BAK’AR SHUKA…!

46

by @hauwaausmanjiddarh

*BAK'AR SHUKA...!*

   


       NA


*HAUWA A USMAN*

    ~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


4️⃣6️⃣


Washe gari yana tashi yayi wanka ya shirya ya fice, minti 18 ne ya sada shi da gidansu, suna jin tsayawar mota suka fito harabar gidan, Mama nata rawar jikin ganinshi bakinta yak'i rufuwa, yayinda Abbah ke tsaye ya zuba mishi ido ganin yadda yayi wani fresh dashi, Mama na rik'e dashi har falo, kallanshi Abbah yayi sosai ya fitar da numfashi yace " Ajlaal!, yadda ya kira sunanshi ba k'aramin karya mishi zuciya yayi ba, a hankali ya d'ago ido ya zubawa Abbah ido.


"Ka sani babu da wani d'an sai kai, kai kad'ai Allah ya bamu balle idan babu kai muce akwai wani Wanda zai d'ebe mana kewa, gashi girma ya kamamu mu duka, lokacin da muka fi buk'atar ka a kusa damu, lokacin da muke buk'atar taimakonka, lokacin daya kamata ace ka karb'i ragamar dukiyata amma a lokacin ne zakayi nesa damu kayi watsi da al'amuranmu akan mace?


Kanshi k'asa yace " wallahi Abbah ba haka bane, " to yaya ne Ajlaal, ai ko babu amfanin da zakayi mana zamu so ganinka kusa damu.


" Kayi hak'uri in sha Allah zan gyara.


" Aikin kenan ayi hak'uri kullum abinda kake fad'a kenan.


" Wannan karon nayi maka alk'awarin zan rink'a zuwa kullum ina ganinku, " to mai zai hana ka dawo kusa damu gaba d'aya?


Kafin Ajlaal yayi magana Mama ta watsa mishi uwar harara tana fad'in " dan Allah karka dameshi, karka matsawa yaron nan ka barshi yaji dad'in lokacinshi ya morewa rayuwarshi haba, tsit Abbah yayi bai sake cewa komai ba, kallanta ta mayar ga Ajlaal cikin zak'uwa tace mishi " wacece yarinyar da kayi maganarta?


Cikin mamakin da Abbah ya kasa danneshi yace " unbelievable Ajlaal ne ke maganar mace?


"Wannan wace me sa'ar ce?


Kallanshi Mama tayi ta watsar irin ba'a saka bakinka ba d'innan ta mayar da kallanta ga Ajlaal tace " ya sunanta?


A shagwab'e yace " Mama!


"Eh! Wallahi a matse nake kayi aure naga 'yan jikokina, " ki bari tukunna da d'an sauran lokaci kad'an.


"Wanne lokaci ne ya rage?


"Kaga a bari ya huce shike kawo raban wani, da zafifi kan bugi k'arfe.


"Karki damu Mama wannan bazai huce ba balle ya kawo raban wanin, ita d'in tawace ni kad'ai, an riga an rubuta ni kad'ai ne mamallakinta, wannan karon bazan tab'a bari wani ya sake shiga tsakanina da soyayya ta ba, dariya Mama tayi tare da cewa " kayi komai danka mallaketa yak'i a soyayya ai halak ne, Abbah nasan yayi magana amma wani nauyi na hanashi.


Gidan ya yini bai bar gidan ba sai dare, sun sha hira, yana fitowa daga gidan yayi dialing number ta, bugu d'aya ta d'aga wayar tare da kara wayar a kunnenta batare datace mishi komai ba, yasan fishi take yi dashi dan haka tak'i yi mishi magana, idanuwanshi ya lumshe, had'i da sauke ajiyar zuciya a hankali, cikin taushin murya yace " kiyi hak'uri, soyayyarki ce tasa ni aikata duk abinda na aikata Deeyanah.


Cikin kunnenshi ta fitar da numfashi kana tace " ya wuce, murmushi yayi kamar tana ganinshi yace " yaushe zamu had'u na sake bada hak'uri sosai?


Kafin tayi magana yace " au na manta ashe fa Boss yace shi zai rink'a kaiwa unguwa da kanshi duk inda za'a aje ko?


Murmushi tayi me sauti dan tasan akwai abinda yake nufi, " fad'i kawai ina jinka! ta fad'a tana dariya,

" tunda haka ya zab'a ya zamuyi?


"Tunda shiya zab'i ya zame mana driver ai hikenan, ya fad'a yana dariya, itama dariyar tayi tace " kaga a matse nake fa kwana biyu bamu had'u ba yaushe zanzo a d'an sosa min?


