DA'IMAN ABADAN

31-40

by @jameelarhsadiq6388

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*

_Hot love and fate story_


Na

_YAR'MUTAN KANKIA_


_MANAZARTA WRITERS_



*BOOK ONE*


*Wannan page din naki ne Sis Asma Baffah 🥰*


*Banyi posting da weekend , posting day Monday -Friday in shaa Allah*


*PAGE 31&40*



***



"Awww Babe cikina zai fashe fah." Ya ida maganar yana yarfa hannu gami da dafa cikin,rufe bakinta tayi da hannu tana dariya tana maimaita yanda yayi maganar,sakale yayi da baki yana kallonta maiyasa komai tayi sai yayi mata kyau?komai nata yana sonshi dan yana mata kyau ta dade tana dariyar sai da tayi mai isarta ta dakata tana kallonshi tace.


"Please nidai nidai sai ka cinye wannan ko nayi maka kuka uhm uhmm." Cikin salon shagwaba da sarganta tayi maganar tana cinno dan karamin bakinta gaba,lumshe kyawkyawan idanunshi yayi yana budewa yarrrr haka yaji tsikar jikinshi ta tashi rasa yanda zaiyi yayi sai kawai yayi hunging dinta yana maida numfashi dan ba karamin tafiya da imaninshi shagwabar da tayi mashi tayi ba,jin shi yake a wata duniya wanda bai taba zuwa a cikin ta ba,wani irin yanayi ya tsinci kanshi a ciki, shafa bayanshi ta kamayi tana tura hannunta a cikin sumar kanshi tana dan murzawa sai da suka kusan 10min a haka sannan ta dagoshi tana cewa.


"AK are you ok."!? A dan tsorace tayi tambayar dan ta tsorata da yanayin da ta ganshi a ciki a hankali ya daga mata kanshi yana cewa.." Babe ki taimakeni ki aureni please."


Dan tureshi tayi daga jikinta tana girgiza kai, da sauri ya riketa yana cewa.."wallahi idan baki aureni ba na kusa zama dan iska,dan gab nike da nayi komai a irin wannan yanayin da nike ciki."


Sake tureshi tayi cikin zubda hawaye tace.."AK dan Allah ka daina yi man maganar aure zuciyata zata buga na rokeka." Girgiza kai shima yayi yana share mata hawayen da ke zuba kamar yanda shima hawayen yake zubdawa yace.


"Karda laifin wani ya shafi wani Jiddah wallahi kece rayuwata karda kice ba zaki aureni ba. wallahi zan shiga cikin yanayin da fatar baki ba zata katantashi ba Babe. kiyi ma Allah ki duba halin da nike shiga a kanki mana."


Shuru kawai tayi tana shafa bayanshi har sai da ta tabbatar da ya dawo normal sannan ta cireshi daga jikinta ,tana janyo trolleyn da ya shigo da ita ,rike trolleyn yayi yana cewa.


"Zaki aureni." Rintse idonta tayi da karfi tana mai girgiza kai gami da furzar da iska mai zafi tace..."Ka bani lokaci AK zanyi tunani akan maganar okay."?daga mata kai yayi yana kissing din kamatunta sai kuma yaja baya da sauri yana cewa.."Sorry ba zan sake ba." A hankali kuma yace "Astagafurillah ya Allah." Duk da a hankali yayi maganar amman taji shi murmushi kawai tayi tana fiddo wani turare da ya dauki hankalinta sosai. dan yayi mata kyau sosai dan sunsuna kamshi tayi tana lumshe ido ta kalleshi tace.


"AK inason turaren nan sosai Ammie tasan choice din na ina sonta sosai."


Murmushi yayi yana tayata daga sauran kayan.ta nuna jindadinta sosai sai sake duba kayan take tana godiya ya dade sosai.bai bar gidan ba sai dare dan a gidanta ya wuni,shi ke jinsu sallah sosai kuma wunin nashi yayi mata dadi ya cire mata kewa dan har ji tayi kamar karda ya tafi.


Bayan tafiyarshi kwashe kayan tayi ta kaisu bedroom sannan ta dawo ta kwashe plate da cup din da yayi using ta kaisu kitchen ta wanka ta dawo ta gyara parlor.


