HAƊUWAR ZUCIYA

CHAPTER 1 SHIMFIƊA

by @111643396306696762233

SHIMFIƊA

Yau wayewar garin ranar laraba an tashi da wani irin lullumi, sakamakon ruwan sama da a ka kusan kwana ana yi a jihar Kano, tun kafin ƙarfe goma sha ɗayan dare har zuwa bayan uku da rabi na gefin asubahi ruwan na sauka a wurare da dama, musamman kudanci da gabashin jihar, babu hadari a garin face sassanyar iskar damina da ke kaɗawa, wasu alamu na gwada mawuyacin abu ne rana ta ɓullo tsakanin giza-gizan da suka lulluɓe sararin samaniya.

Dai-dai lokacin ƙarfe goma da rabi na safiya ɗaliban jami'ar Bayero rukuni rukuni a harabar makarantar kowa yana harkar gabansa, wasu bitar karatu, wasu ciye-ciye, yayin da wasu rukunin hankalinsu ya karkata ga hira tsakanin juna, 'yammata da ƙawayensu, samari da abokansu har zuwa 'yammata da samari, rayuwar makaranta dai a taƙaice ga waɗanda suka santa.

A ƙarƙashin wata bishiya nesa da wani Block wasu matasa su uku suna zaune kan darduma suna tattaunawa a junansu, a lokaci guda kuma suna yiwa wata tarin gyaɗa mai ɓawo da ke gabansu ɗauki ɗai-ɗai suna ɓarewa gami da jefa wa a bakunansu a marmarce kana kuma cikin nishaɗi. Irin yanayin da ɗalibai suke kasancewa yayin da suka samu 'yar faraga don ƙwaƙwalwarsu ta samu hutun aiki, kana daga bisani kuma su koma fagen daga.

Daga can gefe wata farar mota ƙirar Honda CRV new modern ta silalo a hankali tun daga bakin get har zuwa inda ta samu kyakkyawan matsugunni a waje na musamman da aka tanada domin parking a cikin makarantar. Duk yadda mutum zai yi hasashen mamallakin motar bai wuce ya ajiye shi a jerin waɗanda ba su da wata matsala da ta shafi masu gidan rana ba (Kuɗi).

Sakanni goma a tsakani murfin motar ɓangaren direba ya buɗe a hankali, wani matashi ya fito sanye cikin riga da wandon coat, ƙafafunsa rufe da baƙin takalmi sawu ciki, idanunsa sakaye da baƙin tabarau da ya ƙara fallasa asalin gogaggiyar farar fatar jikinsa mai sheƙi, idan ka yi masa duba na tsanaki takardun da ke riƙe a hannunsa kaɗai ke siffanta shi da ɗalibi, amma a zahiri ya fi yanayi da cikakkun ma'aikatan gwamnati da ke ci da biro.

Ya rufe motar cikin saiɓi kana ya fara taku a hankali yana dube-dube cikin filin makarantar, a haka ya tunkari inda waɗannan matasa ke zaune.

"Salamu alaikum." Ya yi sallama da sassanyar muryarsa mai cike da nutsuwa, hutu har da kamala.

 Ɗaya daga cikin su ya ɗaga kai ya dube shi, "Amin wa alaikassam, ur welcome." Sauran biyun kuwa bisa ga dukkan alamu sun yi nisa sosai cikin duniyar gyaɗa marau-marau ɗin su don haka ba su samu sukunin amsa sallamarsa ba face bin sa da ido kawai. Shaheed ya samu guri ya zauna gefen su kan dardumar duk a lokaci guda ya fara ƙoƙarin tuɓe takalman ƙafarsa.

"Usman yaya lecture ɗin safen nan ta kasance kuwa?" Ya tambaya yana duban wanda ya kira da suna Usman, shine dai wanda ya amsa sallamarsa. Maimakon Usman ɗin ya ba shi amsar tambayar da ya yi masa sai ya ce da shi, "Tun ɗazu muke jajanta rashin ganinka da wuri yau, Tasi'u ma ya kira wayarka Switched Up, ina fatan dai lafiya."

"Shaheed ya lumshe fararen idanunsa a hankali kana ya buɗe su. Ga wanda ya yi masa farin sani zai iya fahimtar yadda idanun suka ɗan sauya zuwa launin ja kamar dai yadda Usman ya lura tun dosowarsa gurin.

