8
by @mshakur
EPISODE 8
“Alhaji, Alhaji” sama sama yaji ana kiran sunanshi kaman amafarki, ahankali yake bude idanunshi dayaji sunmai wani irin nauyi da tunda yake zai iya cewa basu tabamai nauyi hakaba ga kanshi dake wani irin sarawa, alamun mutane yake gani akanshi yana kokarin ganesu kafin idanunshi sugama washewa tastas wani baturin likitan shine akanshi hakan yasa yadan ware idanu da kyau yana kallon inda yake ganin asibiti ne Dr yace “can you hear me Alhaji? Talk to me” yunkurowa Alhaji yayi zaitashi yace “ya akayi nake asibiti? Ina Zayn? Where is my Son”? Yay maganan recalling abinda yafaru dasu a mota kaman direbanshi yay hatsari ne the last thing daya tuna was hayakin daya cika motan. “Ina Zayn dina” Ganin Alhaji yay magana da kyau yama rude sai tambayan Zayn yake yasa Dr yace “are you having pains anyway Alhaji”? girgiza kai Alhaji yayi yace “just headache but bashine damuwa ta ba yanzu ni, ina Zayn, hope babu abinda ya sameshi? Yafadi daga jikina yabugi kujeran mota hope nothing happen to him kasan jikinshi bai son wahala hope wajen daya buge bai kumbura ba, shi yana wani daki ne? Ina yake Dr”? Ahankali Dr yadanja baya sanan ahankali yakalli kofan shigowa dakin yace “police are here lemme send them in they will answer all your questions” baima jira maganan Alhaji ba yafice da sauri, wasu manyan polisawa ne agaban dakin, sai Uncle, Mami da sauran matan Alhaji agaban dakin, matan Alhaji kuka wiwi Mami dai idanunta sunyi jaaaa kana ganinta kasan tafi kowa damuwa amman ta natsu sosai labbanta na motsi alamun kodai zikiri take kokuma addu’a take, polisawan Dr yasa su shiga ciki, suka shiga duk suna tsaye anan gaban dakin sukaji ihun Alhaji, daidai police daya nafitowa yace “come Dr” dasauri Dr yabisu Mami dasu Uncle sukai dakin suma.
“Dr wanan wani kalan wasa ne, wayay kid……na….pi….ng Zay….” Yama kasa karasa magana ya sume numfashinshi na daukewa wani irin salati kowa yahauyi, Uncle yakalli police din yace “Yaya can’t handle this news, do whatever it takes a samo Zayn dan Allah, Zayn shi kadai Allah yabama yaya na, Zayn is his entire life, please bring Zayn back” gyadamai kai Babban dan sandan yayi yace “inhar yanda muke suspecting hakane kidnapping nashi akayi to kuzamto kusada wayoyinku za’a iya kiran daya daga cikinku suyi maganan iya adaddin kudin dasuke so abiyasu kafin su sakeshi, meanwhile bari mukoma bakin aikin mu, idan Alhaji ya farfado yana cikin state dazai iya magana damu Dan shine yasan enemies nashi da wayanda zasuso su cutar dashi ko danshi asanar damu Dan mudawo muyi magana dashi, dole mu tsananta bincike bana fatan case dinan yay nisa” gyadamusu kai Uncle yayi yabasu hannu suka gaisa sanan sukai musu sallama suka tafi
Wanan kenan………
