AYUSHA

7

by @pherty001

©️Fertymerh Xarah💞





Wani abu yake damun Halima a zuciya wanda tana gani Allah bazai yafe mata ba idan bata nemi yafiyar yazeeed ba, amma ta yaya?


Ganin yanda mijin nata yake ta wahala ga damuwa daya saka sosai a ransa akan abunda ta ɗauki laifi ta ɗorawa kanta, ya kamata ta haƙura ta barwa Allah kan hukuncinsa.


Kallon Ayusha take da zuciya ɗaya tana jin ƙaunar yarinyar har cikin ranta, ta tabbata ɗiyar tace kuma jininta meyasa zata ƙi ta a kowane hali tazo mace ko namiji, ya kamata na saduda na haƙura da nawa ƙudirin ƙila nan gaba Allah zai bani wata haihuwa, ta faɗa tana ɗauke wata guntuwar kwallah dana zubo mata da ɗan yatsanta.


Why are you crying Mamee? taji muryar Ayusha wacce ta tsare mahaifiyarta da idanu cikin mamakin me zai saka ta kuka.


Kafin halima ta bata amsa ta cigaba da faɗin ke ba kamar Daddy bace shi kullum yana kuka, yau meyasa kike kuka ko Daddy ya dake kine?


Girgiza kai Halima tayi tana murmushi idanunta cike da hawaye tace meyasa zai dake ni Ayusha? Shima da kika ganshi yana kuka ƙaunar da yake maki ce ta janyo hakan ya damu matuƙa da yanayin da kike ciki amma insha Allah komai yazo ƙarshe.


Shiru Ayusha tayi cikin rashin fahimtar Mamee ɗin ta, sai ta tabe baki kawai ta cigaba da zanen da take yi tana colouring, shigowar yazeed ya saka ta ɗagowa tana kallonsa cikin murmushi cikin boye damuwar da take ciki, tana kallon yanayinsa kamar wanda yake cikin damuwa,


Akwai matsala ne ta tambaya tana kallonsa a sanyaye? Shi ma kallonta yayi tare da girgiza kansa yana faɗin jikin Annam ne ya matsa sosai wannan karon, yanzu yaya yake gayamin yanxu kusan leda uku na jini aka saka mata.


Innalillahi, Allah ka bawa yarinyar nan lafiya, ta faɗa cikin jimami tana kallon sa, dama da sanyi yazo haka masu sickler suke ta fama ina tausaya mata, ko zamu je mu duba tane?


Idan zai yiwu kafin mu bar ƙasar mu je asibiti mu ganta daga nan ma sai nayi sallama da yaya amma bazan gayamasa ga dalilin zuwa na wata ƙasa ba kawai dai zamu je hutu ne.


Ta gyaɗa kai a sanyaye batare da ta amsa ba, jikinta ya ƙara yin sanyi tana son magana tana tsoro da shakkun yanda zai karbi maganar, yanayin ta ya saka shi zuba mata idanuwansa masu hasken gaske, yanayi ne da bai saba ganin ta aciki ba yanayi ne dake nuna nadama akan wani abu, to meke damun ta?


Lafiya kike kuwa? ya tambaya still idanunsa akan ta, da sauri ta gyaɗa kai tare da mutmushin yaƙe tace ba komai lafiya, ya jinjina kai kawai batare da ya gamsu ba kafin ya maida dubansa ga Ayusha dake ta faman zanen gida da aka basu Assignment.


Yace mamana yau ba magana ne, ba zaki kula ni ba? ta ɗan dube shi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ta maida kanta kan abun da take yi tana yatsina fuska, dama bai yi tunanin zata amsa shi ba sai ya tashi yana kallon matar sa, zan shiga na kwanta kafin lokacin sallah sai ki tada ni.


Ta amsa tana kallonsa har ya fice kafin ta sauke numfashi tana dafe kanta da hannu biyu cikin tsoro.


