JAN KUNNE

7

by @sadiyanasir


Ina idar da sallah ko Addu'a banyi ba na mike na nufi dakin Abba, wani bakin yunwa ce ta taso min, A zaune na samesa yana Danna Wayarsa "Hajat kin idar?"


"Eh Abba"


"To ki dauko Mana Abincin" to nace na nufi kitchen na dauko na dawo daki, A plate daya na zuba mana, Murmushi Abba yayi "Shikenan yau kin canji Suwaiba ko? Ban taba cin Abincin dare ba tare da ita ba"


Uhumm kawai nace, Kasar zuciyata kuwa dadi naji, Ashe ba zan sha wahala ba wajen mantar da Abba Aunty Suwaiba, muna ci muna hira har muka kammala, Kwashe komai nayi na kai kitchen na Adanasu gefe guda.


Fridge na bude zan sha Ruwa nayi tozali da Tsumin da Aunty Suwaiba take sha, murmushin mugunta nayi na dauko na zuba mishi idanu "Inace wannan Abin ne yasa Abba yake Mata kirari? Cup na dauka na tsiyaya kadan na kai baki na, wani Hamami naji, da Sauri na furzar, Auzu Billah Ashe babu dadi ma?"


"Hajar?" Naji muryar Abba "Na'am" na Amsa da Sauri, Jikin Sink na nufa na juye Tass na dauraye Galan din. 


A hanya muka hadu da Abba "Lafiya kika zauna A kitchen?"


"Lafiya kalau Abba na gyara wajen ne?"


"Okey hakan yana da kyau, muje bani so kina nisa dani! Kinsan dare? Murmushi nayi muka koma dakinsa, TV na kunna mana muka cigaba da Kallo, gaba daya hankalina yana kan Littafin da nake karantawa, Hammar Karya nayi, Hajar Barci ne?"


"Eh wallahi Abba gashi gobe Monday"


"Hakane! toshikenan jeki kwanta zuciyar Auwalu, Yau kam babu tsoro ko? Zaki iya kwana ke daya?" Da Sauri nace "Eh Abba zan iya" murmushi yayi "Allah ya tashemu lafiya" Ameen na Amsa na fice A dakin na koma dakina.


Key nasa na rufe dakin, tube kayana nayi, ya rage dagani sai zani, Littafina na dauko na kashe wutar dakin na kunna ta Karamar wayata, Haka na dukufa karatu babu ji babu gani har wajen karfe 12, gaba daya idona banda Ruwa babu Abinda sukeyi, Amma sabida jaraba na kasa hakura da karatun na kwanta.


Yanayin yanda tsarin labarin yake! Shiya tafi da Imanina, Ashe ko Rabin Soyayyar cikin Littafin Aunty Suwaiba ba tayi wa Abba, A iya ganin Idona dai, Alkawari na dauka wa Kaina! Duk Runtsi duk wuya sai na Raba Aunty Suwaiba da Abba na, in har zan Kwatanta Abinda Matar Littafin Nan takeyi! To inaga na shawo kan Matsalata.


Sai wajen Karfe daya kafin na hakura da Karatun na boye A kasar Katifata na kwanta barci, Karan Window na naji da karfi A firgice na tashi, Iska mai kyau yake kadawa da Alamun Ruwan sama za'ayi, Jiki babu karfi na tashi na Rufe Window na dawo na kwanta, Wayata na jawo na duba Time, 04:46, tsaki nayi na Ajiye Wayar na cigaba da barci na.


Cikin Barci naji saukan Ruwan sama mai karfi, tashi nayi na zauna gabana sai fadi yake, domin haka Allah ya halicceni Ruwan sama yana daga min hankali, musamman mai karfi haka, cike da tsoro na tashi na shiga Toilet na dauro Alola, ina idar da sallah na bude kofar dakina na fito, lokacin gari harya Fara Haske.


Tura kofar dakin Abba nayi, da mamaki na ganshi A bude, kar dai Ruwa ya tsare Abba A Masallaci? Ko sallama banyi ba na fada dakin,


A zaune na sameshi ya zuba ma wayarsa idanu, da Alama Charting ya keyi, tsayawa nayi na kare mishi Kallo, A yanda nasan Abba na! Ba zai Hanani Abinda na kudurta ba, karasawa nayi na zauna A gefensa na Kama hanunsa na rike cikin tawa.


"Abba na Antashi lafiya?" Ajiyar zuciya ya sauke ya Ajiye Wayar, ya juyo ya dubeni "Hajar Alhmdullah ya Ruwa? Yanzu nake tunanin lekaki, kin san yau kinada Makaranta" Cire hanunsa yayi cikin tawa "hakane Abba Anma Ai Ana Ruwan sama ko?" Murmushi yayi "Hajar to Ai A motor zaki tafi? Kinga babu Ruwanki da Ruwan sama?"