********
Wani irin bude idanunshi yayi tarr sabida wani ruwa wanda yake nan uwa kankara mai kuma bala’in wari dayaji an watsamai, afirgice yatashi zaune yana kokarin tattaba jikinshi amman yakasa sabida hannayenshi da aka kulle warin dayakeyi nawani irin shiga hancinshi yace “f*ck” kafin chan kaman wanda yatuna wani abu yabi hannayenshi guda biyu da kallo dayaga an kulle da igiya dakuma kafafunshi da suma yaga an kulle a igiya an dauresu tamau dan har zugi hannun da kafafun sukemai sanan ahankali yashiga dago kanshi in a very slow manner yana tuna the last inda yake yana tareda Baban shi a mota aka taka burki harya fado yabuge bin inda yake yayi da kallo gabanshi daji bayanshi daji gefenshi daji dayan gefenshi ma daji, Babban daji ne sosai mai girma, sai gawasu mutane daya tabbata maza ne suna sanye da bakaken kaya su hudu da mask a fuska dukansu suna tsaye tare sun bashi baya babban cikinsu da karaman waya Nokia mai tocula yana waya da bayajin abinda yake cewa, jakunkunan yagani irin manyan bag pack dinan guda hudu saikuma babban bargo guda daya, da toculoli sai bindiga dasuke cikin wani babban jaka manya dayasa yaji gabanshi yafadi, ko sunji ajikinsu ana kallonsu daya daga cikinsu ne yafara juyowa hada idanu sukai da Zayn din da idanunshi sukai jajir yana kallonsu taba sauran yayi alamun suma sujuyo sanan yafara tahowa gabanshi yace “Dady’s boy ya tashi daga baccin, Hello Zayyanu” wani mugun kallo Zayn yamai cikin zuciya da fushi yace “who the heck are you guys? What do you want from me? Where am I? Kunsan ni waye”? Har mutumin zaiyi magana wanda ke waya yace “give me chair Lamido” dasauri dayan yajuya yana saramai yace “to Oga” sanan yadauko kujeran karba yayi ya ijiye daidai gaban Zayn yay wani irin zama agaban Zayn yana kallonshi kaman yanda Zayn ke kallonshi da jajayen idanunshi, cikin dakewa yace “kaine Ogan su”? Gyadamai kai Ogan yayi, cikin fushi Zayn yace “then who the f*ck are you”? Fas! Wani mummunan mari yama Zayn da saida Zayn yay ihu. “Shit!” Yakai hannunshi yana shafa wajen tunda aka haifeshi ba’a taba marinshi ba sai yau, cikin wani irin zuciya still yana shafa kuncin nashi da kullallen hannuwanshi yace “how dare you slap? I will make you pay for this, sainasa arayuwan nan baraka karajin kwadayin Marin wani ba” HAHAHA! Ogan yay dariya kaman wani Boss yana kallon Zayn din sanan yakalli yaran nashi yamike tsaye yace “kumai ladabi bakin nan nashi ya mutu kafin nazo nai magana dashi” sanan yawuce chan yana ciro wayanshi yana dialing number dan cigaba da wayanshi.
Wani irin faduwa gaban Zayn yake ganin gardawan maza su uku sunyo kanshi yanaso yatashi yagudu amman babu dama, duwaiwai yashiga ja yana komawa baya suna binshi yace “don’t touch me, don’t f**king touch me, I am telling y……” bai karasa maganan ba daya daga cikinsu yamai kafa abaki sai jini kafin ya ankara saukan dukan maza kawai yakeji ta ko’ina babu ko digon tausayi sumai ta kafa sumai da hannu, tun yana iya ihu har bakinshi yau liss ya mutu yana kwance awajen kaman wanda yamutu bakinshi ya kumbura sosai yana fitarda jini hakama fuskanshi duk ya kumbura sabida da kafansu dake Dante da jungle booth sukamai duka.
“Oga angama” Lamido yafadi suna komawa baya, Oga ya katse wayan dayake yi sanan yataho ahankali yazauna akan kujeran yana kallon Zayn din dake kwance akasa yace “Lamido adagomin shi ya zauna” dasauri sukai kanshi dagashi sukai suka zaunar dashi saida yay kara sabida azaba sanan suka koma bayan Oga suka tsaya.