*


Abba! Abba!! Abba!!! ni Ayusha nake son gani ka kaini gun ta please.


Is a long journey Annam, Abuja to Sokoto yanxu sannan kinga baki da lafia sosai kina buƙatar hutawa idan kika sami sauƙi ni da kaina zan kaiki.


Hawayen da take maƙalewa su ka zubo alamar da gaske take yi akan Ayusha take son gani, tace ba sai mu shiga jirgi ba.


Mtsew Mariya taja dogon tsaki cikin takaici, Allah ka shiga lamarina da Halimatu idan bata asirce min ya' akan y'ar ta ba, wannan jaraba da me yayi kama, babu inda zaki je ba jirgi ba ku shiga iska in gani.


Abdallah ya kalle ta cikin ƙunar rai kamar zai yi magana sai kuma ya fasa sanin a asibiti suke komai zai iya faruwa su zama abun kallo ,idan da sabo ya saba da waɗannan ba abun damuwa bane a gun shi matsalar y'ar cikin ta ma bata tausayin ta bata san ta rarrashe ta ba sai dai jifanta da ko wacce kalma ta fito bakin ta, 


Kuka take babu sassautawa a jikin mahaifinta, a hankali yake shafa bayanta tare da bata kalamai masu kwantar da zuciya cikin yi mata alƙawarin da ta sami lafiya zai ɗauke ta ya kaita inda Ayusha.


Abba ka kira vedio call na ganta to, da sauri ya ciro wayarsa gaban aljihunsa cikin farin cikin ya shawo kanta ta haƙura ya soma kiran ƙanin sa, ba jimawa ya ɗaga suka gaisa da tambayar ya mai jiki, anan yake bashi labarin rigimar Annam, cikin farin ciki yazeed ya fito ɗakin sa zuwa ɗakin Ayusha bayan sun saita kiran zuwa vedio call.


Annam na ganin fuskar Ayusha kan screen ɗin wayar ta saki murmushi cikin tsananin farin ciki, ta dubi mahaifinta kafin ta maida kallon kan wayar tana ɗaga hannunta,


Hy Ayusha...ta faɗa cikin murmushi.

Hyyy... itama ta bata amsa,


Didn't you miss me? Annam ta tambaya still cikin murmushi tana kallon Ayusha ganin babu farinciki a tare da ita.


ga mamakin su girgiza kai Ayusha tayi alamar bata missing ɗin Annam,


Why? Annam ta tambaya tana kallon ta a shagwabe, nan ma shiru Ayusha tayi cikin ƙaguwa da kallon wayar, Yazeed was not happy da yanayin Ayusha ya ƙago murmushin yaƙe yana kallon Annam ta cikin screen ɗin, yace karki damu da yanayin ta Mamee ta bata mata rai ne ta hanata Chocolate,


Oh sorry dear sis, ina da chocolate masu yawa Abbana ya siyo min, kuma ina da biscuits and sweets duka zan zo maki dasu kina so, ga mamakin su gyaɗa kai Ayusha tayi tare da murmushi wanda ya saka Annam farin ciki,


Tace harda ice cream kina so, cikin sauri Ayusha ta gyaɗa kanta tare da faɗin with cake and samosa i like them too,


Oh Ayusha duk ke kaɗai cewar Abdallah yana kallon ta cikin murmushi, Annam tayi sauri tace ai abba zaka siya mata duka ko, yace insha Allah.


Cikin farin ciki suka gama wayar, Ayusha ta dubi mahaifinta tana faɗin,


Daddy ina chocolate ɗin da kace mamee ta hanani?


Kallonta yayi kafin yace ai naga kinƙi ki saki fuska kiyi mata magana ne shiyasa, Annam tana son ki tana kula da ke atleast you can make her your friend. Ta girgiza kanta tare da tunzuro bakinta, no yayata ce not friend, i dont like friends. Why? ya tambaya cikin mamakin maganar ta,


Suna damun mutane, ni dai bana so daddy she is my sister ta faɗa kamar zatayi kuka alamar da gaske bata son ƙawa.


