BAK’AR SHUKA…!

54

by @hauwaausmanjiddarh

*BAK'AR SHUKA...!*



NA


*HAUWA A USMAN*

~ JIDDARH~


Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh

ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh


5️⃣4️⃣


**********Idonta kan makekiyar tv bango tana kallan tashar sunna tv inda Malam Argugun yake wa'azi akan zaman takewar auratayya ji take tamkar sunanta yake kira yana wa'azin dan kusan gaba d'aya wa'azin ya shafi rayuwarta, da zamantakewar aurenta, wani hawayen bak'in ciki masu ciwo ne suka zubo mata, cikin kukan dake cinta tana danne shi tace " in sha Allah yau za'ayita ta k'are, bazan dauwamar da rayuwata cikin tsoro da firgicin tunuwar asirina ba, gwamma kawai na fad'a duk abinda zai faru ya faru.


Ta mik'e zata fita ya shigo sanye da jallabiya yatsanshi na latsa carbin tally counter, dakyar cikin dakewar zuciya ta runtse idonta da k'arfi muryarta na sark'ewa tace " in....ina....san....maga...na dakai, ta fad'a a rarrabe kamar me koyan magana.


"Nooooooo! Ajlaal yace da k'arfi had'i da wawurar computer gabanshi ya bugata da k'asa idanuwanshi sukayi jajir kamar wuta " a'a Deeyanah karkiyi min haka please, data ce zata fad'a mishi bai tab'a d'auka da gaske zata iya sanar dashi ba, bai d'auka tana da irin wannan k'arfin halin da dakewar zuciyar ba, yayi zaton shaci fad'i ne kawai ta fad'a ne danya kyale ta, dayasan da gaske take da yayi mata barazanar kashe shi idan ta sake ta fad'a mishi.


Ba musu ya k'araso ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun har lokacin tana tsaye bata zauna ba, "ina jinki, yace yana bin jikinta dake rawa kamar mazari da kallo, kasa magana tayi ta kuma kasa zama, yakai mintuna goma a zaune yana jiranta, jin batace komai ba yasashi mik'ewa zai bar wajen, tayi saurin zubewa gabanshi had'i da rik'e k'afarshi gam ta saki rikitaccen kuka wiwi kamar wacce ake zarewa ranta.


Komawa yayi ya zauna ya zuba mata ido yana nazartar ta, an sake d'aukar lokaci batayi magana ba, bata kuma da niyyar yin magana, "Lafiya Deeyanah?


Ya fad'a a nutse, jajayen idanuwanta ta d'ago ta zuba mishi ta kalli cikin kwayar idanuwanshi, " bari na kalle ka Yaya wata k'ila bazan sake samun damar kallanka ina matsayin matarka ba, cikin rashin fahimta yace " ban gane ba?


Sake fashewa tayi da kuka tare da sake rik'e k'afafuwanshi gam, " na lalata komai Yaya, na wargaza komai, na cuci kaina, na lalata rayuwata nayiwa kaina babbar illa, na sari kaina da bak'in dafi, nayi BAK'AR SHUKAR da har in mutu bazata daina yad'o ba, Yaya BAK'AR SHUKAR danayi ce ta fara fidda bak'ak'en 'ya'ya, ka yafe idan zai yiyu Yaya.


"Wai meke faruwa ne?


Ya fad'a gabanshi na tsananta fad'uwa, sai da ta runtse idanuwanta da k'arfi dakyar ta motsa bakinta ta had'a kalaman " NA CUCE KA, NACI AMARKA Yaya, daga nan ta kwashe komai tasss tun daga farko har k'arshe ta fad'a mishi.


Ji yayi an fisgeshi an d'aga shi sama an buga shi da k'asa da k'arfi, kamar zararre ya kwashe da dariya yace " Deeyanah kenan a sani na baki da k'awaye balle ince sune suke zagaki ki rabu dani, idan har rabuwa kike san yi dani basai kin biyo ta wannan hanyar ba, dakin sanar dani da zan sawwak'e miki kuma na d'orawa kaina laifin idan ma iyayenmu kike ji, bazan bari kiyi laifi ba zan wanke ki a idonsu, cikin kuka ta kama kafad'unshi ta girgizashi tana fad'in " da gaske nake Yaya wallahil azim babu k'arya a magana ta.


