WAZEER!

Dumb out

by @realsmasher

*CALIFORNIA..*


         Tunda suka zo ƙasar Hamood yai ciku²nsa ya samarwa Wazeer makaranta me kyau,wani private school ne a nan Hollywood Schoolhouse,dake basu da nisa daga gidansu zuwa North McCaddden Place,kullum idan zai tafi aiki zai fara biyawa ya ajiye Wazeer,sannan ya wuce ya tafi gurin aikinshi,tun safe idan Wazeer ya tafi school bai tasowa da wuri,a duk inda Hamood yake lokacin tasowarshi na yi zai dawo ya ɗaukeshi,idan ya mayar da shi gida zai siya masa abinci da komai da zai buƙata,daga nan zai koma Company'n magunguna da yake aiki,ba shi zai dawo gida ba sa can yammaci zai shigo gidan,haka zai zo ya tarar da Wazeer kamar maraya ya takure a guri ɗaya,idan ya tambayeshi mene ne sai dai ya girgiza masa kai yace "nothing" sai idan yaga damuwa sosai tare da shi,in ya matsa masa da tambaya sannan zai tambayeshi Mimi,da farko Hamood sai dai yai masa faɗa,amma da ya fahimci siye zuciyar ɗansa sai da dabara,a hankali ya fara masa magana cikin sanyi² yace "idan ka saki jikinka muka zauna a nan,then ka dage kayi karatu ka zama babba,i promise u zan kaika gurinta,ok?" A hankali Wazeer ya gyaɗa masa kai yace "ok!" Hamood ya bashi hannunsa yace "deal?" Wazeer yace "yes deal.." Ya ɗora hannunsa kan na Dad ɗinsa,Hamood yai murmushi yace "ok! Chapter close,daga yau babu tambayar Mimi,har ka gama school" a hankali yana kallon mahaifin nasa ya sake cewa "zan yi karatu Dad,idan na girma na zama Doctor,sai na dunga yiwa mutane allura" Dad yace "yessss! That's My boy,kayi karatu ka tara dukiya,ka samu suna da ɗaukaka shi ne burina,ina so ka zama babban mutum a ƙasata,ka zama wanda duniya za ta sani,duk inda ka shiga ya zama ana sunkuya maka,ana baka girma.." Wazeer yai shiru kamar yana tunani,a hankali kuma sai ya gyaɗa kanshi yace "ok Dad.." Wannan maganar ya taimaka wajen sauko da zuciyarsa,Hamood ya ji daɗi sosai da yaga ya fara sakewa,kullum baida aiki sai na jansa a jikinsa,yana zuwa school ɗinsa hankalinsa kwance,gidansu su kaɗai ne daga su sai cook ɗinsu me suna Joseph dake zuwa,shi zai gyara gidan yai musu girki,da idan yazo yana gama abunda zai yi yake tafiya,amma daga baya sai Hamood yai masa magana ya dunga zama da Wazeer kafin ya dawo saboda damuwar da yake shiga idan baya nan,dake ya samu ƙarin kuɗi sosai bai musa ba,a hankali tun Wazeer bai sakewa da shi har ganinsa yau da gobe tasa ya fara sakin jikinsa,Allah ya yi shi wani irin yaro ne da bai sakewa da mutane da wuri,har ta kai wani lokaci idan akwai abunda babu a gidan,Joseph zai ɗaukeshi su fita suna tafiya Wazeer na tambayarshi,haka kou idan yana kitchen Wazeer zaije gurinsa,ya tsaya yana ganin abunda yake,tun daga lokacin dukansu suka mayar da hankali kan abunda ya shafesu,Wazeer ya mayar da hankalinsa kan karatu sosai,duk sanda zai tadowa Hamood zancen Mimi,zai ce masa "ba yanzu zan kaika ba,ai mun yi deal sai ka zama babba,ka gama karatu" da haka ya dunga ɗauke masa hankali,a hankali lokaci ya fara tafiya daga kwanaki,satittika zuwa watanni,tunda suka tafi sam babu ruwan Hamood da zuwa gida sai dai waya,Daada tun tana masa faɗan yar da su da yayi har ta koma nasiha da lallaɓashi,amma sai dai yace mata zai zo,lokaci ne bai samu yanzu sosai,idan ƙarshen shekara yayi lokacin Eid zai zo,dake suna yin family meeting,dangi kowa zai zo daga inda yake,a haka akai first Eid-ul-fitr babu Hamood da ɗansa,da fari