Wanka ta shiga ta shirya cikin silk night wear onion colar kayan sun ansheta sosai kashe duka light din gidan tayi ta dawo ta maida ta bedroom dinta damp... Kwantawa tayi tana kashe wayarta baki daya dan bata san takura tana bukatar hutu sosai,daman Beauter sam bata chatting amfanin wayarta a kirata ko tayi game amman duk abunda ya shafi wani tweet,Ig,whatsapp bata yinsu balle facebook ko cikin wayarta babu apps din duka,bata ma son ganinsu dan karda tama bude taga abunda take kokarin ganin ta shafe babinshi a rayuwarta.


Murmushi tayi kawai tana cewa.."ya Allah help me."dan shuru tayi tana girgiza kai tana cewa.."Mama ina kaunarki keda sauran a halina kuna rai na a koda yaushe ina fatan Allah ya hadamu a ranar gobe kiyama,Allah yasa ku cireni a ranku kamar yanda nima nike kokarin yi."


Hawaye ta share tana mai girgiza kanta zuciyarta tayi mata nauyi radadi kawai take mata,tabbas rayuwa cike take da kalubale kala kala kuma kowa da kalar tashi qaddarar ita ta yarda kuma tayi Imani da qaddara mai kyau ko marar kyau ta anshi ta ta qaddarar hannun biyu.


★★★


Koda ya koma gida bai tsaya parlo ba sama kawai ya wuce dan wanka yake bukata urgent koda ya fito wanka jallabiya ya zura yana dawowa parlo gaida iyayen nashi yayi yana ko mawa cikin parlo ya zauna kallo ya kunne ya kai franch24 yana kallon labarai.


Bayan sun gama dinner suka dawo wajenshi aka gama kallon labaran sannan yace..."Ammie Jiddah na godiya sosai." Murmushi Ammie tayi tace.."Luv ba wannan news din nike bukatar ji ba ai,ya kuka kare ta yarda da auren ko kuwa har yanzun."?murmushi yayi yana cewa.."an dan samu cigaba Myluv tace na bata lokaci zatayi tunani."


Nunfashi Ammie tayi tana cewa.."Alhmdulillahi ya Allah ,naji dadi sosai kuma kaga daman ina da niyar gayyatarta tazo muyi dinner tare soon."...."daman abunda ya dace ayi kenan yar'albarka,yarinyar tana bani tausayi and ina son naji labarin rayuwarta idan da hali, ammann ina tsorona karda mu tambayeta wacece ita tayi tunanin ko bamu yarda da ita ba,ina mamakin maiyasa tazo wanann kasar ta bar kasarta ta haihuwa." Cewar Dad yana ajiye news din hannunshi ,cigaba da cewa Ammie tayi.


"Gaskiya kam da ace zata bamu wannan damar da munyi mata wannan tambayar kuwa sannan mu koma da ita kasarta ta gado, dan zama kasar wasu ba dadi gareshi ba gudan watan watarana."


"Is better dai,kai Son kaine zaka cigaba da zuwa inda take kana samun shakuwa da yarda su shiga a tsakaninku kaga komai zaiyi mana sauki." Cewar Dad, d'aga kai yayi yana cewa.."in shaa Allah parent. "



*Nigeria🥀*


Yau babu school dan wanann semester tun Thursday suke gama lectures.shiyasa yau ni Jameey kallo daya nayi ma Zulaihat na gane tana cikin yanayin farinciki da annashuwa bata da damuwar komai a ranta dan fuskarta ta nuna hakan.


Zaune take gefen Zubaida cikin Riga da wando kayan sunyi mata kyau sosai abunka da farar fata fuskar nan sai glowing din kyau take,waya take latsawa tana dan jotting a cikin wani short memo, ga dukan alamu research take akan karatunta .


Kallonta Zubaida tayi tana cewa.."Sis tashi muje karda muyi dare kinga har hudu ta kusa."ajiye wayar tayi tana cewa.."Ok shikenan,amman nidai kunshi da gyaran kai za'ayi man banda kitso." Dariya Zubaida tayi tana cewa.."haba sis dan kinga kawai kina da na zaman parlo shiyasa har kike wannan wulakanci."itama dariyar tayi tana cewa.."koba wulakanci ba?daga nace bansan kitso shikenan kinsan dai akwai zafi sosai shiyasa."


