BAK’AR SHUKA…!

24

by @hauwaausmanjiddarh

*BAK'AR SHUKA...!*




       NA



*HAUWA A USMAN*

    ~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


2️⃣4️⃣


Bata farka ba sai cikin dare, bakinta d'auke da salati ta dafe kanta tare da yamutsa fuskarta, a hankali ta bud'e idanuwanta da sukayi mata nauyi ta fara ganin komai dishi-dishi kafin a hankali idanta ya washe tarr,

k'ok'arin mik'ewa zaune ta soma hannunta dafe da kanta, " yi a hankali, taji an furta daga gefenta, idonta ta sake warewa sosai tana bin inda take da kallo, sai a lokacin ta kula da a asibiti take, hannunta jone da cannula ana k'ara mata ruwa.


"Sannu..! Deen! yace yana tallafe ta, juyawa tayi ta kalleshi, tana d'ora idonta akanshi komai ya shiga dawowa mata, tunaninta ya dawo, wata irin mahaukaciyar k'ara tayi tare da tushe kunnuwanta da hannayenta ta saki rikitaccen kuka tana fad'in.


"Na shiga uku!... na shiga uku na lalace.


"Subhanallah me yayi zafi haka Deeyanah?


Deen ya fad'a yana rik'e ta.

Ammi tace " kul karna sake jin kince kin shiga uku kinji ko?


A haukace kamar zararriya ta kalli Ammin tana girgiza kanta while tana kukan tace " idan da abinda yafi shiga uku ma na shiga, na shiga dubu ma ba uku ba, ina cikin bala'i da musiba Ammi,

wannan wacce irin bak'ar k'addara ce Allah ya d'ora min?


"Me yasa saini?


Rik'e mata hannu Ammi tayi tana fad'in " kowacce dak'ik'a data harba a agogo tana harbawa ne da rubutun wata k'addara a rayuwarmu,

K'addarar da ka iya zama shafi cikin littafin rayuwarmu, fatanmu Allah ya gina mana katangar karfe da mummunar k'addara.


Cikin kuka Deeyanah tace " amma meyasa saini?


"Meyasa akaina kawai zata fad'a?


Idon Deen kanta yace " Deeyanah ki manta da abinda ya cutar dake amma karki sake ki manta da darasin daya koyar dake,

zatayi magana Deen yace " wai mema ya firgitaki haka?


D'an jimm tayi tana tunanin ta fad'a musu ko karta fad'a musu, "kiyi addu'a koma meye yazo miki da sauki saboda taka tsantsan baya hana afkuwar masifa, amma addu'a tana tasiri akan masifar data sauka dama wacce bata sauka ba, Masifa takan sakko sai addu'a ta tareta, suyita fafatawa har ranar tashin alkiyama, kinga masifar bazata cimma ma'abocin addu'a ba,

cikin mutuwar jiki tasa hannu ta goge hawayen dake ta faman zubowa saman fuskarta, " Ammi ki tayani addu'a mummunar k'addara ta afkawa min.


Kallon juna Ammi da Deen sukayi kafin suka mayar da kallonsu ga Deeyanah cikin rashin fahimta Ammi tace " kamar ya ban gane inda maganarki ta dosa ba!?


"Bazaki gane ba Ammi.


"Duk irin bayanin da zanyi miki bazaki fahimci komai cikin zance na ba, ni kaina na kasa fahimtar komai, ko kalma d'aya na kasa fahimta Ammi.


"Ki nutsu kiyi ki kwantar da hankalinki, kyayi mana bayani daga baya, Deen ya fad'a yana k'ok'arin had'a Ido da ita tak'i bashi dama, wani iri take ji cikin jikinta wai itace tayi video tsiraici na batsa?


Itace irin wannan bak'ar k'addarar ta fad'awa, komawa tayi ta kwanta had'i da lumshe idanuwanta hawaye na gangarowa ta gefen idanuwanta.