lokacin su Daada sun yi zaton yana gurin Hoor,sai da babbar sallah ya taho lokacin Abba yasa aje a taho da shi yaga ƴan uwansa,ɗan saƙo ya dawo ya sanar musu cewar ai Hamood yaje ya ɗauke ɗansa,wannan al'amari ya ɓatawa Abba rai,sai dai bai ƙasa a guiwa ba yaje ya sanar da Sarki Abduljalal da brothers ɗinsa,suka ce ya rabu da shi ya bashi lokaci,har Mai martaba ya bashi misali da kansa yace "nima haka nan nake fama da Mujaheed,da alama halinsu ne yazo ɗaya,ai dama ba'a ɗaya a dangi,kada kace za kayi fushi da shi,aita musu addu'ah in sha Allah komai zai yi sauƙi,komai yana da lokaci" dake duk abunda Mai martaba ya faɗawa ƴan uwanshi basa masa musu,haka Abba Waziri ya share batun,kou kiransa Hamood yayi zai ɗauka su gaisa,sai dai dai² da sau ɗaya bai taɓa nuna masa ya san Wazeer na tare da shi ba,tunda har ya iya ɓoye musu ya tafi da shi,suma ba abu ne me girma ba a wajensu su nuna basu sani ba,wani lokaci kuma yakan ce masa "Hooriyah ta tafi da Aliyu kou?" Hamood yace "Mmmm" Abba yace "tou amma shi kenan ta yanke masa zumunci da mu? Baza'a dunga kawoshi dangi ba sai ya tashi bai san kowa ba?" Hamood yace "zan yi mata magana" Abba cikin mamakin halin Hamood ya gyaɗa kanshi,wai shi Hamood zai ɓoyewa zancen,duk yanda zai bugi cikinsa bai taɓa fitowa ya sanar masa suna tare,kawai sai ya watsar da maganar,komai daɗewa ai wata rana zai dawo ya sameshi. Cikin wannan yanayin shekaru suka fara tafiya,lokacin Wazeer na da shekaru 12 wanda yai dai² da sun samu 4 yrs a ƙasar,idan kaga yanda yai girma a shekarunsa za kai zaton ya kai 15,dan a tsaye yanzu ya kusan kamo Hamood,yana ƙara girma kyaunsa da kammaninsa da Hoor suna sake bayyana,haka ma halinshi na miskilanci sai abunda ya ƙaru. Wata rana Hamood na aiki parlour,Wazeer ya samu Dad ɗin nasa,sanda ya zauna gefensa a hankali da huskey voice ɗinsa yace "Dad ina so a canja min school" Hamood dake aiki MacBook gabansa yace "shi wannan da kake yi me yayi?" Wazeer yai shiru,Hamood yace "i'm asking me ya samu wanda kake yi?" Wazeer yace "Dad ba na jin daɗinsa ne,na fi so ka mayar dani school da yake only boys,ban son mix da girls bana jin daɗinsa" Hamood bai tsaya ya fahimci damuwar da yake ciki ba yace "ok! Kaje sai na duba tukuna" daga nan Hamood bai sake tada zancen ba,in fact yama manta,ganin shiru² Dad bai ce masa komai ba shi kuma kawai ya yanke hukuncinsa ya daina zuwa,sai da aka kwana biyu aka kirashi daga school ɗinsu Wazeer,ake sanar masa bai zuwa school,kuma shi a matsayin mahaifinsa baije ya sanar yana da wani matsala ba da yake hanashi zuwa,afujajan Hamood ya sameshi,a kausashe ya kirashi "Wazeer!" Wazeer dake kwance bedroom yana kallon Korean film yai saurin pausing yace "na'am" Hamood yace "me yasa baka zuwa school?" Cikin damuwa Wazeer yace "Dad ni ba na son school ɗin,na ce ka canja min wani ka ce sai ka yi shawara,kuma baka ce komai ba,ba na jin daɗin makarantar kwata²" Hamood yace "ok! Idan na kaika wanda kake so shi kenan?" Wazeer ya gyaɗa masa kai yace "yes Dad" Hamood ya girgiza kanshi kawai ya wuce abunsa. Cikin satin ya karɓi transfer ɗin Wazeer daga Hollywood Schoolhouse zuwa International School Of Los Angeles dake Russell Ave,shima ɗin dai mix ne boys and girls,yawancin schools da suke only boys da Hamood ya duba,sai wanda ake koyar da addinin Kiristanci da yanda za ai bautar Yesu Almasihu,shi kuma duk taɓarɓarewarsa da rayuwa cikin Yahudawa,da zama