Dariya yayi sosai harda dukan sitiyari yace " kamar ko kin san nima a matsen nake, idan zai yiwo gobe kizo mana mu d'an gwangwaje, " to shikenan ba damuwa, Allah ya kaimu, tana k'ok'arin kashe wayar yace " ki cewa saban driver mu yabi min ke a hankali fa, dariya tayi gami da kashe wayar batare data ce komai ba.


Text ta tura mishi kamar haka " gobe ina san ka kaini gidan Raleeya da safe please tace tana san gani na, bata jima da tura mishi sak'on ba ya dawo mata da amsar " Allah ya kaimu.


Yana zaune cikin mota yana jiranta ta fito, kallo d'aya yayi mata ya d'auke kanshi, ta bud'e ta shigo ta zaune a kujerar gaba, " ina kwana, an tashi lafiya?


Yana yiwa motar key ya amsa da " Alhamdulillah, babu wanda ya sake cewa komai har suka hau titi batare daya kalleta ba yace " ina ne?


Tana yi mishi kwatance har suka k'arasa k'ofar gidan Ajlaal, yabi gidan da kallo kamar zayyi magana sai kuma ya fasa ta bud'e motar ta fita tana fad'in " zaka je ka dawo ne?


"Ina nan ina jiranki ki gama ki fito mu tafi, batayi magana ba ta shige gidan, shi kuma ya gyara parking had'i da kwantar da kujera ya kishingid'a yana zaman jiranta.


Ta window suke lek'en Deen, a tare suka kwashe da dariya had'i da tafawa, " ashe dai da Hausawa ke cewa maso kayanka ya fika dabara da gaske ne?


"Shi da kanshi ya kawo matarshi inda za'a d'ebe mata albarkatun jiki ya zauna yana zaman jira a gama ya mayar da ita gida, lalle wata shari'ar sai a lahira, labulen window ta saki ta jingina bayanta da jikin window tace " shi yaga zai iya ai, bamu muka tilasta mishi ba, zab'in shi ne hakan, glass cup d'in hannunshi ya aje saman bedside ya tako gareta fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi ya matseta sosai gami da sake kallan motar Deen yace " so pity, karka damu kad'an zan d'an tsakureta, ya k'arashe maganar tare da had'e bakinsu.


Caraf ta amshe bakinshi ta soma tsotsar bakin tana lasa kamar ta samu ice cream, cikin salo ya d'auketa cak ya zaunar da ita saman k'ugunshi while bayanta na jingine jikin bango ya zame d'ankwalin kanta ya fad'i k'asa yasa hannunshi cikin kwantaccen gashin kanta daya sha gyara ya fara yamutsawa, sosai suka zage suka jiyar da junansu dad'i, ranar kam anyi gogen fata da gaske, cikin kwanciyar hankali sukayi suka gama yadda kasan babu wanda ke jiransu a waje, har wanka sukayi tare.


Tana saka kayanta yace " shanyar can fa da kikayi ta shanyu da kyau harta bushe, kanta ta dafe gami da d'an zaro ido tace "ops kasan na manta dashi?


"Ah! Ba dole ki manta dashi ba tunda kin karb'i damen jijiya harta kai miki karo, pillow ta jefa mishi tana dariya, har bakin get ya taka ta ya d'an tsotsi bakinta yana fad'in " ni dai ban k'oshi ba azo a k'ara min, ta tura shi baya tana dariya, sai da ta saita kanta sosai kana ta fita, bacci ta same shi yana yi cikin mota, har cikin ranta bata ji dad'in yadda ta same shi ba, sosai taji tausayinshi na ratsa ta, a hankali tayi knocking glass d'in window motar, cikin nutsuwa ya farka, motar ya bud'e mata ta shiga ta zauna, " kayi hak'uri na dad'e ko?


Bayyi magana ba yayiwa motar key suka bar wajen, Ajlaal dake tsaye jikin window yana kallansu yayi murmushi gami da kai glass cup d'in bakinshi.


Tun daga wannan rana ya zama cewa Deen ke kai Deeyanah gidan Ajlaal koyaushe, kuma ya jirata ta gama abinda take yi ya d'auko ta har tsayin watanni uku.


Deen na zaune saman dinning table yana cin abinci ta fito daga bedroom hannunta rik'e da waya tana lallatsawa, bai d'aga kai ya kalleta ba balle yayi mata magana, ta zauna saman sofa tana cigaba da abinda take yi itama batayi mishi maganar ba, a nutse ya gama abinda yake yi ya mik'e yabar wajen, kwance yake saman makeken gadonshi k'irar Turkish sai juyi yake yi ya rasa abinda yake yi mishi dad'i gaba d'aya duniyar tayi mishi bak'ikk'irin k'irjinshi yayi mishi nauyi, haushin kowa yake ji, duniyar tayi mishi duhu, abin duniya sun taru sunyi mishi yawa, duk iya bin diddigin Deen da bincikenshi ya kasa gano komai, babu abinda ya iya ganowa, dan duk wani takun da zayyi na Ajlaal na gaba da nashi, idan baku manta ba na fad'a muku Ajlaal nada kwakwalwa da masifaffan k'ok'ari irinsu ne ake kira da genius ko gifted, duk inda kuke tsammanin shegen mugun mai matuk'ar wayo da kwanya Ajlaal yakai, shiyasa Deen ya kasa gano komai duk iya bincikenshi.


