AYUSHA

8

by @pherty001






Shiru yayi yana kallon ta jikinsa a mace, he cant believe abinda kunnuwan sa suke jiye masa,yana son ƙarin bayani sosai yanda zai fahimce ta, Bangane me kike magana akai ba Halima, ta yaya kike son mayar da Ayusha namiji? Jikinta yayi sanyi daga kallon yanayin fuskarsa, wasu sabbin hawaye suka soma zarya a kumatun ta, tace kayi min afuwa Abban Ayush ka yafe min nayi kuskure sanin haka yasa nake nadama, na sanya ka a damuwa akan abunda xamu iya maganin sa cikin lokaci ƙanƙani, results na Ayusha da muke ƙarbowa duka gaskiya ne cewa halittar namiji yafi ƙarfi a jikinta, amma ni nake magana da likitocin su nuna cewa tabbas bazata iya zama mace ba, kafin lokacin komawar mu asibiti mu kai result ni naje na sami likita da wannan alfarmar cewa ayiwa Ayusha kaciya kuma akayi sa'a ka yarda da hakan, a tunani na maslaha ne gare ka zaka haƙura da kasancewar ta mace a maida ta namiji, hankalina ya tashi da naji kana maganar fitar da ita waje ayi mata aiki da yanda suka ƙarfafa maka gwiwar cewa zata iya zama mace. Meyasa yanxu kike gayamin haka?

Saboda na sanya ka a damuwa kuma nayi abinda bashi ne kan hanya madaidaciya ba, ta faɗa tana kallonsa dan Allah ka yafe min mijina. Ajiyar zuciya yayi yana kallon ta kafin yace ni ban ɗauki wannan wani abun damuwa da zaki zauna kina kuka haka ba, illah son zuciya meyasa zaki cutar da y'ar ki har ki bari ayi mata kaciya saboda wani ƙudiri naki, duk lallami da ban baki da kike bani akan na haƙura da zamanta mace ashe da gayya kike yi halima, haba biri yayi kama da mai yanda kike nacewa akan na sallamawa zuciyata na hakura, wallahi da wani yazo min da wannan maganar cewa ke kika aikata zan iya shari'a dashi ko waye shi amma ke kike zuwa Halima ki sami wani ki haɗa baki dashi dan a cutar dani? Meyasa bazaki zauna dani ki gayamin naki ra'ayi akan abinda kike so ta zama ba, ke fa mahaifiyar tace kuma kina da haƙƙi akan ta. Kuka take sosai tace kayi haƙuri wallahi na haƙura na yarda da zabin Allah akan zamanta mace kuma na yarda da zabin ka, me yiwuwa nawa zabin yana gaba idan da rai da rabo, dan Allah kayi haƙuri ka yafe min kada kayi fushi dani mijina. Rungumar da tayi mashi ta ƙanƙame shi ya saka shi ajiyar zuciya, amma a ransa cike yake da mamakin ta wallahi da ba itace ta faɗa da bakinta ba bazai taba yarda zata iya aikata hakan, amma duk ta yaya taje tayi wannan shirin bashi da labari, baya so yaji shiyasa bazai tambaye ta ba amma zuciyarsa sai hasko masa photon ta da wani namiji zaune suna magana yake, hannu yasa ya zame ta daga jikinsa a hankali ya sauka daga saman gadon ya nufi hanyar fita da sauri ta bi bayansa tare da riƙo hannunsa, ta zagaya zuwa gabansa tare da saurin kai gwiwowin ta ƙasa irin na masu neman afuwa, "Dan Allah kar kayi fushi dani mijina, zuciyata bazata jure hakan ba wallahi ina son ka ina son duk wani abu da kake so, sanadiyar damuwar dake ranka ce ta sakani bayyana maka gaskiyar zuciyata Kuma zan iya zuwa na nemi yafiyar Ayusha akan jinya dana saka ta, amma kasani har cikin zuciyata na amince da aikin Ayusha na amince da acire halittar namiji a barta mace. Kamar bazai yi magana ba da kyar yace abinda ban gane ba Halima kina zuwa kina zama da wasu maza likitoci kina neman alfarmar kan a boye min gaskiyar Ayusha, saboda me, And how sure su basu nemi wani abu a gurin ki ba. Subhanallah ta faɗa cikin rawar murya duk jikinta ya ɗauki rawa saboda tsananin firgicin inda maganar sa ta dosa, "ka kyautata zato mai kyau gare ni mijina, bazan taba cin amanar ka da kowa ba, ba halina bane abinda kake tunani, kuma babu wanda ya nemi komai daga gare ni ko da na sisi ne sannan bani kaɗai nake zuwa ba tare da ƙanwata Nana da ita Ayusha". Yace idan na fahimce ki Nana ta san sirrin da muke boyewa game da Ayusha tunda tare kuke zuwa yin komai" tace "wallahi ba abinda Nana ta sani idan mun je tana tsayawa a reception ni da Ayusha mu ke shiga idan ta tambaye ni na kan ce bata da lafiya ne zamu ga Doctor ka da kayi zargi na da aikata wani abu mijina". Shiru yayi yana furzar da iskar bakin sa har yanxu ya kasa samawa abinda Halima tayi matsayi a zuciyar sa ya rasa ta yanda zai ɗauki abun, jin shirun sa yasa ta qara riƙe qafafun sa gam tana mai cigaba da neman afuwa cikin kuka, bazai iya jure kukan ta ba koda kuwa ace laifin da tayi masa yafi wannan girma, yana matuƙar son Halima so bana wasa ba duk yanda ransa zai baci akan ta baya jimawa yake mantawa, ɗagota yayi daga ƙasa ya haɗata da jikinsa tare da shafa bayanta cikin alama ta rarrashi, dalilin haka ya sanya Halima samun nutsuwa ta san ko ba komai tunda yayi mata hakan ya haƙura kenan, a hankali ta soma rage sautin kukan ta tana mai da numfashi a hankali, ta yarda da hukuncin Allah Ayusha macece tana roƙon Allah ya sake bata wata haihuwar ta sami namiji, ita haka kawai Allah ya ɗora mata son ya'ya maza bazata ce ga dalili ba, sun ɗauki tsawon lokaci a hakan kafin daga bisani ya ɗagota daga kafaɗarsa yana kallon ta, "yace abinda kike so ko bana so zan iya yi maki shi ko menene ballantana akan abun da kike da haƙƙi akan sa, ke kika ɗauke ta tun Day 1 har zuwa haihuwa, wahalar naƙuda laulayi da sauran su duk kece kika yi meyasa zan so buƙata ta akan taki, na amince a maida Ayusha namiji idan har zuciyar ki tafi amince wa da hakan amma ki min alƙawari guda bazaki saki kwatanta laifi irin wannan ba, bazaki sake boye min duk wata damuwa dake ranki ba". Girgiza kanta tayi da sauri tana faɗin "wallahi na haƙura Ayusha macece a idon mutane damu, kuma haka zata cigaba da rayuwa idan har ka ɗauki nawa buƙata akan naka tabbas ka nuna min baka haƙura ba, zamu je da ita ayi mata aiki idan anan nigeria kake so ko kuma England da kayi magana amma ni ya'ta macece kuma har a zuciyata hakane". Murmushi yayi tare da ɗora yatsansa akan bakin ta yace "za muje England acan za'a yi mata aikin insha Allah, fatan mu muyi mata addu'ar dacewa tunda acan sun gayamana zata iya rayuwa da kowane halitta muke so. Itama murmushin tayi tare da mai da kanta jikin sa cikin tsananin farin ciki.


