13&20
*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_
Na
_YAR'MUTAN KANKIA_
_MANAZARTA WRITERS_
*BOOK ONE*
*Wannan page din naki ne Pharteemarh kankia much luv🥰*
*PAGE 13&20*
***
"Zaku shigo mu tafi ko sai na fito na balballaku."? Cikin tsawa ya ida maganar da sauri Zulaihat ta toshe kunnenta har rige rigen bude motor suke dan shiga da sauri Zubaida ta bude baya ta riga Zulaihat shiga tana lumshe idonta gami da sauke ajiyar zuciya. dan ta tsorota sosai da tsawa da ya daka masu,ita kuwa Zulaihat tsaye tayi bakin motor tana share hawaye ,kallonta yayi ya girgiza kai yana sakin karamin tsaki zuge glass din yayi yana wulla mata harara cikin masifa da tsare fuska yace..." Mudun na sake magana akan ki shigo wallahi ranki sai ya b'aci zaki shigo ko kuwa."?
Kuka ta fashe dashi tana balle murfin motor ta shiga gaban da bata bukatar shigar ko kulle marfin batayi ba ta daura kanta bisa cinya tana kukanta,tsaki yayi yana kulle motor da kan shi gami da bissmillah yayi ma mota key suka tafi shuru kake jin motar ba abunda ke tashi sai sautin kukan Zulaihat.
Har cikin kasan zuciyarshi haka yake jin saukar kukan nata,ji yake kamar ana yankar mashi naman jikinshi tsabar yanda yake jin rad'adin kukan a cikin jini da bargo,da karfi ya rintse idonshi yana kaima sitirarin motor duka gami da danna giyar motor ji kake k'iiiiiiii haka sound din ya fita, salati Zulaihat tayi tana fadawa jikinshi gami da makalkaleshi tana rushewa da wani sabon kuka,zuciyarta da sauri sauri take bugawa fat fat haka sautin bugawar zuciyar yake fitowa,rintse idonshi yayi yana sauraren yanda zuciyar tata take bugawa sai da ya bata kamar 5min sannan ya tureta daga jikinshi yana balla mata kallon banza natsuwa tayi tana kama bakinta da ke rawar kuka,tsaki yaja mai tsawo yana kallon ta fuskar nan babu annurin murmushi a saman yace.
"Na sake jin koda tarinki sai nayi ball dake ,na kasheki da maruka tunda baki da hankali har yanzun idoit." Rintse idonta tayi da karfi tana budesu gami da goge hawayen da suke zuba bisa fuskarta, tabbas taji ciwon zagin da yayi mata ta rasa mai tayi mashi har haka ya tsaneta?bata da ansa sai kawai ta kalle gefe tana sauke ajiyar zuciya gami da goge hawaye a zahiri tayi shuru kamar yanda ya bukata din,amman zuciyarta taki tayi shuru sai tafasa take tana zubda hawaye sake yi ma motar key yayi suka dauki hanya.bai sake kallon idan take ba har sai da ya iso har kofar gidansu yayi parking sannan ya kalleta.
Itama kallonshi take da idanuwanta da sukayi luhuluhu sun sha kuka, sai ta kara mashi kyau ma,ita kuwa mamaki ne fal a zuciyarta taya hakan ta faru?ya akayi yasan gidansu?fuskarta kasa boye mamakinta tayi sai dai kash tasan ko giyar wake tasha bata isa tayi mashi wannan tambayar ba.ai wasa ma waje gareshi ita a rayuwarta batason taga abunda zai hadasu koda na second d'aya ne.maganar Zubaida ce ta dawo daga ita daga duniyar tunanin da ta tafi...da sauri tabi Zubaida da kallo da har ta kusa shiga gida,sauke ajiyar zuciya tayi tana mai kokarin bude motar itama ta shiga gida, sai dai taji motar a lock take. waigowa tayi tana kallonshi hawayen dai basu daina zubowa ba,so take ta samu ta fita ta shiga gida ko ta samu yin kukanta yanda take so ko zataji sausaucin a zuciyarta.
Girgiza kai yayi gami da kafe ta idonunshi masu sata gigicewa da shiga taitaiyinta a take kuwa,kallonta yake kamar ya samu TV haka yake kallonta kuma yana mamakin yanda take maida kuka abokin hirarta ace ita bata da aiki sai na kuka,ko gajiya batayi idan bata gajiya ai ta rage kodan lafiyarta dan ai ciwon kai ba kanwar uwa bane balle tace,lumshe idonshi yayi yana budewa yace.
