BAK’AR SHUKA…!

34

by @hauwaausmanjiddarh

*BAK'AR SHUKA...!*

  

       NA

*HAUWA A USMAN*

    ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

3️⃣4️⃣

Wayar Babah yabi da kallo kana ya kalli Deen suka had'a ido, sake kiran wayar yayi yaji busy sau uku yana kiran wayar amma busy hakan ba k'aramin hasala ran Babah yayi ba, wayar Ammu ya kira tana d'agawa yace " jeki taho min da Deeyanah, bai jira jin abinda zatace ba ya kashe wayar.

Abbi na d'agawa ta fasa kukan kissa wiwi, " subhanallah lafiya Deeyanah?

Cikin kuka da marairaicewa tace " Abbi Deen ne ya kai k'arata gun Babah kan nace bazan bishi America ba saboda tarbiyyar Deedee, " to! ikon Allah, yanzu Ina Babah da Deen d'in?

"Suna falon Babah, " ki taho falon nima bari naje can na same su, cikin zumud'i ta amsa da "to dan tasan duk wacce za'ayi Abbi bazai tab'a bari ayi mata dole ba, tana kashe wayar Abbi ta kira wayar Babah, amma harta tsinke bai d'aga ba, zata sake kiranshi Ammu ta shigo, a d'an tsorace ta mik'e tana gaida Ammu kafin tayi shiru tana jiran taji abinda zatace mata dan tasan ta ba wasa, " wani laifin kika yiwa Babanki ne!?

Da saurinta ta girgiza kanta gami da cewa " a'a! " hmmm kedai kika sani, yace kije falonshi yana san ganinki, jikinta na rawa tabi bayan Ammu, hanyar part d'insu Ammu ta nufa Deeyanah tayi saurin cewa " Ammu ke bazaki wajen kiran ba?

"Akan me zani?

"Ni 'yar aike ce a tsakaninku mahaifi ne yace na kira mishi 'yarshi na kuma isar da sak'o na meye nawa da zanyi katsalandan a ciki!?

A fili ta sauke ajiyar zuciya cikin ranta take godewa Allah kan k'in zuwan da Ammu tayi, da Ammi ce ma da d'an sauk'i-sauk'i dan tasan idan aka cirza bayanta zata bi, " Wai bazaki tafi bane kika tsaya kika tsare ni da ido kina mimi da baki!?

Saurin barin wajen tayi kafin Ammun tace zata biyota, tana kaiwa k'ofar zata shiga Abbi na kawo kai, a hankali ta fitar da sassanyan numfashi had'i dayin hamdala cikin ranta, sai da ta baari Abbi ya wuce gaba kafin ta bi bayanshi bakinta d'auke da sallama, daga Babah har Deen babu wanda ya amsa mata sallamar sai ma harara da Babah ya galla mata yana fad'in" wato sai da kika biya kika taho da Abbanku saboda kin san baki da gaskiya ko?

Kanta ta sunkuyar had'i da nemar guri ta zauna kana ta d'an rusuna tace " Ina yini Babah?

Batare daya amsa gaisuwar tata ba yace " kije ki fara shiri jibi zaku wuce in sha Allahu, sai da ta k'ara yin k'asa da kanta kana tace " Babah dama bance bazan bishi babu wani dalili ba, kallan banza Babah ya watsa mata yana fad'in " ki rik'i dalilin naki.

"A'a fa Abduljalal karkayi gaggawar yanke hukunci batare daka ji ta bakinta ba itama, "ai dama nasan dan haka ta sako ka a gaba.

Dariya Abbi yayi kafin yace " ta sako ni a gaba kuma?

"Eh mana, danka shigar mata ba, Abbi yayi murmushi kafin ya kalli Deen yana fad'in " meke faruwa ne!?

Cikin girmamawa ya kwashe yadda sukayi kan komawarsu America ya sake fad'awa Abbi, a fili Abbi ya sauke ajiyar zuciya had'i da jinjina kanshi.

"Kaji fa fisabilillahi in ba shirme ba har mijinki yace ki shirya ku koma ki tsaya kina wani b'ata lokaci dan samun waje.

Ita kam ido ta zubawa Deen tana k'ara ganin girma da k'imarshi kan rashin fad'awa su Babah hanashi hakk'inshi da take yi, wani mugun tausayinshi taji yayi bala'in kamata, hawayen tausayinsu dake shirin zubo mata take ta k'ok'arin mayarwa, ji take yi tamkar ta bishi amma wane ita fad'an yafi k'arfinta, dan idan ta sake tayi kuskuran binshi komai yana iya faruwa.

Abbi ya mayar da dubanshi ga Deeyanah yana fad'in " uhunn yi mana bayanin dalilinki nak'in bin mijinki, d'an jimm tayi kalaman Ajlaal na sake dawowa cikin kanta " wallahi muddin kikayi kuskuran binshi kafin jirginku yakai inda zai kai kun samu labarin rugujewar ahalinku da mutuwarsu kaf dan bazan tab'a barin d'ayansu da rai a doron k'asa ba, kuma na saki video na watsa cewa sanadin video batsarki ne yayi sanadiyyar ajalinsu, suka kashe kansu saboda kunyar duniya, zab'i ya rage naki tsakanin ran ahalinki da mutuncinki da kuma k'iimar zuri'arku kaf da kuma binshi America wanne ya fiye miki mahimmanci.

Kanta ta sake sunkuyarwa dan gudun karsu fahimci yadda take kokawa da nutsuwarta, hawayen da take ta dannewa tana k'ok'arin mayar dasu ne, suka kwace mata kafin kace me sun wanke mata fuska.

