9
by @pherty001
©️Fertymerh Xarah💞
Da taimakon wayar da aka samu a motar suka yi ƙoƙarin neman yan uwan masu hatsarin, cikin ikon Allah wayar yazeed aka samu kuma har akwai missed call ɗin ɗan uwa akai, sai suka yi ƙoƙarin kiran number, bugun farko aka ɗauka tare da faɗin "haba yazeed ina ka ajiye wayar ne tun ɗazu nake faman kira, hankalina ya tashi sosai saboda fargaba da nake fama da ita tun lokacin da ka kira ka sanar dani zaka zo Abuja yau, ka daina wasa da ɗaukar kira". Aka yi gyaran murya tare da faɗin bashi bane kayi haƙuri mu haɗu asibitin Abuja. Cikin tsoro da fargaba Alhaji Abdallah "yace meya sami ɗan uwana, waya ke magana ko ka tsinci wayar ne, dan Allah ina mai wayar yake haɗani dashi" yace "mai wayar ya sami hatsari tare da iyalinsa mun bashi taimako ne mun fito dasu acikin motar yanxu zamu ƙarasa dasu cikin abuja akai su asibiti domin a basu taimakon gaggawa, sai ka hanzarta ka same mu acan, amma wace asibiti zaa kai su? Cikin sanyi jiki da murya yace "Maitama District Hospital " ya tsinke wayar tare da faɗin innalillahi wa inna ilaihir raji'un, mariya dake zaune a dinning ta juyo tana kallonsa "meya faru Alhaji, ko daga company ne aka yi maka waya? yace "yazeed ne yayi hatsari mariya akan hanyar su ta zuwa". Tace " kuma dai, to Allah ya kyauta gaba" cikin halin ko in kula tayi maganar alamar abun bai dame ta ba, bai ƙara bi ta kanta ba ya fice daga gidan da sauri, tsaki tayi tana binsa da harara "duk an bi an asirce ka in dai magana ce akan wannan yazeed sai ka riƙa rawar kai, ba laifin ka bane laifin malamin Halima ne bai barka a baya ba, shiyasa ake ƙoƙarin rabani da kai". A asibiti da kyar aka samu aka ceto rayuwar Ayusha, sai dai tana kan oxygen bata san inda kanta yake ba, haka ma yazeed is unconcious duk ƙoƙari irin nasu abun ba sauƙi, Halima kuwa tuni rai yayi halinsa haka ya karbi gawar ta xuwa gidan sa bayan yayi ƙoƙarin kiran yan uwanta dake sokoto da wayar yazeed ya sanar dasu halin da ake ciki. Tun da mariya ta ƙyallah ido taga gawar Halima kwance a falonta cikin jini taji hankalinta na neman gushewa taji duk wata ƙiyayya ta fita ranta, wata nadama take ji a zuciyarta idanunta cike da kwallah ta dubi Alhaji Abdallah da ƙarfin hali ne kawai yake yi a matsayin sa na ɗa namiji," Abban Annam da gaske babu Halima, da gaske ta bar duniya innalillahi". sai ga hawaye "lallai duniya baa bakin komai take ba musamman ɗan adam ki yafe ni Halimatu". Mahaifin Halima ta jirgi ya biyo yaxo Abuja zuwansa bada jimawa ba akayi mata abunda musulunci ya tanadar ga mamaci kana suka kaita gidan ta na gaskiya. Kwana uku da rasuwar ta yazeed ya farfaɗo bakinsa babu abinda yake faɗa sai Halimatu da Ayusha, nurses suka je suka sanar da likitoci bada jimawa ba suka ƙaraso, idanu ya xuba masu duk da fuskarsa duka a kumbure har idanunsa hawaye yake sosai yace "likita ina matata da ya'ta su kaɗai nake son gani, ina cikin azaba a yanzu haka likita komai nawa ciwo yake ka taimaka ka cire min wannan ciwon dan Allah". Yace " insha Allah zaka sami sauƙi ka tashi kamar farko, sabon ciwo dama haka xaka ji ciwo sosai kafin ya fara tafiya a