Ba bacci takeyi ba, tana jin hirar da Ammi da Deen keyi amma bata fahimci ko kalma d'aya cikin maganganun da sukeyi ba, hankalinta baya jikinta, k'ofar d'akin aka bud'e DeeDee ya shigo da gudu yana fad'in Momy, wani abu babba taji ya tokare mata mak'ogwaro ya soki Zuciyarta.


"Momy! Deedee ya fad'a yana fad'awa jikinta.


A fili ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ta d'agoshi tana k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta lullub'awa fuskarta.


"Ki daina bari yana fad'a miki kinga ba ke kad'ai bace kar wani abu ya samu d'an cikinki, Ammi ta fad'a tana kallan yanayin Deeyanah, murmushi tayi batare da tace komai ba, su Babah suka shigo bakinsu d'auke da sallama, "au wai dama tare kuke dashi?


Eh! Mana ya gudo wajen iyayenshi yabarmu ba.


"Sannu Deeyanah ya jikin naki?


Cikin sanyin jiki da muryarta da bata fita sosai tace " da sauki?


"Wai meke damunta ne?


"Ince dai ba bari tayi ba ko?


Abbi yayi maganar a lokacin d'aya yana kallan Deen.


"Ga cikin ya d'an soma fitowa ma ba wani b'ari lafiyar cikin lau.


Cewar Ammi tana kallan cikin jikin Deeyanah.


Deen ya sauke ajiyar zuciya yace " nima dai ban san meke damunta ba Ina shiga gidan na ganta kwance k'asa a sume.


Ammi tace " To wai fad'uwa kikayi ne ko kokuwa dai wani abunne ya faru?


Deeyanah najinsu amma batayi magana ba.


"Deeyanah dake fa ake magana kinyi shiru kina jin mu, batare data d'ago kanta ba tace " bakomai Ammi, "to Allah ya kyauta. 


Gaba d'ayansu suka amsa da "Amin.


Kwanakin Deeyanah uku a asibiti aka sallameta kowa ya fahimci akwai abinda ke damunta dan kallo d'aya zakayi mata kasan tana tattare da tarin damuwa.


Tun bayan komawarsu gida komai nata dana gidan ya canja ta zama wata sukuku ta daina magana sosai sai jefi-jefi ta koma shiru-shirun dole, duk suturun Deeyanah da faram-faram d'inta duk sun zamana babu duk lokacin dazaka ganta sai dai ka ganta zaune ta rafka uban tagumi hannu bibbiyu, dama wayar ta lalace layinta a kashe yake. 


Tana zaune bakin gado ta rufe kanta a d'aki tana rusgar kuka wiki kamar ranta zai fita, idanuwanta har sun kumbura tana fad'in,


" wayyo Allah! na shiga uku!


" Ni Deeyanah na shiga uku rayuwata ta lalace tashin duniyata yazo, na jefa kaina da rayuwata a cikin masifa da babban k'alubalen da babu mai fitar dani sai Allah.


Zamewa tayi daga saman gadon ta durk'usa k'asa saman gwiwowinta ta d'aga hannayenta sama a fili ta soma addu'a.


"Ya Ubangijin Al'arshe ya Ubangijin sammai da k'assai ya gagara buwayi majib'ancin al amura me tausayi mai jin k'ai me yaye damuwa, ya Allah ya ka kawo min mafita, ka jib'anci ramura na, kayi min mafita ka kareni daga sharrin wannan bawa naka kayi min tsari daga kaidinshi, ta zame takai sujjada bata damu da cewar ko hijabi babu a jikinta ba while tana cigaba da rusa kuka.


Tsaye yayi cak yana kallanta cike matsanancin mamaki ya kasa fahimtar komai amma yaji komai, sai dai babu abinda ya iya ganewa kanshi ya juye a fili ya furta.


" Ka kareni daga sharrin wannan bawa naka, kayi min tsari daga kaidinshi?


"Waye wannan d'in da Deeyanah ke magana akanshi?


Yayi maganar kamar me koyan magana, cikin rashin gwarin jiki ya jawo k'afarshi ya k'araso kanta yayi tsaye yadda take rusa kuka sosai yake tab'a mishi zuciya.


