7&8
*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_
Na
_YAR'MUTAN KANKIA_
_MANAZARTA WRITERS_
*BOOK ONE*
*PAGE 07&08*
***
*Inajin dadin comment dinku sosai d sosai yana sani farinciki much luv🌹*
Idanunsu sarkewa sukayi da juna suna kallon-kallon,Beauter tayi saurin sauke kanta kasa zuciyarta na bugawa da karfi da karfi dan tunda take a rayuwarta bata taba ganin kyawkyawan namij mai kwarjini da haiba irin A-Kaɗir ba,sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa..."Sorry." gaba tayi da sauri bata tsaya taji abunda zaice ba,duk da tarin barnar da tayi mashi,binta yayi da ido yana mamakin wannan wata irin yarinyarce?anya kuwa tana da cikaken hankali? dukawa yayi ya dauki Sim card dinshi ya kama gabanshi zuciyarshi fal da tunanin wacece ita?anya ma musulmace duba da irin shigar dake jikinta bata da banbancin da akirata tsirara,rintse idonshi yayi yana dafe kanshi wani bakin ciki na taso mai,da zuciyarshi ta hasko mashi breast dinta da suke tsaye a cikin rigarta da ko arzikin breziya bata sa masu ba,kuma tsaye suke a cikin net din rigar dan rigar gabanta net ne shiyasa suke waje kowa yana gani,iska ya kaima nushi yana cewa.
"Astagafirullah." dan tunda uwar da ta haifeshi bai taba ganin tsiraici ba sai yau,ji yayi bai iya tafiya har sai ya gano inane gidansu sannan wani addini take,idan har kuwa musulmace to tabbas taci amanar musulcin dan kuwa addininta bai koya mata irin wannan shigar ba ta banza,Allah kadan yasan adadin mazan da zata jefa ga halaka masu raunin zuciya mundun ta cigaba da irin wannan kazamar shigar koda kuwa kiristen ce.
Ya kusa daukar minti arba'in zaune a cikin mota yana jiran fitowar Beauter,kamar ance waiga ya ganta rungume jikin wani kato suna tsotsar bakin juna sai wani shafata yake,ita kuma ta narke mashi sai tura hannunta take cikin sumarshi tana sosawa,a tsakiyar gari ba ko kunya take ji yanayinshi ya fara sauyawa sakamakon gamon da yayi sitarin motar ya kaima bugu yana cewa da karfi...."Auzubillahi minas'sheɗanar rajin ya Allah ka shirremu baki daya." sun kusa minti goma suna laluben juna ita da saurayinta sannan ya rakota har bakin mota ya bude mata ta shiga bayan kudin da ya ajiye mata da wani abu cikin leda wanda baisan ko maiye ba,ready shima yayi ya tada motar 5min ya bata sannan ya fara bin bayanta cikin wayau da dubara yanda duk tsiyarta ba zata gane ana bin bayanta ba.
*NIGERIA🥀*
_Kano_
"Ki kula da kanki." ta maimaita karanta text din bata san sau nawa ba,mamaki fal a zuciyata kallon Zubaida tayi tana miƙa mata wayar,kallon Zulaihat tayi tana cewa.."waye wannan kuma." girgiza kai tayi tana sauke ajiyar zuciya tace."nima bansani ba." kwantawa tayi tana dafe kanta dan wani irin ciwo yake mata kamar zai tarwatse mata haka take ji,ko motsi mai karfi bata son tayi dan gani take kamar kan nata zai tarwatse tsabar bala'i kwantawa tayi kawai tana lumshe idonta.
"Sis ko ki kira number kiji waye."? Girgiza kai tayi a hankali tayi magana tace.."A'a Sis,ki saman number ma a blacklist." zaro ido Zubaida tayi tana cewa...."Ayya Sis ba kyau aikata haka fa,ki kasan ko dashi za'ayi." tsaki kawai tayi bata sake ce mata komai ba,adduar bacci tayi kawai.