A hasale cikin fushi Babah yace " wai bada ke ake magana bane kinyi shiru in baki da abin cewa mu tashi mu baki waje.

Wahalallan munfashi ta fitar had'i da lumshe idonta hawayen suka sake tsiyayowa dan harga Allah tana jin d'acin rabuwa da zatayi dashi da kuma nesa da juna da zasuyi, dakyar ta saita kanta ta bud'i baki tace " Abbi dama saboda tarbiyyar Deedee ne, duk da yadda tayi k'ok'ari wajen saita kanta sai da muryarta tayi rawa.

Babah zayyi Magana Abbi yace " ka tsaya a bita a hankali mana, ya mayar da kallanshi gare ta yace " sai ki barshi anan wajen Ammu da Ammi, tunda yanzu ma ba'a hannunki yake ba, muryarta na rawa kamar zatayi kuka tace " Abbi ni dai bana san binshi, da sauri Deen ya d'ago ya kalleta, bata bari sun had'a ido ba tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa, a zafafe Babah yace " ke d'in banza kice bazaki biki mijinki ba, idan kin zauna anan d'in wata uwar zakiyi mana?

"Shashasha sakarya mara wayo kawai, " kayi hak'uri muji dalilinta mana, Abbi ya sake mayar da kallanshi kanta yace " meyasa baki san binshi Deeyanah?

Kanta k'asa tana danne abinda ke taso mata tace " bakomai Abbi.

Da k'arfi ya runtse idonshi had'i da cije lips d'inshi, " wani abun yake yi miki acan na zalunci ko na rashin adalci da kyautatawa?

"A'a ta sake cewa kanta k'asa.

"Wasu abubuwan yake yi wad'anda basu kyautu a addininmu da al'adarmu ba acan?

"A'a, ta sake cewa kanta k'asa hawaye nabin fuskarta.

"To meyesa baki san bin mijinki inda Allah ya k'adarta muku zama?

Shiru tayi dan bata da abin fad'a, "ba tambayarki ake yi ba kin yiwa mututa ne banza dan sakarcin banza?

"Bakomai, haka nan kawai bana san binshi, jin tana ta maimaita bata san binshi yayi bala'in dugunzuma Deen, kun san halin kayanku da bak'ar zuciya take yaji ranshi yayi bala'in b'aci, zuciyarshi tayi bak'ikk'irin yadda kasan gawayi, jijiyoyin kanshi sukayi rad'o-rad'o kamar an zana su, saboda tsabar zuciya har wani yaji-yaji yake ji cikin idonshi, ji yayi ko idan bai tafi da ita ba hakan na nufin ajalinshi ya hak'ura, ko duniya zata tashi bata binshi America, har abada ya gama tafiya da ita ko'ina a duniya, Abbi zayyi magana yayi saurin cewa " shikenan bakomai ta zauna d'in Abbi.

Nan fa Babah yayi tsalle ya dire ya shiga bambami " ke d'in banza ke d'in wofi Deeyanah har kin isa ni mahaifinki da mijinki da kike a k'ark'ashin mu muce ga abinda zakiyi kice ba haka ba, wallahi baki isa ba, ai bake kika haifi kanki ba, ba kuma ke kike auran kanki ba, bake kika haife mu ba, kamar yadda bake kike auranshi ba, muddin kina neman kwanciyar hankali ki shirya kibi mijinki.

Sanin halin bak'ar zuciyar Deen da tun yana yaro in yace yabar abu ya barshi har abada ko za'a kashe shi yasa Abbi saurin cewa " a'a ka tsaya abi komai a hankali cikin lumana da dad'in rai, kar ayi abinda zai zo bayyiwa wani dad'i ba, adalci da fahimtar juna shine farkon abinda ake so a auratayya, yau da gobe sai Allah kamata yayi a karb'i uzurinta a duba mata itama, bawai a tirsasa mata ba.

"Karka d'aure mata gindi, wannan ai maganar banza ce daga bakin mutanen banza ka tab'a jin inda kana wata duniya matarka na wata nahiya fisabilillahi?

"Kai namiji ne, ni namiji ne daga ni har kai mun san yanayin in dai ba kuma so ake ajefa shi a halaka ba, a sashi ya fara neme-neman matan banza ba, Babah ya fad'a yana kallan Abbi.

Abbi zayyi magana Babah yayi saurin cewa " wallahi ko zata mutu acan saita bishi.

Jin Babah ya runtse yasa Abbi cewa " Allah ya kyauta, Babah ya amsa da Amin.

Duk da hukuncin da Babah ya yanke ko kad'an Deen bai ji a ranshi cewar zai tafi da Deeyanah ba, a yadda yake ji a ranshi idan aka matsa yana iya sauke mata igiyoyin aurenshi kowa ya huta.

Shi kad'ai yake ta shiye-shiryen tafiyarshi bai sake bi takanta ba, bai kuma sake yi mata maganar tafiyar ba, itama batayi mishi maganar ba, bai gayawa kowa shi kad'ai zai tafi ba har ranar tafiyar tazo yana janye da trolley ya fito daga bedroom d'inshi dan tuni suka raba d'akin kwana, da sauri ta mik'e tana binshi da kallan mamaki, gaba d'aya tama kasa magana ta zama speechless, take gabanta ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku, tsoro da tsakanin fargaba suka shigeta lokaci d'aya, cikin ranta ta soma maimaita " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un badai tafiya zayyi ya barni ni kad'ai cikin wannan babban bala'in ba?


JIDDARH......