ƙasar da ba tashi ba,bai gurɓata tarbiyyarshi ba,ya samu ingantacciyar rayuwa me tsafta,Abbansa bai basu ƙofar da za suyi wani abu da ya saɓawa addini ba,sai dai idan a bayan idonsa su aikata wani abu na badai² ba. Hankalinsa kwance yake tafiya school tunda Dad ɗinsa ya canja masa sabuwar makaranta,a shekarunsa yanzu babu abunda bai iya ba,har girki shi yake musu saboda zama da Chef Joseph da yayi,idan Hamood bai nan shi kaɗai yake rayuwarsa a cikin gidansu,daga school idan ya taso baida gurin zuwa sai gida,Dad ɗinsa babu abunda bai siya masa,babu abunda yake nema ya rasa,duk wani abu na jin daɗi kafin ma ya faɗa Hamood zai masa,sam bai son ganin only child ɗinsa cikin damuwa,yanzun nan zai fara tambayarshi mene ne? What do you want? A duniya maganar da Hamood bai son ji a bakinsa shi ne abunda ya shafi mahaifiyarsa Hoor,shima kuma tunda ya fara wayo ya fuskanci akwai abunda ya haɗa iyayen nasa ya bar yi masa maganarta,but deeply yana tare da tunaninta,da damuwar son ganin mahaifiyarsa yake kwana ya tashi,sai dai ta ina zai isa gareta? Shi ne abunda bai sani ba,he had a notebook and phone,amma bai kiran kowa bai da number kowa daga family'nsa,daga Dad ɗinsa sai few of his friends,sam bai harka da friends mata saboda Dad bai sake masa yai tarayya da su ba,duk wata hanya da zai bi ya lalata masa tunani akan alaƙa da mace ya yi nasara a gurin nan,rayuwa a ƙasar da ba naka ba kuma ba al'adunku ɗaya ba,sai dai Allah ya ceceka kawai,musamman ace ka buɗe ido ne ka ganka tsakiyar masu jajayen kunne,wanda addininku yasha bamban,sau da yawa friends suna gayyatarsa night party,irin wanda za'a haɗu club da ƴan mata,ayi shaye² ai rawa har a samu keɓewa kou lalata,sai dai yace musu yana da abun yi a gida,sau ɗaya bai taɓa zuwa ba,duk irin maganar da za'a faɗa masa idan an haɗu school,bai damuwa bare ya kula,ya san Dad yaji labarin ya yi wani abu zai ɓata masa rai,yana da gudun abunda zaisa ace ya yi laifi,masifar gudun abunda zaisa yai masa faɗa yake,a rayuwarsa shi wani irin murɗaɗɗen mutum ne da bambantan halaye,yana da fitinannun friends wanda basu ɗauki shaye² wani abu ba face wayewa,suna hulɗa da ƴan mata suyi abunda suka ga dama iyayensu baza suce dan me ba,amma shi duk wannan bai damunsa,baima saka kansa cikin harkarsu,bai barin suzo gidansu saboda Dad ɗinsa ya nuna masa bai son yai making friends,mata kuwa idan ya ganshi da su yasan ranar ransa ne kawai Dad bazai zare ba,ba zai taɓa manta wata rana tun farko²n zuwansu da yake yaro,ya fita gidan ya tsaya waje,wata yarinya a neighbor's ɗinsu tazo tana masa magana tana faɗa masa sunanta da gidansu,kamar daga sama Dad ya fito ya gansu,bai masa magana ba kawai zuwa yai ya kama hannunshi,yana kallon Suzan yace kada ya sake ganinta tare da shi,bai ce masa ƙala ba sai da suka shiga gida,kamar zai cinyeshi saboda faɗa,tun daga ranan karatunshi ya koma akan kushe mata,duk hanyar da yasan zai cire masa tunanin ganin duk wani kyakkyawan hali akan mace,sai da yabi yai blackmail ɗin mace a zuciya da tunaninsa,shi ne abokinshi shi ne komai nasa a California,ɓangaren karatu ma shi yake masa a kwanakin weekends,duk abu mara kyau na lalata tarbiyya cikin hikima yake nuna masa,za ka sha mamaki idan kaga yanda Hamood ke ɗora ɗansa a hanya da bin diddigin duk abunda yake aikatawa,su wane irin friends yake tare da su,teachers ɗinsa a school ya ya suke? A rayuwarsa bai da buri bayan