"Hakane kam amman please yau ayi maki kitson dan Allah, ni rabon da naga kitso a kan nan naki tun muna secondary SS1 an dade. ki daure dai yau kiyi zai yi maki kyau sosai." Sunburo baki tayi tana saka wayarta a bag dinta cikin natsuwarta tace.."Uhm nidai tashi muje kin san dai banzar anguwar da muke abun hawa wahalar samu yake." Tashi Zubaida tayi tana cewa.."hakane kam ,muje amman fa harda kitso za'ayi yau."


Kallonta kawai tayi tana yin gaba abunta dan ta lura idan ta biye mata har biyar na iya yi masu a gida bama hudu ba,room din Umma ta shiga tace mata zasu wuce kudi ta kara daukowa ta basu 7k tace su kara ayi masu mai kyau ansa tayi tana godiya sosai sannan suka fito suka wuce...cikin natsuwa suke tafiya dan sunyi kyau sosai duk da ba wata uwar kwaliya bace a saman fuskarsu daga hoda sai kwali da man leb'e shine kawai abunda suka shafa.


Ita Zulaihat fara ce sosai kuma tana da tsawo bata da hanci sosai dan hanci dan karami ne saman fuskar sai dai tana da daradaren idanu da dan karamin bakinta lips dinta red ne amman light red tana da girar ido gazargazar bata da cikar gira sosai sannan kuma tana da boobs tsaka tsakiya da kuma hips...sai round face dan fuskarta bata da tsawon nan sosai dan round gareta duk da round din ba wani sosai ba.


Itama Zubaida farace sai dai bata taddo Zulaihat haske da tsawo ba,sannan kuma ita tafi Zulaihat hanci tana da hanci da cikar gira sai kuma ita tsawon fuska gareta sabanin Zulaihat da take da round ta kuma fi Zulaihat Boobs Amman kuma bata taddota diri ba kuma.


Basu sha wuya ba suna isa bakin titi suka samu abun hawa ,nan suka gaya mashi Inda zai kaisu sukayi ciniki suka bashi kudinshi,cikin ikon Allah suka isa lafiya bayan sun fito suka shiga Famjamb saloon and more wajene Wanda aka kawata da kayan gyaran jiki kala kala tun daga kan turarruka da dai komai da aka sani na gyara Wanda yake saka fata tayi glowing tayi kyau sosai.


Hannu biyu aka anshesu duk da suna ragular costumers to haka ma'aikatan wajen suke suna haba haba da costumers dinsu bayan sun zauna aka kawo masu lemu da cup cake wanda ake ba costumers bayan sun huta anan aka fara gyaran jiki.kamar wasu amare bayan an gama gyaran jikin aka wanke masu kansu aka gyara.anan Zubaida tace yau su duka za'ayi ma kitso.


Da farko taso tayi gardama amman wajen aka hade mata kai kowa cewa yake dan Allah tayi zaiyi mata kyau. ba yanda ta Iya ta yarda aka fara kitson ,masha Allah. daman gashi Allah ya bata kamar mai shiyasa Sis meena ta zage ta fara harfa mata kitso kana kana,duk da tace karda ayi mata kananu.amman tace sai tayi idan ta tashi tsifa tazo zata tsefe mata.


Shuru kawai tayi ta zuba ma sarautar Allah ido,tana ji tana gani ana kitse mata gashi yanda ake so,ga kuma mai kunshi ta lik'a mata na salatap bayan ta gama ta koma tayi ma Zubaida da itama ana yarrfa mata kitso na gani da fade. dan tana da gashi itama sosai Amman baii kamo na Zulaihat ba....bayan Jan ya kama yayi kyau sosai aka daura masu da black henne shima masha Allah,turarunka wuta da na shafawa aka hada masu sukaje wajen cashier tayi masu bill suka cake mata kudinta suka fito bayan an hada su da ledar chocolate da aka manna sticker din famjamb a jiki.


Tunda suka fito a wajen gyaran jiki suke neman abun hawa basu samu ba,gashi har mangariba ta wuce duhu ya dan farayi,sun shiga damuwa dan basu saba kaiwa irin wannan lokacin a waje ba,sun kusan shafe minti arba'in a tsaye suna hamar tsayar da abun hawa ga Umma da take famar kiran waya suna ina?duk sun rude suna cikin wannan yanayin wata black Benzene ta parka a gabansu gami da zuge glass kallansu yayi fuskarshi dauke da murmushi yace.