*


"Mamee ni yau bazan je school ba ki gayawa Daddy" kallon ta Halima tayi kafin ta cigaba da haɗa breakfast "tace ina so naji dalilin da zai hana maki zuwa school". "Ni bana son zuwa school bazan je yau ba ki bari har gobe" ta faɗa kamar mai son yin kuka hakan yasa halima tsayawa cak tana kallon ikon Allah tun da suke da ita bata taba cewa bata son zuwa school ba sai yau abin mamaki har da hawaye, "tace to ki gayamin dalili mana, haka kawai bazaki je school ba ko baki da lafiya ne? ta faɗa tana taba jikinta babu wani alamun zazzabi a tare da ita, suna haka yazeed ya shigo cikin doguwar jallabiya tare da key ɗin mota a hannunsa alamar zai kai Ayusha makaranta, tana ganin sa ta nufe sa da gudu ta rungume shi tana kuka, "waya taba min mamana yau har da kuka da uwar safiyar nan" ya fada yana ɗaukar ta zuwa kirjinshi. " rigima take ji wai bazata je school ba, ta gayamin dalili taƙi kuma babu wani alamun rashin lafiya a tare da ita". "Wai hakane ? Ya tambaya yana kallon Ayusha, ta gyaɗa kai cikin hawaye "tace ni bazan je school ba daddy ni bana son zuwa yau" "menene dalili? ya tambaya in a calm voice yana kallon ta, tayi shiru sai goge kwallah take ita kanta bata san dalilin rashin son zuwan nata ba, juyin duniya yayi da ita ta kafe akan bazata je ba, rarrashi babu irin wanda bai yi mata ba taƙi yarda, dole ba yanda ya iya yace " a barta mamee tun da tace bazata je ba for today

Only, bata taba haka ba ayi mata uzuri". tabe baki kawai Halima tayi cikin mamakin yanda ya biye mata, Ayusha kuwa murmushi ta soma yi tare da kallon sa ga mamakin sa sumbatar sa tayi a kumatunsa wanda hakan ba ƙaramin farin ciki ya saka shi ba, tare suka nufi dinning domin yin breakfast.


Cikin wata ɗaya suka gama shirye shiryen tafiyar su Engalnd sun yi sallama da yan uwa da abokan su anan cewa zasu tafi yawon buɗe ido da Ayusha, ta jirgin Abuja zasu tafi dan haka sai suka kama hanyar tafiya Abuja, da ace yazeed yana da sani akan abunda zai faru a gaba da tafiyar jirgi zasu yi daga sokoto to Abuja, amma tsautsayi baya wuce ranar sa komai wayon mutum da dabarar sa, tafiyar mota suka yi wannan karon wanda a hanyar su ta tafiya suka haɗu da mummunan hatsari tsakanin kaduna to Abuja, Yazeed da Ayusha basu ƙara sanin inda kan su yake ba a sume aka ɗauke su mutanen da suka kawo masu taimakon gaggawa yayin da Halima nan take rai yayi halinsa.