AYUSHA

6

by @pherty001



Shiru yayi idanunsa a lumshe kamar mai barci, sai zancen zucci yake wanda bai san ya fito fili ba, idan ba mace ba ce ya xanyi?


Haƙuri zakayi, yaji muryar ta a sanyaye, ya buɗe idanunsa a hankali yana kallonta itama ƙurr tayi masa da nata manyan idanuwa, tun dana farka na fahimci ba barci kake yi ba me yayi tsanani haka, mun roƙi Allah haihuwa ba dare ba rana ya karbi addu'ar mu ya bamu to meyasa ba zamu karbi nashi hukunci da hannu bibbiyu ba, shin dama da muka tashi neman haihuwa mun faɗa cewa lallai sai mace zamu haifa? Mu nema masa albarka rayuwa Alhaji ba wai mu saka damuwa da zata hanamu nishaɗi ba mace ko namiji duka abun so ne kuma abun muyi wa Allah godiya ne daya bamu fatan mu ya kasance nagari kuma ya amfani al'umma.


Ajiyar zuciya kawai yayi batare da yayi magana ba, har lokacin ya kasa samawa zuciyar shi natsuwa shi ba wai yana jayayya da Hukuncin Allah bane aa yanda zai fuskanci al'umma ya nuna masu namiji ne ya haifa ba mace ba, sannan ya rayuwar yarinyar zata kasance tun da ta taso a mace kuma tana murna da hakan.


Kayi shiru Alhaji, bakace komai ba.

Kallonta kawai yayi kamar zai yi magana sai kuma ya juya mata baya, bata saduda ba tabi bayansa ta kwanta tare da shafa bayansa alamar rarrashi wanda dama ta san idan yana cikin damuwa bai fiye magana ba.


Washe gari sun gama breakfast Ayusha ta kalli mahaifin ta fuskarta a shagwabe kamar zatayi kuka,

Tace Abba mu zauna a wannan gida kada mu koma sokoto.

Meyasa? ya tambaye ta idanunsa kurr akanta cikin mamaki, kamar bazata yi magana ba sai kuma ta buɗe baki da kyar tace saboda anan gidan babu hayaniya kamar irin gidan mu na sokoto, babu neighbors da zasu dame mu da surutu ko hayaniyar ball.


Murmushi yayi a bayyane cikin jin daɗin dogon zancen nan na Ayusha, bazai iya tuna ranar da tayi magana mai tsayi irin wannan ba, duk wata damuwa daya ke ciki yaji ta kau ya fuskance ta sosai tare da riqo hannun ta yana kallonta, itama kallonsa take cikin idanuwansa,


Yace Mamana bayan wannan sai kuma menene bakyaso, ta girgiza kanta nothing more, yace to bari ina so na tambaye ki wani abu sai ki bani amsa,


Ta tunzuro baki cikin ƙosawa da maganar tare da janye hannunta daga riqon da yayi mata, tace you can ask me anything amma ni bana son tambaya da yawa.


Kina so ki zama kamar ni, i mean iri na? ya tambayeta cikin fargaba a sanyaye yana kallon yanayin ta, ga mamakinsa murmushi tayi wanda ya bayyana fararen haqoranta, ta matsa jikin Halima ta kwanta tana kallonsa,


Ina so na zama irin ka da mamee na, saboda kana sona kana son mamee, kana ɗaukar mu kaje damu ko ina kuma kana siya mana alot of things.


Kallon Halima yayi kafin ya dube ta yana faɗin ba haka nake nufi ba, ina nufin ki zama irina babu gashi, ki riqa saka kaya irin nawa ku....


Nooo ta faɗa da qarfi tana kallonsa kafin ta kyalkyace da dariya, bana so na zama namiji, shi namiji baya kwalliya, baya saka kaya mai kyau, baya lalle baya saka sarqa kuma baya kitso and again baya jin magana, kuma they always fight ko a class, ni bana so kuma ai ni am a girl ko Mamee? 


Halima ta gyaɗa kai a sanyaye tana kallonta kafin ta maida dubanta ga yazeed da tuni idanunsa sun cika da kwallah, tace lafiya dai Alhaji?


Ya girgiza kansa cikin murmushin yaqe yace ba komai, hmmmm ya za'a yi da maganar kaciya ɗinta?


Abinda yafi muje da ita ayi mata na asibiti nafi son sa dana gida.