Dariya Zubaida tayi tana duba lokaci tace. "Banda ansa kenan?and tun yanzun zakiyi bacci ko ten batayi ba,kuma sai 12pm muke da lecture fa." waigowa tayi tana kallonta tace.."har kin manta da neman da Dr yake man ko."?murmushi kawai Zubaida tayi bata sake cewa komai ba,ta cigaba da danna wayarta.
★★★
Ajiye wayar hannunshi yayi yana murmushi ya kalli Moha yace..."Yarinyar tana bani tausayi sosai,gashi kuma tsoranta na burgeni sosai." Dariya Dr Moha yayi yana cewa."ina ruwan Zulaihat,ai na lura matsoraciya ce aiki ya ganka Najeeb." harararshi yayi yana cewa..."aiki kuma?kamar ya aiki ya ganni."?
Gira ya ɗaga mashi yace."ehmana sosai ma,tunda ka ganni kace kana so ba dole kayi hakuri da halinta." Harararshi yayi yana wurga mashi pillow hannunshi yace..."da yake gaya maka nayi inasonta ko."?dariya yayi yana cewa."haba Najeeb karda ka maidani karamin yaro." Tsaki kawai Dr yayi ya cigaba da latsa wayarshi bayan ya gama yayi kwanciyarshi murmushi yayi yana girgiza kai da ya tuna abunda ya faru tsakaninshi da Zulaihat,a hankali yace.."sarki tsoro."
*UKRAINE🥀*
_Landscape Alley_
A dai dai bakin gidanta ta parking din motar ta,sai da tayi ten minute sannan ta fito ta dauki ledar hannunta ta shiga gida tana kokarin kulle kofa ya rike kofar da karfi yana mata wani kallo,take sai da gaban Beauter ya fadi dan wani irin kwarjininshi ya darar mata,ga tsoron da ya kamata dakewa tayi tana aika mashi kallon banza,rabawa yayi ta gefenta ya shige cikin gidan ya barta tsaye sake da baki,da karfi ta tura kofar tana mai cire takalminta ta zura silifas dinta,ta ida karasowa cikin parlorn tsaye yake yana mai ƙarema dan karamin parlorn kallo,ba laifi ya danyi kyau karasowa tayi ta tsaya gabanshi ta ɗaga kanta sama tana kallonshi zatayi magana kenan ya rigata..."daman baki iya tarar bako ba."? Yana maganar yana kauda kanshi gefe,sai salati yake dan shi kanshi yasan ya daure da har ya iya kallonta ya yayi mata magana,dan shigar da ke jikinta kawai take tada mashi da hankali.
Murguɗa mashi dan karamin bakinta tayi tana cewa." waye kai?mai kazo yi man a gida?ko ka fita ko yanzun nasa azo a fitar man da kai." lumshe idanunshi yayi yana budewa a hankali ya saukesu a kanta,yarrrrr haka yaji jikinshi ya dauka ya fara yi,kama hannunta yayi ya zaunar da ita bisa kujera sannan shima ya zauna Murmushi ya sakar mata yana cewa...."are you a muslim."? Waro ido tayi waje tana mamakin tambayar rainin da yayi mata wai ita musulmace,to ai ita yadace tayi mashi wannan tambayar bashi ba,cikin fushi ta tashi tsaye tana tsayawa gabanshi tace..."enough,nace ya isa haka how dare you da zaka shigo har mahalailina kazo kana man banzar tambaya bani son haka fa,maza fitarman daga gida ko yanzun na kira maka police,suzo su fitarman dakai kuma sai nasa andaureka naga wa ya tsaya maka."
