DA'IMAN ABADAN

3&4

by @jameelarhsadiq6388

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*

_Hot love and fate sorry_


Na

_YAR'MUTAN KANKIA_


_MANAZARTA WRITERS_


*BOOK ONE*


*Wannan page din naki ne Aunty Billyn Abdul son so fissabillahi..Ina godiya da yanda kike karfafaman gwiwa🥰*


*PAGE 03&04*


*Masu bukatar a tallah ta masu hajjarsu cikin rahusa su man magana ****


***



Tunda su Zulaihat suka tashi sukayi asuba,basu sake komawa bacci ba,gyaran gida suka hau ayi bayan sun gama gyara tsakar gida daya ta wuce gyaran kitchen dayar kuma ta shiga gyarn daki,sun gyara ko ina yayi kyau sun kunne kayan kamshi,sannan su shiga kitchen dan yin breakfast sunayi suna duba lokaci. bama kamar Zulaihat da bata fatan ko tara tayi masu a cikin gida,dan tana gudun cin mutunci da wulancin Dr Najeeb,da suka kusa idar da aikin ta tura Zubaida wanka ita ta ida.dakatar da ita tayi tana cewa.


"Dan Allah kiyi maintaining din time,kinga takwas yayi karda ki dade a bayin nan." dariya kawai tayi ta ida shigewa room,tana mamakin yanda Zulaihat take tsoron Dr,duk yanda take tsoranshi ta fita.


Bayan ta gama girkin ta ƙara gyara kitchen din ta kwaso abincin ta jerasu saman carpet ta wuce danyin wanka,tana shigowa room Zubaida na fitowa. bata tsaya surutu ba ta shiga,ita kuma Zubaida ta shirya tana fiddo masu da kaya,kafin tasa kayan har Zulaihat ta fito daga wanka,sakin baki kawai tayi tana kallon Zulaihat da ta haɗa fuska tana tsane jikinta,dan kawai karda tayi mata maganar fitowarta da wuri,murmushi Zubaida tayi ta ida shiryawa ta dauki bag dinta,ta fito parlor ta zuba masu abinci tana ida zama Zulaihat na fitowa da sauri...Zubaida ta kalli yar'uwarta fuskarta dauke da murmushi tace.


"Masha Allah sai kace wanda zata gasar kyau." itama murmushin tayi ta zauna tana cewa. "Koba gasar kyau ba." darayi sukayi a tare sannan sukayi bissmillah suka ci abinci,wanke hannu sukayi suna leƙawa room din Umma zaune suka taddata tana karatu gaidata sukayi sannan suka fito lokacin 9:04,babu abunda suke sai sauri minti ukku ya fiddosu bakin titi,nan suka fara neman naped din da zata kaisu school...tun suna duba lokaci har suka daina,duk naped din da suka tsada basu samu ,wasu akwai mutane a ciki,wasu kuma ba hanyar sukayi ba.



Tun daga nesa ya hangosu,baisan lokacin da ya duba agogo ba,ganin nine thirty har ta wuce,gabansu ya tsaye yana zuge glass yace.


"Zubaida Ibrahim ,idan ba damuwa ku taho mu wuce." kallonshi sukayi a tare sannan suka kalli juna murmushi sukayi suka shiga dan basu da zabin da ya wuce haka,sun san mutumin by face course mate dinsu ne,amman basu san sunanshi ba saboda ba sabgar kowa suke shiga ba balle har susan sunayen kowa.



*Jigawa🥀*



Tunda ya zaune yake juya abincin gabanshi,yana mamakin yanda Ammie har yau take maida shi karamin yaro,ajiye spoon din hannunshi yayi yana mai tashi tsaye zai bar dinning area din,kallon shi Dad yayi yana cewa.


"Son ba dai har ka koshi ba."? Maida kallonshi wajen Dad yayi yana É—aga mashi kai,murmushi Dad yayi yana cewa ."Maza zaune kaci abinci A-kaÉ—ir baka gudun ulcer ta kamaka idan baka cin abinci."


Marairaice fuska yayi yana kallon Dad turo baki gaba yayi yana cewa. "Wallahi Dad na koshi ban dade da shan tea ba,kuma zan hada kayana kaga gobe ne tafiyar nan."....maida kallonshi yayi wajen Ammie yana cewa. "Myluv pls gayama Dad banjin yunwa."harararshi tayi tana goge bakinta da tissue tace. "Luv kai dai ka sani ,ni har na gaji dayi maka maganar abinci maybe sai mundawo yi mashi dura ko Habibi." dariya kawai Dad yayi yana rungumo Ammie jikinshi yace. "Kwairai kuwa Noor kin kawo shawara." ya ida maganar yana lakutar mata hanci,hayewa yayi sama dan shirya kayanshi tunda yaga tafiyar da gaske yinta za'ayi,yana gamawa ya wuce gardeen dan shan'iska .


