JAN KUNNE

1

by @sadiyanasir



Ina Tafiya ina Sakawa da War-warewa cikin Zuciyata! Tunanina ina Abba ya tsaya haka! Har ya Mance Dani A Makaranta? Cike da Damuwa na Karasa Gidan mu, Ganin Motar Abba A Kofar Gida yasa na Sauke Ajiyar Zuciya na Fada Cikin Gidan ko Sallama Banyi ba! Sanin Bana Magana da Suwaiba Matar Abba.


Ina shiga Na jiyo Muryar Gwaggo Habiba tana Magana cikin Daga Murya! A hankali na Karasa ta Window baya! Na dakin Aunty Suwaiba na Kasa Kunne "Gaskiya Nafara Gajiya da Irin Bakaken Maganganun da Ake Fadamin A Kanka! Haba Auwalu Sai Kace Akanka Aka Fara Haihuwar Yarinya Uwarta ta Mutu? Ka dauki Soyayyar Duniya ka daura Mata? Gaskiya wannan ba Tarbiya bace, Na Rantse da Allah kaGidan i Matakin Gyara.


Suwaiba Yarinyar kirki ce! Duk Cikin Matanka daka Aura kana Sakewa Babu wacce take da Hakurin ta, to Wallahi na Fada Maka karka bari Suwaiba ta Kubuce Maka! Na Tabbata babu Wanda zai sake Baka Aure! Indai A Garin Bauchi ne"


"Amma Yaya Habiba Kinsan dai... 


"Ya isa Auwalu! bana Bukatar jin Ko Kalma Daya daga Gareka! Ni dai na fada Maka, Kaji Tsoron Allah, Suwaiba Don Allah Kiyi Hakuri, Yanzu Ina Hajaran take Auwalu?"A take Gabana ya Fadi! Jin Yaya Habiba Ta Ambato Sunana! A hankali na koma da Baya nabar Gidan Gaba daya.


Gidan su Waleeda na Nufa da Sauri! Dankar Yaya Habiba ta Ganni A Hanya! Bare harta Fada min Maganar da zata Tabamin Zuciya! Sallama nayi na Fada Cikin Gidan, Kasancewar Rana tayi! Ga zafi! Yasa Babu kowa A Harabar Gidan, Dakin Maman Waleeda na Nufa! Jin Hayaniyar Yara A wajen.


Sallama nayi na daga Labulen dakin, Amir ne ya taso da Gudu ya Rungumeni "Aunty Hajara Oyoyo" daukarsa nayi Cak muka Shiga "Auta ina Waleeda?"


"Barin kirata tana Ciki" to nace na saukesa yayi dakin Maman su, Maida Hankalina nayi Jikin Kallon da Yara suke A TV, Sai jin Hanun Waleeda nayi A Jikina, dan Murmushi Nayi "Baki Karasa Gida bane? Na ganki da Uniform?"


"Humm ke dai Bari Kawai Waleeda, Ina shiga Gida naji Muryar Gwaggo Habiba! Tasa Abba nah A Gaba tana Kan tsigaleshi Akan Aunty Suwaiba, Ni A tunanina zan dawo in samu Abba ya Saki Aunty Suwaiba, Ashe An samu Munafukin da yaje ya Fada wa Gwaggo Habiba? Shine na samu Na fito ba tasan na shiga Gidan ba, bare ta sani A gaba ta zageni Tsaff".


Kama Baki Waleeda tayi "Iko Sai Rabbi! Hajara ni Banga Mai Matar nan ta tsare miki ba! Amma kin dauki tsanar Duniya kin daura Mata? Haba Hajara! Kar kiyi Anfani da Son da Abba yake Miki kina Hana shi zaman Aure! Don Allah?"


"Huhmm ke Ai kullum baki Gane meye Ake nufi! Matar nan shiga Hakkin mu take! Ba hali ta Ganmu tare zata Fara Wani shan Kamshi! Tana Kumbura, shiyasa kawai nace Ya saketa, Mutum da Mahaifinsa Amma bayi da Ikon sakewa dashi?"


"Huhmm! Amma kiyi Tunani! Kar Ace Abba ya fiye Aure Sake, yanzu Aunty Suwaiba ko Shekara ba tayi ba! Kuma kike so ya saketa?"


"Ni ya isheni Malama! Mubar zancen! Ina Mama?"


"Na dawo Islamiya na samu Bata Nan! Yanzu nake Shirin shiga Kitchen na daura Taliya Muci Kafin ta dawo"


"Shikenan Muje in tayaki" Hijab Dina na Cire na Rataya A Jikin Kofa na Ajiye Jakar Makaranta na muka Nufi Kitchen, Muna Aiki muna Hira! A haka har Muka Kammala, Taliyar ta zuba Mana muka dawo Harabar Gidan inda Akwai Inuwa muka zauna! Saka-makon zafin Ranar da Ake kodawa.


Ina sa Hanu A Taliya Yaro yana shigowa bakinsa dauke da Sallama! Dago idanu nayi na Kallesa gamida Amsawa "Wani ne ya Aikoni wai Hajara tazo Nan Gidan?" Murmushi nayi domin Nasan Abba ne "Kace Gani Zuwa! tsame Hanuna nayi na dubi Waleeda, Wallahi Abba ne! Barinzo" Zaro Idanu Waleeda tayi, zaki sha Fada kenan? Bai San kinzo Nanba?"


