DA'IMAN ABADAN

21-30

by @jameelarhsadiq6388

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*

_Hot love and fate story_


Na

_YAR'MUTAN KANKIA_


_MANAZARTA WRITERS_



*BOOK ONE*



*PAGE 21-30*



***



_"Gimbiyar mata karatun ya isa haka mana a ajiye a kwanta fatan kiyi addu'a kafin ki kwanta Luv daga masoyinki H A_


"HA."? Cewar Zubaida tana kallon Zulaihat cikin mamaki da alajabi ta sake cewa.." Sis waye HA."? Zufar fuskarta ta share tana cewa.."I don't know." Kwanciyarta tayi tana rufe jikinta duka dan ita bacci take ji bata son tayi late sam shiyasa bata ba maganar mahinmanci ba,ita dai tasan bata da case da wani HA yayi ya gama koma waye shi ita ba sonshi zatayi ba abunda ta sani kenan.


Girgiza kai Zubaida tayi gami da tsura mata ido tana mamaki waye wannan da yake son shigowa rayuwar Zulaihat waye shi?wannan wani irin sone haka? ya sunan wannan son? wani suna ya dace dashi? boyeyyen so? ko kuma matsoracin masoyi mai tsoron baiyana kanshi? furzar da iskan bakinta tayi tana mai yin addua ta tofesu ta kwanta.


*Washe gari*


Tun bayan da sukayi sallar asuba ita Zulaihat bata koma baccin safe ba dan tasan da matsala idan har ta biye ma Zubaida ta koma baccin safe tsab zasu makara gashi Dr Najib ne garesu early morning, dan haka tana gama azkar ta fada toilet wanka tayo ta zura doguwar rigar material ko mai bata tsaya shafawa ba ta fita ta fada kitchen. doya ta fere dan yamball taji tana bukatar ci bata tsaya bata lokaci ba ta hada kayan hadi da komai doyar na haduwa ta murzeta ta zuba kayan hadi sanann tayi shape din ball din, ta fasa kwai ta fara soyawa tana gamawa ta juye a cooler sanann ta dafa masu tea da yaji kayan hadi da kayan kamshi a parlo ta jerasu sannann ta wuce room dinsu a lokacin 7:30 gashi 9:00 suke da lecture din.


Turus tayi tana zabga ma Zubaida harara da ke kwance tana baccinta hankali kwace sai kace ba lecture gareta ba nine. gashi tasan daga gidansu zuwa makara sai sun kusa 30-40min kafin su isa idan suka tadda goslow ma sai ya kaisu 50-1hour ma,kallon time ta sake yi taga har 7:40 tayi take taji ranta yayi kololuwa wajen b'aci ,ita kullun a rayuwarta ba mai jamata yin late sai Zubaida ai tana sane da wanda zaiyi masu lecture kuma tasan halinshi ba sai an tsaya fada mata ba.


Tsaki tayi tana buga mata bugu mai zafi ma kuwa, sake daura mata wani tayi firgigi Zubaida ta tashi tana kwabe fuska tana cewa.."wayyo Allah Sis mai nayi maki."?tana mai kokarin sake komawa,fisge devut din Zulaihat tayi tana cewa..."haba Sis dan Allah har 8 ta kusa fah kuma kasan dai matsalar da muke samu kafin ma mu samu naped aiki ne balle kuma mu isa a school din. shi kanshi aiki ne kuma one hour tayi mana kadan shine zaki kama bacci haba mana Sis. "


Ta ida maganar tana share hawaye zaro ido waje Zubaida tayi da ta duba time sam ta manta da su na da nine. lecture din Dr Najib da bata koma baccin ba,dirkowa tayi bisa bed din tana nufi toilet ko ta kan Zulaihat bata sake bi ba...itama bata sake bin ta kanta ba gyara gadon tayi sannan ta zaune bisa stool ta shafa mai sai poder da lipstick sannan ta yafa gyalenta da dauki bag din ta ta fito parlo ta zaune. ta fara zuba yamball din sanann ta hada tea time ta sake kallo take taji sun kusa zama sorry dan har 8:05.