na son yaga ɗanshi ya fita daban,kuma shi kansa Wazeer yanda yaga Dad babu ruwansa da wasu mata,babu kowa cikin rayuwarsu daga su sai su,wannan ya bashi damar bin duk wasu footsteps na mahaifinsa,takatsan² yake da komai da kowa,idan ba dole ba babu abunda yake haɗashi magana da mata,a school seat ɗinsa kullum na front shi kaɗai,idan kana neman best student sunansa was the first ever da za kaji,shi yasa Hamood yake bala'in alfahari da shi,bai jin ƙyashin yai masa duk abunda yace yana so. A haka Wazeer ya kammala secondary School at age of 16,babu ɓata lokaci Hamood ya nemar masa gurbin karatu a Stanford University,nan ma dai Wazeer ya so cogewa,dan cewa yayi idan akwai makarantar da yake ba mix ba Dad ya nemar masa,Hamood yace "mene ne matsalarka ne?" Wazeer yace "nothing Dad but.." Hamood yace "tou babu.. Idan za kayi karatu kayi,mata ne ba dole sai ka shiga harkarsu ba,kayi abunda ya kaika ka gama,period.." Haka nan ya amsa,ya duƙufa abunda ke gabansa,ya fara karatunshi cikin tarin nasaraori inda yake ƙarantar abunda ya shafi marketing,bisa umarni da ra'ayin Dad ɗinsa,har kawo wannan lokacin su kaɗai suke ta rayuwa,tsakanin Hamood da gida da kowa sai dai a waya..



*YEAR'S LATER..*



     Yau ake convocation ceremony na ɗalibai a Stanford University of California,babban hall ɗin makarantar ya cika da ƴan uwa da iyaye daga kowane angle na sassan duniya,sai students da suke zaune cikin suite black color sama sun ɗora gowns da huluna,jawabi aketa yi kamar baza'a daina ba,kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin Profs,kafin akazo sallamar ɗalibai,best student of the whole school ake ta koɗawa ana yabo,kafin aka shiga zayyano adadin certificates of degree da yake da,his first ya karanci abunda ya shafi harkar kasuwanci (marketing),secondly ya karanta Medicine and third ya karanta abunda ya shafi nazarin halayyar ɗan adam,cikin wani maɗaukakin murya baturen dake jawabin yace "ba kowa bane wannan dalibi face *ALIYU MUHAMMAD ALIYU.."* Hamood da ya saje cikin turawa ya shiga mamaki,a iya saninsa da ɗansa 2 degrees ya sani,bai san yaushe ya juya yai Medicine ba,amma kuma kou babu komai,yabon da yaji ana yiwa ɗan nasa yasa shi alfahari da jin kansa a gurin,anyi tsit ana ta sauraren ya fito,mutane sai kallon gurin ake aga wane ɗan baiwa ne zai fito,sanda aka sake kiransa,students suka hau ihu ana kiran sunan shi *"WAZEER! WAZEER!! WAZEER!!!* Can daga cikin dubban ɗalibai,wani handsome young man,first class dake tattare da wani irin carisma ya miƙe,idanunsa sakaye cikin farin eye glasses da ya ƙarawa fuskarshi ma'abociyar kwarjini kyau,dogo ne sosai fari kyakkyawan gaske,duk da a rufe jikinshi yake da gown dake saman suite ɗinsa,amma hakan bai hana na gano asalin ƙirarsa ba,irin zaratan mazan nan ne da idan suka tsaya gabanka za kaji shakkarsu kou da basu ce maka komai ba,kallo ɗaya za kayi masa kasa shi cikin sahun sadaukai,masu bada tsoro ga abokin hamayya,doguwar fuskarsa cike da wasu irin sirruka masu wuyar fasaltawa,musamman idan ka samu damar kallon cikin ƙwayoyin idanunsa masu launin ruwan ƙasa da suke lumshe kamar yana jin bacci,ga wanda bai san shi ba zai yi tunanin zallar iyayi ne,amma halittar Allah babu yanda ba ta kasancewa,yayin da kamilalliyar fuskarsa ma'abociyar kwarjini ta kasance a cikin wani irin expensive face mask da ba kowa ba sai wane da ɗan wane,ka kalleshi ƙarya kake kace