8
by @sadiyanasir
"Huhmm lalle Hajara sannu, A hankali zaki gane Aunty Suwaiba tana da Rana A Rayuwarki"
"Ya isa malama, Ke dama kullum idan zan kawo miki korafinta baki taba bani gaskiya! Kullum itace Mai gaskiya! Ko da yake laifi nane da nake fada miki damuwata"
"Ba haka bane Hajara, gaskiya ce baki so, kuma tarayyata dake Amana ce zan fada miki gaskiya idan har hakan ta taso, koda kuwa zaki daina min magana, na tabbata wata Rana zaki fahimci gaskiyar" Tabe baki nayi "Kyaji dashi dai" kada Kai tayi ba ta sake ce Dani Uffan ba har Malamin Maths ya shigo, koda Aka tashi Break ban wani sake Mata ba, Amma dake mun Saba haka ko Ajikinta.
Bayan na dawo daga filin Break ina zama Waleeda ta jefo min Tambaya "Hajara yanzu idan kikayi Aure kika samu Yarinyar Miji Mai Irin halinki shin ya za kiyi?" Kallonta Nayi Sosai kafi na bata Amsa "Ke A tunaninki zan iya Aure na bar Abba ne? Ina Gidan ma Matarsa tana Neman Rabani dashi bare nayi Aure? To kima daina wannan tunanin"
"Huhmm Lalle Hajara kinyi nisa, Aure kuwa Sai dai Idan lokaci bai yiba, Allah ya shiryeki"
"Ameen! Ko Akwai wani Abu bayan wannan?"
"Aa Hajara" Haka mu kayi zaman Yau babu dadi tsakanina da Waleeda har Aka tashi A makaranta, dake Akwai kudi A hanuna, ina fitowa na nemi Abin hawa na tafi Gida, A bude na samu Kofar Gidan mu A wangale, Kama baki nayi "ko dai Abba ne? To ina Motar Abban?" Ganin babu mai bani Amsar tambayata yasa nayi Sallama na shiga.
A zaune na same shi A Kofar dakinsa yana shan rake, murmushi nayi na karasa "Abba Ashe ka dawo? Banga motar ka ba?"
"Na dawo Hajar, Motor tana wajen Gyara, Ina tafiya bayan na saukeki Allah ya Aikomin jarabawa, Belt ta tsinki, Taya ta Fashe, Allah yasa bani tafiya da Sauri, da yanzu Ance miki na Mutu"
"Subhanallah Abu baiyi dadi ba"
"Ki Bari kawai shine na Kira Mai gyara, yanzu haka Lissafin da yamin Akwai Yawa, kuma A halin yanzu babu kudi, Jira nake ki dawo na Lallaba na isa Gidan Yaya Habiba Asan ya za'ayi"
"Ikon Allah, toshikenan Abba Allah yasa A samu, yanzu meye zan dafa kafin ka dawo?"
"Ni dai A koshe nake Hajar, ke dai ki nemi wani Abin kisa A Cikin ki ina dawowa"
"To Abba shikenan" yana Kammala shan Raken sa yamin Sallama ya fita, Taliya na tafasa dake Akwai Sauran Miyan Jiya, Ina Gama cika cikina na wanke duk Kayan da Muka bata na Abinci na koma dakina nayi Sallah, Littafina na dauka na cigaba da karatuna hankali kwance.
Sai da naji kiran Sallar La'asar Kafin na Ajiye, Wayata na dauko na Danna wa Abba kira, Ringin daya Aka dauka "Assalamu Alaikum?"Jin Muryar Mace yasa gabana ya fadi, daurewa nayi na Runtse idanu "Waye ta dauki Wayar? ina Abba na?"
"Yana Cikin Jaka" jin haka yasa na saita Nutsuwara domin na fahimci wacece ke Magaba Gwaggi Habiba ce "Anyini lafiya Gwaggo?"
"Lafiya ya Katatu?"
"Alhmdullah"
"To Allah ya taimaka, Hajara Ya fita Neman na Rufa muku Asirin ma ba zaki kyaleshi ba? Yanzu meye zai miki! Bayan yanzu ya baro Gida?"
"Um.. Um.. dama zan tafi Makaranta ne shine nake so na sanar dashi"
"Ki sanar dashi? Meye Anfanin Suwaiba da bazaki fada Mata zaki tafi makaranta ba? Ai naga dashi da Suwaiba daya suke, wato Hajara ba zaki Gyara Hali ba?"
"Gwaggo Ai...
"Kimin shuru bana bukatar wata Magana, dama A wuya nake dake, idan har sai ya dawo kije Makaranta to kiyita zama, Haba Yarinya sai Kace Kaska? To kiji da Kyau, Auwalu ba dawowan yanzu ba, Motarsa ta lalace, yanzu Haka Neman mafita Ake na gyaran Motor, duk Abinda kike bukata Ai ga Uwarki Suwaiba" kit ta kashe Wayar.
Zufa ce ta karyo min, A hankali Nasa hanu na goge "Kenan Abba bai sanar da ita Aunty Suwaiba bata Gida ba?" Alhmdullah na Ambata na mike jiki A sanyaye na Fara shirin Makaranta.