"Bari kawai Usman, ka san jiya ruwan sama nan ya daken, shine da zan kwanta na sha maganin mura, ban ankara ba har kusan 10 ina barci, yanzu haka wata irin kasala ke bibiyar gaɓɓan jikina."

Sai lokacin Tasi'u ya sako baki bayan ya gama ƙyalƙyala masa dariya, "Amma yanzu ɗan ruwan da ya taɓa ka jiya shi ka ke kira dukan ruwa? Ɗan hutu ne kai kawai."

Shaheed kam ya san halinsa, don haka bai tanka masa ba ya koma ya kishingiɗa yana lumshe ido, idan ya samu dama tsaf zai iya barci a wajen.

Wata siririyar yarinya fara sanye da ɗamammun kaya babu mayafi a kanta ta zo za ta gifta su tana yauƙi idanunta a kan Shaheed ta ce, "Abokai sannun ku da hutawa." Tasi'u ya bi ta da kallo, "Yauwa sannu Amrah." Ya muskuta kaɗan yana ƙoƙarin jan ta da hira, sai dai yana lura da yadda fuskar Shaheed ɗin ta sauya lokaci guda, ya yi kicin-kicin tamkar bai taɓa dariya ba, duk saboda ganin Amrah, don haka ya yi gum da bakinsa, duk yadda yake son kula 'yammata haka yana ji yana gani ta wuce.

Shaheed ya lura da shi, ya ce, "Mutumin banza kawai, ni dai na gargaɗe ka duk lokacin da za ka kula wata yarinya a makarantar nan ka bari sai ba ka zaune kusa da ni, ba zan iya da irin wannan zubar da ƙimar taka ba."

Kafin ya mayar masa da martani wata mota ruwan toka ƙirar Peugeot ta yi parking kusa da ta Shaheed, dukkan su su ukun suka dakata da cin gyaɗar da suke tare da zuba ido suna dakon wanda zai fito cikin motar in ka ɗauke Shaheed da ke ta faman danna wayarsa.

Wacce suka yi tsammanin ganin ce kuwa ta fito daga cikin motar sanye da doguwar riga baƙa, kamar kullum yau ma ta manna baƙin tabarau ɗin rashin mutunci a fuskarta, kamar yadda suka tambara ta, kasancewar Shaheed a wajen shi ya hana su yin sharhi a kanta, kuma sharhin ba zai wuce kan ɗagawa da girman kan da suke ganin tana da shi ba. Muddin za ka daka ta Shaheed ba za ka kula ko wace 'ya mace a makarantar ba.

Sunanta Surayya Farouk, a kaf faɗin makarantar nan ba ta da ƙawa ko aboki, ita kaɗai take rayuwarta, dukkan ƙofofin saurarar jama'a gare ta a kulle suke. Da farko yanayin shigarta da irin motocin da ta ke hawa sun tabbatar da ita a rukunin 'ya'yan masu hannu da shuni da ke makarantar, sannan uwa uba kyawu da ƙwarjinin da take da shi su suke hana kowa tunkarar ko da inuwar da ta zauna bare a kula ta.

Wataƙila saboda ta shigo makarantar da matsananciyar yunwa, don haka kai tsaye Cafeteria ta nufa ta zauna bayan ta yi odar abinda take buƙata.

Tasi'u ya kasa samun nutsuwa. Tun ranar da ya fara ganinta a makarantar zuciyarsa ta kwaɗaitu da son yin mu'amala ko wace iri ce da ita, idan ya samu ABOTA da gudu zai karɓa bare kuma a ce ya yi gamon katar ta faɗa SOYAYYA da shi, a ranar zai tabbatar shi ɗan sa'a ne a rayuwarsa, sai dai a rashin dacensa ko gaisuwa bata haɗa shi da ita, bata cikin 'yammatan da suke bin su.

Kamar mintuna biyu a tsakani ya miƙe yana karkaɓe wandonsa, "Guys bari in samo mana abin sha." Cikin su babu wanda ya iya gano ainihin manufar da ke ɓoye a cikin ransa, don haka duk sun yi amanna kan zai samo musu abin sha ne kamar yadda ya faɗa domin hakan abu ne da ya saba faruwa a tsakaninsu, ya bar gun yana gyara kwalar rigarsa.