"Amincin Allah ya tabbata a gareku ya kuma kyakwawan yan mata." Banza sukayi dashi dan ba wannan ne a gabansu ba,gida kawai suke son ganinsu baiyi kasa a gwiwa ba fito daga cikin motar yana kafe Zulaihat da ido yace.."haba mana Queen ya ana maku sallama a matsayinku na musulmai baku ansa ba ko dai baku san na samu ladar ne."? Kauda kanta gefe kawai tayi tana mai cigaba da abunda take,murmushi yayi yana hade hannayenshi waje daya yace.."ina neman afuwa Gimbiyata,dan Allah ku shigo na kaiku inda zaku dan nan ba zaku samu abun hawa ba,kuma bansan Ku tsaya nan a dunga kalleman ke."?ya ida maganar yana kashe mata ido daya,dan karamin tsaki ta danyi tana wurga mashi harara tace.."mungode."


"Ooo Please Rayuwata karda muyi haka mana." Ita dai bata sake cewa mashi komai ba,balle Zubaida da tunda yazo kallo daya tayi mashi ta kauda kanta bata sake bin ta kanshi ba,amman tana jin duk surutun da yake yi ,shi kuwa bai daina rokan su shigo ya rage masu hanya ba dan ya kusa 30min tsaye yana abu guda ganin da gaske dai ba zasu samu abun hawa ba yasa Zubaida tayi shihada taja hannun Zulaihat suka shiga suka gaya mashi anguwar da zai kaisu..koda suka iso basu wani tsaya surutu ba suka fito cikin motor shima fitowa yayi ya tari gaban Zulaihat yana cewa.. "Nace ba tawan."


Cak ta tsaya tana waigowa ta sauke idonta a kanshi tana kallonshi a dai dai lokacin Dr Najib ya rintse idonshi yana kaima sitiyarin motarshi duka ya bulle marfin motar zai fita Dr Moha ya rikeshi yana girgiza mashi kai yace..


"No Najib please." Da karfi ya rintse idonshi yana kallon Moha,d'aga mashi kai Moha yayi yana mai saka ma motar lock yace.."be a man haba Najib karda ka bani kunya mana,ai ka girmi wannan k'arantar kai ne fa Najib H Abdullah. dan gaye maiji da ilimi da kudi ga kuma nasaba ta ko wace bangare haba mana taya zaka je ka b'ata lokacinka a wajen can kuma girman ka ya zube."


Iska ya kaima nushi yana d'ago idanunshi da kwarjini da haiba ya cika su ya sauke a kan Moha yace.."da ka barni naje na karya ma wancan yaro k'afafu kalli fa Moha har yanzun basu rabu ba mai yake ce mata har haka?mai hakan ke nufi."?


"Komai ma yana nufi Najib nasha gaya maka ka fito fili ka gaya ma yarinyar nan abunda ke cikin zuciyarka kak'i ,na rasa dalili shin son girma ne?ko girman kai?ko kuma son ne bai kai so ba? inason sanin dalili."?


Dan shuru yayi yana kallon Moha girgiza kanshi yayi yana cewa.." Ko daya babu Moha inasonta ina kishinta sosai,yanzun ji nike kamar na kashe wancan jikkin na huta karka so kaji yanda zuciyata take man rad'adi Moha.bansan ya zanyi ba bansan ya zance mata ba,kai ka sani ban taba soyayya ba dan bata gabana asali. na dauki soyayya shirme rana daya lokaci daya kallo daya na kamu da so,ni ina can ina hama da ciwon sonta ita tana can tana kula wanda ni nasan basu kaine sonta da bukatar taba a kusa dani ba."


Numfashi Moha ya furzar yana cewa..."Tabbas ni shedane a irin son da kake ma Zulaihat.so kenan na kuma yarda da wata magana da ake cewa So nufin Allah,Najib tun wuri ka chanza ka tashi daga nauyayen baccin da kake ka farka Najib ka fuskanci aikin da ke gabanka."


"Kamar ya kenan."!?


"Kamar yanda ya dace mana Najib ,Najib dole kazo ka chanza daga Najib din da ,ina nufin ka tashi daga Najib din da Zulaihat ta sani ka koma ma mata wani Najib din na daban." Dan tsagaitawa Moha yayi yana sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa.."wallahi Najib da ace zaka bi shawarata kuma zaka yarda da maganata da ka gama samun Zulaihat,zaku rayuwa da juna *DA'IMAN* sai dai kash nasan ko na gaya maka b'ata lokacina ne kawai zanyi dan ba dauka zakayi ba."


