Babi na ɗaya
by @billysfari
Page 1.
A guje ta shigo cikin makarantar da mota kasancewar qarfe 8:00am na safe take da lectures, gashi kuma har takwas da rabi ta soma wucewa, sanin da tayi cewa babu jituwa tsakaninta da malamin da zai d'aukesu darasin yau da safe d'in saboda irin malaman nan ne masu muguwar matsala had'e da takurawa ga d'alibbai yasa ta sake take wutar motar ba tare da ta damu da dokar rashin yin gudu akan titunan makarantar da kewayenta gabanta na wani irin muguwar fad'uwa, ALLAH ALLAH kawai takeyi ta ganeta a cikin ajin duk da tasan zuwanta adaidai wannan lokacin baqaramar matsala zai iya haifarwa tsakaninta da malamin ba matuqar ta riskesa aciki,
Tana wannan tunanin ne ba tare data ankara ba daidai lokacin da take qoqarin karya hannunta tashiga kwanar da zata sadata da b'angaren da suke daukar lectures d'in tayi saurin taka wani irin wawan burkin da yasa har seda kanta ya kusan buguwa da sitarin motar sanadiyar jin ta bugi wani abu da batasan ko meye ba agabanta, da sauri ta d'ago kanta cikin tashin hankali had'e da zaro idanuwa tasa hannayenta biyu ta safe kanta tana fad'ar "innalillahi wa'inna ilaihirrajiun" cikin firgita da kid'imewa ganin aika aikar da tayi,
Wani kyakkawan saurayine dake sana'ar saida kwakwa da dabino ta kad'e dake qoqarin fitowa jikin kwanar adaidai lokacin data kawo da ake kira MM MAIDABINO wato (Muhammad muhriz mai dabino), sai d'alibbai suka qire sunan suna kiransa da MM MAIDABINO saboda yayi masu sauqin fad'a, duk da irin tarin raunin da sana'arsa tasa ta nuna ajikinsa hakan bai hana tsala-tsalan 'yan matan dake makarantar bibiyarsa da kalmar so ba, saidai kash! Shi ba wannan bane agabansa, don kuwa yaqi basu dama ko sakar masu fuskar da zasu samu bayyana hakan agaresa, kawai shi dai abunda ya sani kuma ya saka a gabansa baiwuce sana'arsa ba, wacce a kullum yake d'auka a matsayin rufin asirinsa a idanuwan mutane, mutum ne shi miskili da bai fiye son duk wata harkar da zata sakashi doguwar magana ba har saida dalili, yanada tsatstsauran ra'ayi da kuma kwar jini sosai, shiyasa duk qwaqwar 'yan matan dake bibiyarsa basa iya tunkararsa kai tsaye su bayyana sirrin zukatansu, yanada sanyin hali sosai da sauqin kai wanda sune suka janyo masa tarin soyayya da kuma dad'in mu'amala acikin mutane, sosai yakan fahimci yarinyar da duk tazo wajensa da manufin soyayyar aranta saboda sauyin da dafin so ke saurin haifar mata alokacin ba tare da sanin taba, amma yana ganin hakan ko mutunci yake da yarinya zaiyi saurin sauya mata fuska ta yanda da kanta zata shiga taitayinta tare da had'iye abunda tázo dashi aranta, sau tari 'yan mata nashan yin fad'a akansa ba tare daya sanma sunayi ba sai dai in ya ji labari acikin makarantar, shima girgiza kai kawai zaiyi yace ALLAH ya kyauta, kyakkyawane naqin qari dake da hasken fata sosai tare da matsakaicin tsayi da kuma qiba, a yanda jikinsa ya nuna azahiri bazaka tab'a cewa shid'in mabuqaci bane har sai ka ankara da irin kayan da yake sakawa kala biyu da akoda yaushe suka zame masa tamkar wasu yunifom, doguwar riga jallabiya baqa da take had'awa da wani wando bula sai kuma wani yadi ruwan kalar ganye riga da wando irin d'unkin mutanen qauye da ake kira zauren d'ari, wanda yauma su d'inne ajikinsa,
Fitowa tayi da sauri cikin motar tana yarfi da hannayenta had'e da nufar wajen data hango wani abokin sana'ar tasa da ake kira Jabir ya tallabosa, take ta sake kid'imewa tare da qarasawa wajen ganin yanda goshinsa da hancinsa ke fidda jini sai faman lumshe idanuwa yakeyi dake nuni da cewa ya bugu sosai ba kad'an ba, acan gefe kuma baronsa ne ya kife gaba d'aya a qasa komai dake ciki ya watse akan titin, dafe goshi tayi kamar zatayi kuka tare da kallon kayan dake qasa zube sannan ta juyo ta maido kallonta agaresa,
"Subhanallahi! Don ALLAH kayi haquri, wlh ban lura da zuwanka ba, I thought babu kowa ne a gabana shiyasa na shigo aguje saboda in samu inyi attending lecture d'in wancan malamin...." kafin tarufe baki taji Jabir dake riqe dashi ya ce,
"Dallah malama rufa mana baki, dama ku 'ya'yan masu kud'in nan haka kuke wlh, sam bakwa d'aukar talaka da wani mutunci ko kad'an, gani kukeyi ki kad'aine mutane su kuma kun maida su tamkar wasu dabbobi"
"Nooo... Wlh ba haka bane!, kawai a tsorace nake, ina kaima kasan halin wasu malan nan tunda a cikin makarantar nan kake wuni kuma kana jin irin abubuwan da suke tafkawa, ALLAH yanzun nan ne akan abu kad'an zasu maido d'alibi baya ko kuma wata shekara saboda tsabar mugunta, musamman idan suka tasoshi agaba, pls don ALLAH kayi haquri MM ka ji?..."
