BAK’AR SHUKA…!

16

by @hauwaausmanjiddarh

*BAK'AR SHUKA...!*




NA



*HAUWA A USMAN*

~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


1️⃣6️⃣


Kuka ta saka mishi sosai me sauti har wanda ke falo yana iya juyowa, bai damu dan wani yaji ba, tausayinta ne yasa shi d'aga ta dole ya koma gefe yana mayar da numfashi, jikinta na rawa taja bedsheet ta rufe jikinta tana cigaba da kukan, baya jin zai iya furta komai balle har yayi doguwar magana wajen rarrashinta dan haka ya jawo ta jikinshi ya rungume ta tsam, sun d'auki lokaci a haka kowannensu yana mayar da numfashi kana ya sake ta ya mik'e, bathroom d'inta ya shiga yayi wanka ya fito d'aure da towel d'inta a k'ugunshi kallo d'aya tayi mishi ta d'auke kanta daga kanshi.


K'ofar fita ya nufa zai fita kamar bazatayi mishi magana ba sai kuma tace " a haka zaka fita Yaya?


Dama ba fitar zayyi ba neman magana ne, " eh! yace yana d'ora hannunshi saman handle d'in k'ofar, sai da ta rufe idonta ta bud'e kana tace " dan Allah karka fita a haka idan akwai mutane a falon fa?


Juyowa yayi fuskarshi d'auke da murmushi yace " kishin kar a ganni a haka ne ko kuma kina gudun karna fita a haka a gane abinda mukayi?


Kanta ta juyar gefe batare tace mishi komai ba, ya sake yunk'urawa zai fita tace " please Yaya.


Sosai yaji dad'in yadda ta nuna kulawa da kishinta a kanshi duk da bata fito ta fad'a ba yasan duka abu biyun daya fad'a ne kishin da kuma kar a gane sunyi wani abu, duk da sun kasance ahali d'aya gaba d'ayansu amma tana kishinshi, dawowa yayi ya mayar da kayan dayazo dasu jikinshi had'i da yi mata light kiss a goshi ya rad'a mata ga abinci nan a tashi aci please, ya fita.


Tashi tayi tana gyara zaman bedsheet d'in a jikinta ta jawo ledar ta bud'e baki ta washe ganin ice cream da pizza ta zage taci ta k'oshi sosai kana ta tashi tayi wanka ta fito parlor.


Da daddare bayan ta gama shirinta tsaf na kwanciya bacci, ta kashe fitila ta fad'a bed tana sauke ajiyar zuciya gami da rufe idanuwanta da nufin yin bacci amma sai me?


Data rufe idonta su take gani kwance saman bed suna romance, saurin bud'e idonta tayi tana jin tsikar jikinta na tashi yarr yarr, a hankali ta sake mayar da idon ta rufe, sake ganin kansu tayi naked suna romance da sauri ta sake bud'ewa tana fad'in " ya Allah! wai dama haka Yaya yake?


"Ni Yaya ke yiwa wannan abun?


"Yau ni Yaya ya tab'awa Boobs har da shafa ni yana wani marairaice min murya yana rok'o na?


K'afarta ta d'aga sama ta sauke tana dariya tace " wayyo Allah na!


Kamar wata doluwa ta rufe idonta d'aya tana fad'in " bari na rufe su d'aya bayan d'aya, ai tana rufe d'ayan idon kwakwalwarta ta sake hasko mata kansu kwance naked, daurewa tayi tak'i bud'e idon ta cigaba da ganinsu while tsikar jikinta na tashi tana jin kamar a lokacin hannunshi ke yawo a jikinta.


Duk yadda taso ta goge abun cikin kanta yak'i goguwa, tayi-tayi ta manta amma abu ya gagara haka taita rufe ido tana bud'ewa kamar mahaukaciya har bacci yayi awon gaba da ita.


******* Dan zatayi period bata tab'a yin ciwon mara ba sai dai kawai taga period d'inta, amma a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin dayasa take yawan jin mararta na karta mata, sama-sama take jin ciwon dan haka bata damu da ciwon ba balle ta fad'awa wani, ta dai tsaida zarginta kan magungunan da Azwah ta bata tana sha suke jawo mata d'an kartawar marar.


Tana kwance saman bed tana bin chart d'in Ciwon 'Ya Mace tana karantawa tana dariya saboda yawancin 'yan Sokoto ne a group d'in ita kuma Allah yayi ta da mugun san Hausar 'yan Sokoto, tunda Azwah ta bada number su aka saka ta bata da aiki sai taita bin voice note d'in 'yan Sokoto tana ji tana dariya.


Turo k'ofar akayi aka shigo bakin Deerah d'auke da sallam, Deerah 'yar Azrah ce.


"Aunty Ammu tace " wai kizo!, tashi tayi zaune tana murmushi tace " yadai naga ana ta faman turo baki hala keda Ammu ne?


"A'a ni da Ammi ne, wai bazan k'ara shan ice cream ba.


"Me kikayi mata da za'ayi miki wannan horo me tsanani haka?


"Danna ce tayi tsofa da kwalliya agaban Abbi.


Cikin dariya Deeyanah tace " ke kuwa ya zaki kushe ta gaban mijinta so kike ki kashe mata kasuwa?


Ta fad'a suna fitowa, " ga abincin Deen ce akan dinning shiga ki kai mishi.