Surayya da ke zaune a mazauninta ita kaɗai a hakan ma wajen ya yi mata hayaniya, jefi-jefi ta ke ɗaga ido tana duban 'yammata da samarin da ke ta faman son birge junansu a wajen, wata alaƙar tana kamanceceniya da soyayya, wata kuwa da ka gani ka san abota ce.

Kunnuwanta suka tsinkayi sallama a kusa da ita, ta lumshe ido ta buɗe, sassanyan lemon Coc da ta ke kurɓa yana ratsa makogwaronta duk da yanayin da ake ciki. Sosai ta ji sallamarsa a karo na biyu, ta kuma san da ita yake, yana tsaye yana dubanta, fuskarsa ɗauke da murmushin da ta kira murmushin yaudara a duban farko da ta yi masa, a hankali cikin wani salo na ƙasaita ta kawar da kanta tana amsa sallamar a ciki-ciki, a ɓangare guda kuma tana mamakin tsaurin idonsa idan har ya ce zai nemi ƙulla wata alaƙa da ita.

A ɓangaren Tasi'u shakkun da yake game da ƙin saurararsa ya ragu a zuciyarsa sakamakon ya samu ta amsa sallamarsa, wani abu ne da bai taɓa tsammanin faruwarsa ba duba da yanayin shiru da miskilancinta.

"Barka da hutawa 'yammata." Ya faɗa cikin salo irin na kula wa da jan hankalin wanda ake son ribata.

Shiru babu amsa daga Surayya da ta ƙudirce a ranta bayan amsa sallamarsa babu wata kalma da za ta yarda ta sake haɗa ta da shi. Ba rayuwarta ba ce, ba tsarinta ba ne kula ire-iren su.

"Idan babu damuwa in taya ki zama mana." Ya faɗa da murmushin nan da ta fi komai tsana a kan fuskarsa tunda ta fara ganin sa, bai damu a kan lallai sai ya samu amincewa daga bakinta ba, ya samu guri ya zauna kan kujerar da ke fuskantar ta don yana da tabbacin zai samu karɓuwa. Wannan ba wani baƙon abu ba ne a tsakanin 'yammata da samari, dama hausawa sun ce, 'A rashin tayi a kan bar araha.'

A target's ɗinsa abota ya so ya fara requesting kafin daga baya komai ya sauya, kamar dai yadda ya saba rufta sauran 'yammatan da yake ɗana wa tarko su faɗa, katsam ya tsinci bakinsa na furta wasu kalmomi da kaf cikin 'yammatan da ya yi babu wadda ya taɓa furtawa makamantansu, ya ƙarƙare da roƙon ko da kalma guda ya samu ta furta masa.

"Gimbiya sarauniyar mata ki daure ki min magana ko da kalma ɗaya, hakan zai sa na samu sukuni kan raɗaɗin da ya ciyo ni na zo gare ki, ni fa masoyi ne na haƙiƙa."

Bata dai tanka masa ba, a nasa ɓangaren kuma ya samu confidence ganin yadda ya ke ta zuba a gabanta kamar kuma tana saurarensa har cikin zuciyarta, irin abinda ake kira yaudarar kai, don haka ya ci gaba abinsa.

"Sunana Tasi'u Ibrahim, ni ɗalibin likitanci ne, mene ne sunanki?"

"Nonsense!"

Surayya ta miƙe a fusace da wani irin ɓacin rai a kan kyakkyawar fuskarta, a wannan lokacin babu wani abu da take jin za ta yi masa ya sa ranta ya huce bisa takaicinsa kawai ta ɗaga gwangwanin lemon da take sha ta juye masa a jiki, farar T. Shirt ɗinsa kuwa ta ɗauka.

A kan idon Shaheed da ya shigo wajen, kansa ya ɗaure, takaici ya rufe shi, ya tsani yarinyar sosai saboda ɗagawa da wulaƙancinta, amma kuma a nan ya fi ganin laifin Tasi'u da kwaɗayinsa ya ja shi zuwa gare ta. Ashe da ya ce musu zai zo ya sama musu abin sha ita ya biyo?

A take ya ji abinda ya shigo da shi wajen ko me ne ne ya fasa, don haka ya juya ya fita yana jin haushinsu su duka, a gefe guda yana jin babu wata mace da ta isa ta wulaƙanta shi irin haka bai ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kanta ba, zuciyarsa ta fara kitsa masa mugun abu a kan Surayya, kowa fa ɗan iskan kansa ne sai idan bai ga dama ba, zai iya dizga ta fiye da yadda ta dizga abokinsa, zai iya sauko da matsayinta ƙasa a makarantar, kai zai iya raba ta da makarantar ko 'yar uban waye ita.

