DA'IMAN ABADAN

51-60

by @jameelarhsadiq6388

*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*

_Hot love and fate story_


Na

_YAR'MUTAN KANKIA_


_MANAZARTA WRITERS_


*BOOK ONE*



*PAGE 51-60*


***



"Every body keep Quite,I said silence." Yanda ya buga tsawar..cikin harzigi ya ida hirgita Zulaihat dan bata san sanda ta fada jikin Alkhamis ba tana makalkaleshi tight tana mai rushewa da kuka,shi kuma Alkhamis k'ara gyara mata kwanciya yayi a kirjinshi yana shafa bayanta ya daura bakinshi a kunnanta a hankali yake cewa.


"Myluv are you ok.?"Kara shigewa tayi sai kirma take tana kuka,wani irin takukin bakin ciki da zafi ya taso ya tokare Dr Najib ko gabanshi baya ganin tsaban kishi da masifa. bai san taku nawa yayi ba sai dai ya ganshi gabansu da karfi ya fisgo Zulaihat daga jikin Alkhamis yana daura mata mari wani marin ya kara aza mata zai kara daura mata na uku Alkhamis ya rike hannunshi yana mashi kallon kai waye?kuma baka isa ba.


Bai san sanda zuciya ta d'ibeshi ba shima ya daura mashi wawan mari dan shi da Alkhamis sai da yaga tartsatsin wuta tsabar azaba kafin ya dawo dai dai ya kara daura mashi wani sai huci yake kamar wani yunwataicen zakin da yayi shekara bai samu abinci ba...cikin jin zafi da azaba Alkhamis ya cacimi kwalar Dr Najib aikuwa nai fada ya kaure a tsakaninsu daman Dr yana sama shima haka Alkhamis din amman duk da Alkhamis yana saman dokin zuciya bai samu nasara a wajen Dr Najib ba,dan Dr Najib ya fishi nesa ba kusa ba,dan yafishi tsawo harda karfin ma.


Ihun da lecture hall din ya dauka yayi attraction din mutanen waje tun daga students har lecturers kuwa. duk wanda ya shigo yaga abunda ke faruwa sai tsoro da tausayin Alkhamis ya kamashi tabbas wannan ko waye bako ne a cikin school din bai kuma san waye *DR NAJIB H ABDULLAHI* da bai yi gigin cewa zai had'a jiki dashi ba wai suyi dambe,koda Dr Moha ya shigo yaga abunda ke faruwa bai tsaya ba ya kira police yace kar wanda ya raba su,su bari masu rabawa suna kan hanya za suzo su raba su.


Ita kuwa Zulaihat tunda ta duke kasa babu abunda take sai kuka gashi daman bata son hayaniya da tashin hankali ko kadan ga kuma zafin marin da Dr yayi tunda tana iya yin kuka a zahiri har ta koma yin na zuci. dan muryarta ta dushashe sannu a hankali ta fara ganin mutane biyu biyu sai luuuuu ta ida faduwa kasa sumaimiya ba tare da kowa ya lura da halin da take ciki ba hankalin kowa yana wajen su Dr Najib.


Suna cikin ba juna kashi sai ga yan sanda sun iso take Dr Moha yaba yan sanda damar kama Alkhamis yace su tafi dashi yazo ya tada masu hankalin makaranta kuma yana fada da malamin makaranta ,aikuwa yan sanda sukayi cak a kan shi suka saka mashi aunka suka tisa keyarshi gaba sai station.


Cikin tsarewa da kamewa irin tashi yace.."duk wanda yasan ba nan bane venue din lecture dinshi just get out,idan kuma nan ne venue dinka get a sit." Yanda Dr Moha yayi maganar ba wasa yasa students suka kama fita daya bayan daya kowa mamaki fal a zuciyarshi mai ya hada wannan fadan? Da tambayar da suka tafi kenan,su kuma yan class zuciyar fal da tambayar mai hakan ke nufi? Dr Najib ya bugi saurayin Zulaihat dan yayi hunging dinta ko dan yana kishi akan abunda ya tadda anayi idan yana kishi hakan na nufin yana son Zulaihat kenan? Suma da wannan tambayar suka samu waje suka zaune sai a lokacin Zubaida ta hango Zulaihat yashe a kasa kamar gawa.


