10
by @pherty001
Lumshe ido yazeed yayi, duk yanda ya so da kau da tunanin Halima ya kasa, yana tuna farkon haɗuwar su, auren su, haƙurin ta, murmushin ta, komai nata gizo yake masa a idanuwansa, he can't believe wai yau babu Halimatu, taya zai iya rayuwa babu ita shi da Ayusha, ya rumtse idanuwan sa hawaye masu zafin gaske suna cigaba da kwaranya , ta ya yayan sa Abdallah zai ce kada ya saka damuwa a ransa ya kuwa san zafin rabuwa da mata ko miji? tsawon kwana biyu a kullum sai an kawo masa Ayusha wani lokacin da kyar take yarda ta barshi a koda yaushe babu lokacin da bata kuka tana so taga mameen ta da kyar suke shawo kanta, jikin yazeed kuwa yana sauƙi sosai kumburin ya fara tafiya haka ciwon jikinsa ya soma warkewa illah azababben ciwon kai da yake fama dashi, dalilin haka likitoci suka turashi x-ray domin a gano matsalar da take damun sa, duka family ɗin suna tsaye suna jiran fitowar likitoci da yazeed yayin da Abdallah sai kai da kawowa yake hannuwan sa duka biyu goye a bayan sa, Ayusher kuwa tana tare dashi duk inda ya jefa ƙafa tana bayan shi, bata yarda da kowa ba kuma kowa bata sani ba bayan shi, sanadiyar zamanta asibiti zuwan da yake suka sami kusanci sosai a tare dashi da Annam da wani lokaci ake zuwa da ita, sai Nana ƙanwar mahaifiyar ta, bayan su duka dangin mahaifinta ba wanda ta yarda dashi ko mariya bata son gani yanda take ganin tsanar ta a idanuwanta tana yawan hararar ta bata san dalili ba, suna tsaye aka fito dashi xuwa ward ɗin da aka kwantar dashi, yazeed ya tsurawa mutanen dake ɗakin ido duka dangin sa ne yaji wata ƙwallah ta zo masa cikin farincikin wannan soyayya daya gani yau a wurin yan'uwan sa, yace " nagode sosai da kulawa da addu'ar ku a gare ni, babu abinda baki zai iya furta maku a yanzu sai dai farin cikin dake fuskata amsa ce a gare ku akan daɗin da nake ji, sai dai ina neman alfarma ɗaya a wurin ku, soyayya da kuke min ina so ta juya kan ya'ta Ayusher Ma'ana ku so ta fiye da son da kuke min ko kuma ni wanda nake mata, ku kula da ita da bata tarbiya fiye da wacce zamu bata ni da mahaifiyar ta, dan Allah kada ku bari tayi kukan maraicin mu......duk suka zuba masa ido cikin mamaki da tsoro suna kallon sa, Hajiya Asmau tace "meyasa zaka ce haka Yazeedu, ai ciwo ba mutuwa bane ka duba da kyau kaga duk wurin nan babu bare duka dangi ne na wajen mahaifiyar ku da mahaifin ku sai waɗanda basu samu zuwa bane kawai babu anan, sannan dukkan mu munzo daga wurare daban daban, gari daban daban saboda nuna maka ƙauna da alhini akan halin da kake ciki, meyasa bazaka gayamana kalamai da zasu kwantar da hankalin mu sai kake magana wacce babu daɗin ji. Murmushi yayi ya dubi Abdallah har zai yi magana sai idanunsa suka sauka akan Nana, yace " Nana kema kinzo kenan, kinji abinda ya faru da Halimatu ko, ki ɗauki wannan tafiyar tamu a matsayin ƙaddara da bawa baya wuce ranar sa, da nasan zan rasa Halima tabbas baza muyi tafiyar ba, amma abune da Allah ya riga ya rubuta ajalinta yana ta wannan hanyar, ki kula da y'ar ki Ayusha tamkar ke kika haifeta, sai ya fashe da kuka mai tsanani yana faɗin " dan Allah ku kula min da ita, ku bata tarbiya, ku bata gata kada ku bari tayi kukan rashin mu, kada ku bari ta taso tana inama ace iyayena suna raye ni dai na baku amanarta, ko da kunsan asalin wacece ita kada ku ƙyamace ta. Da yawa mutanen dake ɗakin suka soma ƙwallah wasu suka kasa haƙuri suka fice daga ɗakin da gudu jikinsu yayi sanyi da kalamai da yazeed yake yi a yau kamar wanda zai mutu, meyasa yake basu wasiya haka? Mariya da yake akwai sauran imani a zuciyarta a yau taji tana nadamar abubuwan da ta aikatawa yazeed, idanunta cike da kwallah ta dube sa karo na farko a rayuwarta da wata kalma mai daɗi da ta fito a bakinta zuwa gare shi," tace yazeed dan Allah abubuwan da nayi maka a baya ka yafe ni sharrin zuciya ne, nayi nadama tun daga lokacin da Halima ta bar duniya, damuwata ɗaya ban samu na nemi gafarar ta ba." yace " na yafe maki Mariya, na yafewa kowa anan nima ina neman alfarmar duk wanda na taba batawa da ya yafe min." haka suka yini ranar kowa jikinsa a sanyaye har dare duk suka koma aka bar Abdallah da Ayusha dama shi anan yake kwana dashi, Ayusha kuma Nana take kwana da ita tare da Hajiya Asmau. Bayan Abdallah ya gama cin abinci tare da Ayusha ya dube ta " ki cewa daddy good night sai muje