Tashi kawai tayi ta shiga kitchen ta dauko flake da foodflake ta zuba masu tea din da duk abunda ta girka masu as breakfast ta saka a basket sannan ta zauna zaman jiran Zubaida..fitowar Umma kenan ta gaisheta kallonta Umma tayi tana cewa.."Mamana har an shirya kenan."?daga kai kawai tayi tana wasa da zoben hannunta. murmushi kawai Umma tayi tana kallonta komai nata a raunane yake bata son shiga matsala tana kokarin ganin ta guje ma duk abunda zai sakata a damuwa a rayuwarta ,girgiza kai tayi tana cewa.


"Tashi yi tafiyarki idan bata fito ba,daga yau karda ki sake jiranta tunda ita bata san ciwon kanta." Girgiza kai tayi tana cewa."Aa Umma ai ta kusa fitowa shiryawa take."


Tsaki Umma tayi tana cewa.."mai ya hanata shiryawar kan lokaci kamar yanda ke kika shirya?na lura sam Zubaida bata damu da karatunta ba.dan haka daga yau karda ki kuskura na sake kamaki kina zaman jiranta. da kinga zaki makara kiyi tafiyarki kinji dai ko."?cikin fada Umma tayi maganar d'aga kanta kawai tayi tana mai sake kallon time 8:12 ,hawaye ne taji suna son zubo mata sharewa tayi da bayan hannun tana dai zaune zaman jiran Zubaida, da dankwali a hannu Zubaida ta fito tana cewa.


"Am so sorry Sis ,tashi mu tafi." Ajiyar zuciya ta sauke tana daukar basket din tace.."Umma mun tafi."A dawo lafiya Allah yayi maku albarka." Da Amin suka ansa suka tafi cikin sauri kamar zasu tashi sama tsabar sauri,cikin minti ukku suka iso bakin titi,suka fara kokarin tsada kake naped duk wanda suka tsada ba hanyarsu tabi ba....time ta duba taga 8:20 komawa gefen titi tayi ta zauna ta bugu uban tagumi tana share hawaye ,ita kuwa Zubaida tsaye take bakin titin tana ta aikin tsada neped amman har yanzun bata samu ba itama duba time tayi taga 8:30 saura 30min kenan ya shiga inalillahi ta kamayi a hankali. ta na tausayin kansu bama kamar Zulaihat da yasama ido a yanzun dan ta lura duk motsinta a kan idonshi ne.


★★★


Tsaki yayi yana kallon Moha yace mashi.. "Gaskiya nayi leting sosai da sosai kuma ban iya fita ban sha koda tea ba." Dagowa Moha yayi daga daure igiyar takalminshi yace.."sorry Najib ga tea can kasha to ka tafi kaga time yana ta tafiya." Tsaki ya kuma yi a karo na hudu yana fasa turarenshi masu kyau da tsada gyara sumar kanshi yayi ya daura rolex dinshi yana mai zura zobenshi a yatsarshi sannan ya fito daga bedroom din ,kitchen ya nufa ya hada tea mai kauri ya sha sanann ya dan leka yace ma Dr Moha.


"Broth am done ,sai ka shigo." ..."OK take care." Cikin motocin da suke fake a parking space ya je ya zabi motar da tayi mashi ya shiga. dan daman already duka motars din gidan duk safiyar duniya sai an wankesu dan bai cika maimata mota ba mudun zai shiga school to sai ya chanza ,da bissmillah yayi ma motar key ya dauki hanya cikin sauri dan tara saura minti talatin.


Tun daga nesa ya hangosu bakin titi,take yaji ranshi ya baci duba time ya sake yi yaga 8:35 tsaki yayi yana rage gudun motar tashi yana mamakin yanda yaran nan suke wasa da karatunsu .mai suka tsaya yi da har yanzun basu shiga school ba?tsaki ya kuma yi yana yin parking a gaban Zubaida zuge glass din yayi yana balla ma Zubaida wata uwar harara take tayi baya tana shan jinin jikinta,maida kallonshi yayi wajen Zulaihat da take zaune kasa tana kukan da ta saba.again tsaki ya kuma saki yana cewa.


"Ko ni zan fito na shigo daku."?girgiza kai Zubaida tayi tana tabo Zulaihat da bata san da zuwan na shi ba.tana can tana kuka ita daya tasan halin da take ciki,wurga mata harara ta yi cikin fushi take cewa.


" Dallah can malama ni ki kyaleni ki rabu dani naji da matsalar da ta damai ni na gaya maki."