Ihu ta kurma tana yin kanta nan hankalin kowa ya koma a wajen duk da ba wanda yayi kokarin tashi daga inda yake amman ido ya koma kansu girgizata Zubaida tayi tana cewa.. "Sis wake up dan Allah ki tashi karki yi man haka karki tafi ki tafi ki barni Sis wayyo Allah ni Zubaida na bani na Shiga ukku na lalace." Rintse idonshi Dr Najib yayi yana maida kanshi gefe duk da zuciyarshi na jin zafin akan abunda tayi. amman sai da gabanshi ya fadi da yaganta yashe sosai yake jin dama shi yake kukan da Zubaida keyi ko yaji sausauci idan ta mutu ta barshi ba zai iya rayuwa ba, dan bai iya rayuwa da ko wace y'a mace idan ba da ita ba itace yake so kuma yake kauna, shi Dr Moha sai a lokacin ya lura da ita dan kallon Najib yayi yana girgiza kai sannan yasa mata suka.kamata aka sakata a mota sai Zubaida da ta biyo ba inda sukayi ma tsinke sai asibiti.


Duk da yana cikin yanayin damuwa hakan bai hana ya tara yan class ba yayi masu gal da masifa ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba,kowa kuwa ya shiga taitayinshi inda suke ganin suma basu kyauta ba da suka tsaya kallon wanann drama ba tare da sun hana ba. duk da wasu da dama tare suka shigo suka taddasu ba kowa yasan asalin abunda ya hada su ba.cikin takaici ya cigaba da cewa.


"Ba ita wannan yarinyar ba ko wacece na tadda tana wanann rashin tarbiyar dole ne na hukuntata a matsayina na malaminta,dan haka ya zama dole ku mata ku tsare mutuncinku kuma ku kama kanku a matsayinku na mata. kunga dai yarda daku da iyayenku sukayi shiyasa har suka turoku wajen nan ,karku biyema zamani da son zuciya ku dawo kuna aikin da na sani and shi namiji komai yayi adone ake cewa sai dai ni ban yarda da wanann maganar ba ,saboda idan shi ba'ayi mashi gori ba watan watarana sai anyi ma yaranshi idan ya haifesu gaba,kuma dai ance abunda kayi ma wani sai anyi ma naka."


Sai da yayi masu tas.ya kuma hada da wa'azi a fuska ya nuna baisan wacece Zulaihat ba a yanayin yanda yayi bayanin ko sunanta bai ma sani ba hakan ya wankeshi daga zargin da students suke mashi na son yarinyar yake ,wasu daga cikin yanmatan class din kuwa hankalinsu ne ya kwanta da kuma natsuwa da ta samaisu sabida son da suke mashi.


Bai fasa yin lecture din ba sai da yayi covering din da yace zaiyi yana gamawa ya kuma ce test zaiyi nan take.ba snap test ba normal test take hankalin Wanda basuyi karatu ba ya tashi nan yan kananun maganganu ya fara tashi a hankali a cikin hall din.


Basu ida sakankancewa da lamarin ba sai da suka ga malamai suna shigowa ana akace su fidda bags dinsu nan ma suka yarda da gaske dai Test zaiyi without notice,kowa natsuwa yayi bayan ya tadaji pen din shi dan yace pen kawai yake bukatar gani a gaban mutun sai da akayi parking din duk wasu papers sannann ya raba question dan full in the blank ne zaiyi masu questions 20 ne over 40 each question yana carry din two mark kuma 15min ya ba test din.


Yanda ya bada question din ba wanda yayi kokarin d'iga ma peper din shi ink saboda tsaurin da question din yayi masu wasu ma cewa suke baiyi masu ba...ga kuma tsaron da ake yi sai kace exams ake ba test kanaji kana gani baka da damar tambayar na kusa dakai. sai dai ido wasu hawaye suka fara wasu kuwa ganin ba sauki sai a wajen Allah reg number dinsu kawai suka saka sunayin submit,time na cika yace.


"Pen off."


Take suka kama ajiye pen dinsu daman ba sanin ansar suka yi ba,hana kowa motsawa yayi da kanshi da malaman da sukazo tayashi suka bi road by road suka kama ansa har suka gama kowa ya kama gabanshi ansar pepers din yayi yana godiya ya wuce office ya ajiye su ya tafi office din DEAN na faculty din koda yaje suka zauna gaisawa suka fara yi sannan yace.


"Dr Najib dalilin da yasa na kiraka inason sanin wai ya akayi maiya faru da har kai fada da wani saurayin dalibarka anzo har office an gayaman.ba mutun daya ba kuma biyu ba ance har Dr Moha ya mik'a yaron a wajen police."