Sake watsamata wata uwar tsawar Jabir da yayi kutunkutun yana masifa yayi a hasale kafin taqarasa maganar da tasata saurin zabura har idanuwanta na kawo qwalla had'e da cewa,
"Rufa mana baki dallah, wannan ai shirmene kikeyi, shikenan don malami nada tsanani sai akace kuyi gudu akan titi? Ko anfad'a maki cewa mu bamuyi bokon bane? irin wannan damuwar mu maza mu zamu fad'eta bawai ke mace da murmushi kawai zakiyiwa malami ya baki *A* ba!, 'yar rainin hankali kawai to babu inda zakije har sai kin kaisa asibiti ko yanzun nan naje nakai qararki ga hukumar makaranta, Ina kuma kinsan cewa dokar bata baku damar yin gudu hakan ba amma shine kikayi sai kace titin gidanku ne"
"Ba haka bane wlh.."
"Karki renawa kanki hankali da wayau, zaki wuce ne muje ko kuwa..?"
Kafin yaqarasa yaji muryar MM da tunda ta qaraso wajen ya kafeta da idanuwa tamkar bashi bane ke neman agaji saboda tsananin azabar buguwar da yayi, amma da kallo d'aya sai yaji ya nemi duka ciwon dake jikinsa ya rasa duk dako har lokacin jinin dake zuba bai dena zubar masan ba, cike da qarfin hali ya ce
"Ya isa haka Jabir mana, barta taje ai tsautsayine, ALLAH ya riga daya tsaro yau hakan zata faru dani ta sanadiyarta, jeki, ba komai kinji ko" ya qare zancen yana nuna mata hanya da hannu alamun zata iya tafiya, jikinta na rawa tanufi wajen motar had'e da cewa,
"Nagode sosai MM" yayi mata murmushi had'e da kad'a mata kai ya lumshe idanuwa ya bud'e alamun tatafi ba damuwa,
Har ta tada motar tata sai kuma ta kashe ta juya ta d'auki gorar ruwa had'e da ciro handkachif a jikkarta dake gefe ajiye tafito ta nufi wajen da suke tsaye Jabir da yayi mutuwar tsaye d'azu baki a bud'e yana zazzaga masa masifa akan don me zaice tatafi, cike da tausayinsa ganin yanda ya dafe goshinsa dake jini kamar zatayi kuka ta ce
"Sannu, ga wannan ka gyara fuskarka kafin nafito lectures sai muje asibitin ko" taqare zancen tana miqo masa ruwa da handkachif d'in dake hannunta, rufe bakinta keda wuya taji Jabir ya ce,
"Mtssss...ka gani ko MM!, wlh duk laifinka ne da kace yarinyar nan tatafi, dubi 'yar rainin hankali don tarena maka da wayau me take qoqarin yi, ka ce abarta taje saboda uzurin data bayar gashi don ta maida mu sakarkari ta sake dawowo, ALLAH kabarni na gyara mata zama tunda ta raina wayon mutane"
Daga ita har MM d'in juyowa sukayi suna kallon Jabir dake ji tamkar ya kaima MM d'in naushi tsabar takaici, cikin marairaice murya tace,
"Kayi haquri mana, ai na fad'a maka bada nufi nayi ba, sannan kuma meye laifi don na kawo masa abunda zai gyara fuskarsa?, ina dai shine wanda nayiwa laifin ba kai ba ko?, To don naroqeka kadena kada tinzirani"
"Idan naqi fa?"