Kallon fuskan Zayn din Ogan yayi yace “welldone boys” sanan yakalli Zayn yace “you look Cute Dadys boy” HAHAHA yakara dariya sanan yace “dagamu sai kai adajin nan babu mai kwatan ka, kariga kabaro Abuja kabaro yankin garinku ma kwata kwata inda zan fada maka inda kake dasaikasha mamaki so kada ma kayi tunanin zaka kubuta daga hannunmu” yay dan shiru sanan yace “mutane uku suka bamu Wanan kwangilan na kidnapping naka, biyu daga cikinsu naso mu halakaka har lahira kamutu kawai babu labarinka, mutum daya kuma nasonka da ranka amman sai an gama karbe komi na mahaifinka sanan za’a maidaka, so the whole case akanka is interesting, kidnapping aikina ne tun inada saurayi amman bantaba kamo babban nama iri ka ba, kasan irin kudin dana samu nakuma ke samu akanka kuwa? Yanzu muka fara wasan” Hahaha yasake dariya sanan ahankali yace “kubashi abinci” hanyar jakansu Lamido yayi sanan yadauko wani bushashen buredi na irin na naira hamsin da pure water guda daya yataho gaban Zayn sanan ya Yar akasa kaman yabama kare, ture abincin Zayn yayi azuciye yace “I am not eating” dariya dukansu sukahau yi harda tafi, tsinkewa zuciyanshi yayi da kyar ya iya bude baki yace “konawa mutanen dasuka saku ku kamoni zasu baku zan baku x10 inhar kun sakeni” duk kallonshi suka tsaya yi kaman wayanda suka gamsu da maganan shi sanan sukahau dariya, kafin Ogan yace “ku karyamin hannunshi daya” wani kalan zaro idanu Zayn yayi tsabagen shock yama kasa magana, ganin sun taho kanshi gadan gadan yasa yafara ihu. “Somebody help me, help me, mutanen nan sun saceni, mutanen nan sun saceni” hannunshi suka fuzga suka warware kullin sanan suka kama left hand din Zayn yanajin yana gani wanda ke kama da doki ya ballamai hannu bass tsabagen azaba sumewa ma yayi, Ogan yace “finally gwara yayi bacci yadameni”.
Wanan kenan……
Tana zaune acikin dakin nan nata ita kadai dayake da duhu ko fitila babu tana zaune ta idar da sallan isha’i taji muryan Rakiya ta kwalamata kira cikeda bala’i. “Farrah” tashi tsaye tayi da sauri jikinta harya fara rawa hannunta dasauri takai ta taba goran pepper spray da Shafa tamata dake makale gefen zaninta tana numfashi da sauri da sauri. “Wai bakiji ina kiranki ba Shegiya Yar Jaka nazo dakin nan naki na tumakai kashekine kawai bazan yiba” Rakiya tafadi ranta abace, ahankali tasa hannu tabude kofan taramo tafito daidai lokacin itama Inna dake sallan isha’i lokacin da Rakiya tashigo gidan tafito tana kwace hijabin tana daurawa kan igiyan tsakar gidan tace “meya faru Rakiya”? Cikin fushi Rakiya takalli Farrah daya fito tana rabewa abango daga nesa dasu, Rakiya tace “yau kin hadu da Modibbo kobaki hadu dashi ba”? Da bala’in sauri Farrah ta girgiza mata kai tana hadawa da yatsu alamun a’a basu haduba, cikin fushi Rakiya tadubi Inna tace “Inna kinga dai yarinyar nan da Baba yasaka mana agida bata gabana bana shiga harkanta, wlh Inna takiyayan mini Moddibo na, ko ganinshi tayi tama chanza hanya dan banso ko hanya yahadasu, Inna yau ina kawomiki karanta na karshe wlh wlh na rantse da zatin Allah ko magana aka kara zuwa akacemin anga ta tsaya tanayi dashi koko kima hada hanya dashi komenama yarinyan nan ita taja, komenamata ita taja, Modibbo nawa ne nikadai ne matarshi a kap karkaran nan, idan kunne yaji……” Inna tace “gangan jiki ya tsira” Rakiya tajuya tawuce dakinsu itakuma Inna takalli Farrah da kanta ke kasa tanaji kaman ta kasheta tace “in ciyar dake sanan in ciyar da Baffan ki da kudina sanan kice zaki kwacema y’ata Modibbo Farrah wlh wlh zan iya halakaki har lahira ki kiyayeni” tana maganan tajuya fuuuu tai ciki ganin Malam yaleko daga dakin ahankali itakuma tajuya takoma dakinta tasamu gefe daya ta kwanta sai bacci Allah yasota takoshi.