Murmushi ya sake yi a karo na biyu yace " kice dai kawai kin daina so na Deeyanah ko kuma dama tun farko bani kike so ba matsa miki akayi batare da an tambaye ki ra'ayinki ba, zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ya mik'e yana fad'in " a gida d'aya aka haife mu muka girma, a d'aki d'aya aka rene mu, mutane d'aya ne sukayi mana tarbiyya Deeyanah idan har ke mace zaki iya aikata wad'annan abubuwan a tarbiyyar da aka bamu to ni namiji da yanzu ba'a san inda nake ba, ki rink'a tunani kafin ki zartar da abu ki tuna da mutuncin iyayenmu dana ahalimu dana gidanmu, koda ace kina san rabuwa dani bai kamata kiyiwa kanki irin wannan mummunan sharrin ba, zan baki kwanaki biyu kiyi tunani idan kinga kina san rabuwa dani shikenan, amma ki sani ina sanki, ina matuk'ar k'aunarki.


Tana gunjin kuka tana fad'in " na rantse maka da girman Allah da gaske nake, amma baiko juyo ba ya fice.


Bayanshi tabi da kallo cikin ranta tana jinjina girman yarda da amintar da yayi da ita, tabbas miji ne nagari, ya yarda da ita fiye da yadda ya yarda da kanshi, da kanta da bakinta ta sanar dashi komai amma duk da haka yak'i yarda ina kuma ga ace wani ne ya fad'a mishi, lalle Deen ya cika cikekken masoyin da za'ayi alfahari dashi a ko'ina a gaban kowa.


Tabbas yana zarginta amma ko kusa tunaninshi bai tab'a kaishi nan wajen ba, bai tab'a kai zarginshi ko kusa da nan ba, shi bama Deeyanah daya sani tun tana jaririya ba ko wata macen baya zaton zata aikata irin haka cikin hayyacinta sai dai idan an gusar mata da hankalinta, ya k'arashe tunanin yana gyara kwanciyarshi.


Kanshi ya d'aga sama yana kyalkyala dariya kamar kafuran farko, " duk da kin sanar dashi babu abinda zai canja yanzu ma aka fara wasan Deeyanah.


Yadda taga dare haka taga rana komai ya dawo mata sabo fil saboda kuka har muryarta ta dishe dakyar ta mik'e da lalube ta shiga bathroom dan bata gani sosai saboda kumburin da idanuwanta sukayi, turus tayi ganinshi zaune saman WC yana ganinta ya mik'e yana dariya " dama ke nake ta jira tun d'azu, hannuwanshi ya hard'e a k'irjinshi ya jingina bayanshi da bango, idonshi cikin nata fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi.


"Malama Deeyanah kenan, kina ta cika bakin zaki fad'awa mijinki ki huta da barazana ta, banyi tsammanin da gaske zaki iya fad'a mishin ba, dan banyi tunanin kina da k'arfin hali har haka ba, amma bakomai tunda fad'a mishin bayyi amfanin komai ba, yak'i saurararki saima gwaleki da yayi yama d'auki maganar taki shirme, kuma shaci fad'i! ya k'arasa maganar had'i da tab'e baki ya d'aga gira d'aya irin I don't care d'innan, a hankali ya taka gabanta ya d'an sunkuya kad'an kasancewar ya fita tsayi, yakai bakinshi saitin kunnenta yace " karki damu har yanzu kina da sauran lokaci kuma ina nan ina jiranki, you're highly welcome k'ofa a bud'e take, ya k'arashe maganar had'i da hura mata iska a kunne ya kashe mata ido d'aya, ya rab'a ta gefenta zai wuce fuskarshi d'auke da murmushin cin nasara.


Har yakai bakin k'ofa zai fita ya jiyo muryarta tana fad'in " Yarda! aminta, yak'ini!


Juyowa tayi ta fuskance shi had'i da sakin hannunta data hard'e a k'irjinta ta furzar da iska daga bakinta tace " mema kace?


"Shirme! shaci fad'i! ya gwale ni, bai saurare ni ba ko?


Idonta ta bud'e tar cikin nashi tana kallanshi eyeball to eyeball tare da fad'in " duk ba su bane, Yarda! Amincewa da yak'ini ne, ya yarda dani fiye da yadda ya yarda da kowa da komai har da kanshi, ya aminta dani ya bani amana fiye da kowa, zuciyarshi nada yak'ini akaina shiyasa yak'i yarda da maganar duk da kasancewar ni da kaina da bakina na fad'a mishi, sai kayi tunani idan da wani ne ya fad'a mishi fa?


"Kwakwalwarka bazata iya hasaso abinda zai faru ba, so ka sani ba gwashale ni yayi ba, yarda dani da yayi yasa, bai zai tab'a tunanin irin wannan muguwar sakayyar daga gare ni ba.


Baki ya tab'e had'e da d'age gira d'aya irin bai dame ni ba, " duk da wannan tarin yarda da yayi dake kike san na wargazata ta hanyar nuna mishi videon blue film d'inki?


