59
*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~
Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh
6️⃣0️⃣
A hankali ta d'ago kanta ta sauke idonta akanshi tana k'ara ganin girmanshi, tun da abin ya faru kowa gudunta yake yi, babu wanda ya tsaya ya saurare ta, ko sau d'aya tak babu wanda yaso jin ta bakinta ko abinda ya faru, a karon farko kuma mutum na farko daya saurare ta, ya kuma so jinta bakinta, kanta ta sunkuyar k'asa tana san hawaye su zubo mata amma babu ko d'igo, a fili ta sauke ajiyar zuciya tana sake d'agowa ta kalli Deen da Babah da kallo, duk da kallo d'aya tayi musu ta gane dolen da akayi musu shinfid'e akan fuskokinsu, kanta ta sunkuyar had'i da bud'e baki zata soma magana Deen yayi saurin mik'ewa ya kalli Babah yace " bari na amsa waya, Babah ya gane guduwa zayyi dan haka yayi saurin cewa " jeka!, dan kar Abbi ya hana shi, shima dole ce ta zaunar dashi.
Murmushin yak'e Deeyanah tayi kana ta soma bada labarin komai tun daga farkon had'uwarta da Ajlaal a makaranta har kawowa mafarin abun bata b'oye komai ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un lalle Deeyanah kin tafka babban kuskure kece babbar me laifi duk abinda ke faruwa ke da kanki kika jawowa kanki, kin shuka BAK'AR SHUKA... shiyasa duk abinda Allah yace a bari barin nashi shine mafi alkhairi, shi kuma Ajlaal yayi amfani da k'uruciyarki yaci moriyar kwakwalwarki ta mace ya dasa miki tsoronshi da firgici cikin ranki da haka yayi amfani ya cimma burinshi a kanki, yayi wasa da kwakwalwarki, ina ita RALEEYA DATA JEFAKI CIKIN WANNAN MUMMUNAR K'ADDARAR?
"Tana ina?
"Ina labarinta yake?
"Sau Dama k'awaye suna da tasiri a rayuwar mutum, sukan kai mutum su baro shi, kamar yadda RALEEYA ta cuce ki ta jefa cikin gagarumar masifar da fitarki sai Allah yaso, ta zuga ki, ta baki shawara kin d'auka, meyasa data baki shawarar baki nemi shawarar kowa ba?
"Gashi nan ke abinda kuka aikata yake farauta ita tana can tana rayuwa cikin jin dad'i da walwala ta barki cikin danasani da nadama, shi kam Babah wani irin haushinta da tsanarta yaji sun k'ara ratsa shi da kafi, musamman ma da yaji sanadin abin ya d'auka k'addararta ce tazo mata a haka, amma yanzu daya ji ita ta jawowa kanta haushinta yake ji sosai, a fili yaja tsoki had'i da mik'ewa ya kalleta yayi kwafa, kamar bazayyi magana ba sai kuma yace.
"Kin cuci kanki kin cuci rayuwarki, kin jefa wad'anda basu ji ba basu gani ba cikin masifar da kika jefa kanki, d'an itaciyar BAK'AR SHUKAR... da kikayi ke kad'ai gashi nan kin raba mana muna cin shi tare dake, gangancinki yayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarki da d'anki, Allah ma kad'ai yasan iyakacin wad'anda zaki zama ajalinsu, nayi takaicin haihuwarki, nayi nadamar aurawa Deen ke, dama ban haifeki ba, ke inama ban auri uwarki ba balle na haife ki, da nasan bak'ar daga zaki zama dana sa an zubar da cikinki tun kafin ki zo duniya, kin b'atawa zuri'ar mu suna har a tashi duniya, kin jefa mu cikin kunyar duniya har mu mutu, kin zubar mana da k'ima da mutumcinmu dan yanzu bamu da wani sauran mutunci a idon Jama'a, muna sanye da tufafi amma ana kallan mu tsirara, matar da tayi dakon cikinki har tsayin watanni tara, tayi nak'udarki, kika tsaga tsatsanta kika fito, ta shayar dake daga jikinta, ta reneki amma ki rasa dame zaki biyata sai da mutuwa Deeyanah bayan ita ta baki rayuwa?