"Gayaman komai ye indai akan Zulaihat ne zan iya, Moha babu abunda ba zan iya ba akan sonta itace fa rayuwata farincikin zuciyata ina kaunarta. uwar y'ay'ana inason naganta cikin farinciki dan farincikinta shine nawa,gayaman please Moha i beg."


"Najib ya kasance kana janta a jiki kana sakar mata fuska ya kasance kullun kana saka ta a walwala Najib,ka tusa mata sonka ta yanda ba tajin zata Iya yin one hour bata saka ka a ido ba ko taji muryarka,Najib ka nuna mata so da kauna da kula yanda zataji kaine kawai namiji a duniya. sauran kuma duk kallon mata take masu,Najib nasan zaka iya idan kasa kanka amman fa."


Shuru yayi yana kallon Moha sai kuma yayi dan murmushi kamar wanda akayi ma dole yana girgaza kai baice komai ba sai ma motar da yayi ma key suka bar unguwar zuciyarshi cike fam da tunani iri iri.


★★★


"Kaga Malan dan Allah na gaji gida nike bukatar shiga." Murmushi Yayi yana cewa.."Sarauniya kenan,kinga ko ni nan bank'i mu kwana a haka ba,amman nidai a taimaka ma dan almajiri." Kallonshi tayi cikin yanayin na gaji.da kuma kosawa tace..."na gama magana nidai ba zan baka number ta ba.ya kamata ka gane ka rabu dani ka tafiyarka haba mana."


Furzar da numfashi mai zafi yayi yace.."okay Tawan naji ba zaki bani number ba.to ko zan iya sanin sunanki."?..."Zulaihat shikenan ai ko."?langwabar da kai gefe yayi yana d'aga mata gira daya gami da dafe gefen zuciyarshi ya girgiza kai yace.."Aa ba shikenan ba nidai gaskiya ,ya zanyi da sonki?inasonki fa karda sonki yayi ajalina Babe please ki bani digits dinki."


Yanda tayi ne yasa shi hade hannu waje daya yace.."Sorry luv gud night take care and sweet dream with only me."tab'e baki tayi tana shigewarta gida ,dan ya bata haushi ita dai bata san naci da kafiya ta lura shi kuma yana dasu sosai,tsaki tayi tana zama bayan ta gaida Umma ta nuna mata kitson da kunshi har zata tashi Umma tace.


"Mamana." Koma tayi ta zauna tana kallon Umma tace.."Naam Umma." Gyara zamanta Umma tayi tana cewa.."da waye kika tsaya kofar gida."?zaro ido tayi tana jin tambayar har cikin brain dinta,dan basu taba irin haka da Umma ba ,take kalar idanunta suka fara sauyawa kwalla ce kwace a saman idon dakyal tace..."Umma wani ne."murmushi Umma tayi tana girgiza kai tace.."wani wa?Zulaihat." Rintse idonta tayi tana budesu sai ga hawaye sun fito cikin rawar murya tace.."Umma nima fa ban sanshi ba,kawai rage mana hanya yayi daga Famjamb shine yace na bashi number kuma ban bashi ba."


"Share hawayen ko na mareki,daga tambaya sai kuka?maiyasa kuka hau motar wani?sau nawa zan gaya maku ban yarda da hawa motar da baku sani ba?sai wani abu ya samaiku azo ana Allah wallahi bayan sai da na hanaku hawa dan kun rainani kuka hau ko."? Cewar Umma cikin fada,girgiza kai tayi tana share hawayen tace.." Dan Allah Umma kiyi hakuri ba zamu sake ba,yanzun ma dan ba yanda zamuyi shiyasa muka hau."


Harararta Umma tayi tana cewa.."maiyasa baku kirani waya ba kuka ce babu abun hawa ,ai da sai nazo da kaina da abun hawan na daukeku ko?daman nayi ma Zubaida ke nike zaman jiran shigowarki kina babba zaki zama babbar banza?ina kika kai hankalinki da tunaninki?ki tsaya kofar gida da namiji kowa ya wuce yana kallonku kamar mararsa ilimi,to daga yau karda na kuma ji balle gani wallahi ranki zai b'aci sosai idan kuma ba'aji ba zan dauki mataki mai girma sai na taitaraku na maidaku Jigawa naga yanda za'ayi idan ni nan kun rainani maza tashi ki barman waje."