Yace shikenan naji bakyaso, amma idan ta ƙara kira ki riƙa sakin fuska kuna magana sosai, yayar kice she is my daughter too.


Ta gyada kai kafin tace chocolate ɗin fa, banda abinki Ayusha na taba hana ki chocolate, dama mahaifiyar kice take hanawa muje na mata magana yanxu zata baki.


**


Halimatu.......!!! ya kira sunan ta a hankali cikin muryar barci, ba zato taji muryarsa wanda hakan ya saka ta jin tsoro a tunanin ta barci yake.


Wai me yake damun ki, me kike boye min ne, kwana biyu na fahimci akwai damuwa a tare dake menene shi Halima?


Ba komai, ta faɗa a sanyaye tare da mai da kanta jikin pillow,


Yace babu komai amma kike zaune kina tunani, dama a zamantakewar mu akwai abinda zai dame ki da zaki kasa gayamin, menene yake hana ki barci.


Tace babu komai fa, kawai kai na ne yake ciwo.


Shikenan naji babu komai, yanxu zan bar maki ɗakin tunda ban isa na san damuwar ki ba, amma ki sani daga yau bazan ƙara zuwar maki ɗaki ba, ya soma ƙoƙarin sauka daga saman gadon da sauri ta riƙo hannunsa cikin marairacewa tana kallon sa,


Meyasa zaka min haka, duk tsanani ko menene faɗan mu da fushi bamu taba yiwa juna yaji ba.


Yace tabbas haka ne amma wannan dole ta saka nayi maki haka, ban taba boye maki damuwa ta ba amma yau ni kike boyewa taki famuwa tukunna ma me kika ɗauke ni a zuciyar ki wane matsayi kika bani.


Rungume shi tayi tsantsa kamar zata shige jikinsa, rungumar da bata taba yi masa irin ta ba yanda ta matse shi sosai a jikinta, cikin kuka 


Tace ka yafe min, nayi maka laifi mai girma wanda tunanin hakan ya sakani damuwa da ruɗani, ina tsoron Allah ya kamani da haƙƙin ka akaina dan Allah ka yafe min Yazeed.


Tun da yaji ta ambaci sunan sa hankalinsa ya tashi abinda bai taba ji ba, kukan ta ya ƙara rikita shi jikinsa ya ɗauki rawa, kada dai Halima tana cutar shi ne bai sani ba, cikin ƙarfin hali irin na ɗa namiji ya tallabo fuskarta dab da tashi suna shaƙar ƙamshin juna idanun sa ya zuba mata bazata jure kallon kwayar idanun sa ba ta maida ta rufe,


Na yarda dake Halimatu, nasan duk girman laifin da zaki min bazaki abinda zai cutar dani ko rayuwata ba, koma menene na yafe maki tun kafin naji amma dont break my trust, i mean s... tayi saurin katse sa ta hanyar ɗora hannunta kan bakinsa,


In dai ta wannan ne bazan taba cin amanar ka ba, na san daraja da mutuncin aure na bayan haka ina matuƙar son ka ina son kasancewa da kai har ƙarshen rayuwar mu, bazan iya cin amanar ka ba Abban Ayusha ta faɗa cikin kuka.


Yace to menene, ki gayamin naji menene yake damar dake haka kike min asarar hawayen ki masu tsada?


Ta sunkuyar da kanta ƙasa tana share hawayen fuskar, taja numfashi kaɗan kafin tace Dr Wahab likitan da muka fara gani da farko bayan haihuwar Ayusha gaskiya ya gayamana akan zabin daya bamu, amma likita na biyu da muka gani bayan ta shekara biyar abinda ya faɗa da result da muka kai wasu da gaske ne wasu kuma i bribed the doctors, ma'ana ina da sa hannu cikin son mai da Ayusha Namiji saboda namiji nake so na haifa ba mace ba.