Murmushi yayi yana cewa.."Sir ai nasa su da suka rugo suka gaya maka abunda suka gaya maka ya wadatar."girgiza kai Dean yayi yana cewa.."Dr inason ka sani kai kana da mahinmmanci a faculty din nan kaii ba a iya faculty ba duka school din nan kana da mahinmanci nasan kai kasan da haka,kaga dan sunzo sun gaya man shurutunsu ba zance ba zan sauraresu ba,zan jisu amman dole naji daga bakinka dani nasan ruwa baya tsami banza."


Murmushi yayi yana gyara zama ya gaya Dean Iya abunda yasani komai bai boye mashi ba..shima kanshi Dean sai da yaji ranshi ya b'aci cikin rashin jindadi yace.."A gaskiya wanann yarinyar bata kyauta ba Sam bata da tarbiya dan haka zamu kira iyayenta mu zauna dasu muji shin su suka koya mata wasa da maza ko kuwa."?


Rintse idonshi yayi yana girgiza kai yace.."ina neman alfarmar karda a sako iyaye a cikin wanann maganar." Shima Dean girgiza kan yake yana cewa.."saka iyayen shine dai dai Dr dan susan halin da ya'r su take ciki sai suka saka mata ido sosai akan tarbiyarta,barin kuma sai naga kamar b'arnane dan nasan iyayenta basu san ila ma tana da saurayi ba ko kuma basu san suna tare da shi ba."


Numfashi ya sauke yana cewa.."hakane kuma ni yanzun zanje asibitin naga halin da yarinyar take ciki." Mik'a mashi hannu Dean yayi yana cewa..Allah ya kara maka girma Dr." Murmushi kawai Dr yayi ya fito sai da ya biya office dinshi ya dauko question peper biyu sannan ya wuce.


★★★


Ta farfado daga sumar da ta tayi ta wucin gadi.sai dai tak'i tace komai sai hawaye kawai da ke kwarara a fuskarta,Dr Moha tunda ta farfad'o yace ta rufe masu baki karda ya sake jin tarin kukanta yana tambayarta maiyafaru da har akayi fad'a kasa magana tayi sai ma kukan zuci da take tunda ya hanata na baiyane...wata irin tsanar Alkhamis ce tazo ta baibaye zuciyarta da gangar jikinta har cikin ranta take jin bata sonshi bata son mai sonshi,ita kanta kunyar kanta take ji akan abunda ta aikata har ji take anya zata iya kallo yan class dinsu?da wani ido zata kalle su ma?balle Dr Najib kuma Allah kadai yasan irin hukuncin da zai mata.


Shi dai Dr Moha maida hankalinshi yayi a wajen Zubaida tana gaya mashi tun daga farkon haduwarsu har kawowa yau da abu da ya faru yaji ba dadi sosai ya kuma yi ma Zubaida fada sosai akan ba motar kowa ake shiga ba a wannan zamanin suna iya shiga motar yan iska ko kuma motar masu sace mutane aje a yankasu a banza kuma su suka kai kansu.


Share hawayenta itama Zubaida tayi tana cewa.."wallahi wallahi Sir daman mun bari tun ranar da Umma tayi mana fada ,daman bamu taba shiga ba sai a kanshi kuma sabida naga dare yayi shiyasa da bamu shiga ba wallahi."


"Is better dai Zubaida ya kama ta dai ku daina din har abada.yanzun duniyar nan tazo karshe mutanen cikinta ba gaskiya ne da su ba.kadan ne masu gaskiyar ,ai da sai ku kira Najib da kuka rasa abun hawa ku gaya mashi kuna waje kaza yazo ya daukeku na tabbata zaizo."


Dan zaro ido Zubaida tayi tana girgiza kai tace.."Sir ai bamu da Number Dr ,kuskurene mun aikata ba zamu sake ba in shaa Allah." Shuru yayi yana kallon Zulaihat yanda ta maida kanta k'asa tana aikin share hawaye. sai yau ya yarda da maganar Najib da yace mashi ita kukane abokinta bata da aiki sai kuka, kauda kanshi yayi yana kallon time kiran likita yayi yazo ya duba drip din da ya saka maka dan so yake yaje gida,daman exams question ya kawo ma exams officer shi ya shigo dashi school din ya tadda wanann tashin hankalin....koda likita yazo ya kara dubata cire mata yayi yana dan rubutu saman wata peper kallon Moha yayi yace.