"Allah ya d'auki ranki kamar yadda kika zama sanadiyyar mutuwar Aina'u.
Da sauri ta amsa mishi da " Amin Babah, Amin ya Allah, Ubangiji ya amsa rok'onka ya karb'i raina na huta dan nima na gaji da wannan bak'ar rayuwar, zayyi magana Abbi yayi saurin mik'ewa ya jashi zuwa waje, bai jima ba ya dawo, sai da ya d'an saita kanshi kana yace " wallahi ko abinda na mallaka a duniya zai k'are saina ga bayan Ajlaal da duk wanda ya d'aure mishi gindi, yadda ya saki kuka saina zubar da hawayenshi, yadda ya saka mu cikin halin bak'in ciki da damuwa shima saina saka ahalinsu kaf a cikin kwatankwacin halin daya saka mu, saina tona mishi asiri duniya tasan waye shi.
********Cikin kwana d'aya Abbi ya gama duk wani shirye-shiryen da zayyi ya d'auki manyan kwararrun lawyers wad'anda zasu tsaya mishi a kotu, ranar litinin aka kaiwa iyayenshi sammacin kotu, babu yadda Babah bayyi da Abbi ba amma fur Abbi yak'i sauraranshi.
Abbah da kanshi ya kira Ajlaal ya sanar dashi batun sammacin da aka aiko, yayi dariya had'i da cewa " na sani ai tun kafin ma yakai kotun nasani, Allah ya kaimu ba damuwa, ashe ma iyakacin nan ya tsaya duk cika bakin nashi, Abbah yayi mamakin ganin ko a jikin Ajlaal dan haka yace " kaji tsoran Allah, kaji tsoran ranar had'uwarka da Allah, wallahi idan kaine wanda ka lalatawa yarinyar nan rayuwar to ka sani kaima Allah bazai barka ba, da sannu Ubangiji zai saka mata, ya mayar dakai abin kwatance, ya wulak'anta ka kafin mutuwarka ta riske ka.
"Na lalata mata rayuwa kodai muka lalatawa juna rayuwa?
Dan yaji maganar da Deeyanah ta fad'awa su Abbi sai a lokacin shi kanshi Ajlaal d'in yasan hak'ik'anin abinda ke faruwa, ya kuma alwashi akanta.
"Ina zaman zamana lafiya ta shigo rayuwata ta wargaza min duniya ta Abbah, duk abinda ya faru itace sanadi itace ta jawowa kanta, da kanta tayiwa kanta BAK'AR SHUKA....
Abbah zayyi magana Mamah tayi saurin tarar numfashin shi da fad'in " dan zatin Allah ka kyale yaron nan ka shafa mishi lafiya wannan wacce irin masifa ce ka saka yaro gaba ka tsare shi da maganganun banza, Ajlaal fa ba yaro bane ya girma ya isa ya yankewa kanshi hukuncin dayace da rayuwarshi.
"Yanzu maganar tawa ce ta zama maganganun banza?
Fuska ta yatsina had'i da tsare shi da ido tace " eh! koba hakan bane?
Abbah bayyi magana ba ya mik'e ya fice.
Ranar zaman kotu
Kotun ta cika mak'il da mutane da wad'anda suka zama dole da gayyar sod'i 'yan san ganin kwakwaf, masu san su gani da idonsu ba abasu labari ba, bak'ar mota Range Rover me bak'in tint da duk bin kwakkwafin mutum bazai ga wanda ke cikin motar ba, ta faka a harabar kotun ,daga ita sai Abbi ne suka zo kotun dan kowa k'in zuwa yayi, Babah ko cewa yayi bada shi za'a d'aurewa k'arya gindi ba shidai dayaga zai iya yaje can yayi tayi.
