Chapter 15
by @sadiyanasir
"Dazu ba karamin shiga damuwa nayi ba, jin yanayin muryarki ya daga min hankali Fadila, har sai da Fatima ta fahimci Akwai Abinda yaken damuna, tunanina ya tsaya ne ko Abba ya miki wata Magana da bai gamsheki bane game da bukatar dana nema A wajenshi.
Domin hankalina ya gaza kwanciya! tabbas nasan ba kiyi barci sosai ba, gashi Alamu ya bai yana A idanunki don sun kunbura, Dun Allah Fadila kisanar dani Abinda ke faruwa, idan ba haka ba zaki barni cikin zullumi, Please Fadila"
Zuba mata idanu yayi cikin yanayi na tausayawa. Ajiyar Zuciya Fadila ta sauke tayi murmushi "Yaya Muktar ka kwantar da hankalinka Idan kaga ba muyi Aure ba to Allah ne ya kaddara Niba Matarka bace, kuma kai ba Mijina bane, Amma Ummi da Abba duk hankalin su ya kwanta da kai, Magana mai dadi Abba yamin tare da Addu'ar Alkairi A tsakani"
"Shikenan Fadila na yarda nasan ba za kiyi min karya ba, Amma meya hanaki barci daren jiya? Please karki Boyemin kinji?" dago idanu tayi ta dubeshi "Yaya Muktar tunani nakeyi zan bar Kasar nan zani wata Uwa Duniya Karatu, bani da kowa A can, zanyi kewar Gida Matuka, gashi Aunty Sady za tayi Aure ba nanan, wannan Abin yana damuna"
"Fadila... A hankali ta share kwallar data zubo mata A idanu "Na'am Yaya Muktar" ta Amsa gami da dago Kai ta dubeshi "Fadila ko kin san cewa idan Ummi da Abba suka gano irin damuwar da kike ciki sabida maganar fitarki Karatu Cairo Zai jawo ki fasa zuwa gaba daya"
"Aa Yaya Muktar ka daina fadin haka insha Allah saina cika burina"
"To shikenan Amma kinsan wannan hanyar da kika bullo da ita zai jawo miki zama A gida ko? za suyi tunani idan kinje babu Abinda xaki iya, sannan yawan tunanin Gida zai haifar miki da ciwo Matsananci, Please ki daure Dun Allah.
Sannan Maganar Auren Aunty Addu'a zaki bita da ita, kuma Ai zaki dawo zaki ganta, to meye A ciki? Dun Allah ki kwantar da hankalin ki, kinsan na fiki tunani da hangen nesa, to ya kamata ki nutsu kiyi naxari sosai Akan Maganata kinji? insha Allah zaki gano Abinda na fada gaskiya ce"
Share Kwallah tayi "shikenan Yaya Muktar nayi maka Alkawari zan rage damuwar da take damuna insha Allah zaka sameni mai cika Alkawari kuma, Yaya Aunty Fati?"
"Yauwa Fadilata Allah ya miki Albarka Aunty Fati tana gida lafiyanta kalau, yanzu hankalina ya kwanta na tabbata idan naje office zan sami karfin Gwuewar da zanyi Aiki, yasu Ummi da Abba?"
"Kowa lafiya Yaya Muktar".
"To Alhmdullah meye labari? ya kamata kiyi min hira mai dadi, kullum idan muka hadu nike miki hira ke bakiyi min?"
Dariya tayi ta rufe idanunta da tafukan hanunta, wani sanyi yaji A zuciyar shi "Fadila Ina Sonki matukar So, ke da Matata kuna da Matsayi sosai A Zuciyata, Dun Allah idan zama ya hadaku ku zauna lafiya da juna ku samarmin Farin ciki A Rayuwa ta kinji?"
"Insha Allah Yaya Muktar karka damu, Amma in tambayeka Mana idan babu damuwa?"
"Ina jinki baki da matsala".
"Dun Allah Yaya Muktar Aunty Fati tasan kana nema ta?"
Murmushi yayi jin tambayar da baiyi zato ba "Aa Fadila ban sanar da itaba, Amma mai yasa kika min wannan tambayar?"
"Yaya Muktar mai yasa zaka boye mata, kana so rashin yarda ya shiga tsakaninku ne? da taji labari A bakin wasu gwara Ace A bakin Mijinta ta fara ji, na tabbata ko da za taji ciwon Abin to kadan ne, tunda baka Munafurce taba"
Ajiyar Zuciya ya sauke "Shikenan Fadila Maganarki gaskiya ce, insha Allah zan sanar da Fatima nan bada jimawa ba"
"Yauwa Yaya Muktar Nagode" Mikewa yayi "to nikan na tafi Office zamuyi waya Anjima" itama tashi tayi "shikenan Yaya Muktar muje na taka maka zuwa Gate" fita sukayi ta rufe kofar Palon suka nufo waje, har jikin Gate ta rakashi tana mai daga mishi Hanu harya kule A layinsu.