"Sannu da aiki."
Dan shuru yayi yana dauko mata wani farin handkerchief sai kamshi mai dadi yake, ya bata babu wasa a fuskarshi yace mata.."maza goge wannan sakarcin banzan a fuskarki tun ban karyaki anan ba."ansa tayi tana goge hawayen sai da ta gogesu tas sannan ta mik'a mashi tana maida kanta kasa dan a takure take sosai da sosai, ansa yayi yana dan sakin tsaki yace.."kuka kuma ba zan hanaki yi ba, idan kin shiga gida ki cigaba daga inda kika tsaya ni nasan abunda zan maki gobe a school fita ki ban waje."
D'aga kai kawai tayi tana ficewa cikin motar a natse ta nufi hanyar gida yana kallonta har sai da yaga shigewarta ya sauke ajiyar zuciya gami da sakin murmushi yana cewa."Myluv ba dai rigima ba."Murmushi ya kuma saki da ya hango zallar shagwabe da rigima da tsoro a tare da ita yana son halinta sosai ba kamar tsoronta yana tsaye mai a rai kuma yana sakashi a cikin nishadi mudun zai tuna. haka ya juya dan komawa gida.
Koda ta shigo cikin gida bata bi ta kan Zubaida ba gaida Umma kawai tayi ta shigewarta room din su ajiye back bag din ta tayi tana shigewa toilet ta watsa ruwa tana fitowa ko mai bata tsaya shafawa ba saboda zafin da akeyi kaya ta samu mararsa nauyi da ta kura ta saka ta nemi hula ta sakama kanta ta fito parlo zama tayi tana kallon Umma cikin langwabar da kai gefe tace.
"Umma mai aka girka mana."?
kallonta Umma tayi cikin sonta da tausayinta tace." Favorite dinki yar gidan Umma." Murmushi ya baiyana a fuskarta ta na cewa.. "Thank you Ummana Allah ya kara nisan kwana." Tashi tayi taje kitchen dan zubo shinkafa da wake da man kulli da yaji,a can ta tadda Zubaida tana neman spoon ko kallonta batayi ba, again ta wuce ta fara abunda ya kawota a kitchen din,dariya Zubaida tayi tana cewa.
"Sis har ya tafi kenan."? Ko kallonta batayi ba balle ta bata ansa ida zuba man tayi tana bin gefenta ta wuce tana sakin karamin tsaki dan har yanzun haushin Zubaida take ji har cikin ranta,koda ta fito zama tayi ta fara cin abincinta tana kallo a hankali ,itama Zubaida fitowa tayi tana zama kusa da ita tana cewa.." Allah dai ya ida nufi Sis,amman wallahi hadin ya bata color sosai." Ta ida maganar tana kanne mata ido,hawaye ne suka fara zubowa tana kallon Umma cikin muryar kuka tace.
"Umma kice mata ta fita a harkata ba ruwanta dani tunda dai ni ba sa'arta bace." Tana turo baki gaba ta ida maganar gami da share hawaye, dakuwa Umma tayi ma Zubaida ta na cewa."karki kuma tsokanarta daga yau." Maida kallonta tayi wajen Zulaihat tayi tana cewa.."kukan mai kuma zakiyi mana?ba nayi Mata magana ba."?kukan ta ida rushewa da shi tana cewa. "Umma baki ji abunda take ceman ba shiyasa nidai kawai ta daina ba na so nidai kawai." Tashi tayi tana bar masu parlon hararar Zubaida Umma tayi tana cewa.
"Har sau nawa zan ce maki ki daina janta tunda bata so kuma ba yayarki bace."?
Itama Zubaida jikinta shanyi yayi tana maida kanta kasa cikin rashin jindadi tace.." Yi hakuri Umma in shaa Allah daga yau na daina ba zan kuma ba."
"Da ya fiye maki sai kisan yanda zakiyi ki bata hakuri kinsan dai yar'uwarki marainiya ce bata da kowa sai mu maimakon ki sata farinciki sai ki dunga b'ata mata rai karki sake daga yau ki dunga tuna bata da uwa kuma bata da uba ke ya dace ki zama kamar uwarta dan haka karda na sake ganin irin haka daga yau."