"Kibari Kawai ina zuwa! Nasan meye zance dashi" Dakin Maman Waleeda na shiga na dauko Hijab Dina na Fice, A jikin Motarsa na Hangosa ya Harde Hannaye! Kana Ganin Fuskarsa kasan yana cikin Damuwa, Take naji Raina ya sosu, Jiki A sanyaye na Karasa "Sannu da zuwa Abba nah?"


Dago idanu yayi ya Kalleni "yanzu kin Kyauta kenan Hajar? Babu inda ban dubaba Amma Bakinan? Me yasa kika kasa Jirata kika Zo nan?" Dan Turo Baki nayi na dubesa "Abba Naga An watse yasa na tafi Gida, ina shiga Naji Muryar Gwaggo Habiba tana Magana Akan Aunty Suwaiba shine kawai na fito nabar Mata Gidan, Amma kayi Hakuri"


"Shikenan ya wuce Amma karki Sake, Suwaiba tana Neman Mu Sami Matsala Babba Hajar, Sabida Wulakanci Harta taka Kafarta babu Izini taje Gidan Yaya Habiba takai Karata? Kuma Akanki? Bayan tasan Duk Duniya Babu wanda zai Kawo Kushe A Kanki Ya sha A Hanuna?"


Sake Turo Baki Nayi Abba "Wallahi Na tsani Matar nan, Ka Sallameta Kawai! Ni Mu Zauna Kawai Nida Kai Abba nah! Bana So ka sake Wani Aure" Kwafa kawai Abba yayi ya bude Motor ya shiga, Karasawa nayi Na bude daya Gefen nima na shiga, Sai da Muka Shiga Layin Gidan mu Kafin ya Dubeni, Hajar "Kin san Meye Yaya Habiba Tace?" Da Sauri Nace "Aa Abba?"


"Humm wai zata daukeki ki Koma Gidanta duk Ranar da Suwaiba ta sake Kai Mata Kara Akanki" Dafa Kirji nayi na Dubesa "Abba Nikan Mutuwa zanyi Wallahi idan na koma Gidan Gwaggo Habiba, Wallahi bata So na" Cak ya tsaya da Motar har sai da Na tsoratani, Rai A bace ya dubeni "Hajar baki da Hankali ne? Meya kawo Zancen Mutuwa Kuma?


Kin Mance Yaya Habiba Ita kadaice Nake Gani Naji Sanyi A Zuciyata? Don Allah kar kice zaki Kullaceta, Awannan Gabar bazan Zuba Idanuba, Ki taimakeni Don Allah? Rashin Mahaifiyarki yasa Na Susuce da Soyayyarki! Yau idan Kika bar Duniya ya kike Ganin Rayuwata zata Kasance? Kar kisake Fadin Haka idan Har Kina Sona Kinji?"


Ajiyar Zuciya na sauke "Insha Allah Abba nah Muna tare Ba yanzu Zamu Mutu ba"


"Yauwa Hajar! Zuciyar Abban ta" Dariya nayi, Hira ya Rinka Jata dashi Har Mika iso Kofar Gidan.


"Don Allah Duk Abinda Suwaiba zata Miki Karki Kulata, kinji Dai Abinda Yaya Habiba tace?" Turo baki nayi "shikenan Abba Naji" Bude Murfin Motar nayi na Fice, Sai da Yaga Shigata cikin Gidan kafin ya tada Motar.


A zaune na sameta A tsakar Gida tana Gyara Alayyahu! Wani Irin Kololon Bakin Ciki naji A zuciyata na Ganinta da nayi, Ba tace dani Uffan ba Na wuce, Nima Bata isheta Kallo ba Na Ratse ta Gefenta Na wuce dakina.


Wayata na Ciro Keypad da Abba ya siyamin idan Ina da Bukatar wani Abu, Dialling Number Abba Nayi, Ringin daya Ya dauka, Cike da Shagwaba nace "Abba meye kace Aunty Suwaiba ta dafa ne?" Daga bangarensa Yace "Tuwo Miyar Taushe tace za tayi" Dan daga Murya nayi Yanda za taji "Abba ba zanci Tuwo ba, Kawai Zan dafa Mana Cus-cus da Kai! Idan ka dawo Muci, Shuru Yayi Baice Komaiba, Abba Kayi Shuru kuma?"


"Shikenan ki dafa Hajar idan Har kina so" Cike da Murna na kashe Wayar na cire Uniform Dina Nasa Kayan Zaman Gida, Alola nayi Na daura Sallar Azahar! Ina Idarwa na fito nayi Kitchen, Aunty Suwaiba tana ciki tana Hada Miyar Tuwo, Tabe baki nayi Na shiga Store din Gidan na Dauko Cus-Cus guda Daya, Kayan Miya nagani A Markade Cikin Blender! Na dauko na Zuba cikin Tukunya "Kutumar Uba....... Kalmar data Fito daga Bakin Aunty Suwaiba kenan......