Da asuban fari ta bude ido tana fitowa ta zaga bayangida sanan tadauro alwala, tadawo dakin ita harta saba rayuwa acikin duhu salla tayi na asuba sanan tazauna tana addu’a, mahaifiyarta kafin tarasu takoya musu karatu sosai dan haka ta iya ta iya salla daidai gwargwado sanan bata wasa da addu’a.
Gari nafara haske tafito ita kadai da sanyin safiyan nan nan tadauki tsintsiya ta share gidan tass, sanan tai wanke wanke, saida tagama sanan tabama tumakan gidansu da shanaye abinci daidai lokacin Inna tafito daga daki fitowa tayi daga wajen tumakan ta tsugunna har katsa alamun gaisuwa ko amsata Inna batayiba tawuce bandaki itakuma tadauki tulu dan fita debo ruwa rafi tanada kuzari da zafin nama nan da nan tashiga cike ko’ina, tana cikin tafiya zata koma rafin zuwan karshe kenan zatayi ko’ina yacika agaban rafin taga Modibbo tsaye rikeda wani paranti mai kyau da buredi kekai da kofi babba dayacika da shayi sai cinyan kaza agefe soyayye dakuma soyayyan kwai, kallo daya tamai tawani irin juya, dasauri yabiyota yace “Farrah Farrah tsaya” tana shirin kwasa dagudu yasha gabanta yana kallonta yana murmushi yabi kayan jikinta da kallo sunyi daka daka dan tabe baki yayi yakalli fuskanta dahar wani sheki yake dudda ko wanka ma batayi ba ga uban gashi a goshinta da giranta baki sudik har wani kyalli suke yace “bakiji ina kiranki bane zaki gudu, Kari nakawo miki nasan ba’a baki abinci awanan gidan bani tulun nan kigani” yakai hannunshi zai sauke tulun daga kanta dasauri takoma baya tace “iiiiii” cikin yanayi na kurmanci alamun yabar shi, jiyayi ranshi yabaci daurewa yayi yamika mata tray din yace “to gashi kici” dauke kai tayi takalli gefe dasauri dan bamataso taga abincin ranta yabiya, sosai yaji ranshi yabaci cikin fushi yace “wlh idan baki amsaba zansa akulleki amiki bulala dariya wawiya kawai sabida kinga ina sonk……” “Farrah” wani irin bari jikinta yayi jin muryan Rakiya daga ita har shi Modibbo juyawa sukayi suka kalli Rakiya, kana ganinta zakaga tsantsan bacin rai da kishi a idanunta dan takai minti daya tsaye a wurin amman ta daure dasauri takaraso wajen Farrah tai baya dasauri danta dauka dukanta zatayi Rakiya tasa hannu ta amshi tray dake hannun Modibbo tace “Allah sarki Hamma haka kake sona kabama Farrah takawomin gida, gidan su Atine fa zani nace bari nabiyo tanan, nagode Hamma Modibbo” tai maganan tana amsa tana juyawa dantama Farrah mugun kallo amman harta bace daga gudun, juyawa Modibbo yayi fuuu yawuce batare dayace ma Rakiya uppan ba, saida yabace mata sanan tai kwafa tawuce gida.
Awani irin zuciye Rakiya tashiga gidansu tana ihu. “Farrah, Farrah” Inna datagani na rege shinkafa atsakar gida tace “Inna ina Farrah”? Baki Inna ta tabe tace “kinfasan tunda tagama gyara gida ta debo ruwa sai kwasan awakai da shanaye ta wuce daji kiwo ko Rakiya baki sani bane? Me Wanan ahannunki” ko kallon Inna batayiba tajuya tawuce tashige dakinsu.