Fakkriya

Visitors

by @112438632248185038931

ina dawo gida na tarar su ammi suna ta aiki na tambaya ko lfy amma tace ce baki zamuyi baffan ku na abuja ne zasu zo dukan su hutu kano kuma naji yace wa babban ku ma anan zasu sauka saboda cen gidan nashi ana dan yi musu gera ne da farin cikina bace amma bari na yi wanka nazo na tayaku ,mama tace ki huta auta yanzu fa kika shigo da murna ta na tafi sama nayi wanka nayi sallah sai na sauko na kamawa su mama aiki haka mukayi abin ci kala kala da snacks da juice,muka jerasu ,sana. Nasa ka su rosa suka sake saka turaran huta muryar baffa naji a bayana auta wanan kamshin abinci har waji ina ji nace wanan aikin auta na ce ina ta dariya nace baffa i munyi kokari ko yace allah yayi miki albarka amma ta kalli mama tace kin ji sankai ko mun huni muna aiki amma wadda ake yabawa daban .atare duk mukayi dariya baffa yace toh ayi hakuri kuma allah ya yi muku albarka ameen duk muka amsa . I munyi magana da matawale ma yace mun sun taso .nama tura yayan ku suje airport din su jira su .

alh matawalle yau sun tashi da zimmar zasu kawo ziyara kano dan tin da aiki ya maidashi abuja ya bar kano sai dai su shigo ziyara ko indai wani abu ya tashi suke zuwa kano ,duk gidan yau murna suke zasu zo kano dan rabun su da kano tin bikin yaya siyama wanda akazo kano akayi biki cen gidan kakan su da yake galadanci cen family house din su alh matawalle .kuma wana karan zuwan nashi mai muhimaci ne sosai shi yasa ma yace sai weekend zasu zo saboda ya na so har faruq suzo kano ,cen na hago wani black saurayi ya juya baya tin daga bayan nashi ma kasan namjine guy din ya hadu sosai shi ba fari ba kuma ba bakiba dogo ne sosai yana da hanci sosai kyayyawa ne ajin farko kuma ga class yanaji da shi . Amma fa babu fara ‘a a face din shi dan kamar kowa yana farin ciki da zuwa kano ban da shi . Ummi ce naji tana cewa haba babana ace kai kulum indai zamuje kano baka farin ciki kuma su gashi sunan san ganin ka ,wI meye matsalr ka ne da kano ,toh sai ummi babu damma sukan ka kawai sai su fara fada wai kaki aure kowa yayi ,ko kuma hajiya babba tafara turo min wanan kwalayan jikokokin nata tana wai na zabu daya ,indai baso take su raina ni ba ,wallahi nama kunyi tafiyar ku kawai dan ni ina da abunyi ma allah ummi ,pls kiyiwa baffa magana . Ummi kawai ta zuba masa ido , yanzu kai baba na haka zamu zuba maka ido ace kowa yana aure kai kaki fitar da mata ,haka ake rayuwa gaskiya ya kamata ka gera kasamu ka fitar da mutum daya ,kadai jin abunda abban ku ya fada maka last month,ni baruwa na a cikin a toh ,kuma hajiya i gata take yi maka tin da kai ka kasa ,ga shi nan usman i tare kuka taso yanzu yaran shi biyu amma kai baka so a fada maka gaskiya .kuma ka huce mu tafi kafin ma ran abbanka ya baci