Tasi'u yana kallon sa'ar da Shaheed ya bar gurin, kunya duk ta dabaibaye shi ganin yadda duk jama'ar da ke wajen idanunsu na kan shi, suna kuma jiran ganin yadda zai yi, ba shi da abun yi da ya wuce shima ya ja ƙafafunsa ya yi gaba, dai-dai lokacin ita ma Surayya ta tattara nata ya nata ta bar gun ranta a ɓace, komai ya fice mata a rai.

Duk waɗannan abubuwan da suke faruwa suna da alaƙa ne da labarin Sa'adatu da ke cikin shekara ta biyu da shiga makarantar, wacce ƙaddara ta afka mata tun ranarta ta farko, ba ƙaddarar komai ba face SO,

Da fari ta yi zaton kyawu da ƙuruciyar Shaheed ke birge ta kamar sauran 'yammata, sai daga baya ta fahimci wani irin jarababben so take masa da bai yiyuwa a misalta irinsa. Abubuwa da dama sun zama cikas a rayuwarta, duk lokacin da ta tuna wa ce ce ita, me ne ne matsayinta sai ta ji tsanar kanta ta rufe ta.

Ita saɓanin Surayya Farouk ce da ta mallaki komai na rayuwa a ganinta, tabbas suna da tarin bambanci, Sa'adatu ta zaɓi rayuwa ita kaɗai a cikin makarantar ne ba don komai ba sai don tana ganin matsayinta bai kai ta haɗa kanta da sauran mutane ba, da zarar ta shiga cikin 'yan uwanta ɗalibai sai ta ji duk ta muzanta.

Shakka babu a wannan zamani da kowa ke rububin taka matsayin da yake so Sa'adatu ta yarda tana da kyau, amma yanayin rayuwar da ta tsinci kanta da irin gidan da ta fito sun taka rawar gani sosai wajen ɓoye asirtaccen kyawun nata.

Sa'adatu ba fara ba ce tas kamar Surayya, fatarta mai kyau ce, tana da cikakkiyar sura mai Jan hankali, idan ana maganar kyau sai dai a shafa fatiha, tana da manyan idanu da dogon hancin da ya ƙara wa faskar tata kyau, bakinta madaidaci, duban ta a karon farko zai tuna maka da kyakkyawar jarumar ƙasar India Madhuri Dixit musammn idan ta yi murmushi ko dariya, idan tana tafiya sai ka ɗauka yanga take, sai dai ba yanga ba ce, halitta ce kawai natural, a zahiri yadda take ɗaukar kanta ma sam yanga bata dace da ita ba.

Yanzu da take tafe a kan hanyar ta ta komawa gida daga makaranta cike da rangajin yunwa ta zaɓi tafiya da ƙafafunta ne saboda dalilai guda biyu, na farko dai yau garin sam babu ranar da ke saka ta ciwon kai muddin ta shiga ta daɗe a cikinta, sai abu na biyu da ya tilasta mata tafiyar ƙafar bai wuce ƙarancin kuɗin abin hawa ba, duka chanjin da suka rage a jikinta ba za su kai ta gida ba duk da cewa gidan ba wani nisan ku zo a gani ke gare shi ba.

Ta share hawayen da ke ƙoƙarin saukowa kan dandamalin kumatunta da ta tuna tsawon Lokacin da ta ɗauka tana addu'ar Allah Ya cire mata son Shaheed daga cikin zuciyarta, sai ramewa take tamkar ana gutsirar ta, babu kuma wanda ya ke gane ramar da take sai mahaifiyarta, ta rufe ta da cewa wahalar karatu ce kawai, domin babu yadda za a yi ta iya buɗar baki ta faɗa mata ta kamu da so.

A irin ranakun da so ke wahalar da zuciyarta wasu lokutan ta kan yi ƙundumbala ta gifta ta wajen da Shaheed ya ke zama musamman idan ta ga shi kaɗai ne wai ko ta samu ya dube ta ko da sau ɗaya ne, me yiyuwa ya san Allah Ya yi tsiron halittarta a doron duniya, sai dai 'yammatan da suka fi ta ma ba su dame shi ba bare ita karan kaɗa miya.


Mu ci gaba a Chapter 2