Kauda kanshi gefe yayi yana mai sauke ajiyar zuciya,yarinyar tayi ta ko wane fanni tana da kyau tana da sura da kuma diri sai dai mai idan musulmace to rayuwarta tana bukatar gyara,tana bukatar ta samu mai gaya mata gaiskiya da kuma a dunga tuna mata da akwai mutuwa sannan kuma akwai kwanciyar ƙabari da kuma ranar hisabi,idan kuma bata sani ba a gaya mata sauke ajiyar zuciya yayi yace.."ihu nami kuma?just i ask you,answer my question please i have to said something!sauke ajiyar zuciya yayi ya cigaba da cewa....."ina jiran ansarki dan dare yayi myluv nacan hankalinta tashe na kai wannan lokacin ban dawo gida ba." wani irin faduwar gaba ya ziyarceta da taji ya anbaci myluv,to wacece ita kodai matarshi ce tambayar da tayi ma kanta kenan har bata san tace..."ita ur luv din matarkace."? sai da tayi mashi tambayar sai kuma taga maiye nata na sannin wacece a wajenshi take haushin kanta ya kamata,kallonta yayi yace..."baki da hurumin sannin haka,tunda ba zaki gaya man addininki ba,ni zan tafi saboda da dare yayi, ba tsayuwa nazo yi nan ba kuma ba kwana naxo na tayaki ba yanmata na barki lafiya kiyi bacci mai dadi." har sai da ya kusa fita sannan tace...."dakata." waigowa yayi yana kallonta,ida ƙarasowa tayi wajenshi tace.."am a muslma(ni muslma ce) and what."? Girgiza kai yayi yana cewa..."babu yanmata sai da safe." ya ficewarshi,komawa tayi cikin parlorn tana tunanin wayeshi mai yazo yi wajenta kodai aljanine shi,numfashi ta sauke ta ida shigewa bedroom dinta wanka kawai ta samu tayi ta shirya ko hodar ibilis dinta bata samu damar shaƙa ba ta kwanta zuciyarta fal da tunanin waye wanann mutumin,ya dace kuwa tasan waye shi.bata da ansa.ciwon kai taga yana neman baibayeta ta lumshe ido sai ga bacci yayi gaba da ita.
★★★
"Daga ina kake A-Kaɗir."? Kallon damuwa yayi kwance bisa fuskar Ammie,ga idanunta sunyi ja alamun tanajin bacci amman rashin dawowarshi kan lokaci yasa ta hana idonta baccin,sauke numfashi yayi yana kama hannunta suka zaune a bisa sofa kwantar da kanshi yayi a ƙafaɗunta yace..."daga wajen wata." shi dai bai iya karya ba balle yayi ,kuma idan yayi mata karya ribar mai yaci ita mahaifiyarshi ce baida kamarta a fadin duniyar nan,ɗago da kanshi tayi tana cewa..."wata kuma."!? Ɗaga mata kai yayi yana cewa..."eh Ammie wata,but ki dan karaman lokaci zan maki bayaninta ,yanzun na soma bincike akanta nasan wacece ita,yar wata kasace ita,sannan maiye yayi asalin zuwa nata wannan kasar har take zaman kanta." dafashi tayi tana cewa...."naji Abu-kaɗir nakuma baka lokaci dan nasan ko wacece wannan da kake kokarin bibiyar rayuwarta ba banza ba,kuma na yarda da tarbiyar da nabaka nasan ba zakayi abunda Allah ya hana ba." Murmushi yayi yana mai kara jin son mahaifiyar tashi,dan iyayen nashi suna saurin fahimtarshi.da kuma kula dashi da lamiranshi,shafa kanshi tayi tana cewa..."tashi muje kayi dinner sai a kwanta ko."? Kwabe fuska yayi yana turo baki gaba,shi dai kuwa yanzun zata matsa mashi da yaci abinci.