Doguwar rigar atamfa ce a jikinta sai hijab data sakko dashi fuskarshi ta rufe fuskarta ruf Abbi na binta a baya, ihuuuuu mutane suka soma yi mata had'i da jifanta da duwatsu, aiko kan kace me anyi mata jina-jina an fasa mata goshi da bakinta sai jini ke zuba, dakyar aka kwace ta a hannun mutane aka shigar da ita kotun, sai da rigar jikinta da hijab d'in suka yage, yana zaune a bancin farko kusa da Abbah da Mama, akanshi idonta ya fara sauka ya sakar mata shu'umin murmushi had'i da kashe mata ido d'aya, Abbah na d'ora idonshi akan yarinyar matsanancin tausayinta ya kamashi, ita kam Mama in banda uwar harara babu abinda take watsawa Deeyanah.
Tana cikin jikin Abbi yana ta kakkare ta suka zauna, bayan an natsa magatakardar kotu ya mik'e ya gabatar da k'ara, ya karanto k'orafi, Alk'ali yayi gyaran murya had'i da cewa " ina me k'ara?
Cikin nutsuwa Abbi ya mik'e da ita a jikinshi suka fita gaban kotu, Alk'ali ya sake cewa " ina wanda ake k'ara?
Cikin izza ta tak'ama ya fito ya tsaya daga d'aya b'angaren suna fuskantar juna, Alk'ali ya kalli Abbi yace " fad'awa wanda kake k'ara akan abinda kake k'ararshi, Abbi ya kalli Deeyanah yace " kada kiji tsoron komai da kowa ina tare dake, Allah zai tsaya mana, kiyiwa kotu bayanin komai bisa gaskiya da amana, bakinta na rawa, muryarta na shak'ewa while hijabinta na zamewa ya fad'i saboda yagar dake jikinshi, ta kwashe komai ta fad'awa kotu bata rage komai ba, nisawa Alk'ali yayi had'i mayar da kallanshi ga Ajlaal yace " to kaji abinda ake tuhumar ka dashi?
"Eh naji!.
"To me zaka cewa kotu!?
Gyaran muryar yayi kana cikin shariya yace " to ni dai gaskiya ban san komai akan wad'annan maganganun ba, yadda kowa yaga videon ta haka nima na gani, ni nama manta da ita, na dad'e da rufe babinta a rayuwata.
Alk'ali ya mayar da kallanshi gasu Deeyanah yace " to kunji, a hankali ta d'aga ido ta kalli Ajlaal ya d'auke idonshi gami da basarwa, Alk'ali yace " kuna da sheda ne?
Abbi ya kalli Deeyanah cike da tausayawa, itama shi ta kallan kana ta mayar ga kallanta ga Alk'ali tace " eh akwai shaidu.
D'an shiru Alk'alin yayi yana nazari kana yace " ku koma ku zauna, sai da yayi rubutu sannan ya sake d'agowa ya kalli inda lauyoyi suke yace " ina lauyan me k'ara?
Lokaci d'aya lauyoyi bakwai suka mik'e tsaye sosai mamaki ya fito k'arara saman fuskar Alk'alin cike da mamakin yace " dukkanku lauyoyin me k'ara ne?
Suka da eh cikin girmamawa, bayyi magana ba ya juya b'angaren Ajlaal yace " ina lauyanka?
Murmushin gefen baki yayi had'i da cewa " bani dako d'aya.
Jinjina kai Alk'alin yayi kana yace "lauyoyin me k'ara kuna da abin cewa?
D'aya daga cikinsu ya karkace ya soma magana, ya dad'e yana magana kana yayi shiru d'aya daga cikinsu shima ya fara maganar, sai da kuka gama kaf kana ya kalli Ajlaal yace " kana da abin cewa?
"A'a, Ajlaal yace fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi, Alk'ali ya fara rubutu, ya d'an d'auki lokaci me tsayi yana rubuce-rubuce kana ya d'ago, "zamu cigaba da sauraren wannan shari'ar a ranar 30 ga wantan 6 na wannan shekarar inda masu k'ara zasu gabatar da shaidunsu a gaban kotu.