na raka ki nasan Nana tana jiran ki." ta tashi ta nufi inda yazeed yake kwance cikin tsananin azabar ciwo wanda shi kaɗai yake jin haka ta sumbace sa a goshi da kumatunsa as usual yanda take masa a kullum," i will miss you Daddy" murmushin yaƙe yayi cikin zuba mata manyan idanuwan sa, "zan fi kowa kewar ki Ayusha, na roƙi Allah ya raya ki bisa tafarkin musulunci, ya albarkaci rayuwar ki Ayusha" cikin murmushi tace "Amin." Abdallah ya riƙa hannunta zasu tafi yazeed ya riƙasa wani zafi yaji a hannunsa ya dubi yazeed a razane yace " kaji zafin jikin ka kuwa, kana jin zazzabi shine bazaka yi magana ba, bari na kira doctor." a'ah yaya ko ka kira babu abinda zai iya min, ni kaɗai nasan abinda nake ji a jikina kuma ni kaɗai naji abinda likitocin suke faɗa a yau wurin x_ray, dama ina son magana da kai akan Ayusha, bani da haufi akan kulawa da zaka bawa Ayusha, ina so ka riƙe ta amana ka bata gata kamar Annam ka kula min da ita, duk ƙasar da take son karatu ka kaita, ina da manyan ƙaddarori masu yawan gaske kuma nasan zaka juya mata su har ta kai matsayin da zata mallaki hankalin kan ta, duk abinda take so ayi mata." Abdallah yace " yazeed kana bani mamaki, Ayusha ya'ta ce jinina ce haka nake jin ta kamar Annam a zuciyata, ko da kuɗin ka ko bada kuɗin ka ba zan iya ɗaukar nauyin ta da karatun ta kowacce ƙasa take so a duniyar nan, kuma xan bata farinciki wanda ko kana raye iyakar abinda zaka iya yi mata kenan, meyasa kake nuna min abina ba naka bane, naka kuma na y'ar ka ne kawai? Yace " kayi haƙuri yaya ba abinda nake nufi kenan ba, akwai rai akwai mutuwa kuma akwai hali irin na matar ka na gori, ina tsoron watarana mariya ta bijire akan bazata zauna da Ayusha ba kamar yanda tayi min, ina tsoron mariya ta.....Abdallah ya katse sa cikin ajiyar zuciya " na fahimce ka hakan bazai taba yiwuwa ba idan har Ayusha zata bar gidana to Annam ma zata bar shi, duk duniya ta shaida kuma ta sani kaine mahaifin ta kai ka haifeta amma duk wata soyayya da kulawa babu wacce bazan iya yi mata ba ka kwantar da hankalin ka, na riƙe ka da amana na zauna na kula da ci da sha, na kula da sutura da wurin zaman ka, na kula da karatun ka tun rasuwar iyayen mu ballantana abinda ya fito cikin ka? Murmushi yazeed yayi cikin gamsuwa da kalaman yayan sa yace " nagode yaya Allah ya saka maka da Al'jannah akan ɗawainiya da kayi tawa tun bayan rasuwar iyayen mu, Allah shi zai biya ka, abu na biyu kayi haƙuri nayi ma babban laifi amma ka ɗauki hakan a matsayin wani sirri ne na rayuwata wanda ko yanzu dole ce ta saka zan gayama, ban boye maka ba dan baka da matsayin da zan gayama na boye maka ne dalilin matar ka mariya saboda idan ta san da wannan maganar tabbas duk duniya zata san wacece Ayusha, kuma dalilin haka wasu zasu iya ƙyamatarta, amma kayi min alƙawari bazata taba sanin wannan sirrin ba har sanda zaka cika min burina dana Halimatu". Abdallah yace "menene shi yazeed, akwai sirri da yawa dake tsakanin mu wanda har yau mariya bata san da shi ba, ni ba namiji ne mai yawan surutu da komai sai ya gayawa matarsa ba, tun farko da baka boye min ba kona sani bazata taba sani ba, shin menene ke da Ayusha wanda kake gudun mutane su guje ta ko su ƙyamace ta, ni har ynxu idanuwana suna tunani akan ta na kasa gano wani aibu a tattare da yarinyar." sauke numfashi yazeed yayi da kyar kafin ya soma bashi labarin komai tun daga haihuwar Ayusha har kawo ynzu da sanadiyar accident ɗin su, ya qara da cewa " yaya cikin biyu nake so kayi min ɗaya ka ɗauke ta ka kaita waje ayi mata aikin batare da kowa ya sani ba ita ɗin mace muke so nida mahaifiyar ta shine burin mu, ka cika mana wannan burin yarinyar mu ta kasance mace." " nayi mamaki yazeed da zaka boye min babban lamari irin wannan, har kake zirga zirga zuwa nan asibiti abuja baka taba sanar dani ba banji daɗin hakan ba, ya riƙo hannunsa yana kallon cikin idanuwan sa " na yi maka alƙawari duk inda zan kai Ayusha ayi mata aiki mariya bazata taba sani ba kuma insha Allah idan ina raye sai na tabbatar da anyi aikin an cire mata halittar namiji dake jikinta na cika maku burin ku na kasancewar ta mace." yace " nagode yaya, nagode nagode.....
Washe garin ranar da asuba jikin yazeed yayi tsanani, aka kira doctors da gudu suka shiga ɗakin, duk wani ƙoƙari nasu sun kasa ceto rayuwar sa, Rai yayi halinsa, Allah ya gafarta masa.