"In sha Allah Umma." Tashi tayi ta nufi room din nasu kwance ta taddata tana aikin kuka, hawa tayi bisa bed din tana kwanto da kanta bisa cinyarta ta fara lailashinta sai da ta tabbatar da ta dawo normal har tana mata murmushi suka ji wayarta tayi notice ma'ana sako ya shigo a cikin ta Zubaida ce ta dauko tana cewa.
"Sis message ne fa ya shigo." Tashi tayi ta nufi hanyar toilet tana cewa.."share Sis nasan Mtn ne zasu isheni da shashancinsu." Ida shiga tayi tana wanke fuskarta ta fito tana kallon Zubaida da ta kurema wayar ido kamar tana kallon abunda ya bata tsoro a cikin wayar zama tayi tana cewa.."what wrong."? Sauke numfashi tayi tana mika mata wayar dan tsaki tayi tana ansar wayar dan son ganin abunda ta gano a wayar har ya sata mamaki kurama dan short message din tayi da ido tana kara maimata karantawa.
_barkinki sarauniyar kyau sarauniyar zuciyarta uwar y'ay'ana ki barman zuciyata haka ki taimaka man ki daina kukan nan hakanan dan yana konaman zuciya da gangar jiki Myluv_
Ajiye wayar tayi tana kallon Zubaida cikin nuna damuwa tace."Sis na bani waye wannan kodai aljanine."!?
A tsorace ta tayi mata maganar har tana yarfa hannayenta tana son sake rushewa da kukab,hakan da tayi ne ya ba Zubaida dariya dan bata san ta daria ba sai da tayi mai isarta ta kalli Zulaihat tace.
"Ko daya ba aljani bane mutune dan uwanki kamar kowa kawai dai sonki ne yayi mashi kamun da idan kina cikin farinciki jikinshi zai bashi idan kuma kina cikin bacin rai da damuwa haka ma jikinshi yana bashi."
Numfashi mai zafi ta furzar tana lumshe ido dan har hankalinta ya kwanta da Zubaida tace ba aljani bane kallonta tayi tace.."to waye shi Sis."
"Nima ban sani ba Sis ,sai dai ya dace ya baiyana kan shi ko wane idan ba haka ba yana ji yana gani zakiyi mashi nisa ki zama mallakin wani *DA'IMAN ABADAN* kuwa. kinga yayi dakon so a banza."
Ita dai Zulaihat batace komai ba sai ma kallon Zubaida da tayi tana cewa.. "Sis baki yi mamakin yanda Dr Najib ya san gidanmu ba,ni abun ya tsorata ni sosai."
Murmushi kawai Zubaida tayi tana cewa."nima nayi mamaki amman ba sosai ba.dan na lura ba da wasa zai shigo ba,abunda dai ya tsorata ni da ya kusa kashemu dazun kinsan Allah Sis nasa har na mutu ma kukanki ya maidoni na ga ashe da sauran ranmu."
Tsaki tayi tana cewa.."banson Dr Najib sam ko ganinshi bansan yi Sis, shi da yaso kashemu dan nayi kuka shine har da zagina yace man idoit naji haushi sosai wallahi." Girgiza kai Zubaida tayi tana cewa.."karda ki sake furta Kalmar tsana ga kowa ba ma a wajen Dr Najib ba Sis,sannan ki zama jaruma a duk inda kike ki rage wanann kukan naki dan ba zai anfaneki da komai ba,balle ma kina tare da Dr Najib dole ki chanza idan ba haka ba kuwa Sis zaki sha doka kala kala a wajen shi kinsan dai halinshi ba sai na gaya maki ba."
Tsaki ta Kuma ja tana daukar handout dan maganar ma baki daya ta fice mata a rai,itama Zubaida bata sake cewa komai ba ta dauki ta ta handout din ta cigaba da karatun itama.
*URKAINE🥀*
Shuru Alhaji Nurandeen yayi yana sauraren Matar tashi har sai da ta kai karshe sannan ya maida numfashi yana cewa.."ikon Allah kenan Yar Albarka. So kenan shi So ai nufin Allah ne kuma ba ruwanshi da kyau ko nasaba ,inba haka ba har akwai yarinyar da Myson zaice yana so tace bata sonshi,idan kyau ake bukata yana dashi haka kuma dukiya ko ni kaina bansan iya adadin dukiya taba balle shi kanshi A-kad'ir da yake neman na kanshi, da gobe zamu koma Nigeria dan nagama duk abunda ya kawoni dole tafiyar ta fasu dan samama gudun jinina farincikin dan haka kiraman shi naji ita yarinyar yar wace kasace ."