"Moha gaskiya yarinyar nan tana bukatar hutu sosai stress yayi mata yawa dan jininta gab yake da ya hau." Zaro ido Moha yayi yana cewa.."hawan jini Dr."d'aga mashi kai yayi yana cewa.."yes of course."Dr Moha ya bude baki zaiyi magana kenan Dr Najib ya shigo yana cewa.."aikuwa yanzun ta fara hawan jini da irin wannan halin nata to gab take da kamuwa da ciwon zuciya ma." Su duka da kallo suka bishi banda Zulaihat da ta maida kanta gefe tana share hawayenta tana mamakin irin tsanar da Dr Najib yayi mata.ashe ta wuce duk tunaninta wata irin tsana ce wannann? da har yake mata fatan ciwon zuciya? Sosai tajin zafin kalamanshi har cikin ranta wannan wata irin jarabace?a hankali tace.."in shaa Allah kai ne zaka kamu da ciwon zuciyar kafin ni,I hate you."


Duk da baiji abunda take cewa ba ,Amman yana kallon bakinta na motsawa kwafa yayi yana aiyana Iya rashin mutuncin da zai aikata ma yarinyar.dan wani irin haushinta yake ji har baisan ganinta da ya ganta sai ya hangota lafe a jikin katon banza.dan karamin tsaki yayi yana ba Zubaida question gami da wulla mata harara ansa tayi tana yin kasa da kanta maida kallonshi wajen Zulaihat yayi yana jan dogon tsaki gami da cilla mata harara yace.


"Zaki tashi ki ansa ko kuwa sai nayi ball dake.?"


Turo baki tayi gaba ta tashi zaune hawaye na bin fuskarta bayan hannu tasa ta share hawayen,jefa mata question din yayi yana kallon time yace..." 15min remain." Kallon juna akayi tsakanin Zubaida da Zulaihat tsawa ya buga masu yace.."lokaci na cika zan ansa ku tsaya bata man lokaci." Hawaye ne suka fara zubo mata tana duba question din a hankali ta kalleshi tace.


" Pen."


Tsaki yayi a karo na ba adadi yace.."ina naki."?gauda kai gefe tayi bata ce komai ba sai ajiye peper din da tayi shima baice komai ba ya maida kallonshi wajen Zubaida da take ansa question din..girgiza kai Dr Moha yayi yana mik'a mata pen ansa tayi tasa reg number dinta ta fara answering question din cikin natsuwa nunawa tayi kamar bata san da zaman nashi ba a wajen. sai answer question din ta kawai take tanayi tana share hawayen fuskarta kafin yace time yayi ta mik'a mashi pepers tana komawa tayi kwanciyarta tana lumshe ido,kallon peper yake yana kallonta sai kuma ya danyi murmushin gefen baki.


Itama Zubaida bashi tata tayi tana yin kasa da kanta ansa yayi yana dubawa again dan murmushin yayi yana kallon Dr Moha yace..."mu tafi gida ko."?


"Aa bari Dr yazo ko sai mu saukesu sai mu wuce police ko."? Tabe baki yayi yana cewa.." Aa ba yau ba barshi suyi mashi hankali sanann." Murmushi kawai Moha yayi baice komai ba dan baya bukatar maganar tayi tsawo a gabansu karda yayi tabokara,wayarshi tayi ring ya fiddo ya dauka baice komai sai can yace.."OK shikenan Sir." Ya zare wayar daga kunnanshi yana kallon Zulaihat yace.


"Makaranta na bukatar ganinki keda iyayenki a senate gobe da misilin karfe goma na safe."


Gaba yayi yana barin room din bai tsaya jiran abunda zatace ba da kallo tabi bayanshi tana mai rushewa da kuka,haka itama Zubaidar kuka take tabi bayanshi Moha ne ya tsaya taimaka mata suka

fito sai kuka take.


Tsaye take gabanshi tana cewa. "Sir dan Allah ka taimakemu mun shiga ukku karda iyaye su shigo a wannan maganar wallahi har abada ba zata sake ba,kuma d...d'aga ma Zubaida hannu yayi yana cewa.." Lokacin da take wasa da katon banza kin hanata?baki hanata ba sai ma dariya kika koma gefe kinayi.abun da suke dai dai ne yayi maki kyau. to yanda baki hana aikata barnaba ki sani ba zaki hana makaranta aikata gyara ba maza b'aceman da gani."