Kwantar da Kaina nayi A jikinsa nace "Hakane Amma Abba Barci na keji" hanuna na sake sawa cikin nashi, na daura dayan A kansa ina wasa da sumar Kanshi "Ko dai baki da lafiya?"

Kada kai nayi "Lafiya Abba"


"To shine kike narkawa haka Hajar? Sai kace Yar shekara 4? Tashi ki koma can ki kwanta?" Turo baki nayi Abba Amma idan Aunty Suwaiba ce baka hanata zuwa kusa da kai! Amma ni gashi kana kowarata"


Matsar dani gefe yayi ya juyo ya kalleni "Hajar Ikon Allah, Aunty Suwaiba Ai Matata ce, ke kuma Y'ata ce, kinga A Musulunci yanda kike min hakan bai dace ba, Matata ce kawai take da ikon yin haka"


Kallonsa nayi fuskata dauke da damuwa "Shikenan Abba tunda kafi son Aunty Suwaiba Akaina" tashi nayi na fito A dakin gaba daya na koma dakina, A bakin gado na zauna na fashe da kuka, Lalle ina da Sauran Aiki, kafin Abba ya daina Anbaton Aunty Suwaiba zan sha bakar wahala.


Na jima ina kuka daga karshe na share hawayena, wani Abinda ya dauremin Kai! Kuma ya bani mamaki shine, A tarihin Rayuwata Abba bai taba ganina cikin fushi ya share ba, Amma Yau ya kasa zuwa ya lallasheni? Shikenan Aunty Suwaiba tayi galaba Akaina?.


Sai da nayi Kuka na mai isata kafin na mike na fito A dakin, Kitchen na shiga na daura sanwar indomie na dawo daki nasa Uniform Dina, kasan cewar gari Akwai sanyi yasa banyi Yunkurin wanka ba, A Plate na juye mana nayi Sallama na shiga dakin, karan Ruwa naji Alamar yana toilet, Ajiyewa nayi na soma gyara dakin, Yana fitowa yace "Hajar Yar Albarka, sannu da kokari? Har kin shirya?"


"Eh Abba ga Abinci?"


"To shikenan jeki dauko Jakarki ki rufe ko ina kizo" To nace na fita na Aiwatar da Abinda ya umurceni, ina dawowa na samu har yasa kaya, nan muka zauna muka Karya.


"Hajar yau fa mun makara, karfe takwas fa?"


"Abba Ai ruwa Akayi! Ba zasu bugeni ba"


"Hakane to maza mu tafi".


Tunda muka shiga motor babu Wanda yace Uffan har muka iso kofar Makaranta, kudi Abba ya Ciro ya mika min "gashi koda Abinda zaki Bukata, idan kun tashi ki Hau Napep ina ga ba zan samu zuwa ba, idan yaso Zamu hadu A Gida ko?"


"Shikenan Abba Allah ya kiyaye" Amen ya Amsa na bude kofar na fita.


Kasancewar Anyi ruwan sama ko taron Assembly ba'ayi ba, Aji na wuce Direct, Waleeda harta rigani zuwa, Ajiye jakata nayi na zauna "Yau kin Makarane Hajara na rigaki zuwa?"


"Huhmm ba dole ba! Nice nayi Aikin komai fa"


"To ina Aunty Suwaiban?"


"Taje gidan su yaji"


"Shikenan Ai dadi ya kamata kiji, tunda Abin nema ya samu"


"Huhmm ke dai waleeda ki Bari, Wai An kashe Maciji ne ba'a sare kai ba, Abba dai tunda Aunty Suwaiba ta tafi gidan su bani gane kansa, Duk ya fita a hankalinsa, babu Ruwansa Dani, koda yaushe cikin tunani yake".


"Eh mana Hajar, Ai tausayinki yasa yake tunani, damuwarsa shine yanda zaki kasance babu Aunty Suwaiba, gashi Yau Ai kin Makara, kuma da tana Gida babu Abinda za kiyi, sai dai kici ki taho, ya Kamata ki Roki Abba ya dawo da ita, wallahi Maman mu idan tayi tafiya dukan mu kamar bamu da lafiya haka muke kasancewa! Har sai ta dawo, sabida itace jigon Gidan"


Tabe baki nayi "Nima da Uwatace A Gidan Ai hakane, Amma Tafiyar Suwaiba shine Alkairi, taje kawai, Allah yasa ya bita da takardan Saki........