Rufe Gidan nayi na tafi da key din Makaranta, na tabbata idan ya dawo bai sameni ba dole zai biyo sawu, Abin Mamaki har Aka tashi A islamiya babu Labarin Abba, haka na lallaba na koma Gida zuciuyata cike da damuwa, ina shiga na dauki wayata da niyyar sake Kira wata zuciya ta hanani, tunanina kar Gwaggo Habiba ta sake dauka.
Ajiyewa nayi na zuba tagumi, tunanin halin da Abba yake ciki duk ya Addabeni, Haka na zauna ina saka da war-warewa Agun, Akayi Kiran Sallar Magrib, Nan take gabana ya tsananta Faduwa sabida tashin hankali, cike da dauriya na dauki Wayar na sake kiran Layin, harta tsinke ba'a dauka ba, sake Kira nayi da sauri, wannan Karo User Busy Aka samin.
"Kai ina! ya zama dole naje gidan Gwaggo Habiba" da hanzari na samu nayi Sallar Magrib Nasa Katuwar Hijab Dina na fito, tsayawa nayi A kofar Gidan ina tunanin idan naje Gidan Gwaggo Habiba meye zance mata? Kuma na tabbata dole ta Fahimci Aunty Suwaiba bata Gida, Na jima ina tunani, daga karshe na yanke shawarar Isa gidan.
A hankali na Fara takawa zuwa Bakin hanya inda zan sami Napep, tun banyi nisa dake Tafiya ba! na lura da Saurayin dake bina A baya, Takaicine ya isheni na Tsaya! Domin na Bashi hanya ya wuce! Idan har tsare mishi nayi, tsayawa yayi ya harde Hannayen sa A Kirji, ganin haka yasa na zuba Uban tsaki na cigaba da tafiya ta.
"Hajara don Allah kiyi hakuri ki tsaya Magana zan miki da bai wuce 2minute ba? Girgiza kai kawai nayi na cigaba da tafiya ta, Don Allah nace fa? Ki duba Girmansa?" Tsayawa nayi Cak ko juyowa banyiba nace "ina jinka fadi Matsalarka A 2minute din daka Anbata?"
"Yauwa Hajara nagode da wannan Karamci, A takaice dai! Ni Sunana Kamalu, Nine mai Sabon shagon Waya da Aka bude Wancan Satin na bakin hanya, Wallahi Hajara tun ganina dake na Farko A Rayuwa naji kin Kwantamin A Rai, A lokacin na Kudurta A zuciya ta na Sami Abokiyar Rayuwa, na shiga bin Duk hanyar da zanbi don na sami Ganinki mu Fahimci juna.
Naso na sami Abbanki Akan Maganar, Amma A binciken da nayi, sai Aka cemin Ai kina SS 1 ne yanzu, kinga babu ta yanda za'ayi Abbanki ya Amince da hakan, duba da zamanin da muke! Yanzu karatu Akeyi, shiyasa na kudurta A zuciya ta! Zan rika bibiyarki har na samu damar Magana dake.
Don Allah idan ba zaki damu ba mu karasa can? kiji meye yake bakina" kallonsa nayi, irin Kallon dake jifata dashi yasa na kasa magana, duk da A duhu ne Amma saida jikina ya Amsa da Kallon da yake min "Kayi hakuri, kaga yanzu dare ne! A tarihi na bani fitan dare idan ba tare da Abba na ba, ka Bari da safe tunda A unguwar kake sai muyi Magana"
"To shikenan! kamar Karfe wasa? Kuma Aina Zamu hadu?"
Hasken motor na gani yana haskani, gaba nane ya tsananta faduwa, tabbas Abba ne "Kayi Hakuri Kamalu Ka tafi ga Abba na wallahi, kawai za muyi magana" OK yace min ya juya da Niyyar tafiya, kamar daga Sama naga Abba A gabana, Mari ya shiga zuba min ta koina A fuskata "Wayyo Allah na shiga uku! Dauki Jama'a" na shiga Fadi da Karfi.
Da Sauri Kamalu ya dawo, Sai jin Muryarsa nayi yana Fadin "Ranka shidade kayi Hakuri don Allah, Akai zuciya nesa?" Wurgi dani Gefe Abba yayi A kasa, da Sauri Kamalu yayi Kaina, jiki na Rawa ya shiga fadin "Sannu Hajara! Sannu"
Shako Kamalu Abba yayi "Meye gaminka da 'Yata? Da har zaka fito da ita waje? Tambayarka na keyi?" Take idanun Kamalu ya kada sabida Bacin Rai "Ranka shidade! Nan bakin hanyane ka cika min Riga zanyi Maka bayani?"
"Bazan sake ba ka fadamin meye ya hadaka da Hajar?" Murya A kausashe Kamalu yace "Soyayya ita ta hadamu, soyayya irin ta Aure"
"What? Sake Kamalu Abba yayi ya juyo ya nuna min yatsa, Hajar Soyayya? Dama idan bana Gida fitowa kikeyi?"
"Aa Abba" na fada da Sauri, Ganin Haka Yasa Kamal barin wajen da Sauri kafin Abba ya sake rikosa.......