Murmushi Ammie tayi tana shafa gefen fuskar mijin nata kissing dinshi tayi tana tsotsar lips dinshi kadan gami da dan cizawa kashe mashi ido daya tayi tana cewa.."angama Oga na." Murmushi yayi yana shafa lips dinshi gami da binta da ido har ta bace ma ganinshi ajiyar zuciya ya sauke yana kallon iyalin nashi cikin tsantsan sonsu da kaunarsu ,suna isowa bisa cinyarshi A-kadir ya daura kanshi yana cewa..
"Welcome back Dad." Murmushi Dad yayi yana shafa kanshi yace..."thank you Son,naji wani labari maidadi kuma marar dadi wacece wannan yarinyar mai kuma tazo yi a wannan kasar karka boye mana komai mu iyayenka ne ka gayamana gaskiyar wacece ita yanda komai zaizo mana da sauki."
Dan shuru yayi yana tunanin ta ina zai fara taya zai gaya masu zaman kanta take a kasar nan taya zai gaya masu karuwanci take a kasarnan,kuma idan sukace mashi Ina suka hadu yace mai?ajera ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Dad yace.
"Dad ba kowa bace face mai zaman kanta a wannan kasar ba karatu ya kawota ba haka ma ba business ne ya shigo da ita wannan kasar ba,tazo ne zaman kanta tana abunda ta gadama shine kawai abunda na sani a tare da ita dan ko sunanta ban sani ba shine gaskiyar maganar Dad."
Ya ida maganar yana tsurama Dad din nashi ido dan yana son yaga yanda ya dauki maganar tashi,abun mamaki murmushi ya gani dauke saman fuskar Dad din, yana shafa gefen fuskar A-kadir din sai da ya gama murmushinshi ya maida kallonshi wajen Ammie da itama murmushin take dan ita bata da matsala abunda luv din ta yake so tana sonshi bata da damuwa da wani karuwancinta damuwarta Dad dinshi. daman tunda taga yana murmushi sai taji sanyi a ranta.
Gyaran murya Dad yayi yana cewa."idan har kana sonta my son zanyi yanda zanyi naga ita wannan yarinyar ta zama mallakinka *DA'IMAN ABADAN* zanyi wanann kokarin ku kasance cikin farinciki har karshen rayuwa ,Abu daya zakayi ka bani address din ta zamuje nida Ammie dinka danyin magana da ita yarinyar in shaa Allah." Murmushi yayi yana boye fuskarshi a jikin Dad dinshi yana mai kara jin son iyayen nashi yana shigarshi ,girgiza kai Dad yayi yana cewa.
"Dan nema ka gama jin kunyar ka bani address mu tafi dan ance da zafi zafi akan buga karfe."
Tashi yayi yana shigewarshi room dinshi sai murmushi yake. da ya shiga room din sannan ya tura mashi address din through SMS,bayan Dad ya gama karanta Address din yayi dariya yana cema Ammie.
"Yar'Albarka yarinyar ma a estate dina take zaune." Murmushi Ammie tayi tana cewa.."masha Allah komai yazo da sauki kenan wace estate din a ciki."
"Landscape Alley,tashi muje dan nasan waye Abu-Kadir shiyasa na yarda da ya auri yarinyar. duk da ban ganta ba amman ta ban tausayi a rayuwar da ta zabama kanta sai kiga mun shiga aljana ta hanyarta, dan cireta daga wannan kazamar rayuwar Allah yaga zuciyarmu Allah ya daura mu a kanta ya kuma bamu ladar."
Amin." Ammie tace tana yafa gyalen abayarta suka fito drive har ya taso Dad ya dakatar da shi yace ya hutar dashi da kanshi zaiyi driving din ,da bissmillah ya tada motar sai landscape Alley dai dai parking lot din gidanta sukayi parking din motarsu.sannan suka fito Ammie ce ta fara nocking tana kara karema estate din kallo dan tayi mata kyau tasan da estate din bata taba shigo taba sai yau ta dalilin beauter.