Girgiza kai Dr yayi cike da mamaki ashe ta iya fada har haka?komai kyau yaka mata shi tsiwar da tayi ma Zubaida yanzun sai yaji daman ta dauwama a haka dan ba karamin kyau tayi mata ba.


Da hannu Zubaida ta nuna mata shi tana maiyin gaba ta barta da sauri ta tashi tana nufar motar dan zuciyarta har tafasa take tsabar takaici. tasan ta ta samaita yau kuwa Allah kadan yasan hukuncin da zai yanke mata,budewa tayi ta shiga da sallama bakinta cikin rawar murya,maida kanshi gefe yayi yana girgiza shi,sannan ya maido da kallonshi kanta yace.


"Wancan Basket din wa kika barma shi yaje ya dauko maki."? Girgiza kai tayi tana bude marfin motar ta fita ta dauko basket din tana bude baya ta dungurama Zubaida shi a cinya.ta koma ta zauna a mazauninta,tada motar yayi yana kallon Zubaida yace.


"Kema ta fara koya maki makara ko."?


Da sauri Zulaihat ta dago kai tana kallonshi sai ta maida kanta a cinyarta tana kuka a hankali a hankali. wai ta fara koya mata makara bayan duk makarar da suke Zubaida ce sanadi,itadai Zubaida kasa tayi da kanta batace komai ba cigaba da cewa yayi.." Wannann shine na karshe da zaki sake biye mata tana b'ata maki lokaci da kinga ta tsaya shirmanta ki tahowarki. ki kyaleta idan ba haka kema sai na hukuntaki fatan zaki kiyaye."?


A hankali tace.."in shaa Allah Sir." Daga nan basu sake magana ba sai wuta da yake ba mota daga gefen ido kuwa Zulaihat yake kallo tana bashi mamaki ,ita dai tayi kuka ko gajia da kukanma ba tayi,bata gudun ciwon kai sam.baice tayi shuru ba duk da yana jin radadin kukan nata har can cikin kasan zuciyarshi.daurewa kawai yake dan so yake yaga kafin 9:05 tayi yana cikin school cikin ikon Allah suka iso yaje wajen da yake parking yayi gami da kashe motar ,kallonta yayi yana mai bata ruwa yace.


"maza wanke fuskar nan tas."


Ansa tayi tana bude marfin ruwan ta wanke fuskar handkerchief ya mika mata nan ma ansa tayi ta goge fuskar,kallonta yayi yana cewa.."kukan ya isa haka maza tafi lecture hall." Daga mashi kai tayi nan ma tana daukar bag dinta ta fita gaba tayi ko ta gode batace ba,murmhshi yayi yana girgiza kai sannan shima ya fito sai da ya fara shiga office dinshi ya ajiye laptop dinshi da abunda ya dace sanann ya nufo lecture hall dan bada darasi.


Tunda ta shigo bata kalli inda Zubaida take ba dan ta kai ta karshe sosai.duk makarar da sukeyi ita ke janyo masu,amman saboda ya tsaneta ko ya fara binciker cikinsu wacece taja makarar amman saboda shi mugune bai iya hukunci ba ya daura laifi a kanta. kwafa tayi tana mai fiddo joting da pen ba ta wani dade da zama ba ya shigo as Usual fuskar nan a murtuke kamar wanda aka kashe ma dan fari,sauke ajiyar zuciya tayi tana mai gyara zamanta dan so take ta gujema duk wani laifi dan ta lura nemanta yake da sheri. (Lol Team Zulaihat Kun fara koya mata rashin ta ido fa,kuma dai kunsan Dr Najeeb baya daukar wurgi😂)