Cikin kuka tace.."mun tuba Umma ba zamu kara ba in shaa Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana." Umma bata ce mata komai ba. sai ma tashi tayi ta bar mata parlon itama tashi tayi ta nufi room dinsu tana kuka,koda ta shigo hango Zubaida tayi zaune ta buga tagumi harararta tayi tana shigewa toilet dole tayi maganin Zubaida dole ta nuna mata itace babba ,ba yanda za'ayi ace yarinya kullun ta dunga jama mata fada, ita ta ja suka shiga motar yanzun gashi ta ja mata fada a wajen Umma,koda ta fito wanka shiryawa tayi cikin kayan bacci tana dauka handout tace.


"Kinga abunda ai kika ja mana ko?kedai kullun sai kin jaman daga wannan sai wanann karki kara daga yau kuma kin dai ji abunda Umma tace ba sai na maimaita maki ba." Dafata Zubaida tayi tana cewa.."Sorry Sis banyi haka dan wani abu ba wallahi,naga dare nayi ga babu abun hawa gashi Umma na ta kiran no way shiyasa har muka shiga, amman daga yau andaina ya kuka kare dashi.?"


Ya mutse baki tayi tana cewa.." Yayi ya gama maitarshi ya kama gabanshi dan ba zan Iya bashi number na ba gaskiya." Numfashi ta sauke tace.."Amman naso ki bashi Sis ba fa zaman gida zamu dauwama munayi ba,ya kamata musan abunda ya dace fah ,dan watan watarana dole muyi aure ko muna so ko bamu so."


"Nidai rabu dani da wanann maganar Sis. kinga dai exams tana matsowa.ba wanann bane a gabanmu please."


"Hmm sis kenan duk da haka dai." Cewar Zubaida tana anshe handout din hannunta,wurga mata harararta tayi tana cewa."bani bansan haka fa karki sake."turo baki Zubaida tayi tana cewa.."nima ai bansan haka gaskiya maiyasa baki bashi number ba."? Kallon ikon Allah take ma Zubaida duk da taji haushin an she mata handout da tayi amman maganarta tana bata mamaki takan rasa maike damunta wani lokacin idan tana hauka dan karamin tsaki taja tana cewa.."son shi ne ko? To zanyi ba shikenan ai ko."?


"Wayyo Allah Sis maiyasa zakice haka shifa yana sonki kuma na lura yana da kirki da sakin fuska ba kamar Dr Najib ba."


"Matsalarsu daga shi har Dr din,nifa Sis ba kowa Ce magana nike son anayi ba wallahi.da naga magana bata da amfani nike shafeta nayi hidima ta fah." Cewar Zulaihat tana an she handout dinta a hannu Zubaida...dariya Zubaida tayi tana cewa.."Maganar Dr Najib din ce bata da fahimmanci ko kuwa ta wannan guy din."?


Tabe baki tayi tana cewa.."All." Yanda tayi maganar ne yaba Zubaida Dariya sai da ta dara tace.."Aa ba dai Both ba gaskiya Sis." Tsaki tayi ta tashi ta bar mata room ta koma parlo danyi karatunta ,itama dauka nata kayan karatun tayi ta cigaba da dubawa dan nextweek ake fara exams.


★★★


Koda su Dr suka koma gidanku basu sake maganar Zulaihat ba .duk da har yanzun abun ya tsaya mashi a rai,idan ya kulle idonshi ita yake hange tana ma wani k'ato murmushinta mai tsadar gaske ,murza hannayenshi yake yana mai kaima kujera naushi a hankali yace.


"Ba zata yuyu ba ke tawace ni daya, tabbas zan iya karya mutun idan har yace zai shiga gonar da ba tashi ba." Dan shuru yayi yana kurbar black tea din da Moha ya hada masu ajiye cup din yayi yana jinginar da kanshi a jikin royal yace. "Why?why?maiyasa zakiyi man haka ?maiyasa zaki hada soyayyata da wani banza kazami ?maiyasa zakiyi man wasa da rayuwata."?


Tsaki yayi jin kanshi har ya fara ciwo tashi yayi yana shigewa bathroom yayi wanka ya kwanta.


Koda ya kwanta bacci kaura yayi ma a idonshi ya rasa maike mashi dadi a rayuwa, shawarar Moha ce ta fado mashi a rai baisan lokacin da ya tashi zaune yana cewa .." Never ba zan iya ba Moha. ba zan dauki shawarar nan taka ba ta banza ba.dolenta ta soni kuma dole ta aureni ko tana so ko bata so dani kawai ta dace ba da wani ba,dan ni daya tal akayi ta ita din lifepartner dina ce."