" Gaskiya bai kamata kiyi mishi wannan BAK'AR SHUKAR a zuciyarshi ba, dan bazata tab'a barin zuciyarshi ba, ina baki shawarar kibi shawarar daya baki ta sakinki kike son yayi, kice mishi eh kawai kinga asirinki bai tonu ba, ki dawo min mu dasa.


" Turrrr dakai da wannan k'azamin tunanin naka, wallahi dana dawo maka na gwammaci mutuwa sau dubu, na gwammaci duniya da abinda ke cikinta su gujeni su kyamace ni, na gwammaci kwanan bola.


"Un'un'un me yayi zafi haka Malama Deeyanah Allah ya bada hak'uri?


"But you're out of time, lokacinki yana tafiya dan sauranki 55hrs, kwanaki biyu da wasu 'yan a wanni, I hope you're ready for the fight, duk wata dak'ik'ar agogo dake bugawa tana tafiya ne da komai naki, tik tok tik tok get ready, ya fad'a yana barin wajen, tabi bayanshi da kallo batare datace komai ba.


***********A hankali ta tura k'ofar d'akin ta shiga cikin sand'a kamar b'auniya, yana zaune saman sallaya bacci na fisgarshi jin an tab'a k'ofa yasashi ware idanuwanshi akan k'ofar yana jiran me shigowa, ganin itace ya sashi lumshe idonshi had'i da sake bud'e su akanta, raban daya tsaya ya k'are mata kallo har ya manta, ta rame sosai ta fige tayi bak'i, duk tayi wani sukuku da ita yadda kasan mareniya, gabanshi ta zube ta d'ora hannayenta akan k'afarshi yayinda data kifa fuskarta akan cinyarshi, ta fashe da kukan k'unci.


"Yaya ka tsaya ka saurare ni, lokaci yana k'ure mana a kowanne lokaci komai yana iya faruwa, ka tsaya muyi shawarar ta inda zamu b'ullowa al amarin tun kafin dare yayi mana, Ajlaal bashi da imani babu abinda bazai iya aiwatarwa....


Turare ta yayi daga jikinshi ya mik'e tsaye had'i da nuna mata k'ofa yace " fita!


Cikin mamaki ta kalleshi tace " bazaka tsaya ka saurare ni ba Yaya?


"Me yasa kak'i yarda da duk abinda zan fad'a maka ne?


"Ni fa ba k'aramar yarinya bace, ina da hankali da tunani na bazan yiwa kaina irin wannan mummunan sharrin ba, dan Allah ka tsaya ka fahimce ni.


Idonshi kanta yace " in banda nayi miki farin sanin dako kaina banyiwa shi ba, da saina ce ko shaye-shaye kika fara, to idan kuwa bakya shaye-shaye to tabbas ciwon hauka ne ya sameki ko kuma kwakwalwarki ta samu matsala.


Kamar tab'abb'iya ta soma girgiza kanta tana fad'in " a'a babu ko d'aya, ka yarda dani wallahi gaskiya nake fad'a maka, idonshi ya runtse da k'arfi yace " nace ki fice min daga d'aki ko?


Ta bud'e baki zatayi magana yace " out! a tsawace sai da d'akin ya amsa, rushewa tayi da rikitaccen kuka tana fad'in " wallahi tallahi Yaya da gaske nake naci amanarka da Ajlaal, nayi zina da aurenka, kuma yayi video lokacin da muke aikata zinar yana yi min barazanar muddin ban koma muka cigaba ba zai sakarwa duniya video, ka yarda dani dan Allah Yaya, cikin b'acin ran da kalamanta suka haifar mishi ya damk'e ta yaja ta zuwa wajen d'ak'in, tana turjewa tana ta kiciniyar kwacewa while tana ihuuun kuka tana rok'onshi ya yarda da ita.


" Yaya zakayi danasanin k'in yarda dani d'in da kayi, zakayi nadamar rashin sauraro na da rashin d'aukar magana ta da muhimmanci, jefa ta yayi waje ya mayar da k'ofar d'akinshi ya rufe, bata bar k'ofar d'akin ba saima bugun k'ofar d'akin data farayi tana kuka tamkar ranta zai fita tana fad'in " ka yarda dani dan Allah Yaya.


Ya rasa abinyi ya rasa abin kamawa, kanshi ya gama kullewa gaba d'aya, wani iri yake ji cikin kanshi, bathroom ya shiga ya d'auro alwala ya tada sallah ko zai samu nutsuwa.


Tun daga wannan lokacin Deen ya ida fita a sabgar Deeyanah d'an abincin da idan ta dafa da yake ci yanzu ya daina ci, duk wani abu da zai had'ashi alak'a da ita ya daina yi, ko magana bayayi mata, yayinda babu irin nacin da rok'onshi da Deeo batayi ba akan ya tsaya ya fahimce ta suyi magana, dan lokacin su na k'urewa amma yak'i sauraronta dan a tunaninshi zuga ta akeyi ta rabu dashi.


