Hanya.


Shukura Resturant ya wuce Direct yadan saya Abinda zai ci ya wuce Office, da Sauri ya shiga ya fara Abinda ya kawo shi, Amma lokaci zuwa lokaci Fadila gizo take mishi lokacin da take mishi Mungun Kallo, gaba daya sai yaji Jikinshi tayi Sanyi.


Muktar kuwa duban Fadila yayi bayan Sun zauna "Gimbiya sam banji dadin Jin Muryarki 'Dazu dana kiraki da Assalatu ba, gaba daya sai naji Duniyar bata yimin Dadi, tunani na fara ko Abba ya fada miki wata Magana ce game dani ba tayi miki dadiba yasa kika rasa nutsuwa harya haifar miki da ciwon Kai.


Wallahi Fadila kinga dai bamu jima da haduwa ba ko? to Amma ina Girmama bukatarki, duk Abinda ya sameki ji nake tamkar ni ya sama, Nutsuwa bata dawomin jikina ba har sai da nakiraki naji muryarki A yanda na santa...