Da taimakon 'yan sandan kotun aka shigar da ita mota, koda suka koma gida babu wanda ya tambayesu yadda ta kasance a kotu, har shi kanshi Babah da Ammu, sosai ran Abbi ya b'aci da burus d'in da sukayi dasu, amma ya kanne bayyiwa kowa magana ba.
Tana shirin shigewa d'aki Abbi yace " kina da shaidun da zaki gabatar a kotu?
Cikin sanyinta da muryarta da bata fita sosai tace " eh! akwai text's d'in dayake turo min ta wayata da voice note ta WhatsApp kuma har yanzu suna nan a wayata.
"D'auko min wayar. Abbi ya fad'a yana zama.
Shigewa tayi cikin bedroom ta bud'e wardrobe ta zaro wayar tana fitowa ta kunna wayar dan ta manta rabanta da amfani da waya, yana zaune ta rusuna ta mik'a mishi wayar, ya karb'i wayar dai-dai lokacin data gama kunnuwa, mik'a mata wayar yayi yace " saka password d'in, ta karb'a ta cire password d'in ta sake mik'a mishi, yana k'ok'arin shiga WhatsApp wayar tayi hooking yayi-yayi wayar ta dannu tak'i dannuwa, sai kuma ta farfarfar, sai wayar ta kashe kanta, kallanta Abbi yayi yace " dama wayar nada matsala ne?
"A'a bata da matsalar komai, zayyi magana wayar ta kunna kanta, ta dad'e kafin ta zama normal bisa mamakin su komai na wayar ya sauka wayar ta dawo kamar sabuwa, babu abinda bai goge ba, murmushin takaici Abbi yayi yace " an datsi wayar (hacking) an goge komai dake kan wayar, cikin tashin hankali ta warce wayar daga hannun Abbi ta shiga duba wayar hannunta na rawa, amma yadda kasan yanzu ta bud'e wayar daga kwalinta, cikin tsoro idanuwanta waje tace " yanzu ya zamuyi a kotu bamu fa da wata shaidar bayan wannan?
Murmushin takaici ya sake yi a karo na biyu kana yace " sai dai mu jira ikon Allah.
Kotu Day2
Kotin tayi mak'il da jama'a, Alk'ali ya shigo kowa ya mik'e tsaye sai bayan ya zauna kana kowa ya zauna, bayan an natsa Alk'ali ya nemi lauyoyin me k'ara suka fito gaban kotu.
"Yana duba takardun gabanshi yace " ina shaidar da zaku gabatarwa da kotu?
Kallan juna lauyoyin sukayi kana d'aya daga cikinsu yace " babu wata shaida mun rasata, a fili Alk'ali ya fitar da nannauyan numfashi kana yace " zan sake baku dama ta biyu kuma ta k'arshe kuje ku sake binciko shaidar da zaku gabatar a gaban kotu, lauyoyin suka rusuna had'i da yin godiya suka koma suka zauna, d'an shiru ne ya ratsa kotun, Alk'ali yayi ta rubuta kana d'ago yace " an d'aga shari'ar zuwa nan da sati uku zai kama 20 ga watan gobe na wannan shekarar, kooootuuuu! ya mik'e ya fice kana kowa ya fice, fuskarshi d'auke da murmushi ya kalleta hannuwanshi hard'e a k'irjinshi yana tauna cingam, bayyi mata magana ba ya wuce ta gabansu yana fito.
Daga Deeyanah har Abbi jikinsu yayi mugun yin sanyi dan sun hango fad'uwa da rashin nasara k'arara, basu da wata makama ko mafita, jikinta a sanyaye ta wuce Abbi dake zaune a falo, d'an tari yayi yace " Deeyanah babu abinda za'a iya samu wanda zai tabbatar da laifin Ajlaal a kotu?