ka hango wani aibu tattare da shi,fuskarsa ɗaure babu alamun fara'a,cikin izza irin na mutanen da suka haɗa jini da sarauta yake tafiya,takunshi kaɗai ya fita daban,students ƴan uwanshi sai kurantashi da zugasa suke,har ya isa ya karɓi shahadarsa sannan ya wuce zai tafi aka kirashi tare da bashi damar cewa wani abu akan tarin nasarorin da ya cimma,a hankali ya tsaya yana kallon kowa,kamar haɗin baki students suka fara ihu ana "remove the mask.. We want to see u once.. Remove! Remove!! Remove!!!" Ihun da ya cika gurin yasa shi juyawa ya kalli inda Dad ɗinsa yake,Hamood da ya sake manyanta saboda shekaru 20 ba nan bane,a hankali ya ɗan lumshe masa ido tare da gyaɗa masa kai,hannunshi dake cike da gargasa har kusa da dogayen fingers ɗinsa ya kai a hankali zuwa bayan kunnensa ya ciro mask ɗin,nan kyaunsa ya bayyana,ko wata macen albarka bare akai kan gender ɗinsa,kafin kace me flashes sun fara tseren capturing pics ɗinsa,tunda yake school even if ace da mistake babu wanda ya taɓa ganinsa sai yau,kamar mara gaskiya kullum cikin ɓoye fuska yake,zo kaji ihun murna da tafi a gurin abokanshi,a gurguje ya shiga yin jawabin da aka umarceshi,banda kamilalliyar huskey voice ɗinsa babu abunda yake ratsa gurin da kunnuwan mutane,idan yai magana ɗaya sai ya tsaya kafin yai na biyu,kamar wanda ke da matsalar magana kou yana research ɗin abunda zai faɗa,yana gamawa ya wuce ya sauka aka hau yi masa tafi,Dad banda murmushi babu abunda yake,saboda alfahari da yake da ɗansa,a haka aka kammala taron aka gama,ana fara fita mutane suka fara nemansa suyi hotunan tarihi,amma kamar aljani sama kou ƙasa aka rasa shi ya ɓace ɓat a gurin,Dad daya taho gida daga baya,ya yi zaton Wazeer na can school suna hotuna da bankwana,yana zuwa gida yai parking ya sauko motar,cikin tarin farin ciki ya shigo gidan,cike da mamakin ganinsa zaune a parlour yana shan coffee yasa ya taho yana buɗe idanunsa,har yai wanka ya canja kaya,daga shi sai short trouser da armless riga baƙaƙe da suka amshi jikinsa suka fito da surarshi,yanda yai girman nan za kayi zaton ya kai irin 30+ ɗin nan a shekaru,da mamaki Dad da ya shigo yana kallonsa ya zauna yana cewa "thought u were in school taking pictures with ur friends" ɗan motsa baki yayi kamar zai magana kuma sai yai shiru yaƙi cewa komai,Dad ya girgiza kanshi yana dafa shoulder ɗinsa yace "are u alright Son?" A hankali ya furta "i want to be back home now.. I want to see my family Dad" murmushi Dad ɗin nasa yayi,a hankali yace "it's ok.. Get set za muje soon in sha Allah,za kaga kowa da kake so,ok?" A hankali ya gyaɗa kanshi sai dai bai ce komai ba,Dad yai murmushi yana kallonsa da alfahari yace "u made me proud Son,u really made it.." Bai ce komai ba ya ci gaba da sipping coffee,Dad ya tashi ya wuce bedroom ɗinsa. Cikin satin Hamood ya shiga shiri,kamar me shafar aljanu shima haka nan yaji yana son komawa,ya ɗebi shekaru rabonsa da gida,ba don komai ba sai saboda ya inganta rayuwar ɗansa,a yau wannan burin ya cika dan haka zai koma gida cikin family'nsa da alfahari. Tunda Dad yace masa ya fara shiri,bai ɗauka haka da gaggawa za su wuce Nigeria ba,sai dai ya ga Dad ɗin shi yana ta shirye²,ranar da jirginsu zai taso da safe Dad ya sameshi zaune yana buga TV game,tsaiwa bayan kujeran da yake kai Dad yayi yana kallonsa yace "ka gama shiryawa ne kou da saura? I think few hours yai mana saura a nan" saurin ɗago kanshi