Cikin kamaiwarshi da natsuwarshi da kwarjininshi da kuma haiibarshi da miskillancinshi da ya kara mashi girma a idanun students din nashi ya fara yi masu bayanin abunda ya tarasu bakajin motsi komai sai gudun fan da ke tashi a cikin hall sai kuma kaukausar muryarshi da ta kaurayen hall din baki daya ,lecture ta dauko dadi dan babu wanda bai ganewa sabida ya iya koyawa iya koyawa. tafiya tayi tafiya dan har ya kusa kaiwa inda yake son ya kai ya fara jefo masu question,hall daukar tsuwar waya yayi, wayar Zulaihat ce ake kira da sauri ta datse ta tana mai data meeting, gami da rufe bakinta tana zaro idanu waje ,baki daya hall din sai da kowa yasha jinin jikinshi ana mamaki wani mai tsautsayin ne ya manta bai maida wayarshi silent ba ,bayan kuma kowane yasan role din Dr Najib bai son ana shigar mai lecture da waya na ring(general), jikin kowa lagwas yayi masu waigawa nayi dan gani wane ko wacece wannan, ita kuma ta dukar da kanta kasa tana jiran hukuncin da ya dace da ita wato get out,gyaran murya yayi take attention ya koma wajenshi kowa ya shiga taitayinshi dan karamin tsaki yayi ya cigaba da abunda yake questions yayi masu ana bashi ansa sanann yasa akayi mashi questions shima ya bada ansa,hada koman shi yayi yana kallon Captain ya kama gabanshi, captain ne ya hau step yace.


"Dr Najib yace wanda aka kira waya yana cikin lecture karda ya rigashi zuwa office din shi."


Rintse idonta tayi tana budewa da sukayi jajajir kwallah ne kwance cikin idon kiris suke jira su fara anbaliya,share kwallah tayi tana tashi ta yafe size bag dinta ta fito da sauri Zubaida ta biyo bayanta tana cewa.


"Sis ya akayi kika manta baki maida wayarki off ba."?


Kallon Zubaida tayi tana share hawaye tace.." Sis mantuwa ce kawai,nasa na saka off bari naje nidai na bani da nasan zan hadu da wannan mutumin a makarantar nan wallahi da ba zanyi karatun ba."


Rufe bakinta Zubaida tayi tana cewa.."laaa Sis ki daina cewa haka pls kije kiji mai zai ce maki kizo muci abinci kinsan bamuyi break ba and pls ki share hawayen nan mana."


Juyawa kawai tayi bata ce mata komai ba dan ita bata hawaye take ba. balle wata yunwa ta wanann azzalimin take tana tafiya tana kuka kamar wata karamar yarinya.bata damu da kallon da mutane keyi mata ba,ita kadai tasan yanda takeji bata son tana shiga case dinshi. amman kamar baki kullun cikin yi mashi laifi take a hankali ta bude baki cikin rawar murya tace.


"Wannan ne karshe in shaa Allah am tire na gaji na gaji sosai." Da hannu ta rufe bakinta tana mai share kwallan da suke zarya a saman fuskarta a bakin office dinshi ta tsaya tana kare ma kofar office din kallo,wannan shine zuwanta na biyu a wannan wajen kuma zai zama karshe da yarda Allah.


Matsawa tayi gefe tana mai da kanta kasa, zuciyarta da sauri da sauri take bugawa sakamakon kamshin turarenshi da ya kawo mata ziyara.duk da bata daga kanta ba amman jikinta ya bata yana kusa da ita,lumshe idonta tayi tana budewa a hankali gami da maida kallonta wajen office din,budewa taga yayi ya shiga sauke ajiyar Zuciyata tayi tana mai daura hannunta a door din office din tayi nocking,shuru baice komai ba sake wani nocking din tayi nan ma dai bai ce komai.sai da tayi sau ukku ana hudun ne yace.


"Come in."


Da sallama ta shigo cikin office din tana mai tsayawa gefe a hankali cikin natsuwar da ta zamai mata jiki tace.."Sir gani." Dan dagowa yayi ya kalleta sannan ya ajiye pen din hannunshi.nuna mata kujera yayi da hannu,bata tsaya bata lokaci ba taja ta zauna tana sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zoben hannunta.


Kureta yayi da ido yana mai kare mata kallo ya kusa 5min yana kallonta sannan ya sauke numfashi yana cewa.


"Zulaihat."


Dago kanta tayi tana kallonshi a hankali tace."Naam Sir." Gyaran zamanshi yayi ya cigaba da cewa."maiye matsalarki?maike damunki?gayaman matsalar Zulaihat kinji."?cikin kwantar da murya da sakin fuska yayi mata maganar,ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai tace.


"Bakomai Sir.babu matsalar komai." Shima girgiza kai yayi yana cewa." Ba zaki gaya man matsalar ki ba ko Zulaihatu?idan babu matsala mai yake janyo maki yawan makara? sanann maiyasa kika bar wayarki kunne bayan kinsan bansan haka? Kodai raini ne yake kokarin shiga tsakaninmu."?