Jimmmmm tayi tana nazari kana ta d'ago kanta dake k'asa ta kalli Abbi tace " wallahi babu dama a waya ta ne kuma ya goge komai dake kan wayar, cikin jimami Abbi yace " bakomai akwai Allah, kuma yana bayan me gaskiya, muyi addu'a, ta d'aga mishi kanta had'i da wucewa bedroom d'inta.
Kotu Day3
Abbi da Deeyanah jiki ba kwari a sanyaye suka isa kotun cike da sanyin gwiwa, shiko yasha kwalliya da k'ananan kaya sai k'alli yake yana shek'i fuskarshi d'auke da wadataccen murmushi, ya kafe ta da ido baya ko blinking, tana jin yadda idonshi yake yawo a jikinta amma tak'i kallan inda yake, Alk'ali ya shigo kamar yadda aka saba kowa ya mik'e sai bayan ya zauna kowa ya zauna, magatakardar kotu ya mik'e ya karanto shari'ar da za'a saurara, bayan ya gama Alk'ali ya nemi ganin lauyoyin me k'ara.
"Kunzo da shaidar?
Kansu k'asa cikin rashin kwarin gwiwa suka amsa da a'a dan sunyi iya yinsu wajen neman hujjar da zasu gabatar a gaban kotu amma dayake Ajlaal shege ne baibar kafa ko d'aya ba yasa basu samu komai ba, sunyi duk wani bincike da bin kwakkwafi amma babu abinda suka samu.
Alk'ali ya d'auki lokaci me tsayi tana rubutu kana ya d'ago ya kalli Ajlaal yace " kana da abin cewa?
Baki ya d'an tab'e had'i da girgiza kanshi yace " a'a bani da wani abin cewa.
"Sakamakon rashin hujja da shaidun da za'a gabatar a gaban kotu dan kotu ta samu gamsuwa yasa ni Alk'ali Bala Muhammad na yanke hukuncin korar k'arar had'i da rufe kundin shari'ar a ranar 20 ga watan 4 na wannan shekarar, ya buga stamp a jikin wata takarda ya mik'e, hannuwanta ta dunk'ule da k'arfi had'i da runtse idanuwanta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Abbi ya furta a zahiri cike da takaicin rashin nasarar da sukayi, jiki a sanyaye suka fito daga kotun suna shirin shiga mota ya k'araso inda suke yayi mata kallan cikin ido gami da tauna cingam, har ya juya zai tafi sai kuma ya dawo ya kalli cikin idonta yayi murmushi had'i da cewa " kina tunanin zakiyi nasara akaina ne!?
"Shifa Ubangiji ba azzalumin sarki bane, Ubangiji na kowa da kowa ne ko arne wanda ba musulmi ba ya rok'e shi zai amsa.
Hawayen data dad'e tana addu'a da fatan zubar su ne suka gangaro kan kuncinta, tasa yatsa ta d'auke hawaye had'i da kawar da kanta ta kalli gefe na tsayin seconds 2 kana ta mayar da kallanta gare shi tace " ka kuma yin nasara akaina, meyasa kake yin duk wad'annan abubuwan Ajlaal!?
"Meyasa kake san lallai dole saika lalata min rayuwata?
"Akan me wanne laifin nayi maka!?
Kallan rainin hankali ya watsa mata kana yayi murmushi yace " nima tambayar dana dad'e ina yiwa kaina kenan kafin na samu amsa ta a ranar da kike fad'awa mahaifinki da ahalinki sirikinki labarin silar faruwar komai, kuma ki daina cewa na lalata miki rayuwa, idan da wanda ya lalatawa wani rayuwa a tsakaninmu kece kika lalata min rayuwata, meyasa Deeyanah?
"Meyasa kika dagula komai keda k'awarki akan san zuciyarku?
" Meyasa ina zaman zamana lafiya da rayuwata a duniyata kuka shigo duniyata kuka tarwatsa min komai?
"Me nayi miki?