hankali a hankali idan kana karban treatment, fatan mu ka kwantar da hankalin ka kada ka saka damuwa da zata iya haifar ma da wani ciwo daban". Yace 'Matata da ya'ta suna lafiya doctor? "Eh suna lafiya suma suna karban nasu treatment" likita ya faɗa cikin ƙoƙarin rufe masa gaskiyar matarsa ta rasu, Ayusha ta farfaɗo tana tare da Abdallah babu abinda take ambato sai mamee da dady, yazeed ya ƙara kallon doctor tare da faɗin "ka haɗani da yayana dan Allah" "ok ba damuwa" cewar doctor yana kallon ɗaya daga cikin nurses ɗin "ki kira shi a paediatric yanxu" shima likitan ya juya ya fice. Bada jimawa ba Abdallah ya shigo da hanzarin sa hannunsa riƙe dana Ayusha ya nufi ɗan uwansa kamar zai yi tsalle ya faɗa jikinsa saboda tsananin murnar ya farfaɗo, yace 'Allah ubangiji ya tashi kafaɗar ka ya baka lafiya ɗan uwa" sai ga ƙwallah na bin kumatunsa ya ƙara da cewa "duk su gwaggo da uncle sun zo amma kana barci yanxu haka suna can gidana bari na kira su domin sun ƙagu su ganka ka farka suna cikin tsananin damuwa" ya soma ƙoƙarin danna wayarsa da ƙyar yazeed ya ɗaga hannunsa da yayi masa nauyi ji yake kamar bana shi bane ya riƙe hannun Abdallah shima Abdallah kallonsa yake ya girgiza masa kansa alamar kada ya kira kafin ya juya yana kallon Ayusha suna haɗa ido dashi tayi saurin boyewa bayan Abdallah alamun tsoro ƙarara a fuskarta, " i dont want to see him Abba, he looks ugly, take me to my Parents please" ta faɗa kamar zata yi kuka, a hankali yazeed ya lumshe idanunsa sai ga hawaye masu zafin gaske suna kwaranya a idanun sa, Abdallah ya saka hannu ya janyo ta zuwa gabansa tayi saurin rumtse idanun ta da gaske fuskarsa tsoro take bata yanda ta kumbura idanunsa suka yi ja alamar kwanciyar jini a cikinsu yake bata tsoro ta ƙanƙame Abdallah sosai "please take me to Daddy and Mamee, i dont want to stay here" "wannan shine Daddy Ayusher, just look at him kinƙi kallonsa da kyau ne ya saka kin kasa gane shi" cak ta tsaya tare da ɗago kanta tana kallon Abdallah cikin mamaki ya gyaɗa kansa cikin tabbatarwa tare da riƙo hannunta ya haɗa dana yazeed wuri ɗaya "ki kalle sa da kyau abinda kike gani a jikinsa accident da kuka samu ne ya canza sa xuwa haka" da sauri ta juya tana kallon yazeed tsura masa ido tayi sosai cikin son tabbatar da zancen Abdallah la shakka wannan shine daddy ta sai ta juya da sauri tana kallon ɗakin kamar mai neman wani abu kafin ta juya cikin tsoro tana kallon Abdallah " then mamee fa, where is she? Yace " kiyi magana da daddy tukunna zan kaiki inda mamee she is fine." babu zato babu tsammani sai ganinta suka yi jikin yazeed kaɗan taji masa ciwo Abdallah zai janye ta daga jikinsa yazeed yayi saurin ƙanƙameta cikin tsananin azabar da yake ji a jikinsa sai ya fashe da kuka, kuka mai tsanani kukan daya ɗaga haankalin Abdallah domin bai taba jin irin sa daga yazeed ba, shima sai ya soma nashi kukan duk iya juriya yau ya kasa yin ta, tayaya zai iya fuskantar wannan family masu tsananin son junan su ya gayamasu ɗaya daga cikin su ta zama babu a duniya, no bazai iya ba dole yan uwansu su zasu sanar dashi idan ya sami sauƙi. " My daddy, my