Kallon MM tayi idanuwanta cike da qwallah, ta ce,
"Ungo MM, zan nemeka idan nafito" wafce kayan Jabir yayi a hannun MM daya karb'a yana kallonta, ya sake damqa mata a hannu
"Jeki da tsiyarki ba'a so, waya sani ma koda gangan kikayi 'yar rainin hankali" da sauri MM ya sake miqa mata hannu ya karb'i kayan yana fad'in,
"Qyalesa kawo nagode sosai, jeki abunki kawai indai wannan ne bazai haqura ba yanzu ko kwana kikayi kina basa haquri, abokina me shi sosai baya iya jurewa duk wani abu da zai sameni"
Jiki ba qwari ta sake miqawa MM kayan sannan tabar wajen ranta na suya ganin irin banzar kallon da Jabir keyi mata, dama shi haka halinsa yake sam baya shiri da 'ya'yan masu kud'i rayuwarsa, acewarsa sunfiye wulaqanci don haka yake saurin hasala da lamarinsu saboda gujewa wulaqancin irin nasu daya tsana, ita kuma ta tsani ayimata irin wannan kallon don ba haka take ba, nan da nan sai taji ta qara tsanar malamin da suke kira Ingaski, acewarta duk shine silar faruwar wannan abun data tsani ayi mata zargin tanayi kamar yanda Jabir ke tunani, abun haushi ma ko taje yanzu inba ALLAH ya sota ba daqyar zai barta tashiga don har qarfe tara da mintuna goma sha biyar tayi, d'an tsaki taja cike da takaici sannan tafad'a cikin motar tata ta tayar tayi gaba tanajin tamkar tafashe da kuka,
MM kuwa saida yaga tabar wajen sannan yakoma gefe ya bud'e gorar ruwan data bashi ya wanke fuskarsa sosai sannan ya d'ago handkachif d'in da niyar sake goge fuskar yaji wani irin daddad'an qamshin turarenta dake jiki ya dakar masa hanci, lumshe idanuwa yayi ya bud'e had'e da rumqe handkachif d'in sosai da tafin hannunsa yana jin wani irin yanayi dabai tab'a tsintar kansa a ciki ba.
Zaro idanuwa Jabir dake tsaye yana kallonsa yayi had'e da dukan kafad'arsa cikin jin haushi da takaicinsa ya ce,
"Wai meye haka kakeyi Muhriz?, Janan ce fa ba wata ba?, Look! alqur'an ko katashi muje mu kwashe kayan can ko nayi tafiyata kaji na fad'a maka, don wannan iskancin daka d'au hanya ni bazan juri kallonsa ba"
"ALLAH Janan ce Jabir?"
"A'a ba ita bace kai ne"
"Oh my God!, Kasan me kuwa?"
"Bana son ji malan, kawai katashi mutafi kaji ko, anya ma kaine kuwa? Kaga yanda ka wani qura mata idanuwa sai kace wani sabon maye?, Sai kace ba Muhriz d'in dana sani ba mai shegen nuqufarci da miskilanci ga 'yan mata!"
"Bari kawai Jabir, wlh nima ji na nakeyi tamkar bani bane yau, ji nake tamkar an sauyani daga asalin MM d'in daka sani akan Janan, wani irin yanayi na dinga ji da ban tab'a jiba akan wata 'ya mace lokacin data matso kusa dani na fizgata, gaba d'aya yanda kurar qarfe haka na dinga ji wani abu na fizgata zuwa gareta, shin me hakan ke nufi Jabir?" Jabir daya saki baki yana kallonsa cike da mamaki ya ce,
"Hakan na nufin tabbas kasamu tab'in hankali Muhriz, wannan kad'ewar da tayi maka yasa kasamu sauyin tunani da manta kowaye kai da matsayin da kake dashi a makarantar nan, shin ko ka manta kai bakowa bane sai mai tallan dabino da batasan asalinka ba?, Ita kuma 'yar masu kud'ice dake ji da kanta ko ka manta alwashin daka d'auka?"