"Kin cuce ni! kin zalunce ni kin lalata komai Deeyanah, bamfa isa na canja kaina ba, ban isa na koma daddad'a kuma sauk'aka'k'iyar rayuwata kamar ta baya ba fa, ya k'arashe maganar hawaye nabin kuncinshi, ba k'aramin firgici ta shiga ba, tayi bala'in tsorata dan bata tab'a tsammanin yaji labarin ba, lalle akwai k'ura tunda har taga hawaye a idanun Ajlaal.
Cikin rawar murya tace " am....am... dan Allah kayi hak'uri wallahi ban san abun zai zama haka ba, nima shawarar k'awata nabi, na sani ni me laifi ce nice ummul aba'isin faruwar komai amma dan Allah kayi hak'uri ka kyale ni haka, idan ma fansa zaka d'auka akaina ka d'auki fiye da fansarka.
Yatsa yasa ya kawar da hawayenshi yayi murmushin da saida gabanta ya fad'i, lokaci d'aya taji yammmmm a cikin jinin jikinta.
"Gamuwar Gayya tafi ta gayya zafi Deeyanah! ada daban san silar faruwar komai bama banyi niyyar na kyale ki ba balle yanzu dana san kece kika zab'i hakan da kanki, wallahi bakiga komai ba yanzu ma aka fara wasan, sannan duk wanda yayi k'ok'arin shiga tsakanina dake saina ga bayanshi ko waye, haka duk wanda ya hanani aurenki a baya da kuma yanzu shima ya shirya ina nan zuwa gareshi, haka zalika duk duk wanda yayi k'ok'arin dakatar dani.... Lips d'inshi ya cije yana kallan Abbi, ya juya yabar wajen tabi bayanshi da kallo cike da matsanancin tsoro da fargabar da suka shige fiye dana koyaushe.
Ran Abbi a matuk'ar b'ace ya shiga gidan Ammu na zaune kan sofa tana sauraren karatun alkur'ani mai girma tana bi ya shigo, d'an kallansu tayi ta kawar da kanta gefe tana fad'in " sannu da zuwa!
Banza yayi da ita be amsa ba, dan yau haushin kowa yake ji kuma dai-dai yake da kowa, "saboda wulak'anci ace kana shari'a a kotu babu wanda zai tambaye halin da ake ciki, ko maganar babu wanda ya tab'a yi min, ta gane da ita yake dan haka ta mik'e zata bar wajen.
" Au wato ma dan wulak'anci shine ina magana zaki tashi kibar wajen?
"To Alhaji me kake nayi?
"Babu! nace babu! ya fad'a a harzuk'e, " Allah ya baka hak'uri bani nakar zoman ba, ta fad'a had'i da saurin barin wajen, nan Abbi ya zauna yana ta bambami babu wanda ya kula shi, Babah ma har yazo bakin k'ofa zai wuce zai shiga yaji bala'in yayan nashi, dan haka ya juya, sukayi kacib'us da Deen da shima part d'in zai shiga, " karka shiga neman wanda zai huce takaicin rashin nasararsu a kotu yake, aiko karaf a kunnen Abbi, nan fa ya k'ara harzuk'a ya zage yaita ruwan masifa kan me uwa da wabi har ma'aikatan gidan bai kyale ba, yayi iya yinshi babu wanda ya tanka mishi balle a samu wanda zai kula shi harya gaji dan kanshi ya bari.
K'arfe biyun dare tana zaune zaman dirshan a k'asan tile's a falo ba kuka take yi sai dai bala'in da take ji deep down gwara kukan sau dubu, ba zato ba tsammani sai ganinshi tayi a kanta tsaye, ta d'aga kai ta kalle shi batare da tayi magana ba, ta sunkuyar da kanta k'asa, " Deeyanah!
Ya kira sunanta cikin taushin murya, kamar bazata d'ago ta kalleshi ba sai kuma ta d'ago, zubewa yayi gabanta bisa gwiwowinshi ya fakaici idonta cikin zafin nama Ajlaal ya shak'a mata wani abu a hancinta, a galabaice tana marisa ta kalle shi had'i da cewa " meee meee kaaaaa shak'aaa minnn!?