Beauter na zaune a parlo taji ana danna door bell ,banza tayi ta share ta cigaba da cin tupa din ta tana kallon zeeword,dan batayi da kowa zaizo ba kuma ita k'aidarta ce bata kula bakon da bata san da zuwanshi ba,tsaki tayi jin anki daina dannan bell din take ranta ya bata A-Kadir ne ya sake dawowa a karo na ukku kenan?cikin fushi ta tashi ta nufi door din dan karta mashi rashin M bata damu da kayan da ke a jikinta ba dan mini sikert ne iyakar cinya sai amless dakyal ta rufe cibiyar ta sai gashinta da ta baza a baya da yaji gyara,face din ta babu ko digon makeup amman duk da haka face din glowing take lips din ta pitch sai shek'i suke cikin fushi da bacin rai take cewa..
"Heyyyyy wai waye ne zai sakaman ciwon kai."? Ta ida maganar cikin tsiwa tana bude kofar idonta sauka yayi saman fuskar Ammie. da take tsaye fuskarta dauke da murmushi, take nauyin Ammie da kunyarta suka dirarma Beauter.itama murmushin tayi ma Ammie duk da bata santa ba. amman taji tanajin kunyarta sosai ma,dan weaving tayi mata tana cewa.." Welcome Ma please come in." Murmushi Ammie tayi tana shigowa tace.."Thank you My Daughter."
Juya kalma My Daughter Beauter tayi sai taji jikinta yayi sanyi sosai.take yanayinta ya sauya dan har Ammie sai da ta lura da hakan,sai sharewa tayi tana cewa.."Daughters zan iya zama."daga mata kai Beauter kawai tayi itama tana samun waje ta zauna tana kallon Ammie. da take son tambayarta wacece ita?daga ina kuma mai tazo yi a gidanta har take kiranta da sunan yarta?murmushi Ammie tayi tana cewa.
"Bani daya bace nazo da mijina yana waje yana jiran a bashi izinin shigowa ko zaki dan saka koda afteradress ce."? Kasa yi ma Ammie gardama tayi sai tashi da tayi batace komai ba ta shiga bedroom din ta sauya kayan jikinta tayi tasa abaya kamar yanda Ammie ta umirceta harda saka hula ta kulle gashinta sannan ta fito,da kallo Ammie ta bita tana cewa.
"Masha Allah My Daughter kinyi kyau sosai bari naje na shigo da Dad ko."? Nan ma batace komai ba sai ma daga mata kai da tayi tana binta da kallo wacece ita koma wacece tayi mata matarta daga gani tana da daddatako. da sallama suka shigo ita da Dad ansa Sallamar tayi tana mai kallon Dad dan yayi mata kama da wanda ta sani sai dai ta manta ina ta taba ganin fuskar sannu da zuwa tayi masu tana mai tashi ta shiga kitchen ruwa da fruit ta kawo ta ajiye masu,da kanta ta zuba masu ruwan ta basu sannan ta yanka masu watermelon da pineapple da apple ta kuma ajiye masu ,godiya sukayi mata bayan sun gama shan ruwan sanann Dad ya fara magana.
"Sunana Alhaji Nurandeen Abu-kadir jigawa,wannan kuma matata ce sunanta Umma Salma Abubakar ko ke zamu iya sanin sunanki."!?
Murmushi tayi tana cewa.." Ur welcome." Dan shuru tayi kuma sai tace.."Am Hauwa'u Abdullahi Jibirin." Kallon Kallon akayi da Ammie da Dad ajiyar zuciya Ammie ta sauke cikin mamakin jin tana da sunan hausawa amman basu kawoma ransu yar Nigeria bace duk da Beauter bakace amman bakinta bai kama da na yan Nigeria ,murmushi Ammie tayi tana cewa.
"Masha Allah Hauwa,Allah yayi ma rayuwar ki albarka ko wace kasa kike sanann maiye religiou dinki."
Har cikin ranta haka Beauter taji dadin yanda Ammie ta saka mata albarka dan rabon da taji Kalmar ma har ta manta ji tayi hawaye suna son zubo mata tasa bayan hannu ta gogesu tana mai hana su zubowa tace cikin murmushi.
"Nigeria and am a Muslim." Kasa boye mamakinta Ammie tayi a wannan karan dan sai da fuskarta ta nuna haka kuma ta hango damuwa a saman fuskar Beauter kuma taga sanda take goge hawayen da suka zubo mata,to maiyasata kuka? Kuma maiyasata karaya har haka?tabbas da wata a k'asa a taitare da yarinyar nan,ruwa ta dauka tasha tana cewa.