Yace nima haka nayi tunani kuma ba sai mun koma gida sokoto ba mu tsaya anan har ta warke tun da ko Yaya Abdallah bai san da zuwa na Abuja ba, kinga rufin asirin mu ne wannan ba wanda xai sani.


Ta gyaɗa kai cikin gamsuwa da shawarar shi tana shafa kan Ayusha a hankali cikin tausayi da jimamin yarinyar abinda ke ƙara ɗaure masu kai yake basu mamaki sam babu wani abu a zahiri game da yarinyar da zaka kalla kace namiji ce komai na halittar ta mace ce amma taya gwajin likitoci zai riqa nuna masu cewa ita ɗin namiji ce? Wannan sanin gaibu sai Allah wanda a nasu gani akwai abinda Allah ya boye game da Ayusha wanda su da likitocin babu wanda yasan gaibu.


Bayan kwana biyu aka yiwa yarinyar kaciya a lokacin ta fara damunsu da fitina gashi bata jin rarrashi, duk wani abu da batayi a da yanxu kam tana yinsa tunda aka yi mata kaciya, basu da nutsuwar zuciya ko hutu kullum kuka take acire mata bindi ita bata son bindi kamar na mage, bata son bindi kamar na Affan yaron maƙocinsu da ta taba ganin sa ba wando a gidan su.


Tasha ganin gaban ya'ya mata da maza musamman baƙi da suke yi a gidan su idan an cire masu pampers sunyi kashi ko kuma idan mamin ta taje gidan qawayen ta da ita tana gani amma babu mai irin nata abun yana bata mamaki bata san yanda zata fito tayi magana da mamanta akan hakan ba and a tunanin ta kowa da biyu ake haihuwar sa acire masa ɗaya wannan kaciyar da aka mata take tunanin ko itama zaa rabata da bindin ne amma sai taga sabanin tunanin ta wanda hakan ke sanyata kuka da rigima iyayen sun kasa fahimtar ta.


Mamee sai yaushe xaa cire min bindi ni bana so, maganar ta saka Halima juyowa tana kallonta a tsorace cikin mamaki, wane bindi kike magana za'a cire maki? Ta tambaye ta idonta akan nata, da yatsa Ayusha ta nuna mata hawaye na bin kuncinta, tace ni a maidani asibiti acire min wannan bana so .


Jim tayi cikin rashin sanin abin faɗa kafin daga bisani ta shafa kan yarinyar tana faɗin idan ya warke za'a je a cire maki ki daina kukan bana so.


Ayusha ta gyaɗa kai cikin gamsuwa.


Bayan wani lokaci ta warke sosai suka je da ita asibiti duk wani bincike da likitocin suka yi akanta sun tabbatar hormones na mace yafi qarfi a jikinta akan na namiji wanda har haihuwa zata iya, hakan ya qara rikitar da Alhaji yazeed da Halima domin duk inda suke zuwa ana gayamasu namiji yafi qarfi a jikinta akan na mace, bayan wannan kaciyar kuma an gano na mace yafi ƙarfi a jikinta akan na namiji, wannan abun akwai ruɗani acikin sa, daga baya likitocin sun ƙara mashi bayani namiji ko mace zasu iya zaba su barta amma idan zasu ƙara haƙuri zuwa yarinyar ta kai shekara 12 a ƙara tantancewa zai fi.


Wannan bayanin likitoci ya kwantar da hankalin Alhaji yazeed ya koma gida da murna sosai shi da matar sa Halima, daga baya suka yanke hukuncin zuwa da Ayusha ƙasar England domin ayi mata aiki acire halittar namiji a barta a mace ɗin ta, basa son wani bincike da zasu ƙara bayan shekara 12 bayan duk waɗannan da aka yi kuma sun yarda da bayanin likitan 100%.

washe gari suka tattara suka koma sokoto ba dan komai ba sai dan makarantar Ayusha, ansha rigima sosai da ita kafin ta yarda su tafi ita acewar ta baza su bar Abuja ba zasu cigaba da zama bata son sokoto.


*


Annam jikin ya tashi sosai daga ciwon ƙafafu sai hannu, daga ƙarshe sai da suka kwanta da ita asibiti aka sanya mata jini sa'anan ta sami sauqi sosai.


Ayi haƙuri da wannan pls.