Tsuntsayen dake shawage a wajen kawai yake kallo yana murmushi,duniya yana tsintar kanshi cikin farinciki marar musaltuwa idan yazo gaya yanda tsuntsaye suke rayuwarsu gwanin sha'awa,tsaki yayi da ya tuna gobe kamar haka baya kasar baki dayanta yana wata kasa,kasar da ko sunanta baisan a fadi.


''Ya Allah."


Ya furta ahankali yana gingina kanshi jikin kujera ya lumshe fararen idanuwanshi yana lazimi a cikin zuciyarshi,dan aikin kenan ABU-KAÆŠIR baida aboki ko daya,shi daya yake rayuwarshi sai kuma iyayenshi da suka dauki son duniya suka daura mashi,basu san suga ko kuda ya tabashi saboda shi daya tillo Allah ya basu,amman duk gatan da suke nuna mashi hakan baisa sunyi sake wajen bashi tarbiya ba.



*KANO🥀*



Go slow ya bata masu lokaci basu shiga BUK ba sai karfe 10:09 ,tuni Zulaihat idanunta suka kawo kwalla da ta duba time ,kamo hannunta Zubaida tayi tana cewa. "In shaa Allah bai kai da shiga ba." tare suka ce "Allah yasa." jikinsu duk yayi sanyi ganin makarar da sukayi waigawar da Zubaida zatayi taga Dr Najeeb ya wuce su da kadan tafiya yake cikin natsuwa kamar baisan taka kasa saboda miskillnci da ya taru yayi mashi katutu a rayuwa.


Rufe baki Zubaida tayi da tafin hannunta tana fiddo ido waje tsabar tsoro bakinta na karma tace. "Sis ga Dr Najeeb can fa zai shiga hall." a tare suka waiga ita da Ahmad aikuwa suka sa sauri su samu su rigashi shiga,sosai suke sauri cikin ikon Allah Ahmad ya fara shigewa sai Zubaida,baiwar Allah Zulaihat daman ita ba gwana bace a wajen saurin .ganin abokan tafiyarta har sun samu shiga sun barta idan kuma tayi wasa tabbas sai ya rigata shiga,batasan lokacin da ta fashe da kuka ba.tana ballawa da gudun bala'i yazo daidai zai shiga kenan, Zulaihat tayi kukan kura ta ingijeshi ta shige hall din.kowa na wajen sai da lamarin ya firgitashi ,Zubaida kuwa zaro ido tayi waje babu abunda jikinta yake sai karma da kuma tausayin yar'uwarta da ya kamata.


Tunda ta samu ta shigo ta samu waje kasa ta zauna tana maida numfashi gami da share hawayenta ,da sauri sauri take sauke numfashinta so take ta samu taga ta daidaita natsuwarta....ida shigowa yayi fuskarshi tamau babu yabo babu fallasa kamar ko yaushe,ko ta kan Zulaihat baiyi ba dan ko inda take bai kalla ba ya cigaba da abunda ya kawoshi ,kowa yayi concentration akan abunda ya kawoshi ,fuskar kowa cikin annashuwa take saboda dadin da lecture din ta dauko,kuma kowa ya ganne sosai anyi mashi question ya bada answer ,shima yayi question an bada answer haÉ—a system dinshi da komae nashi yayi sannan ya dauko kanshi yace.


"Captain."


Da sauri Captain ya tashi yana cewa. "Yes Sir." bai sake cewa komai ba sai da ya kusa fita sannan ya tsaya yace. "Ka gayama wanda ya shigo last kace komai yake karda ya yarda na rigashi zuwa office." yana gama fadin haka ya ficewarshi take hawaye suka fara zarya a saman fuskar Zulaihat ,dafata Zubaida tayi tana share mata hawaye tace. "Kice Innalillahi wa'innaalaihirajun,kita maimaita ta in shaa Allah ba abunda zai maki Sis tashi ki tafi kinji yace karda ya rigaki isa office din."ɗaga kai kawai tayi tana mai share hawayen fuskarta karƙafa mata gwiwa yan class din sukayi ,fitowa tayi tana tafiya a hankali cikin natsuwa da ta zamai mata jiki,amman ita harga zuciyarta gani take sauri take.



*Jigawa🥀*



Waigawa yayi yana kallon Dr Nmandi international airpot ,sauke ajiyar zuciya yayi yana mai sauke idonshi kan flight din da zasu hau yayi,ana gama binciken da za'ayi masu suka shiga sai da yayi addu'a sannan ya shiga ciki. jirginsu ya tashi daga nigeria zuwa Ukraine.



*KANO🥀*


Tafiya take tana wasa da ring din dake a hannuta,hawayene kawai suke shatata bisa kyawkyawar fuskar,jefa ƙafafunta kawai take dan kuwa ko kadan Zulaihat bata kallon gabanta,kuma sannan ko kadan batasan inda take cilla ƙafufunba ,tsabar tsoro da firgici kallo daya zakayi mata kaga tsintsin tsoro da tashin hankali ƙarara a tare da ita.