Cikin Gida ta koma nan tasamu Abba harya tashi yana zaune A Babban palo, karasawa tayi ta durkusa "Abba Antashi lafiya?" Murmushi yayi "Lafiya lau Fadila yaya Gidan?"
"Alhmdullah Abba" Mikewa tayi Abba barin shiga"
"To shikenan bakomai, kice Ummin ku tazo ina kiranta"
"To Abba".
A store ta sami Ummi ita da Sadiya "sannun ku Ummi harkin kammala Aikin?"
"Haba Fadila kusan Hour guda kina waje kiyi tunanin ban kammala ba? Aini jima da hada komai, , kije ki dibi yanda zai mik kici".
"Eyya Ummi sannu da kokari Abba yace kije yana Palo" tsame hanunta tayi cikin Buhun "To zoki taimaka mata kusamin wannan A Buhu, barin je" fita tayi Fadila tacigaba da Aikin.
Sadiya ce ta dubeta, "Nikan Fadila in tambayeki mana?"
"To Aunty ina jinki".
"Nikan meye Matsalarki da Sadiq ne? dazu na lura da yanayinki kamar baki son Alakata dashi, Dun Allah Fadila ko yana da wata Aibune daban saniba?"
Ajiye buhu tayi ta kalli Sadiya da idanunta suka kada izuwa Jaa lokaci guda "Aunty Sady ya fada miki wani Abu ne? ko wani Abun kika ga nayi mishi dazun?"
"Aa kawai dai yana yinki ne, gashi suna gaisawa da Muktar kika jashi kuka tafi, shiyasa nayi tsammanin wani Abu" kama hanunta Fadila tayi "ki kwantar da hankalinki kinji Aunty na? wallahi ina son Abinda kike so matukar zai saki farin ciki, Bahaguwar Fahimta kika yimin, Dun Allah ki fahimce ni kinji? Ina Sonki da Sadiq kuma ina yimiki Addu'a kullum Ubangiji ya tabbatar da Alkairin dake cikin neman da kukeyi"
Murmushi Sadiya tayi "Ameen 'Yar Kanwata ina Sonki da yawa, har kinsa Zuciyata tayi sanyi, dazu gaba daya sai ina jina babu dadi" Dariya Fadila tayi "Lalle Aunty kina son wannan Guy din, Allah yakaimu lokaci musha biki gashi kash bani Kasar za'ayi".
"Wallahi kibari kawai nikaina zanyi missing dinki Ace bikina baki A wajen"
"Karki damu Ai bikin suna dani za'ayi" Murmushi Sadiya tayi to Allah yakaimu lokacin, nidai fatana kawai Allah yasa kije ki dawo lafiya ki samemu"
"Ameen ya Rabbi Aunty nah, haka suka cigaba da hira har Ummi ta dawo ta karbj Fadila ta fita domin taje ta karya.
Sadiq kuwa Aiki sosai yau yayi, sai wajen karfe Biyar kafin ya kammala ya dau jakarshi ya fito, yana isa bakin Motor Kiran Khalil ya shigo wayarshi "Hello Abokina ya Akayi ne?"
"Lafiya lau Khalil ya yau din?"
"Normal Wallahi kana inane?"
" Gani na fito daga Office zanje Gidan Abinci saina wuce gida"
"Ok nima ina kusa dakai barin karaso mu wuce kawai"
"Alright ina jiranka".
Ba'a dauki lokaci ba Khalil ya karaso suka karisa Gidan Abinci, sai da suka zauna Khalil ya dubi Sadiq "nikan ina labarin Mutuniyar taka ce, jiya kasan Aina naganta kuwa?"
Cigaba dacin Abincin shi yayi "ku dai kuka sani Kai da ita"
"Kai dadina da kai baka cin ribar zance, Mutum zai zo maka da labari Amma kana basar dashi"
Dariya Sadiq yayi "to labari ne wannan? wai tsaya khalil! wai ni meye hadina da Zuby ne kake yawan takura min? kabi ka tsauwala wa Rayuwata Akanta? Yarinyar tunda ka tusamin ita har yau na kasa ya kiceta A jikina, ka hadani da Karfen Kafa, shiyasa Kullum zaginka nake"
"Wallahi Khalil Abu daya yasa nake ragawa Zuby A Rayuwa, shiyl yasa kaga har yanzu bamu rabuba, Yarinyar tayi dai_dai da Macen dana keso, Sam bata gajiya da Na Miji, Nina san babu wasa Amma Zuby tana kuremin lisaafi.