Murmushi tayi tana cewa..."naji ka koshi to kasha koda tea da cake ne bansan ka kwanta cikinka babu komai a ciki myluv."marairaice mata yayi yana maƙale kwafaɗa yace.."nidai luv na koshi ni tauna cake din ma wahala yake man." girgiza kai tayi ta tashi bata ce mashi komai ba ta dama mashi kunun gyaɗa yaji madara sosai sai sugar din dan kadan ta zuba mashi dan tasan baya shiri da zaƙi ko kadan,dawowa tayi ta zauna ta fara bashi da kanta da wayau da dubara ta samu yasha da yawa sannan ta kyaleshi yaje ya kwanta,sannan Dad ya shigo shi ya ida shanye kunun kaɗir sanann sukeje suma suka kwanta.
*NIGERIA🥀*
“ Dan Allah ki tsaya ko tea ne ki daure kisha.” girgiza kai tayi tana cewa...“nidai a'a na koshi wallahi ban san ya rigani zuwa ban san na ƙara yin wani laifin kuma.” kallonta Umma tayi tana cewa...“duka yanzun karfe 8:13 tayi maza zaune kiyi break ban yarda ki fita bakici komai ba.” kallon Umma tayi hawaye suna zarya a saman fuskarta tace..“ wayyo Allah Umma yanzun idan na tsaya shan tea din nan,hour nawa zan bata anan kuma yace ya taddani a bakin office dinshi.” kwafa Umma tayi tana cewa...“har yaushe na fara faɗa kina faɗa Zulaihat?to tun kafin na taso maki ki tashi kiyi abunda nace,kuma ki share hawayenki tunda ba bugunki nayi ba da zaki kama yi man kuka.” share hawayenta tayi tana sipping din tea din duka ta samu ta sanye shi ko ta tafi bata ce masu ta tafi ba.ta kama gabanta zuciyarta fal da tsoro.
Tafiya take tana share hawaye bata damu da kallon da ake mata ba,dan ita tasan cikin tashin hankalin da take. bata san wani irin hukunci zai yanke mata na,bata taba shiga cikin case din ko wani malami ba tunda ta shiga buk,and ita ko magana bayi take da kowa ba,kaddara bata wuce ranarta amman kaddarata ta hadata da Dr Najeeb malamin da kowa ya shida bai da ragi balle ragowa baya saurara ma kowa baya ɗaga ma kowa ko malaman ba da kowa yake huɗa ba ,amman ita Allah ya hadata da shi akan laifin da ba zata iya kwatanta girmanshi ba,cikin ikon Allah da yardarshi Zulaihat tana isa bakin titi ta samu naped sai dai ta samu akwai mutu ɗaya a ciki,hanyarsu ɗaya amman ba waje daya zasu tafi ba dan shi goran dutse zai tsaya ita kuma buk za'a ida wucewa da ita,ba haka taso ba,amman da babu gwara akwai ba dadi lokaci ta duba karfe tara da rabi ji tayi kamar ta anshe naped din ta tuƙa da kanta dan gani take kamar baya sauri,sai dai kash sai da go-slow ya dan dakatar dasu sannan ta samu suka ida shiga cikin school,ko ida tsayawa bata bari ya ida yi ba,ta fitowarta ta mika mashi 1k bata ko tsaya ansar chanji ba ,tayi wucewarta cikin sauri da sar-sarfa haka take tafiyar ko gabanta bata gani sosai tafiya kawai take tana wulla kafafunta ba tare da tana duba inda take jefa ƙafafun nata ba,hawaye kuwa tsiyaya suke kamar ankunna famfo,bata damu da ta tsaya ko goge fuskar ba,turus ta tsaya bakin office din tana duba lokaci tana kallon office din ƙarma da ƙarƙarwa jikinta ya farayi dakyal ta iya daura hannunta a bakin door din tana yin nocking,rintse idanunta tayi da taji ance....
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000
VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp
#NAJEEB✓
#ZULAIHAT✓
#A-KADIR✓
#BEAUTER✓
#LOVE✓
#FATE✓
#JAMEEY✓
#VOTE✓
#COMMENT✓
#SHARE✓
#PLEASE✓