Baya tayi luuuuu zata fad'i ya tare ta, ta fad'a jikinshi ya sab'eta a kafad'a tare dayin waje da ita, d'an nesa da gidansu ya kaita inda zata iya hango gidansu tarwai ya ciro wata 'yar kwalba a aljihunshi ya shak'a mata a hancinata, batafi minti biyar da shak'a mata abun ba ta farfad'o, zambur tayi ta mik'e ta ja baya kanta ta kalla sosai kana ta fara waige-waige ta kasa fahimtar inda take ta dad'e kafin ta fahimci a inda take, ta juya ta fuskance shi maganarta na sark'ewa tace " meeeee neee neee kuma?
Murmushi ya sakar mata had'i da kallan cikin idonta ya d'age mata gira d'aya tare da nuna mata gidansu da idonshi, a d'an tsorace ta juya ta kalli gidan, ganin bataga komai ba, yasata sake kallanshi tace " me kake shirin aikatawa?
Bayyi magana ba illa murmushin daya sake yi mata had'i da sake nuna mata gidansu da idonshi, gidan ta zubawa ido na wajen minti biyar amma shiru, " wai me.......
Wata irin mahaukaciyar k'ara ce ta sakata yin shirun dole, saida k'asar wajen tayi girgiza ji kake durummmmmmmm! Dammmmmm! yadda kasan k'arar fashewar dutsen zuma rock ko gigitacciyar tsawar da akeyi lokacin damuna, durk'ushewa tayi a k'asa gami da sanya tafukan hannayenta ta toshe kunnuwanta.
Iface-ifacen mutane da salati ta fara jiyowa, a hankali ta zame hannayenta daga kan kunnuwanta, wani rikitaccen tsoro ne ya ziyarce ta lokaci d'aya, tana daga durk'ushen amma tana jin yadda k'afarta da jikinta ke rawa, dakyar ta tattaro d'an ragowar k'arfin daya rage mata ta mik'e, kallanshi take yi tana san tambayarshi k'arar meye amma ta kasa koda motsa bakinta balle ta iya furta koda kalma d'aya, fahimtar abinda take san tambaya yasa shi sake nuna mata gidansu da ido, tsoro, firgici da tashin hankali ne suka hanata juyawa ta kalli gidansu, hannunshi ya d'ora saman kafad'arta ya juyar da ita, idonta ne ya sauka akan gidansu dake ci da wata irin mahaukaciyar wuta, wata irin rawa k'afarta ta d'auka kafkafkaf jiri ya d'ebeta ya watsar gefe, kwakwalwarta ta tsaya cak, zuciyarta ta daina bugawa, komai nata ya tsaya cak ya daina aiki, yadda kasan mutum mutumin da aka dasa haka ta koma, tana ganin mutane nata ihuuuu ana tururuwar zuwa kai taimako amma ta kasa ko motsi, akan idanuwanta iyayenta, mijinta, yayyanta, 'yan uwanta da ahalinta gaba d'ayansu kaf suka k'one k'urmus tana jiyo salati da ihuuun azabar fitar ransu a cikin kunnenta amma babu yadda zatayi.
Duk iya k'ok'arin mutane sun kasa tunkarar gidan saboda tsananin k'arfin wutar daga nesa ma suna jiyo hucin wutar balle sunje kusa, ko mutum d'aya ba'a iya cetowa ba har ma'aikatan gidan sun k'one, jama'a sai tururuwa akeyi ana salati, bazata tab'a manta wannan bak'ar rana ba, ranar data rasa kowa nata a duniya, ta zama ita d'aya tilo tana reto a duniya, hoton wannan mummunar ranar bazai tab'a goguwa cikin kanta ba.
