48
by @mshakur
EPISODE 4️⃣8️⃣
Kusan duka yaran gidan babu wanda yasan akwai wani abu dazai faru yau Baffa dai yasa Baba karami yasayo drinks harda su Maltina da ruwan gora, matan gidan kuma harda Ammi aka hau girki yaran gidan kuma duk suka tafi school, Baba sabida haushi tun 6 yatafi aiki Baffa dai saida yakirashi ya jaddadamai biyu tamai agida, Yasmeen 9 ta tafi school abinta yau har 6 takeda lectures.
Ana idar da sallan juma’a Baba yadawo gida gidan an gyara yay kal kal an shimfida manya manyan tabarmai a compound kasan bishiya girgixa kai kawai yayi yawuce ciki wanka yayi ya shirya cikin babban kaya harda Malum Malum da hula ya fesa turare yafito waje daidai ana sallama Baffa ya kalleshi yace “muje mu shigo dasu” baiyi musu ba suka fita atare, Hamad ne ke tuki sai Maheer agefenshi Maheer yasaka wata faran shadda jumper da hulan Hamad akai wlh kaga Mageer zaka dauka ango ne, Malam Sani da Baba sai limamun anguwan su wanda yake abokin Baba ne sosai, duk suna tsaitsaye Baba yafara fitowa daga gidan kallo daya Maheer yamai yasauke kanshi kasa sabida yanda Baba yamai wani kalan kwarjini a ido gaisawa su Baba sukayi dasu Malam Sani hakan yasa Hamad yataho tareda dan jan Maheer daya kasa motsi Malam Sani yace “surukin naku akwai bala’in kunya, wannan shine yayan shi Hamad” yanuna Hamad dake bama Baffa hannu Baffa yakarba cikeda murmushi yace “ina gajiya” sannan yanuna Maheer da kanshi ke kasa yace “wannan shine Maheer” ahankali Maheer yabama Baba dake kallonshi hannu karban hannun Baba yayi murya chan kasa Maheer yace “ina yini” ba yabo ba fallasa Baba yace “lpy lau” tareda karbe hannunshi, Baffa yace “bismillan ku kushigo” shiga ciki sukayi Ammi dasu Yaya ta window suke lekawa kaman yara dukansu are so excited Ammi tace “waye surukin nawa naga samari biyu” Yaya tai pointing Maheer dake sunnar dakai tace “daga ganin mai kunyan chan shine mai neman Yasmeen” wani kalan murmushi Ammi tayi tace “surukina badai kyau ba kaman bakin balarabe Masha Allah tubarkallah” shewa sukayi, jin Baffa na kwala musu kira yasa duk suka saka hijaban su suka daddauki su drinks da ruwan gora suka fita dashi, anatse Baffa yace “ga iyayen Fateema nan” gaggaishe su sukayi Maheer yakasa dagokai suka wuce suka koma daki sannan Baffa yace “to bismillan ku”.
Gyaran murya Baba Makaho yayi yace “to godiya ya tabbata ga Allah ubangiji daya hallice mu ya raya mu sa’an nan ya nuna mana wannan rana, dafarko dai sunana Alhaji Maheer Makaho, haka aka haifeni da makanta, gaskiya dana taso iyayena basu da shi ahaka ahaka dai nasamu wata makauniya irina marigayiyi mukai aure Allah yamata rasuwa yanzu” atare kowa yace “Allah gafarta mata” ahankali yace “Ameen” sannan yace “bazan muku karyaba dalilin d’ana ne nazo gidan nan yau, yarana biyu da Hamad wanda shi likita ne saikuma Maheer pharmacy yakaranta amman bai sami aiki dashi ba Allah yabashi aikin koyarwa english kaman yanda nafadi, banda shi duka yaran nan nawa da scholarship sukai karatu akasan waje Alhamdulillah” Baba yasakeyin shiru kafin chan yace “yaran nan yarane dasuka taso na koya musu ladabi biyayya natsuwa da bin Allah ma’aiki, Maheer yasameni da maganan yaga wata daliba a makaranta sunanta Fateema yanaso soyayya irin ta aure bawai soyayyan da akeyi a zamanin nan ba, saidai yabukace ni dana fara ganawa da iyayenta amai izini yanemeta tukunna dan bai dace yatari yarinya a school yana mata magana ba karatu tazo yi a school ba soyayya ba” jinjina kai Baffa yayi maganan na shiganshi, cikeda dattaku Baba yace “to gani ga babban aminina da yarana gakuma Liman shima aminina ne kuma zai iya wakiltata ako’ina munzo mu nemama danmu iznin neman auren diyarku idan babu kowa, idan suka daidaita nan bada jimawa ba ayi aure da izinin Allah to mekuka ce”? Shifa Baffa yasan halin kaninshi to bazai taba bari yakori mutanen arziki da mutunci haka bane dake neman Yasmeen ba, anatse Baffa yay gyaran murya yace “a gaskiya naji dadin wanna halin karamcin irin naku da sannin amfanin iyaye, sannan babu wani wanda ke neman aure Yasmeen wato Fateema dan haka nabashi izinin nemanta idan har komi ya daidaita saimu hada bikinsu taredana yayarta Sa’adatu da za’ayi nan da wata daya In sha Allahu” murmushi kowa yayi ana Alhamdulillah, Baba da tunda suka zauna Maheer yake kallo atsanake yace “Fateema is AS genotype dinta, menene genotype dinka”? Kowa bin Baba yayi da kallo Baffa kaman ya make Baba dan baisan what’s all this ba yanzu aka fara magana za’azo kan genotype nan gaba, dan dagokai Maheer yayi yakalli Baba kafin ya sunnar da kanshi kasa dasauri, cikeda kamala yace “ni AA ne Abba” hamdala Baffa yayi hakanan yaji yanason Maheer wlh dan yaron ga kunya ga sanyi ga rashin magana, daukansu Baba bazaice komiba yace “I need general blood test naka from a well known hospital saikuma” yadanyi shiru bai damu da yanda kowa ke kallonshi ba Baba yace “ban yarda ka taremini yarinya a titi ko a school ba ban yarda ba, Fateema karatu nakeso tayi banson tai loosing focus, ranan lahadi zan iya baka kadinga zuwa har nan daki a falon mahaifiyarta ka ganta kuyi magana na tsawon awa daya” gyadamai kai Maheer yayi ahankali, Baba yace “banson yawan kira, kira once in a day ya isa” sake gyadamai yayi” Baba zai kara magana Baffa yatareshi da sauri ta hanyar cewa “to Masha Allah, yanzu dai in sha Allahu tunda yau juma’a ranan lahadi saiyazo shida yarinya su zanta zamu kira yarinyar mu tambayeta idan tai na’am dashi zamu danyi yan binciken mu kafin mukiraku mu sanar daku kuzo asa rana da izinin Allah” dasauri Baba yace “zata cigaba da karatu” wannan karan Baba Makaho bai bari Maheer ya amsaba dan kafin yay magana yace “In sha Allah ai ilimi gatan bawa ne, ilim adon diya mace Fateema zata cigaba da karatu harsaitaji ya isheta” Baba zai kara magana Baffa yace “to bismillan ku muci abinci” badan Baba yaso ba ya kalli Baffa sannan yadauke kai.
Wannan ne last part na FREE PAGES Thank you for reading, idan kinason cigaba da karantawa u can open KYALKYALIN KAUNA 1 PAID.
love you😍