"Ashe kasarmu daya ma Hauwa,Allah yayi maki albarka ya kareki daga sherin zamani kinji My Daughter." Daga kai tayi tana murmushi tace.."Amin Amin Mom thank for prying. " dan shuru suka dauka na dan lokaci sannan Dad ya cigaba da cewa.
"Hauwa'u daman munzo ne akan danmu." Dasauri ta daga kanta tana kallon Dad shima Dad din murmushi yayi mata yana d'aga mata kai ya cigaba da cewa.."kwarai kuwa munzo akan danmu ,Abu-Kadir Nurandeen wato A-kadir yazo yace mana yana sonki kuma yana son ya aureki amman kinki ki kulashi balle ki bashi hadin kan da yake bukata a tare dake wato aure. shine mukazo da kanmu mu rokeki alfarma dan Allah Hauwa'u ki taimaka ki auri A-kadir yana sonki muma kanmu iyayenshi munason ki dawo cikinmu ,mu zama family daya."
Tashi tayi tana girgiza kai tana mai rushewa da kuka,maiyasa kukazo mata da wannan alfarmar bayan kallo daya tayi masu taji ta samu iyaye wanda itama zasu ringa saka mata albarka,amman maiyasa? maiyasa? ba zata iyaba .ba zata iya jin zata sake soyayya ba ,ba zataji zata iya sake kallon d'a namiji ta gaya mashi kalaman soyayya ba.dukawa tayi a gabansu tana girgiza masu kai cikin yanayin tausayi da tausayin kanta tace.
"Kunzo man da abunda ba zan taba iyawa ba,dan Allah ku fahimceni Ku kuma yi man uzuri ,da ace zani iya da na anshi wanann alfarmar taku dan gani daya nayi maku naji inasonku kuma nasamu iyaye naso ace wata alfarmace ba wannan ba. da nayi maku ita ba tare da bata lokaci ba.dan kunyi man abunda na dade ba'ayi man ba,wato saman albarka da kuma yi man addua abunda yake da tsadar samu a wajena. dan rabon da a saman albarka ko ayi man adduar shekarun basu fado amman maiyasa kuka tambayen abunda ban iyawa."?
Tashi Ammie tayi ta dafa Beauter tana share mata hawayen fuskarta cikin nuna kulawa da damuwa tace.." Munji maganarki Hauwa kuma mun fahimceki amman kina da Wanda kike so ko."?
Da bayan hannun ta share hawayenta tana girgiza kaii tace.."ko daya Mom bani da wanda nike so,asali ma na tsani soyayya kuma bani yinta." Kallon Dad Ammie tayi tana auna maganar Beauter ta tsani soyayya mai akayi mata mai zafi haka a soyayya har tayi mata wannan tsana mai muni haka? Har zatayi magana Dad ya rigata yana cewa.
"Karki damu Hauwa'u mun fahimceki fatan zaki cire komai ki cire mun taba yi maki wata magana ta ki so danmu,ina son ki cigaba da yi mana kallon iyaye ko zamu samu wannan alfarmar."?...daga kai tayi tana cewa.." Amman Dad sai..."zamu samu wannan alfarmar eh ko Aa Hauwa."?Ammie ta katseta ta sake maimaita mata tambayar Dad,murmushi kawai Beauter tayi tana fadawa jikin Ammie ta rungumeta itama Ammie rungumeta tayi tana cewa.
"Allah yayi maki albarka Hauwa yayi ma rayuwar ki albarka Hauwa ya kareki da kariyarshi. mungode da wannan karancin da kikayi mana." Sakin Ammie tayi tana kallonta tana mai mamaki karanci irin na matar daga ita har mijinta yanzun taki yarda da soyayyar dansu amman hakan baisa sun nuna mata fushinsu ba sai ma kauna da suke nuna mata.hakan kuwa yayi mata dadi sosai har ta sake dasu suka danyi labari da exchanged content suka bata address dinsu sannan suka wuto gida.
Koda suka koma gida sai da sukayi wanka suka huta sannann suka kira A-kadir sai da suka yi dinner sannan Dad ya kalleshi yace.
"My son." Dago kanshi yayi yana kallon Dad sanann yace.."Naam Dad." Shafa gefen fuskar shi Dad yayi yana cewa.."munje gidan yarinyar da kake magana kuma mun ganta munyi magana da ita sunanta Hauwa'u Abdullahi Jibir yar asalin Nigeria ce,yarinyar tana da saukin kai amman idan akaje mata da saukin kai kuwa,munyi mata maganar soyayyarka ta nuna mata bata da interest akan soyayya,da farko naji haushi sosai sai na lura da wani abu a wajen yarinyar."