Juyawa Zubaida tayi tana share hawayenta zuciyarta cinkushe da bakin ciki tabbas gaskiya ya gaya mata ,amman mai yakawo iyaye a cikin wannan maganar?tabbas ta tabbata yau mai rabasu da Umma sai Allah ta ina zasu fara bata wannan labarin marar dadin saurare? ,kamar wanda kwai ya fashe ma a cikin ciki ta bude motar Dr Moha ta shiga gidan baya maida marfin motar yayi yana mata key suka dauki hanya,shuru motar tayi ba abunda ke tashi sai ajiyar zuciyarsu sosai tausayinsu ya kama Moha.


Har kofar gida ya kai su yana kallon Zulaihat yace.."kuje ku cema Umma idan ba damuwa ina son magana da ita."kamar daman jira take ta rushe mashi da kuka tana cewa.."na bani Sir wallahi kasheni zatayi dan Allah ka rufaman asiri wallahi mun tuba ba zamu kara ba." Rintse idonshi yayi yana budewa cike da tausayinsu yace..."Zulaihat dole agaya mata ko kin manta gobe makaranta take nemanku?akwai matsala fa idan har ba'a ansa kiran ba Zulaihat aikin gama ya gama tunda har makaranta tasa baki a case din. da dai ace gayen baiyi dambe da Dr Najib ba da duk hakan bata faruba idan aka zuba ido ba'ayi hukunci ba ance gobe a sake kenan."


Kara jin wata tsanar Dr Najib tayi fiye da ta farko dan komai ya faru a yanzun shine sillar komai. mutuminnan ya zamai mata masifa a rayuwarta ya zamai mata tauraruwa mai wutsiya.da ace yabi komai a hankali yayi bincike da duk haka bata faru ba ,amman da yake zuciyarshi a wuya take kamar ta kafiran da. ai gashi ya ballo mata august,sauke numfashi tayi tana bude motar ta fita ta shige gida bata dade ba ta dawo tace ma Dr Moha ya shiga inji Umma.


Kusan tare suka shigo cikin gidan,har parlo tayi ma Dr Moha iso sanann ta komawa kitchen ta kawo mashi ruwa da lemu zuba mashi tayi ta koma room din Umma...Zaune Umma take tana lazimi dan d'agowa tayi tana kallon Zulaihat tace.."Mamana lafiya dai ko.?"Dan murmushi tayi kadan tana cewa.."Umma bakomai yana parlo." Kallonta Umma tayi tana nazarinta tabbas ba lafiya dan yanda suka shigo da yanda suke komai jiki sakake ta gane da akwai abunda ke faruwa,numfashi ta furzar tana cewa.."OK shikenan gani nan fitowa."


Tashi tayi tace.."To Umma a fito lafiya." Koda ta fito bata koma parlon ba ta shigewarta room dinsu tana zama ta buga tagumi tana share hawayenta. da wani ido zata kalli Umma?shikenan mutuncinta ya zube a wajen Umma tunda har ta aikata wanann shirman hawaye ta share tana kurama wayarta ido da take kawo haske dan tsaki tayi tana wurga ma wayar harara. tashi kawai tayi ta fada bathroom ta watsa ruwa dan rage ma kanta zafin da take ji kaya mararsa nauyi da takura ta saka ta dauko quri'ani mai girma ta fara karantawa.


Koda Umma ta fito cikin fara'a ta anshi Dr Moha suka gaisa cikin mutunta juna.bayan sun gama gaisawa yayi dan jam kadan dan kallonta yayi yana maida kanshi kasa ya fara zaiyano mata duk abunda faru wanda Zubaida ta gaya mashi kalma A bai kara ba kuma bai rage ba har damben da akayi da Dr Najib da kai Zulaihat asibiti sai da ya kai karshe ya dan maida numfashi yace.


"Umma wanann dalilin ne makaranta tace tana bukatar ganin Zulaihat da iyayenta,amman dan Allah Umma karkisa damuwa a ranki in shaa Allah tunda Najib yana wajen na tabbata komai zaizo da sauki ba abunda zai faru."


Girgiza kai tayi tana kallon Dr Moha tace.."Malan daman abunda nike guje masu kenan.shiyasa kullun cikin gaya masu nike banda kula samari barkatai kamar wasu sakarkaru ina yawan gaya masu su kula da mutuncinsu da kuma kama kansu ko magana bance suyi da wani namiji mai tsawo da zata wuce minti goma ba. dan banga dalili ba . kaga yanda kunnan k'ashi a inda ya kaita.ka haifi d'a baka haifi halinshi ba."