" Deeyanah!


Ya kira sunanta a hankali cikin nutsuwa, bata ji shigowarshi ba balle motsinshi sai muryarshi dataji a kanta, da sauri ta d'ago daga sujjadar yana d'ora idonshi a kanta gabanshi ya fad'i saboda gaba d'aya kamaninta sun canja yadda kasan ba itace Deeyanah ba.


Itama a mugun tsorace take dan tana gudun koya fahinci maganganunta, a hankali yasa hannayenshi ya d'agota ya zaunar a gefen gado ya fita, bai dad'e ba ya dawo hannunshi d'auke da ruwa ya mik'a bata ta karb'a tashanye tas ta mik'a mishi kofin tana sauke ajiyar zuciya.


Ido ya zuba mata batare dayace mata komai ba har tsayin lokaci kafin yayi gyaran murya yace " meke faruwa dake ne Deeyanah?


Bata d'ago kai ta kallaeshi ba balle tayi magana.


" Ina tunannin duk duniya babu wanda kike da kusanci dashi sama da ni a halin yanzu, nafi kowa damar sanin damuwa da matsalarki Deeyanah, ni nafi kowa cancanta dana share miki hawayenki dake zuba, dani ya kamata ki raba damuwarki, ki daure ki fad'a min abinda yake damunki dan mu tari matsalar tunda wuri,

karki bari sai abun ya girmama ya wuce mu tare shi, koma meye ki sanar dani dan ina da tabbacin ya shafeni, kina da matsayin dako aure bai shiga tsakaninmu ba zan tsaya miki tsayin daka akan matsololinki balle kina matsayin matata kuma uwar 'yayana, dan Allah mu raba k'uncinmu, damuwarmu, bak'in cikinmu da kuma kukanmu tare, ki sanar dani dan girman Allah ni kuma nayi miki alk'awarin ko abinda na mallaka zai k'are kuma ko zan rasa rai na zanyi miki maganinshi please.


Yayi magamar so calm.


Tasan duk abinda ya fad'a gaskiya ne, amma tayaya zata kalle shi ta sanar dashi ta hau matar Ajlaal har ya kaita gidanshi yayi zina da ita?


Ta yaya zata sanar dashi tayi zina da Ajlaal da aurenshi a kanta?


Bayan tasan kishin Deen a kanta, tasan yadda yake bala'in kishinta, tasan duk duniya babu wanda ya tsana sama da Ajlaal, jifa yadda ya nemi yin hauka a baya da bama soyayya suke yi ba, balle yanzu da suka had'a jiki tasan mutuwa Deen zayyi idan yaji wannan maganar.


Yadda tayi shiru tana tunani ya k'ara tabbatar mishi da lalle akwai wani abu, ya bud'e baki zayyi magana tayi saurin cewa " bakomai!


Cike da mamaki ya kalli kwayar idonta tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa " bakomai fa kikace?


Cikin sanyin jiki tace " bakomai Abban Deedee babu abinda yake damu na, kamar zayyi magana sai kuma ya fasa, ya mik'a mata kwalin sabuwar waya yana fad'in " gashi wancan bazata gyaru ba layinki yana ciki.


Yadda kasan ya mik'o mata wuta taja baya da sauri had'i da girgiza kanta tace " A'a Yaya ka barta a wajenka letter zan karb'a.


Abun kuma ya fara bashi tsoro yadda Deeyanah ke san waya amma itace yau ke rejecting waya, sun sha yin fad'a da ita akan waya dan ta bawa waya mahimmanci sosai a rayuwarta, danya tabbatar da abinda yake zargi ya sake tura mata wayar ta zabura taja baya muryarta na sark'ewa tace " no please Yaya ka barta zan karb'a, harta fice idonshi nakanta cike da matsanancin mamaki fal ranshi ya kasa magana.


Cikin bacci sama-sama taji kamar ana shafa mata fuska, a hankali ta bud'e idanuwanta da dama ba wani baccin kirkine a cikinsu ba karaf idanuwanta suka sark'e cikin na Ajlaal.......


JIDDARH...