yayi yana buɗa ido yace "what?" Dad ya gyaɗa masa kai yace "yes!" Ɗauke kai yayi kafin yace "but Dad u never told me yau za mu tafi" Dad yace "and yanzu ga shi na faɗa maka,da me kayi tunani? Baza mu tafi ba?" A hankali ya gyaɗa kanshi yana ci gaba da game abunshi yace "Mmmm" Dad yace "ok! Get up kaje ka shirya maza²" a hankali ya ɗago kamar zai magana sai kuma ya fasa ya ajiye handle ɗin,cikin wani takun isa ya tashi ya wuce bedroom ɗinsa,kayanshi da ya san zai buƙata ya shiga zubawa a luggage,smart watches ɗinsa da turaruka da komai nasa,buɗe ƙofa akayi kou da ace bai juya ba ya san waye,Dad dake tsaye yana kallonsa yace "i think ka ɗebi duk abunda kake buƙata,coz baza mu dawo ba" saurin juyawa yayi yana buɗa ido sosai yace "whatttt?" Dad yace "yes! This is my plan.. Mun tafi kenan baza mu dawo ba,sai in da wani abu kuma da zai iya kawo mu" gyaɗa kanshi kawai Wazeer yayi,kafin ya juya ya ci gaba da abunda yake,duk kayanshi yayi parking cikin ɗan lokaci,all abubuwan da yake so bai bari ba,yana gamawa ya shiga bathroom yai wanka,a gurguje ya gama komai ya shirya cikin wani cotton lightweight sport coat jacket black,rigar ciki da skinny mens jeans blacks,gashin kansa a kwance luf² da gemunshi mara yawa da cika,idan yai shiru dake ɗabi'arsa ne babu yanda za'ayi kayi tsammanin jin kalmar Hausa ɗaya a bakinsa,dan sam bai kama da yaran hausawa ba,daren ranar basu yarda sun sake kwana California ba suka biyo jirgi,yana gefen window yana kallon waje zuciyarshi cike da kewar mahaifiyarsa,tunani iri² suna flashing a ƙwaƙwalwarsa,me yasa duk tsayin lokacin Mimi bata taɓa nemansa kou Dad tace ina yake ba? Me ya haɗa ta da Dad wanda yaja tai fushi har da shi? Kou da wasa bai taɓa jin Dad ya ambaci sunanta ba,me yasa? Mutane da yawa bacci suke amma shi idonshi biyu,tunani ne cunkushe cikin ranshi,kamar lokacin farkon tafiyarsu wannan karon ma awanni suka shafe suna keta giragizai kafin suka iso Nigeria da dare guraren 8pm,jirginsu na sauka Dad ya tashi tare da zaro luggages ɗinsu ya ajiye,Wazeer dai kallon waje kawai yake,a hankali yana sauke ajiyar zuciya me nauyi,ya tashi ya ɗauki lugagge ɗinsa tare da biyo bayan Dad suka biyo sahun masu fitowa,sanyayyar iskar daya bugeshi irin na lokacin damuna me cike da ni'imatacciyar yanayi,yasa a hankali ya lumshe idanunsa da suke cikin eye glasses ɗinsa,haka suka shiga ratsowa tare da mutanen da suka sauka ƙasar,kasancewar Dad bai kira kowa ba saboda dare,suna fitowa ya tare musu cab ya sanar masa inda zai kaisu,kayansu duka suka sa booth kafin suka shiga back seat,me taxi yaja suka kama hanyar bari airport,tafiya suke suna bin yanke har sanda suka iso gidan sarki ta can baya guraren babban masallacin juma'a,Wazeer dai kallon ƙasarsa ta haihuwa kuma ƙasar iyayensa kawai yake,duk ya manta komai ganin kansa yake as baƙo,har sanda suka iso dai² gidan Wazirin Kano,asalin gidansu kuma mahaifar mahaifinsa,gidan kakanninsa da ya tashi yaga suna rayuwa,buɗe mota Dad yayi suka sauka,Dad ya sallami me taxi daya sauke musu kayansu,Wazeer ya juya yana kallon babban ƙofar shiga zauren gidan da yake akwai haske,mutanen da ya hango ciki ya dunga bi da kallo,shekarun baya da abubuwan da bai manta ba suka shiga flashing masa a ƙwaƙwalwa da idanu,farin dattijon da ya hango akan kujera wanda kamanninsa basu ɓace ba ya tsare da mayun idanunsa,kakanshi mahaifin mahaifinsa da bazai manta da shi bane