Waminal Hub

7

by @asmybaliyu



Baki jin hausa ne??"Ya fada sounding so very harsh,malam meye matsalarka da hijab Dina."itama tayi Maganar cike da gajia da al'amarin Aliyun,

Fisgota yyi yana huci yake fadin ni kike fadawa magana.."Kallonsa take a tsorace ganin yarda ya rikota ,kokarin kwatar kanta take Amma ta kasa shaye da toka yake fadin"kin san cikin Rules dinmu bbu gardama karki yimin Rashin kunya ya fada yana saka hannunsa yana cire hijab din jikinta duka,wannan karon riga da skirt ne na material ajikinta kalar pink ,kallo daya yayiwa kayan yasan na batool waxeer ne .Dan ita kadai ke saka ire-iren waya'nnan dinkunan,tsaki yaja sosai kayan gaba daya basuyi masa ba duka sun fito mata da halittar jikinta,ki canja kaya gani a bakin kofa ina jira......."Ya fada yana barin dakin,da kallo tabisa cike da mugun Jin haushinsa,wasu kayan ta shiga dubawa black Abaya ta fidda ta saka gamida Rolling din mayafin akanta samun kanta tayi da fesa turare tana fita sukayi ido biyu dashi,

daure fuska tayi shima Fuska bbu walwala yayi gaba tana binsa a baya.gaba dayan su kallo ya dawo kansu,

Wara ido batool waxeer tayi tana kallon yayan nata ,ina ya samo wannan black beauty din."laylah sai bin Nooriyah take da kallo,har suka karaso cikin dinning Area din.da sauri batool ta karaso gabansu ta kama hannu Nooriyah ,tana murmushi take fadin Yaya ina kasamo wannan kyakkyawar."Yaya itace wacce xaka aura??"Gaskiyya tana da kyau ,batool waxeer ta fada tana wani rungume Nooriyah ,toh saketa haka mana jamata kujuera ta xauna."Ammah ta fada tana kallon Batool din,

Murmushi batool tayi tana jawa Nooriyah seat ta kusa ga Aliyu waxeer,ta russuna cikin girmamawa tana fadin barkar ki da xuwa cikin familyn waxeer."Batool waxeer ta fada sounding so very happy,wani irin Abu ya tsayawa Layla a wuya.sai murmushi take kwakwalowa ,bata san meyasa tun farkon ganinta da Nooriyah taji Bata sonta,har ga Allah tasan tafi Nooriyah komai sai kamar tana ganin kamar ba haka bane,tana son wani ya fada mata Nooriyah tafita komai .kayi serving din matarka ka tambayeta mexa taci."da ido yake bin Ammah da kallo tamkar da wani yare ta fada masa hakan,

dan russunawa yayi murya can kasa yake fadin"tell me mexaki ci??"Kur idon laylah akan su ,sai taga sunyi mata wani irin kyau.har sai taga Aliyun yafi Khalil waxeer iya kula da macce."Abunda xaka ci shi xanci ta fada tana kallonsa,daure fuska yyi ganin ta gama Raina sa.ganin ido akansu yasa baice komai ba ya shiga serving dinsu plate daya yayi masu,sakin baki da ido batool waxeer tayi tana sakin wani irin blushing.bata taba ganin yayanta yana tarairayar macce ba irin yau,ko Areefa Mansoor da yake fadar yana so bai Bata irin wannan kulawar,

Da ido kurum Nooriyah ke binsa me Aliyu waxeer ke nufi??"Yana nufin agaban Ammah xataci Abinci tare dashi,muryar Ammah taji akanta tana fadin"kici Abinci Mana Nooriyah ,ta Yaya xataci Abinci plate daya da Aliyu waxeer".suna hada ido ya wani ware mata ido gamida bude mata hannuwa,duk Abunda suke a idon laylah sai taji gaba daya ta tsani Abincin,wani irin kishin Nooriyah yaxo ya tsaya mata a xuciya ,idan batayi da gaske ba Nooriyyah xata xama best daughter in-law a wajen Ammah ,taga yarda Ammah ke wani rawar kafa akanta....A hankali ta Mike tsaye ,ta subbaci Khalil waxeer gefen kuncinsa tana fada masa ta wuce sashensu kanta nayi mata ciwo,nan ta juya tana yiwa Ammah sai da safe.ita dai Ammah binta kurum take da ido ganin yarda yanayinta ya canja lokaci daya,gefen Nooriyah mamaki take taya Layla xata subbaci Khalil waxeer agaban surukarta?"

Nan laylah ta juya tabar parlon da sassarfa ,shi dae Aliyu cin abincinsa kurum Yake,hakama Khalil waxeer sunaci suna hirar business dinsu,

Ammah itama ta Mike ta koma parlor har lokacin Nooriyyah takicin komai, Khalil ya kalleta yana fadin kici Abinci plz kibar biyewa Aliyu shegen cin tsiyane dashi ,xakiyi aiki sosai a wannan bangaren."da sauri Aliyu ya kalli Khalil waxeer yana dakune fuska.dage gira Khalil yayi yana fadin"na fadi karya ne."Kusan lokaci daya Aliyu da Khalil suka Mike suka bar dinning area din,ya rage daga ita sai batool dama batool ta matsu subar dinning din,ta dawo kusa ga Nooriyah tana murmushi take fadin"Aunty noory taya kika sace xuciyar Yah Aliyu haka?"murmushi kurum Nooriyah tayi taki cewa komai,Haka batool ta shiga janta da labari sama-sama take Bata Amsa,bbu laifi ta Dan sake da batool,sai kusan 10 sukayi sallama da batool kowa ya nufi makwancin sa,washe gari Mai gyaran jiki taxo ta fara yiwa Nooriyah gyara ,kusan kwana 4 Aliyu baisa ta a ido ba gata bangaren farhaan ya damesa ya hadasa vedio call da Nooriyah.Ammah taki basa damar hakan,

Tace baxasu hadu ba sai ranar da xasu hadu wajen sakasa lalle.haka Aliyu yyi xuciya ko parlon Ammah ya daina shigowa,bangaren kayan da Nooriyah xatayi amfani dasu na hidimar biki tayi magana da laylah ta damka komai a hannunta,cike da kosawa da xance laylah ke fadin"Ammah ki samu wani ki basa banda lokaci Kuma duka masu yimin dinkuna basa da Alkawari kar axo asamu matsala."tayi Maganar in I don't care manner.murmushi kurum Ammah tayi tana fadin bbu komai xata samu wani,karshe batool ta damkawa komai ita duka ta xabarwa Nooriyah din kalar dress din da xatayi Amfani dasu,da aka kawo kayan Ammah ta yaba sosai da hakan,acan bangaren laylah kuwa bincike takeyi sosai taya Aliyu waxeer ya yarda xai auri wannan Yar kauye marar wayewa wacce,da alamar batada ilimin boko ko kadan."tasan wannan bashi ne mafarkin Auren Aliyu waxeer ba,tayi ta Kiran lambar Areefa Mansoor a kashe ko xata samu karin bayani akan hakan ,Areefa Mansoor kawarta ce ta sanadiyarta suka hadu da Aliyu waxeer.Yarda tasan Areefa Mansoor haka kawai baxata barwa wata Aliyu waxeer ba.yarda take mafarkin samun sa,tasan akwai dalilin wannan Auren dalilin takeso taji ko Ammah xata daina wannan Rawar kafar Akan Nooriyah.....


ASMY#❤️