Sororo tayi a tsaye tana kallan Ammun kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta nufi dinning ta d'auki tray d'in ta nufi d'akinshi, bata tsaya yin knocking ba ta shiga, gadon bayanshi ta fara sauke idonta kafin tayi k'asa da idonta, idanuwanta ta zaro kamar zasu fad'o k'asa tayi saurin juyawa ta fice daga d'akin, yau kam taga babbar illar shigarwa mutum bedroom batare da neman izinin shiga ba, dan tayi danasanin shiga.


"Kai! Anya tsirara na ganshi kuwa?


Ta tambayi kanta cikin tantama da kokonto, " kai gaskiya ba lalle ba inaga dai idanuwa na ne basu gano min dai-dai ba.


"Wai bazaki kai mishi abincin bane sayya huce?


"Kinyi tsaye kina magana ke kad'ai sai kace tab'abb'iya, cike da yak'inin gizo idanuwanta sukayi mata ta sauke tray d'in k'asa tayi knocking.


Daga ciki ya bata izinin shiga, ta durk'usa ta d'auki tray d'in ta shiga, ta riga ta gama tsaida tunaninta gizo idanuwanta keyi mata, amma duk da haka ta shiga cikin sand'a gabanta ta fad'uwa, kamar ance ta fad'o idanuwanta ta kalle shi, tsautsayi ya sata sauke idanuwanta kan naked body d'inshi da sauri tayi baya duk ilahirin jikinta na tsuma kamar wacce taga dodo.


"Wai dama da gaske ba kaya a jikinshi!?


Ta tambayi kanta, idonta ta runtse tare cewa " fisabilillahi yasan ba kaya a jikinshi ya bani izinin shiga?


Juyawa tayi ta koma falo Deerah na zaune kusa da Ammu, tsaye tayi jikin kujera bakinta na rawa tace " Deerah zo ki kaiwa Uncle abinci, ba musu yarinyar ta taso ta karb'i tray d'in, har Ammu ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa, zagayowa tayi zata zauna kan sofa had'i da sauke ajiyar zuciya.


"Yes! shigo.!


Taji ya bawa Deerah izinin shiga, tunanin kodai har yanzu bai saka kaya ba tayi, wata k'ila yayi zaton itace shiyasa ya bada izinin shiga, saurin dakatar da Deerah tayi da fad'in " dakata! bari nazo na kai mishi.


Cikin ranta tana fad'in gwara in kai mishi da kaina kada Deerah ta shiga ta ganowa kanta bala'in daya girmi kanta, tray d'in ta karb'a daga hannun Deerah ta shiga d'akin kanta k'asa kwata-kwata batayi gigin d'ago kanta wannan karon ba, duk da tana tunanin k'ilan ya saka kaya.


Saman centre table ta aje tray d'in ta juya zata fice, " baki iya gaisuwa bane?


Ya fad'a kamar ba shine yayi maganar ba, still kanta a k'asa bata d'ago ba tace " ina kwana?


Sharewa yayi, yayi kamar baiji ta ba, tasan ya jita sarai halin nashi ne zai tab'a mata, baki ta tab'e had'i da nufar k'ofa zata fita duk abinda take yi yana kallanta ta cikin mudubi.


"Kishin har 'ya'ya dama?


Da sauri ta juyo ta kalle shi tana neman tabbacin maganar da yayi, amma ya basar yadda kasan bashi ne yayi maganar ba, ta kuma juyawa zata fita yace " me yasa baki gyara min d'aki na ba yau?


Tasan tsabar neman magana ne dan kuwa ta gyara d'akin, shiru sukayi babu wanda ya sake cewa komai, jin yayi shiru yasata sake juyawa zata fice, " ki gyara min bedroom d'ina.


Gadon dayake a gyare tsaf tabi da kallo kana ta mayar da kallanta kanshi cike da k'osawa tace " me zan gyara?


"Ko'ina ya bata amsa a tak'aice, bata sake yin magana ba, dan bata jin zata iya magana a yadda take jin mararta na kartawa ta soma galabaita, a daddafe tana yamutsa fuska ta zubo da gaba d'aya filallikan k'asa ta yaye bedsheet d'in ta kakkab'e gadon ta sake shinfid'a bedsheet while tana cije lips, jin mararta take kamar zata fad'o k'asa k'arfin hali kawai take yi tana daurewa amma tana jin azaba.


Yana kula da yadda take cije lips da yamutsa fuska sai dai bayyi tsammanin bata da lafiya ba yayi tunanin rashin kunyarta ce zata tab'a mishi, a hankali ya tako inda take ya rungume ta baya, mazaunanta na gogar mararshi, yayinda hannunshi ke kan mararta, " wash tace tana lumshe ido saboda yadda taji zil har cikin kanta, tana jikinshi ta gama gyara gadon, kana ta zame jikinta daga nashi ta zuba mishi dadaran idanuwanta da suka canja launi tace " Yaya zan kwanta!


Light kiss yayi mata a kumatu yace " ki kawo min abinci, kanta ta d'aga mishi danta samu yabarta ta fice, danji take kamar zata mutu, tana had'a hanya tana ganin bibbiyu ta k'arasa bedroom d'inta ta zube a saman bed sharaf.


Bai kula da halin take ciki ba, dan haka ya cigaba da shirinshi harya gama bata kawo mishi abincin ba, saman bed ya zauna yana jiranta amma shiru...


JIDDARH