zaune sai dai ya manyanta sosai,a hankali yaja luggages ɗinsa ya nufi zauren ba tare da ya jira Dad ba,bakin ƙofa inda takalma da yawa suke zube ya tsaya,kwaɓe takalminsa yayi a hankali yai sallama,Abba Waziri dake sauraren wani dake masa magana ya ɗaga kanshi yana amsawa "amiin wa'alaikumus salaam warahmatullah wabarkatuh" kamanninsa babu abunda ya canja a idanunsa,sai dai girman da yayi ya bashi mamaki sosai²,kallonshi yake kamar yanda shima yake kallonsa,kafin a hankali ya mayar da idonsa kan Dad da ya ƙaraso,kou tantama babu wanda yake tunanin shi ɗin ne,jikanshi da yake tsananin so da kewa,takawa cikin zauren Wazeer yayi yana ajiye luggages ɗinsa a gefe,ya tafi gaban Abba Waziri ya zauna,idanunsa suna fidda wani irin sirrin kewar family da yayi na tsayin shekaru 20 ya furta "barka da dare Abba" Abba Waziri ya kai hannunshi a hankali ya dafa kan Wazeer,cike da so da kewa ya furta "takwara kai ne kai girma haka?" Ɗan murmushi Wazeer yayi,Abba Waziri yace "ya hanya kun iso lafiya?" Wazeer yace "lafiya lau" hausarshi fa abun kallo da saurare ne,saboda yanda yake magana ɗaya bayan ɗaya cike da sarauta,Dad ne yazo ya zauna kusa da Wazeer,kansa a ƙasa saboda ya san shi me laifi ne yace "barka da dare Abba" Abba Waziri ya kalleshi yana haɗiye fushinsa yace "kuna lafiya?" Dad yace "lafiya lau alhmdllh.. Mun sameku lafiya?" Abba yace "alhmdllh!" Sauran mutanen gurin suka gaisa dasu,kafin Abba ya kallesu yace "ku shiga cikin gida zan shigo yanzun nan na sameku" respectfully uba da ɗan suka amsa suka tashi zuwa ciki,fadawa suka biyosu da manyan luggages ɗinsu,suna isa ɓangaren Daada suka shiga da sallama,Daada data tsufa dan ma akwai jin daɗi ta amsa sallamar tana kallonsu,fuskarta cike da tsantsan farin ciki ta furta "Mamman.. Yanzu kuke tafe?" Sai kuma ta kafe Wazeer da kallo hawaye suna ciccikowa idanunta ta furta "Zainul-aabideen! Me gidana Waziri.. Kai ne kai girma haka? Kai ne ka zama saurayi?" Ɓata fuska yayi yaƙi kallonta,shi fa a faɗi komai amma kada ace masa ya girma,hannu bibbiyu ta kai fuskarsa ta riƙo tana faɗin "yaka nan,zo ka zauna kusa da ni" zaunawa yayi kusa da ita sosai,Daada ta kai hannunta kanshi tana shafa kwantacciyar gashin kanshi da akaiwa wani irin haircut me bala'in kyau,tace "o'o! Ni Sa'adatu ashe ina da rabon sake ganinka ɗan nan,babanka ya ɗaukeka yai tafiyarshi,tsayin shekaru ashirin kenan bai sake barin wani ya ganka ba sai yau.. Wannan da a wani guri muka haɗu da kai ai bazan shaida kai ne jikana ba" Wazeer yana kallon yanda take hawaye,ya ɗan fiddo idanunsa yace "tou kukan me kike kuma?" Daada tace "ba dole nai kuka ba ɗan nan,rabonmu da kai tun kana ɗan yaro baka fi haka ba" ta kwatanta tsayinsa da hannunta,tace "kawai mutumin nan Mamman ya ɗauke ka yai tafiyarshi babu sanarwa,duk tsayin shekarun nan bai taɓa kawoka ka ganmu mu ganka ba.. Kou hakkin mahaifiyarka da ya rabata da kai aka barshi,ya isheshi bare an ƙara masa da namu.. Ai kai dai Mamman da kai da Mujaheed (Jay ɗin littafin Kallo ya koma sama) halinku sai ku,ni ban san wane irin abu ke faruwa da ku ba,a ina kuka gado halin nunƙufurci da ƙeta Allah masani" kallon Daada Dad yayi kafin yace "Jay ya dawo ƙasar ne" Daada tace "uhumn! Ya dawo ba'a jima ba,haka yazo mana da gagarumin abun mamaki,ai ku dai wannan yara halinku sai ku,babu yarda a halin ɗan yau" Dad dai kallonta kawai yake,Daada tace "duk tsayin lokacin nan