Ganin wankin hula na neman kaishi dare ya tashi yayo alwallah ya fara sallah ko yaji sausaucin radadin da zuciyarshi take mashi ko yaji dama dama akan son yarinyar.


*Ukraine🥀*


Kusan kullun AK yana hanyar gidan Beauter bai kuma dawowa sai dare idan kuma ya dawo ya gama shiryawa zai kirata waya ne nan ma zasu sha firarsu sanann suke kwanciya...duk da shakuwar da ta shiga tsakanin Abu-Kadir da Beauter Amman har yanzun taki yarda da bukatarshi dan da zaran yayi mata maganar zata fashe mashi kuka sai yayi dakyal yake samun tana shuru.


Duk abun yabi ya damaishi bashi daya ba harda su Ammie abun na damunta sosai da sosai. ya rasa dalilin da yasa yarinyar take haka kodai kadir din ne bata so?idan har shine bata so ya dace ta fito fili ta gaya masu.su kuma zasu fahimceta ta fiddo wanda take so su daura mata aure da shi. kuma Kadir yayi hakuri Allah ya haddashi da wata.


Yau koda ya tashi bai jin dadin jikinshi dan kanshi ciwo yake ga kuma mood dinshi da ya chanza kamar mai malaria,daurewa kawai yayi bai nuna ma iyayenshi ba,ya dan zauna yaci abinci kadan sannann ya kwanta yana jin yanda Ammie keta surutu da Dad amman baice masu komai ba,sai ma lumshe idonshi da yayi dan abun duniya ya taru yayi mashi yawa.


Ji yayi hawaye na zubo mashi kuma zuciyarshi tana mashi zafi sosai,dafe zuciyarshi yayi yana dan cize lebenshi da bakinshi dan shi kadai yasan yanda yakeji,goge hawayen kawai yayi yana juya masu baya.dan karda ma yace zai tashi ya koma room dinshi suce bai lafiya.


Tabbas ya yarda So gamo jinine wata ila shi jininshi ne bai hadu da na Beauter ba shiyasa taki sonshi,da zai iya da tuni ya cire sonta daga zuciyarshi ko ya huta da abunda yake ji gamai da ita,da ace ana sayen so da kudi to da ya kashe ko nawane dan ganin ya sayi soyayya a wajen Beauter ,shi ta soshi ko da ita ba zata soshi ba.son da yake mata kadai ya ishesu suji dadin duniya, bai taba tunani rayuwa zata juya mashi baya haka ba,shi yake so ba'a sonshi tabbas wanann babbar jarabawa ce ta rayuwa kana son maso wani koshin wahala.


Kallon juna akayi tsakanin Ammie da Dad take hawaye suka fara zuboma Ammie janyota jikinshi Dad yayi yana share mata hawayen yace.."Myluv dan Allah karki saka kanki a damuwa kinji."?dagowa tayi tana kallonshi cikin damuwa tace..." Taya zan ki shiga damuwa bayan Son yana cikin damuwa?duba kaga fa yanda ya koma akan so."


Kallonshi yayi yana cewa.."nagani.kamar yanda kike jin ba dadi haka nima nike ji ,sai dai inason mubi komai a sannu zata soshi yanzun ma haka tana sonshi pan din da ake tare da ita yasa ta kasa fahimtar haka, mu cigaba da bin ta a haka zamuga ribar hakan watarana."


A hankali tace..."in shaa Allah."cigaba da tautaunawa sukayi akan lamarin da sake shirya wani plan din.dan su lura kamar plan A ba zai bulle masu ba,amman zasu kara bata lokaci kafin su koma plan B...


*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350

6GB-1620

7GB-1890

8GB-2160

9GB-2430

10GB-2700


*AIRTEL*

500MB-180

1GB-350

2GB-700

3GB-1050

4GB-1400

5GB-1750

6GB-2100

7GB-2450

8GB-2800

9GB-3150

10GB-3500


*GLO*

500MB-180

1GB-350

2GB-700

3GB-1050

4GB-1400

5GB-1750

6GB-2100

7GB-2450

8GB-2800

9GB-3150

10GB-3500


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500

6GB-1800

7GB-2100

8GB-2400

9GB-2700

10GB-3000


VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp



*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari

DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

*****

*****