"Hakuri za'ayi Umma wallahi suna cikin yara masu tarbiya da kuma ilimi a cikin yan set dinsu akasi ne kawai aka samu. dan Allah karkiyi masu komai dan sun tsorata kuma nasan ba zasu sake ba."


Dan shiru Umma tayi tana cewa.."suma sake mana sun san ai ko su suwaye bamu da komai sai wanann gidan da kuma kasuwar da nike. itace rufin asirinmu sun san da haka idan kuma rigima zasu ringa janyo mani ai shikenan ko.?"


Girgiza kai yayi yana bata hakuri sai da ya tabbatar da ya lailasota sannan ya bar gidan cike da tausayinsu basu da komai sai gidan da suke cikin?Allah sarki a gaskiya ya jinjina ma Umma da take mace take daukar nauyin karatun mutum biyu duka a jami'a ga kuma ciyarwa ga sutura.


Koda ya tafi Umma room dinta ta koma tayi shirin kwanciya inda suke bata kalla ba. dan sun kaita bango wai Zulaihat take tsale a gaban namiji zata anshi abu a hannunshi ina hankalinta da tunaninta suke je a lokacin?jin bata jin bacci yasa ta tashi ta fara karatu ko taji sausaucin da zafin da zuciyarta ke mata.


Koda Moha ya koma gida sai da yayi wanka da sallah sannan ya zauna abinci Dr Najib ya kawo mashi yaci ya koshi yasha ruwa ya fara gayama Najib duk yanda sukayi da Umma.Amman ya samu ya lailasheta kafin ya bar masu gidan,girgiza kai Najib yayi yana cewa.


"Baiwar Allah sosai take bani tausayi matar nan wallahi. yanzun maiye mafita Moha."? Kallonshi Moha yayi yana cewa.." Mafita daya ce bayan angama case din ka fito fili ka gayama Umma kana son Zulaihat ta baka dama kawai ku sasanta sai ayi aurenku bai zama dole ba sai ta gama karatunta ba sannan."


Numfashi ya sauke yana cewa.."nima tunanin da nike yi tun dazun kenan,idan ba auren akayi ba.zuciyata zata iya fashewa dan na lura samari na kai mata hari."


"Abunda nima nagani kenan.ta ida karatunta a dakinta daga ita har Zubaidar kawai." Cewar Moha yana duba wata news girgiza kai Najib yayi yana cewa.."ai ita Zubaida bata da matsalar Zulaihat dan na lura tafi Zulaihat hankali sosai." Harararshi Moha yayi yana cewa.."kana tunanin zuba maka ido zanyi kenan ka rigani aure?idan ma haka kake tunani ka daina nima nagani inaso dan haka gobe muyi ma Umma magana kawai ta bamu aurensu dan ni banda matsala da Zubaida. duk da ban gaya mata inasonta ba ,amman raina na bani ba zata ki ansata ba a matsayin masoyi Kaine dai damuwar."


Tabe baki Najib yayi yana cewa.."ai nima banda matsala bari fa kaji. ko tana so ko bata so sai na aureta. kai infact ma sai na Aureta dole."


Galala Moha yayi yana kallonshi zaiyi magana ya d'aga mashi hannu yana tashi daga wajen yace.."kai dai ka zuba ido kayi kallo daga gobe wasan zai fara."



*🤣Dr Najib muma mun zuba namu idon muga yanda wasan zai fara kuwa🤗*



*🤧 mura ga ciwon kai dake damuna ayi man addua sanann ayi hakuri da wanann sai mun hadu next page*


*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350

6GB-1620

7GB-1890

8GB-2160

9GB-2430

10GB-2700


*AIRTEL*

500MB-180

1GB-350

2GB-700

3GB-1050

4GB-1400

5GB-1750

6GB-2100

7GB-2450

8GB-2800

9GB-3150

10GB-3500


*GLO*

500MB-180

1GB-350

2GB-700

3GB-1050

4GB-1400

5GB-1750

6GB-2100

7GB-2450

8GB-2800

9GB-3150

10GB-3500


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500

6GB-1800

7GB-2100

8GB-2400

9GB-2700

10GB-3000


VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp


*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari

DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

*****

*****