Dago kanta tayi tana kallonshi hawaye na shatata kamar mai. rufe baki tayi tana girgiza mashi kai gami da kefa kanta saman table tana rushe mashi kuka,tsaki yayi yana buga mata tsawa har yana bugun table din da ta daura kanta a kai yace.


"Wallahi idan har bakiyi man shuru ba sai nayi ball dake stupid,dukanki nayi?ko kuma kuka nace kiyi man?maza kama bakin nan kiyi shuru ko na karkasheki da maruka shashhsa kawai."


Share hawayen tayi tana mai ja da baya dan ta tsorata sosai bata son tsawa ko kadan, hirgicewa take idan har akayi mata ita ,sai da ta kusan yin minti goma sannan ta bude idonta tana sauke ajiyar zuciya a jere,dan karamin tsaki yayi yana tura mata ruwa a gabanta,babu gardama ta dauka hanunta har kirma yake tsabar tsoro ta kosa ta bar mashi office din ,tana nadamar shigowarta jami'a baki daya.da tasan zata hadu da wannan kalubalen da tun asali bata kawo kanta ba,sai da ta shanye ruwan tas sannan ta ajiye cup din,daman yunwa take ji sosai dan bata samu taci abinci ba gyaran murya yayi yana kallonta yace.


" Zulaihat."


Yanda ya kira sunanta ne cikin kwanciyar murya da tausasa murya sai da taji sunan har cikin brain dinta dago shanyeyen idanuwanta tayi tana daurawa a kanshi sai kuma ta janye tata fuskar tana cewa..."Na'am." Murmushi yayi yana lumshe ido muryarta akwai dadi sosai dan tana mashi dadi sosai,duk da bata da R amman yanda harrufan ke fita daga cute mouse dinta suna tafiya da imaninshi dan ma yana kokarin yin control da tuni ansa samu matsala dan lips dinta suna tada mashi da sha'awarshi mudun zai daura ido a Kansu, tura hannunshi yayi cikin laulausar sumarshi ya furzar da iska mai zafi a bakinshi dan shi kadan yasan mai yake ji akan yarinyar,yakan rasa wani irin so yake mata kallo daya a ranar farko da ya ganta a ranar yaji bakon yanayi a kanta,yana fata yana marari kuma yana muradun su kasance tare har *ABADAN*,yana son ta kasance farincikinshi ta kasance inuwarshi har *DA'IMAN* taya bakinshi zai furta mata kalmar so?yarinyar da har yanzun hankali baibi jikinta ba,har yanzun kururciya na dauwainiya da ita, tabbas yana da aiki babba a gabanshi dole ya koya mata abubuwa da dama ciki kuwa harda daina wannan saurin kuka kamar wata rubarbiyar mota. (Anya Dr Najeeb kana son team Zulaihat su baka kuwa kna kiranta rubarbiyar mota nidai ba ruwana warrr🤭)


"Maiyasa kike makara sannan maiyasa baki mai da wayarki silent ba dazun."? Sake jefo mata tambayar yayi yana mai kafe dan cute lips dinta da ido,su ba pink bane kuma ba red bane haka kuma ba black bane ,za'a dai iya ce masu brown lips ne a hankali take motsa su ta fara cewa.


" Sir ba laifina bane a wajen makara."murmushi yayi yana lumshe ido ya budesu yana saukesu a kanta yace.."idan ba laifinki bane laifin waye."?ajiyar zuciya ta sauke tana cewa.."Zubaida Sir wallahi ke jaman makara a koda yaushe idan kaji karya ka kira Umma ka tambayeta ko yau itace ta koma baccin safe."


Ta ida maganar cikin shagwabe tana turo baki gaba,shafa kan shi yayi yana cewa.. "Naji wannan maiyasa baki mai da wayarki off ba?ko kuma ki saka ta a silent."


Nan ma cewa tayi.."mantawa nayi ina saurine bansan ka rigamu shiga shiyasa." Girgiza kai yayi dan firar nayi mashi dadi sosai bai son a kawo karshenta sam shi kanshi mamakin kanshi yake yanda ya saki baki sai zuba yake kamar wata radio, tabbas son da yake ma Zulaihat ya wuce tunaninshi dan baki ba zai iya kwatanta girmanshi ba,cigaba da cewa yayi.."Amman ai ni nazo daku maiyasa baki maidata off ba tun a moto."?