Cigaban Labari........


Saukar ruwan tsarin data ji a jikinta ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, lokaci d'aya amai ya taso mata sakamakon dukan hancinta da warin ruwan yayi, bata gama dawowa cikin hayyacinta ba yaji muryar wani figigin mutum ramamme kamar a hureshi ya fad'i yana sanye da riga 'yar shara yana fad'in.


" Yawwa Alhamdulillah yau nayi kamu dama na dad'e ina kwantan b'auna a wajen nan ina san na kama tsinannun dake bin duhun dare suna yi mana iskanci a cikin kangon nan, tur daku munafukai duk kunbi kun addabi yaran unguwa da tumaki, ku baga mutane ba ku baga dabbobi ba, cikin sanyinta tace " wallahi ba... bayan hannunshi ya saka ya gwab'e mata baki ya d'ora da " bak'ar annamimiya rufe mana baki, imma kwastamominki kike jira to wallahi tun da sauran rab'a a zuciya ta ki tashi kibar wajen nan inba haka ba na nad'a miki na jaki, na zage iya k'arfina nayi miki mugun duka, ya k'arashe maganar had'i da tofa mata wawwaran yawonshi a fuska me d'oyi kamar rub'abb'iyar jab'a, gefen bakinta dake zubar da jini tasa hannunta ta goge, ta kalle shi sosai kana ta mik'e tabar wajen, har ta d'anyi nisa tana jiyo bambamin bala'in mutumin.


Duhun daren bai bata tsoro ba taita tafiya harta fita daga dajin ta isa titi, babu kowa gari yayi tsit baka jin komai sai sautin kukan tsuntsaye, tana cikin tafiya wata bak'ar mota hayis ta faka a gabanta wasu k'attin maza suka fito, basuyi wata-wata ba suka damk'e ta nan fa dambe ya b'arke tsakaninsu, ihuuuun neman taimako ta somayi da iya k'arfinta.


"Wayyo Allah jama'a a taimake ni zasu sace ni, ban san su ba!.


Tsaye yayi gefensu hannunshi na dama rik'e da sharb'ebiyar adda while d'aya hannun yana rik'e da wani abu da duhu ya hana su gane kome nene, idonshi kanta yana kallanta yace " a karo na farko a rayuwarki ki nemi taimako na, ni kuma nayi miki alk'awarin d'ayansu bazai bar nan a raye ba, d'aya daga cikin mutanen ya tunkaro shi yana fad'in " kai har waye da kake cewa d'ayanmu bazai bar nan a raye ba?


"Kalli yawan mu fa! Mu bakwai kai kuma kai d'aya ne, ya fad'a yana hankad'a shi baya, bai kula mutumin ba yace " ki nemi taimako na, ya fad'a idonshi kanta.


" Wallahi dana nemi taimakonka na gwammaci ni da kaina da k'afafuwa na na bisu duk da kasancewar ban sansu ba ban tab'a ganinsu ba amma ina da yak'in sun fika tausayi da imani, a hasale yayi magana da k'arfi cikin zafin rai " nace ki rok'e ni ko?


Kallanta ta mayar ga k'attin mazan tace " muje ko!, ta fad'a tana wucewa gaba zata shiga motar, yasan halin Deeyanah da shegen taurin kan tsiya kamar na kafiran farko, ya tabbatar data rok'i taimakonshi gwara ta bisun, idanuwanshi ya runtse da k'arfi ya bud'e a lokaci d'aya suka canja launi zuwa asalin jajaye, cike da matsanancin mamakinta k'attan maza suka bi bayanta zasu shige motar, yadda kasan k'iftawar ido ya sare kan uku daga cikinsu.


Kallan gangar jikin matattun dake zube k'asa babu kawuka suka yi kana suka mayar da kallansu gare shi, d'ayan na k'ok'arin ciro bindiga ya sare kanshi shida na bayanshi, ihuuu sauran biyun suka saki had'i da yankar daji a guje dan ceton rayuwarsu.


"Ni kad'ai ne a duniya nake da ikon cutar dake, ni kad'ai ne nake da ikon saka hawayenki zuba, ni ke da iko akanki, ni ke da ikon yi miki komai bayan ni babu wani mahaluk'i daya isa ko inuwarki ya cutar, bai jira amsarta ba ya juya bar wajen.


Kallan gawarwakin tayi babu d'igon tsoro a tattare da ita, ta dad'e tana kallansu kana tasa k'afa ta tsallake su tayi nata waje.......


JIDDARH.....