"Ban manta ba Jabir, amma koma meye naji son Janan a zuciyata"
"Tab! To ina shawartar ka da kayi gaggawar anfani da d'an sauran hankalin daya rage maka kafin ya ida gushewa ka tashi mubar wajen nan, kamanta da ita domin kuwa duk kanwar jaa ce babu kafi balle na d'ara, kana kallon idanuwanta zakasan biri zaiyi kama da mutum, in kuwa kace ba haka ba to Zan sakar maka gatari, amma kasani ita d'in bata dace da mafarkinka ba, ni kaga tafiyata kafin d'alibbai sufito sufara fahimtar alqiblarmu, amma dai kayi tunani akai"
Jabir ya qarasa fad'ar hakan yana nuna gefen kansa da yatsa,
"Sam baka fahimta ba Jabir, a gaskiya bana Janan tazama cikin bara gurbin dana tsana, kuma ni zuciyata tariga data kamu da sonta daga kallo d'aya"
Cak Jabir ya tsaya daga tafiyar da yakeyi kafin can ya juyo cike da mamaki yace,
"Me kace MM?, Mai maita banji kaba sosai, kardai ace zargin da zuciyata keyi kake son tabbatarmun? Noooo...am not supporting that, Janan bata dace dakai ba, idan zaka farka ka farka kawai kazo mukwashe wudancan kayan ko kuma natafi nabarsu a markanesu akan titin can kamar yanda aka tashi markaneka"
Miqewa MM yayi cike da kuzari ya kakkab'e jikinsa tare da nufo wajen Jabir yad'an daki gefen kafad'arsa yana dariya,
"Comoon...sonta nakeyi fa nace ko tun yanzu zaka soma takun saqa da uwar d'akin taka ne?"
"Wa?... ALLAH ka tsari gatari da sarar masai, ai ko kai baka isa kazamo uban gidana ba balle ita, kawai ina tsoratar maka shan duka ne tunda kai raggo ne, amma tunda kace kana iya had'a gatari bari na sakar maka b'ota, idan gyad'a taji wuta da kanta zatayi d'wad'o, kad'ai san ita ko 'yar gidan waye da kuma abunda mahaifinta zai iya yimaka idan kaje masa a irin wannan siffar"
Seda ya dafa kafad'ar Jabir had'e da d'an sosa gefen kunnensa tukuna ya ce,
"Eh, ai cewa nayi ina sonta bawai nace zan fad'i mata ina sonta ba ko?, Ina son na auna halin Janan dana sauran mata tunda har zuciyata ta zab'eta, ban damu da kowaye mahaifinta ba da kuma mezai iya yimun, kawai nagartarta da qarfin mutuntakarta nake buqata, matuqar nasamesu awajenta a wannan yanayin data sanni, tofa shikenan haqata ta cimma ruwa"
"Shikenan, munga bugun lamba, bara musa idanuwa muga yanda film d'in zai kaya, badai girin girin ba tayi mai"
'Daure fuska MM yayi tare da bud'e sauran ruwan dake cikin gorar ruwan ya watsa masa a fuska yana fad'in,
"Kaifa d'an iska ne Jabir, bakinka baya fad'ar abu mai kyau, in sha ALLAH wannan zatayi mai har kuzo kuriqa lasa"
Jabir dake dariya ya ce "ALLAH!"
"Zaka gani ne"
"To ai shikenan, nidai don ALLAH da girmansa kab'oye wannan son azuciyarka kuma kayiwa bakinka takunkumi wajen aikata kuskuren fad'arsa awajenta kamar yanda tsala-tsalan 'yan matan dake bibiyarka keyi har sai kaga kamun bakin ludayin daga wajenta, inba haka ba kuwa, tofa ka fad'a ruwan dafa kanka da kanka"
"Angama matsoracin wofi, ka kwantar da hankalinka ai dole zanyi yanda kace tunda nasan ko waye mahaifinta duk da dai alamu sun nuna ita d'in ba halinsu d'aya ba"
"Aifa, ni nasan tunda karoga ka saka alaqar zuci tsakaninku babu yanda za'ayi ka iya fahimtar duk wani aibinta yanzu, don haka ga filinan ga mai doki"
"Ashe ko zaku sha sukuwa malan Jabir" ya amsa masa a miskilance yana murmushi tamkar bashi bane suka gama shaqiyanci dashi yanzu,
Da haka suka je suka tattara dabinon da kwakwar suka kwashe waje d'aya suka saka cikin buhu, Jabir yakira aka sake kawo masu wasu suka koma gefe inda suka saba zama sukaci gaba da sana'arsu kafin d'alibbai sufara fitowa daga wajen lectures.
_*WAYE MUHAMMAD MUHRIZ MAIDABINO?*_
*ALLAH KAJIQAN IYAYENMU 👏*