Babu abinda ke motsi a jikinta har idonta baya motsi yadai tsaya cak akan gidansu, murmushi yayi had'i da sunkuyawa ya kama hannunta yajata ba musu kamar rak'umi da akala tabi shi sukuku, duk inda ya cire k'afarshi nan zata d'ora tata kamar mutum mutumin da aka sassak'a da ice, babu abinda ta sani, ta manta komai da kowa, ita kanta ma ta manta wacece ita, babu abinda zata iya tunawa, yana rik'e da hannunta suka isa can nesa inda ya aje motarshi, ya bud'e mata gaban motar yace " shiga! amma ko gezau batayi ba, da kanshi ya saka ta cikin motar ya zaunar da ita, kana ya zagaya ya shiga yaja motar, bai tsaya ko'ina ba sai a harabar gidanshi, ya fito ya zagaya ya d'auke yayi cikin gidan da ita.
Saman bene ya hau da ita ya shiga d'aya daga cikin bedrooms ya shinfid'e ta saman gado, ya juya zuwa fridge ya bud'e ya d'auko kwalbar ruwan allura da saban sirinji yaja ruwan allurar ya kifa ta tare da mayar da gashin kanta gefe yayi mata allurar a k'eyarta, wata irin jijjiga jikinta ya d'auka lokaci d'aya hak'oranta suka rink'a kaf kaf kaf, bak'in cikin idanuwanta ya d'auke sai farin while idonta na far far far, ta dad'e haka kafin jikinta ya saki ta kwanta lakwas.
Kwashewa yayi da mahaukaciyar dariya tare da fad'in " nayi miki allurar mantau na shafe miki duk abinda ke cikin kwakwalwarki kinyi LOOSING MEMORY sai abinda na sanar dake zaki sani, ni kad'ai ne zab'inki kamar yadda na fad'a miki a baya, abinda naga dama dashi zaki yarda dole, nine dolenki sai yadda naga dama zanyi dake......
To Jama'a anan na kawo k'arshen littafin BAK'AR SHUKA... na 1 sai mun had'e a littafi na 2 dan jin yadda zata kaya.
Allah ya sani naso na rubuta muku littafin Bak'ar Shuka kyauta saboda Darussan dake cikin labarin amma rashin comment d'inku yayi matuk'ar bata min rai naji babu dadi, na tsara labari na zauna na rubuta muku amma comment ya garara haba dan Allah abun akwai ciwo akwai taba zuciya, idan nayi posting daga masu turo stickers sai masu cewa thanks, comment din mintuna biyar ne bazaku iya bata lolaci ku rubuta ba ni dana bata awanni ina rubuta muku ban gaji ba, abun yana yiwa marubuci ciwo wllh, musamman 'yan Wattpad da 'yan group d'in Bak'ar Shuka, dan haka na saukakawa junanmu ni nadaina jin haushi da rashin jin dadi, mai son littafin Bak'ar Shuka littafi na 2 ta biya #400 ta siya ta karanta ta yadda ko bakuyi comment ba bazan taba damuwa ba tunda nasan siya kukayi kudi kuka biya ni.
Ina labarin Raleeya?
Mecece kalar tata k'addarar?
Wanne bala'in ne ya fad'a mata ita kuma?
Menene asalin k'ullin dake tsakanin Ajlal da Deeyanah?
Metayi mishi dayake bibiyar rayuwarta?
Ya zata kaya a tsakanin su?
Wacce irin rayuwa Deeyanah zatayi a hannun Ajlal bayan yayi mata allurar mantau?
Da gaske zata manta duk abinda yayi mata da kowa da komai?
Waye Ajlal?
Meye assalinshi?
Wacece Hajiya Halima mahaifiyar Ajlal?
Menene Asalin K'ullin dake tsakanin Alhaji Bassam da Hajiya Halima?
Waye Nagoje?
Meye alak'arshi da Hajiya Halima da Ajlal da Deeyanah?
Ina sauran matan Alhaji Bassam biyu da 'ya'yanshi suke?
Idan Deeyanah ta dawo cikin hayyacinta wanne mataki zata d'auka akan Ajlal?
Ina Deen?
Ya mutu ko yana raye?
Yaya Rayuwar Deeyanah zata k'are?
Domin warware wannan k'ullin da kawo k'arshen sark'ak'iya biya #400 kacal
✍🏻
Hauwa A Usman
Jiddarh