wai ashe zuwa yayi yai aurensa babu sanin kowa a dangi,ya je ya auri wata baindiya har sun haihu da ita yara biyu.. Kai wannan al'amari ya jima yana bani mamaki" shigowar Abba ne ya dakatar da maganar da Daada take,suka amsa sallamar da yayi,Abba na ta kallon Hamood har ya zauna,sake gaisawa suka yi kamar babu komai,Abba bai cewa Hamood komai ba,sukaita hira da Wazeer yana tambayarshi abubuwa da yawa game da rayuwarshi. Washe gari da safe around 11am suna zaune parlon Daada har Abba da bai fita ba,ya kalli Wazeer yace "Wazeer tashi maza kaje waje,akwai maganar da nake so nayi da mahaifinka,akwai driver na nan yana jiranka,ka shiga mota ku tafi" respectfully Wazeer ya amsa,Dad ɗinsa na kallon Abba yace "Abba ina zaije daga zuwanmu? Ina fact bai san ko'ina ba" Abba Waziri ya kalli Wazeer yace "tashi maza ka tafi,Allah ya tsare" Dad zai sake magana Abba yai masa tsawa yace "ka rufe min bakinka Muhammad,kada kasa nayi abunda ba dai² ba a gaban ɗanka girmana zube a idonshi" saurin wucewa Wazeer yayi ya fita,yanda Abba yace masa yayi²,yana fitowa ɗaya daga cikin drivers ɗin Abba dake jiransa ya buɗe masa mota ya shiga ya rufe,ya koma ya buɗe mazauninsa ya tada motar suka hau titi,tafiya kawai suke Wazeer dai yai shiru sai jujjuya tsadadden wayar hannunshi yake kawai yana tunanin inda Abba yasa a kaishi,har suka shiga wani unguwa da manyan gidaje ne kawai ciki,dai² wani babban gida driver yai horn,Wazeer ya zubawa gidan idanunsa yana kallo,get keeper yazo ya buɗe musu suka shiga ciki yana ɗaga musu hannu da yi musu barka da zuwa,Malam Uba yai parking ƙasan tent sannan ya sauko ya buɗe masa,a hankali ya sauko daga cikin motar ya tsaya yana kallon babban compound ɗin gidan,Malam Uba ya matso yana ɗan rusunar da kanshi yace "ranka shi daɗe shiga ciki za kayi" kallonsa Wazeer yayi,bai ce masa komai ba ya fara tafiyar nan nashi kamar yana counting steps ɗinsa har ya kai entrance,kamar yana tunani da son fahimtar wani abu,ya daure ya kai hannunshi saman ƙofar yai knocking,daga ciki me aiki tace "ana zuwa" bai kai minti 2 a gurin ba aka buɗe,sannu da zuwa tai masa,fuska ɗaure yaƙi kallonata,saurin bashi hanya tayi,ba don ta san wane ne shi ba sai saboda kwarjinin da yai mata,wucewa yayi kai tsaye bai ce komai ba kou sanar mata gurin wanda yazo,shi kansa bai san ina Abba yace a kawoshi ba,kuma driver da ya kawoshi ma bai faɗa masa ba,ya ƙarasa saman tsadaddun kujerun parlon ya zauna yana kallon komai na gurin,ya matsu yasan ina ne nan,da dalilin da yasa Abba yace a kawoshi,me aiki da jikinta ke tsuma tai saurin dawowa tana faɗin "bari na sanar da Hjy ta yi baƙo.." Idan ya kalleta tou ta sa rai zai ce wani abu,ganin kamar ba ya magana yasa ta wuce stairs ta dunga haurawa da gudu²,ba'ayi minti 3 ba ta sauko tana faɗin "ga ta nan zuwa" wannan karon wayarshi yake operating kanshi a ƙasa,tana gama faɗa masa saƙon ta wuce tana waiwayensa da mamakin rashin maganarsa,a fili tace "kou dai kurma ne?" Sai kuma ta shige kitchen tana faɗin "wataƙila.." Haka kawai tausayinsa ya rufeta tace "kuma kyakkyawa da shi,ashe ba ya magana.."  





    ```#Woaw! Maraba da sauka Wazeer,ga dai mutumin an zama cikakken saurayi,me za ku iya cewa akansa? Masu neman WAZEER kuyi join group saboda samun update akan lokaci..``` ***





*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****





#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.