"Sorry Sir na manta ne kawai."


"OK karki sake daga yau bani wayar nan and maza tashi kije kici abinci karda yunwa ta kamaki."


Kallonshi tayi tana kallon wayar tata,take taji maiyasa bata saka wayarta pin ba, gashi nan ai tasan dole yayi mata bincike ta bani idan yaga wannan messages din da ake turo mata tsab zaice soyayya ta tsaya shiyasa ma take makara a school ,jiki sake ta tashi tana bashi wayar ta bar office din da kallo ya bita yana mai, mai da hankalinshi wajen wayar tata.


Firstly whatsapp ya fara shiga yana duba masu yi mata magana yayi blocking din wanda yaji ba suyi mashi ba. sannan ya ajiye wayar gefe ya cigaba da aikinshi....itama Zulaihat koda ta koma wajen Zubaida ta gaya mata yanda sukayi da an she wayarta da yayi dakyal ta samu ta iya cin yamball din guda biyu ta dan kurbe tea din kadan dan komai ya fice mata a rai.


*Ukraine🥀*


Tunda su Ammie sukaje wajen Beauter basu sake zuwa ba,amman kusan kullun sai Ammie tayi waya da ita ta tambayi lafiyarta sosai Ammie take janta a jiki tun Beauter na d'arid'ari har tazo da ta saki jikinta dan da kanta take kiran Ammie tana jin lafiyarta kuma bata kwantawa bacci har sai ta kira Ammie. sunyi sai da safe da kuma sakon gaida mata da Dad haka suke duk ranar duniya har sun ma saba.


Shi kuma A-kadir kullun da sonta yake kwana yana tashi har a cikin zuciyarshi yake jin ba zai iya rayuwa ba idan babu Beauter. a kusa dashi yana sonta kuma yana kaunarta ,ya rasa dalilinta nakinshi maiyasa ta zabi zaman kanta akan zaman aure? Wannan wata irin rayuwace marar dadin ji? Yau tunda ya tashi da niyar zuwa wajenta yake sai dai ayi duk wance zasuyi ya gaji ya kai bango ba zai zuba ido ba. ya bari sonta ya nemi kashe shi ba,idan ma kudi take bukata zai bata ko nawane indai zata aureshi.


Da wannan gudurin ya tashi dan haka wanka yayi ya shirya cikin kananen kaya masu kyau da tsada golden milk sosai color ta anshi fatarshi ta kara fiddo mashi da kyaunshi da haskenshi.agogo ya daura a hannu ya kuma fashe jikinshi da turare masu kamshi da tsada glass dinshi ya daura a saman handsome face dinshi mai kwarjini da haiba,kara kallon kanshi yayi a mirror yana sakin murmushi dan shi kanshi yasan yayi kyau sosai.


So gently yake saukowa daga saman upstair yana saukowa parlo ya daura kanshi bisa Ammie yana kissing dinta yace.."Morng Myluv. "Shafa kanshi tayi tana cewa.." Morng too Luv,so masha Allah wannan wanka ina zuwa kuma."?dariya yayi yana zama bisan dinning tea ya hada yana tsurbe a hankali ya kalleta yace.


"Gidan Jiddah zani inason naga ya take nayi kokari ai sosai nafi one week ban sata a ido ba."


Murmushi Ammie tayi tana tashi ta shiga bedroom dinta wasu turare ta debo da dubai abaya kamar guda goma ta saka a cikin wani trolley yar'karama ta fito dasu lokacin ya gama shan tea din,mika mashi tayi tana cewa.."idan kaje ka kai mata and kace ina gaidata." Ansa yayi yana mai kara yi mata kiss ya wuce.


Bayan fitarshi da addua Ammie ta rakashi har da share hawayen da taji sun zubo mata,tana fatan faruwar lamarin dan tana son ganin Hauwa tabar wannan rayuwar da ta tsinci kanta a ciki,tana jin yarinyar har cikin jinin jikinta komawa tayi ta zauna tana mai kiranta waya ta gaya mata zuwan Abu-kadir ta aikoshi zai kawo mata wani sako ,godiya tayi mata bayan ta sauke waya ta kalli kanta daga ita sai half best da mini siket sai taga rashin dacewar ya shigo ya taddata haka.


