HAƊUWAR ZUCIYA

CHAPTER 10 Ɗanɗano daga Littafin RANAR KUSKURE...

by @111643396306696762233

Kaɗan daga littafin RANAR KUSKURE...

Ya tsuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba, "Me ki ke nufi Aysha, me yasa soyayya da aure za su haramta a tsakaninmu? Shi addininku bai san darajar soyayya ba ne da har yake gindaya mata sharaɗi, Aysha ki sani a soyayya babu wani sharaɗi, ina sonki kina so na, wannan ya wadatar, kuma babu wanda ya isa ya canza hakan. Ki tsaya ki saurari zuciyarki please..."

"Idan na saurari zuciyata babu abinda take faɗa min sai sonka da ƙaunarka Samuel, idan kuma na saurari mahaifana da dangina sai su ce min kuskure ne rayuwa da sonka bare har ta kai ga na aure ka, ya zan yi ne Samuel?"

Ya ƙura min ido a cikin duhun daren tsayin lokaci yana duba na, bashi da niyyar sake furta wata kalma, bisa ga dukkan alamu dai bai gamsu da maganganuna ba, har yanzu abu ɗaya ya sani kuma ya yarda da shi shine; tunda muna son juna ni da shi ko ta wace hanya ya zama wajibi mu rayu tare.

"Mu yi wani abu da kai Sam." Na furta ina duban yadda ya zama kalar tsausayi.

Har yanzu bai ce da ni uffan ba.

"Ka musulunta ni kuma zan aure ka in bi ka garinku mu yi rayuwar farin ciki tare."

Sai na ga ya gyara zama a hankali murya a sanyaye ya ce, "Aysha ina son addinina kamar yadda ki ke son naki, ina da magabata kamar ke waɗanda ba za su so jin cewa na bar addinina katsam ba, Aysha shin dole sai na bar addinina sannan zan mallake ki? Me yasa addininku ya cika tsauri, me yasa addininku ba shi da adalci?"

"Ba addinina ba ne ba shi da adalci Samuel, kai ne dai ka kasa yi masa adalci sannan ka kasa yiwa kanka, addinina haske ne mafi rinjaye daga cikin addinai, idan kana neman addinin da ya darajta ɗan adam da soyayya ka samu addinin musulunci ka gama."

Lokaci guda ya miƙe tsaye, ya fara ja baya yana girgiza kai, "No Aysha, addininki kawai kike bawa kariya, ni da ke kowa yana ganin cewa shine a kan dai-dai, me zai hana mu jingine maganar addini mu yi aurenmu Aysha?"

"Ba zai yi yu ba Samuel, duk auren da ya amsa sunansa aure da addini yake tinkaho, domin shi kadai ne zai iya kare shi, ina sonka ina ƙaunarka, bani da burin da ya wuce in aure ka mu kasance tare har abada, amma ba zan yarda in aikata wannan kuskuren ba, idan ba za ka iya musulunta ba mu haƙura kawai."


Yana tafe da izinin Allah...


MUSTAPHA ABBAS R/LEMO

***

Follow my account