Yana kwance ya tsunduma duniyar tunani saurin mik'ewa yayi tare da cewa " wait! tuno lokacin da suke hira da Deeyanah tace mishi ta nemi Raleeya ta rasa, bata sake jin labarinta ba tun bayan aurensu yayi, ya sake tuno tunda suke zuwa gidan Raleeya bata tab'a rako Deeyanah ba, bata tab'a cewa ya shiga su gaisa ko ta fito su gaisa ba, " da wani abu! lalle da akwai wani abu a wannan gidan ya fad'a a fili, bai tsaya yin shawarar komai ba ya mik'e, d'akinta ya shiga kamar an hankad'ashi ciki ya fad'a d'akin, ta fito daga wanka daga ita sai towel, " shirya mu fita, cike da mamaki ta kalleshi had'i da kallan agogon bango tace " unguwa kuma?


"Wacce irin unguwa cikin daren nan?


"Eh! nace ki shirya koma ina ne idan munje zaki gani, batayi tsammanin wani abu ba tace " to bani minti biyar na gama shiryawa, " shirya ina jiranki, yace yana zama saman gado, batayi magana ba ta soma shiryawa bata d'auki lokaci ba ta gama, ta zira hijab tare da d'aukar wayarta ta kalleshi tace " muje ko?


"Bani wayarki, yace yana mik'a mata hannu, cikin matsanancin mamakin dake bayyane saman fuskarta tace " wayata kuma?


"Eh ita, mik'a mishi wayar tayi tana kallanshi sosai, ya sata gaba yana binta a baya suka fice, " wai ina zamu ne?


Ta tambaya ganin ya hau babban titi, bai bata amsa ba illa mayar da hankali da yayi kan tuk'inshi, ganin suna d'aukar hanyar gidan Ajlaal yasa hantar cikinta kad'awa, cikinta ya juya da k'arfi, murmushin yak'e ta k'ak'aro tare da dakewa tace " idan ka gama da waya ta ka bani, hankalinshi nakan tuk'in da yake yi yace " ban gama ba, yayi maganar a tak'aice, wani irin mugun bugu k'irjinta ya shiga yi, zuciyarta na tsalle kamar zata tsaga k'irjinta ta fito, jinta take yi tamkar a saman ruwan k'ank'ara take zaune, hannuwanta take ta faman kwantala saboda tsabar tashin hankali batare data sani ba, batayi aune ba sai gani tayi yayi parking a k'ofar gidan Ajlaal, wata irin muguwar tsuma da kerrrrma jikinta ya d'auka lokaci d'aya.


A hannunta take jiyo sautin tsinkewar jijiyoyin kanta, duk wata k'ofar gashin dake jikinta ta soma tsatsafo da gumi, ko mala'ikan mutuwa ta gani akanta iyakacin abinda zata ji kenan, saurin kallanshi tayi cikin matsananciyar kad'uwa da firgita tana goge gumin kumatunta tace " me kuma muka zo yi anan?


"Ina san magana da Raleeya ne yau, ya k'arashe maganar had'i da sakin murmushin da bata isa ta iya fassarawa ba, yawun daya wuce mata ba shiri yasata kwarewa, sosai take tari while idonta kanshi tana kallanshi da idanuwanta da suka firfito kamar zasu fad'o k'asa, da k'arfi tsiya ta tsaida tarin, muryarta na shak'ewa tace " bari na shiga na kira ta, fuskarshi d'auke da murmushin har zuwa lokacin ya kafe ta da idanuwanshi dake k'ara firgita ta yace " nop! karki damu ba sai kin shiga ba, bari na samu yaro mu turo yayi yo mana sallama da mijinta in yazo shi sai yayi mana iso zuwa wajenta, " babu wanda fa ke shigar musu gida saboda tsaro, suna ma da k'attin k'arnuka, ta fad'a kamar me koyon magana, bai bi takanta ba ya bud'e motar ya fito, jikinta na rawa ta bud'e motar ta fito itama tana fad'in " ba saika aika yaro ba ka barni na shiga nayi mata magana mana.


Almajirin daya zo zai gifta shi ya kira tare da cewa " dan Allah shiga gidan nan kayi mana sallama dame gidan kome gadin gidan, Almajirin ya amsa da "to!, had'i da nufar gidan.......


JIDDARH.....