Ikon Allah ne kawai yakai Zulaihat bakin office din Dr Najeeb,É—aga rinaunin idanunta tayi tana kallon office din,share hawayen da suke tsiyayo mata tayi da gefen hannunta ,tana motsa dan karamin bakinta ta karanta.


_DR NAJEEB H ABDULLAH_


Take tausayin kanta ya kamata,batasan wani irin wulakanci da cin fuska zaiyi mata ba,tunda take bata taba shiga case din malami ba,a BUK amman yau kaddarata ta haÉ—ata da Dr Najeeb,mutumin da kowa ya sheda a cikin Buk bashi da ragi sannan kuma bai raga ma kowa.


Tsugunnawa tayi baki office din ta daura hannu bisa kai ta rushe da wani kuka marar ƙara cikin tausayin kanta tace. "Allah ka taimakeni,Innalillahi ni Zulaihat yau na gama shiga ukunna" dirsam ta zauna ta hada kanta da giwwar kafarta ta cigaba da kukanta.


*KYIV UKRAINE🥀*


KYIV INTERNATIONAL AIRPORT UKRAINE jirgin su A-KaÉ—ir yayi leading a babban birinin Ukraine,bude dadaren idanunshi yayi.yana mai tura hannunshi cikin gyaren-gyaren sumarshi,after 30min,aka bude ma pessenger suka fara fitowa.


So gently haka yake saukowa daga saman matakalar jirgin sai kace wanda yake tausayin kasa ko kuma bai san taka kasar ma haka ya sauko daga saman matakalar jirgin,furzar da iskan bakinshi yayi yana mai ƙarema airpot din kallo.


"Ba laifi. "


Abunda yace kenan yana yin hunging din Ammie shi,shafa kanshi Dad yayi yana cewa. "Nidai kullum sai an nuna man banbanci ko KaÉ—ir."?sakin Ammie yayi yana kama kunnenshi biyu gami da langwabe kanshi gefe ya turo baki yace. "Na isa Dad." yana ida maganar ya rungumeshi,shima rungume shi yayi yana cewa. "Love uh son." a hankali yace."love more my parents." Dariya sukayi sannan suka shiga mota drive ya tafi dasu masaukinsu.



*NIGERIA🥀*


_kano_


Ya dade tsaye yana kallonta,dan karamin tsaki yayi yana kauda kanshi gefe harararta yayi sai kace tana kallonshi, tsawa ya buga mata yana cewa.


"Hi,what are you doing here."firgigi ta tashi tana fadawa jikinshi tana mai fashewa da wani irin kuka,da karfi Dr Najeeb ya rintse idonshi,dan wani irin yarrrrr haka yaji duka jikinshi ya dauka ga wani irin yanayi da yaji ya saukar mashi wanda tunda yake a duniya bai taba tsintar kanshi a cikin irin yanayin ba sai yau, yau dinma yanzun.


Ita ko Zulaihat ta makalkale a jikinshi ,sai kara tura kanta take a tsakankanin wuyanshi da kafadarshi tana tura mashi na shanunta da suke tsaye tsam,wata irin ajiyar zuciya ya sauke yana mai nemo jarumtarshi ya cirota daga jikinshi yana kuma buga wata uwar tsawar da tafi ta farko yace.


"Are you mad." wata sabuwar ƙara ta sake saki tana kara yin hunging dinshi,idanunta a runtse suke tana girgiza kai,taitaro karfinshi yayi ya fiddota daga jikinshi ya ɗaga hannu ya daura mata wani wawan mari,ya kara daura mata wani wata uwar ƙara ta saki tana...


*Ku sani comment dinku shi zai bani kwarin gwiwar cigaba da sakin book din nan free kamar yanda nace idan kuma baku comment to zan maidashu paid ne akwai masayanshi over dan haka comment kawai nike bukata ya wadatar dani ahto maganar gaskiya ce 😂🌚*


*AMATULLAH RAHUSA DATA*


*DATA SERVICES AT APPORDABLE PRICES*


*MTN*

500MB-150

1GB-280

2GB-560

3GB-840

4GB-1120

5GB-1300

10GB-2700


*AIRTEL*

500MB-200

1GB-400

2GB-800

3GB-1200

4GB-1550

5GB-1950

10GB-3850


*GLO*

500MB-200

1GB-400

2GB-800

3GB-1200

4Gb-1550

5GB-1950

10GB-3850


*9MOBILE*

500MB-500

1.5GB-1300

2GB-1500

3GB-1800


*Validity 30days*

Checkbalance codes

*MTN* *460*260#

*AIRTEL* *140#

*GLO* *127*0#

*9MOBILE* *228#


*VIA THIS ACCOUNT*

8160508316. Jamila Bello Abubakar. Opay bank


*** for call or whatsapp

#Comment

#Share pls