Tashi tayi ta shiga bedroom dinta wani sabon wanka ta sake cikin wani milk lace ta shirya dinki teabubu da Ammie ta kawota mata ,gyara gashinta tayi ta maidashi baya dakyal ta samu ta daura kallabi dan ba iyawa tayi ba dan rabonta da saka irin kayan nan har mantuwarta ta manta sosai da tayi kyau.sweet ta jefah a bakinta ta fito dan zuwa ta bude kofa. dan tun fitowarta daga toilet taji door bell kuma tasan shine tunda yau batayi agreement da kowa ba zasu hadu yau,koda ta bude bashi hanya tayi ya shigo ta mai da door din ta rufe.


Kamar da gaiya take matsa duka hallintun jikinta sai dai mai sam batasan tanayi ba.dan haka take tafiyarta yanga ta gama bi mata jinin jiki,kafeta yayi da ido yana jin sonta da kaunarta suna yawo a jinin jikinshi. yana Sonta yana kaunarta yana sonta a haka bai damu da irin rayuwar da take ba shi dai yasan *A HAKA YAKE SONTA* koda kuwa yarane a gabanta da ta haifa ba ta hanyar aure ba. yaji kuma ya gani,hure mashi iskan bakinta tayi tana cewa.


"Wannan kallon fah."? Firgigi ya dawo daga duniyar da lula yana mai sauke idonshi a kanta,langwabar da kanshi gefe yayi yana cewa.." Please ki ban ruwa nasha." Dan turo baki gaba tayi tana cewa."kai matsalar ka kenan saka mutun aiki."murmushi yayi yana kashe mata ido daya yana cewa.."wai ki fara tun yanzun,Babe nayi missing dinki sosai."


Dan harararshi tayi tana tashi ta shiga kitchen fruit ta dauko mashi da shawarma sai ruwa ta kawo ta ajiye mashi ,kallonta yayi tana turo baki gaba yace.."wayyo Babe ba zaki saman ba ni dan bawan Allah."batasan sanda murmushi ya subuce mata ba dan hakan da yayi sai yayi mata kyau sosai kuma ya tuna mata da wani abu mai wuyar mancewa a tarihin rayuwarta batasan sanda ta ja kumatunshi ba tana cewa.


"Kaki ka girma babba dakai kana shagwaba." Murmushi yayi yana shafa inda ta lakuta a kumatunshi yace.."a wajenki ni yarone wanda zaki rena da salon kaunarki Jiddah ina sonki ina kaunarki kece rayuwata ina fatan na rayu dake a inuwar aure har *DA'IMAN ABADAN* bani fatan wani abu ya rabamu ko mutuwa ina fatan ta fara daukeni ta barki."


Kalamanshi sun kashe mata jiki sosai kuma take tausayinshi ya kamata. wani irin sone yake mata har haka daga shi har iyayenshi bayan ita rayuwarta ta gama lalacewa ta gama zama abun kyama a wajen mutane masu tsafta irinsu, kodai idanuwansu basu gane masu abu da kyau?itafah karuwa mai zaman kanta tana rayuwa mai muni amman duk da haka suke sonta a haka?inama ace zata iya tabbas da sai ta saka masu da hallaci da sai ta nuna masu ita yar halak ce marar manta alkhari,amman mai ba zata Iya ba ,ba zata iya auren kamilin mutun ba irin A-kadir da yarinyar kirki ya dace Wanda zata kawo mashi da mutuncinta har gida ba Irinta ba wanda take gantali take yawon ta zubar,numfashi kawai ta sauke tana mika mashi ruwa,ansa yayi yana sha gami da yi mata godiya.


Da kanta ta yanka mashi fruit din tana bashi yana ci sai shagwaba yake zuba mata ita kuma tana mashi dariya sosai ta sake dashi hakan kuma yayi mashi dadi sosai,ya yarda da maganar Dad da yace tana da saukin kai idan aka fahimceta ya yarda da hakan kuma sosai yaji cikinshi ya cika har yana neman fashewa dan tun da yake bai taba cin abu irin wannan ba.


Shawarma ta sake budewa tana mai kai mashi a baki,rike mata hannu yayi yana girgiza yace..



*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari

DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

*****

*****


Vote

Comment

Share pls