daddy i love you so much ta faɗa cikin kuka." ta dubi Abdallah tace "kace likita yazo yayiwa daddy na allura fuskarsa da idanunsa su dawo normal muje gida." da kyar suka shawo kanta ta yarda ta daina kukan sai dai tana jikin yazeed kwance tana mai da numfashi yace " yaya dan Allah kada ka boye min komai ka gayamin gaskiya idan Halima tana raye, ina jin wani abu a jikina kamar wani abu ya same ta tun daga lokacin da naji Ayusha ma bata saka mahaifiyar ta a ido ba, ni musulmi ne nasan ƙaddara kuma nayi imani da jarabawa ta ubangiji ko wacce iri ce amma rashin gayamin haƙƙiƙanin gaskiya zai saka zuciyata kwankwanto da tunani." Abdallah yace " indai har abinda ka faɗa da gaske kake to ka bari ka sami lafiya tukunna zamu yi maganar tare da su gwaggo." yace "ta yaya kake da tabbacin zan iya kai gobe? Cikin tsananin faɗuwar gaba Abdallah ya zare ido yana kallon yazeed "wannan wace irin magana kake yi yazeed, ciwo ai ba mutuwa bane, mutane nawa suka yi hatsari suka ji rauni fiye da naka kuma a yau suke rayuwa kamar ba'a yi ba, kada ka bata min rai daga farin ciki da nake ciki na farfaɗowar ka." yace " ka sanar dani matata tana raye ko babu ita? ya faɗa tare da kafe Abdallah da ido yana son samun amsa daga yanayin sa, cikin ruɗani Abdallah ya girgiza kansa yana tsuke fuska, " wai me kake nufi ne yazeed meyasa kake kirawa kanka mutuwa kake kirawa Halimatu, na gayamaka tana raye illah ta fiku jin jiki ne..... yayi saurin katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu, " na sami amsa ta a tare da kai yaya, karka manta ni ƙanin kane uwa ɗaya uba ɗaya na fi kowa sanin ka, halin ka, da ɗabi'un ka fiye da kowa koda matar kace, daga yanayin ka na gane matata bata raye." sai ya fashe da kuka ya kasa dannewa tare da faɗin "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Ayusha ta ɗago tana kallonsa cikin mamakin meya saka mahaifinta kuka yau, hannu tasa tana share masa hawaye "stop crying daddy, kana jin zafi ne a kira likita ya cire maka pain, sorry daddy." ta faɗa cikin shigar rarrashi kamar yanda yake yi mata idan bata da lafiya " Abba a kira likita ya cire masa ciwon ka gani daddy na yana kuka bana so yana kuka." ta faɗa tana kallon Abdallah, "kaima kuka kake yi, kaji ciwo ne? to amma ai baka cikin motar mu ba tare muka yi accident da kai ba? Yayi saurin goge kwallar sa yana murmushin yaƙe, haka shima yazeed, ya ɗago a hankali yana kallon sa" tun yaushe ta...ya katse sa, "yazeed dan Allah ka huta idan jikin ya warware duka zamu yi magana, kuma kada ka ɗauki damuwa ka saka a ranka dan Allah na roƙe ka zan tafi da Ayusha gobe zamu dawo da ita, itama baa sallame ta kada likito ci suzo suna neman ta." ta maƙale kafaɗa, " i dont want to go ina so na zauna da daddy na" yazeed ya dube ta tare da faɗin " zamu kasance tare har abada Ayusha bazan bari kiyi maraici na rashin uwa ba, kiyi haƙuri anjima kaɗan idan doctor yazo yayi min allura na daina jin zafi zan zo da kaina tare zamu yi barci." murmushi tayi mai bayyana farin cikin jin kalamansa babu gardama ta saƙala hannunta da hannun Abdallah suka juya tana ɗaga masa hannu shima haka yazeed.