To Abinda yasa kawai nake raga mata kenan, ina samin yadda nake so A wajenta"
Dariya Khalil yayi "shege Abokina yanzu kam kasan dawar garin, Ai dama na fada maka, Matukar ka Amince da Yarinyar nan to kai da damuwa kuma kunyi hanun riga, domin nayi tarayya da Zuby kuma naji dad'in ta shiyasa kawai data Ganka ka kwallafa Rai yasa na dage har sai da ka Amince da ita.
Ba gashi yanzu har wani tumbi kayi ba, kana samun kaya kana diba sosai" Dariya sukayi gaba daya suka cigaba da cin Abincin su, Wayar Khalil ce tayi ringin Hanu yasa ya dauka "Yane Babban Yarinya? kefa kina da wulakanci dazu babu irin kiran da ban miki ba Amma kikayi kunnen Uwar shegu dani, Meye kike bukata yanzu?
Shuru yayi nadan wani lokaci kafin ya cigaba da Magana, to shikenan naji bakomai Zan baki, yanzu ina Aroma Please ki Gaggauta kizo ki kawomin Systerm dita, idan kika kara 20 minute zaki samu na tafi.
Magana yake yana kallon idanun sadiq dake cin Abincin shi cikin nutsuwa sai kinzo" kashe wayar yayi ya cigaba da cin Abincin shi.
Sadiq ne ya dubeshi "Wato kai Kam ka mayar da neman Mata Abinci ko? yanzu kuma yarinyar su waye ka samu haka?" dariya khalil yayi "Wata 'Yar wahala ce Abokina idanunta basu waye ba ni nake son in Gogar da ita Duniya, Yarinyar sabuwar hanu ce in fada maka, nine nan na fara budeta A leda shiyasa nake Sonta sosai.
Gashi idanunta basu bude da kudi ba Kamar wa incan Kauyawan, burinta taci ta koshi shikenan, inaga irin Yaran da iyayenau basu kula da su dinnan ne, domin daga yanayin suturarta zaka gane.
Kasan Abin mamaki ma kuwa? kuma fa A Gidan iyayen nata take"
"Ikon Allah mai makon ka taimaka mata ta gyara Rayuwarta sai kuma ka warga zata? yanzu ka kyauta kenan? kuma ba Aurenta zakayi ba, haba Khalil wallahi Akwai hakki, Abinda kakeyi tayi yawa gaskiya"
"Kaga Mallam ya isheka haka? nifa ba dole nayi mata ba, A facebook fa muka hadu, tace na taimaka mata da 2k nace bakomai zan bata 10k Amma mu hadu da ita, tace min bakomai inhar zan taimaka mata bakomai.
Nikuma da tazo na gwada mata Salo irin tawa tuni ta fada tarkona nan danan taba da kai bori ya hau, Ashe Virgin ce, nina dauka Yar hanu ce, kaji yanda wasan ta soma.
Kuma ina dauke mata dawainya tunda burinta Abinci ne, babu wani kashe kudi da yawa, Amma kaga shedaniya Zuby din nan? idonta A bude suke"
Kallo kawai Sadiq yabi Khali dashi, gaba daya tsoronshi ne ya kama shi lalle Khalil yayi nisa, yana tsaka da Mamaki wayar Khalil ta kara ringin, nan ya kwatanta mata inda suke, tunda ta shigo idon Sadiq yake kan Yarinya.
Jikin shi ne yayi sanyi, Yarinyar ba tafi 18yrs ba kana ganin yanayin shigarta kaga na kamilar Mace, gaba daya A nutse take, bakin ciki ne kawai ya turnukeshi, ganin irin Cutar da Khalil yayi wa yarinyar nan, harta iso inda yake idonshi na kanta yana tunani.
"Sannu". tace dashi, nan hankalinshi ya dawo jikin shi "Yauwa Sannu ya kike?"
"lafiya Ta Amsa, wata leda ta Ajiye A Gaban khalil, gashi na gama nagode"
"Okey ina ce kin kalla duka?"
Sunkuyar da kai kasa tayi Alamar kunya "Ok yace kawai ya dauki Systerm dinshi yasa A gefen shi, Oya zauna Akawo miki Abinci"
Cike da jin Kunyar Sadiq ta zauna, gaba daya jinjina rashin Kunyar Khalil tayi, yanzu idan Abokin nashi ya fahimci Blue Films Khalil ya bata taje ta gani Aita shiga uku, Shikenan zai fahimci meye tsakaninsu da Khalil? Zufa ce kawai takaryo mata...