Kallon Dad yayi cikin damuwa yana cewa.."Dad mai ka lura dashi a wajen JIDDAH?Dad inasonta ina son na rayu da ita *DA'IMAN ABADAN* Dad please help me."
"Lura da son da kake mata yasa nayi control din zuciyata har na gano da akwai rauni a cikin zuciyarta wanda har yanzun yaki ya warke. kuma rauni a hanyar soyayya akayi mata shi. shiyasa ta tsani soyayya ta kuma ki kara ba so dama a karo na biyu,Son yanzun ta zama yar gida zamu cigaba da janyota a jiki har mu samu ta gaya mana abunda yasa ta daina soyayya ta nan ne kawai zaka samaita,amman idan har kace zaka nuna mata iko da isa ba zaka taba samunta ba balle har ku rayu *DA'IMAN ABADAN*."
Shuru yayi yana kallon Dad ruwa ya dauka yasha yana cewa.."Dad maiye solution."?dariya Dad yayi yana cewa solution daya ne shine ka fita a harkarta ma'ana kabar mata maganar soyayya ka koma nuna mata ta zama yar'uwarka kawai kana janta a jiki a haka zaka dasha mata tausayinka a zuciyarta zakasha mamaki and nasan waye kai sai dai zan kara tuna maka duk inda ka samu kanka kaji tsoron Allah."haka suka gama maganarsu suka wuce room dan kwantawa.
*NIGERIA🥀*
Koda ya koma gida wanka yayi ya shirya ya shiga kitchen ruwan tea kawai ya dafa sai ya dauko shawarma daya ya fara ci.time ya duba yaga har tara ta wuce na dare murmushi yayi yana kallon Dr Moha da yake ta danna waya yana murmushi, girgiza kai Dr Najib yayi yana daukar shima wayar tashi data ya bude ya shiga whatsapp ya dan yi replying din messages din da suke important a wajen shi. sannan ya koma IG nan ma yaga post din da suke da mahimcin a wajenshi sai da ya gama sannan ya kashe datar yana maida cup da plate din da yayi using dasu kitchen yana dawowa an she wayar hannun Dr Moha yayi yana tsaki yace.
"Aikin kenan danna waya ko gajia bakayi Moha kuma baka tsoron ko ciwon ido ko."? Harararshi Dr Moha yayi yana cewa.." Nidai Malan kaban wayata sai mutun yana jin dadi kazo ka tsinke mashi haba man."
Tsaki yayi yana cilla wayar a aljihu yana cewa.."ank'i a bada wayar haba Moha ni kana ban mamaki wani lokacin wallahi akan mai zaka bata lokacinka a wajen aikin banza."
Tashi Moha yayi yana cewa.. "Kasan Allah sai kaban wayata ashe aikin banza.soyayyarce aikin banza?idan aikin banza ce kai kakeyinta."? Wurga mashi wayar yayi yana tsaki yace.." Ni nace maka ina soyayya ai ko."?daukar wayarshi yayi yana cewa.. "Sai kace kana soyayya zamu yarda ai kasan dai ni ba karamin yaro bane ,wallahi Najib ina baka shawara tun wuri kace ma Zulaihat kana sonta idan ba haka ba sai dai kaji anyi bada kai ba." Tsaki kawai yayi yana kwanciyarshi baice ma Moha komai ba sai ma yan rubutu da yayi da wayarshi yana turawa ya kashe wayar switchoff yayi addua ya kwanta kallonshi Moha yayi yana murmushi yace.
"Naga yanda wannan soyayya zata yuyu kullun sai zafin tura mata massage kana tsuke mata fuska haka kake son yarinya ta soka baka da sense kuwa Najib."
★★★
Karatunsu kawai suke sune basu fara shirin kwanciya ba sai wajen 2 na dare shima Zubaida tace gaskiya a kwanta dare yayi daukar wayarta tayi dan ta maidata switchoff nan taga message kamar ba zata karanta ba sai kuma ta bude dan karantawa. yarda wayar tayi bisa gado tana ja da baya baya kallonta Zubaida tayi tana daukar wayar ta fara karantawa kamar haka..
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000
VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp