61-70
*🌺DA'IMAN ABADAN🌺*
_Hot love and fate story_
Na
_YAR'MUTAN KANKIA_
_MANAZARTA WRITERS_
*BOOK ONE*
*PAGE 61-70*
***
*Washe gari*
Umma da kanta ta tashi ta gyara ko ina na gidan, harta abinci sai da tayi sannan ta koma room dinta tayi wanka tai zaman shiryawa...koda suka fito tsakar gida dan yin aikin gida suka ga Umma tayi, da kallo suka bi gidan suna kallon juna jiki a sanyaye suka nufi kitchen.dan hada masu breakfast nan ma warmers biyu suka tadda a kitchen din,koda suka duba sai suga lunch ne da breakfast. nan ma kallon juna sukayi suna kulle warmers din suka koma room dinsu,suna shiga Zulaihat na fad'awa saman bed ta rushe da kuka tana cewa.
"Shikenan Sis mun bani mun shiga ukku,Umma tana fushi damu daman nace maki shurunta ba na lafiya bane.yanzun mu ya zamu yi da rayuwarmu Umma tana fushi damu.!?"A tsorace tayi tambayar tana kallon Zubaida da itama fuskarta take cike tam da hawaye fashewa ne kawai ya rage tayi,hawayenta ta share tana cewa cikin muryar kuka.." Sis Addu'a kawai zamu yi sannan mu bata hakuri duk tsanani yana tare da sauki Sis,tabbas munyi laifi kuma zamu gyara ba zamu sake ba har *ABADAN*." Kukanta kawai ta cigaba dayi tana son yin magana amman ta kasa bata san mai zatace ba,bakinta ya kasa furta komai tabbas zata shiga masifa kuwa idan har Umma tace zata cigaba da yin fushi dasu mai yai zafi haka,tabbas zuciyarta ba zata iya jurar fushin mahaifiyarta ba sam,wayarta tace ta fara ring sharewa tayi tana sakin tsaki cikin kukan da take,sake shigowa wani kiran yayi ganin bata da niyar dauka yasa Zubaida dauka tana kanga wayar a kunne tayi shuru sai goge hawaye take,cikin kaukausar muryashi ta cikeken namiji yace.
"Ina kofar gida ina jiranku kije kice ma Umma ta fito."dab ya kashe wayar bai jira ansarta ba. da sauri Zubaida ta cire wayar daga kunnenta tana bin wayar da kallo wannan murya ko a mafarki ta jita sai ta ganne mai murya,Dr Najib ina ya samu number Sis? taya ya samaita? tasan dai ko Zulaihat tana ciwon hauka ba zata taba ba Dr Number dinta ba,mutumin da ta tsana a rayuwarta mutumin da ko muryarshi da kallonshi Zulaihat bata son ji da gani,numfashi ta sauke tana dire wayar a gaban Zulaihat tace.
"Sis tashi ku tafi lokaci na tafiya kuma Dr Najib yana kofar gida yana jira karda kuma ki sake yin wani laifin kuma." Tashi Zaune Zulaihat tayi tana kallon Zubaida fuskarta cike da mamaki Dr Najib kuma? Ya akayi tasan yazo yana jira sai kace aljana tsaki tayi tana cewa.. "Dan Allah Sis ki daina yi man haka bani so,kin san dai ban son ana kiran sunan mutuncan a gabana ,ni wallahi gabana faduwa yakeyi idan aka anbaci sunanshi ina dalili.wallahi na kusa neman green card na chanza school na gaji da bala'in shi. daga wannan sai wannan ina dalili." Hijab dinta Zubaida ta mik'a mata tana cewa.."serious ba wasa nike ba Sis, shine ya kira waya yanzun nan yace ki fito." Zaro ido tayi waje tana ja da baya gami da dafe kirjinta tace.."Inallillahi na bani ni Zulaihat taya haka zata faru bayan ko number na baya da shi." D'aga kafad'a Zubaida tayi tana cewa.."Nima tambayar da nayi ma kaina kenan,kinga ba wanann case din bane a gabanki yanzun.ki tashi kuje ki samu kiga kiyi successful a wannan kiran da makaranta take maki.idan kin dawo mun zauna musan mafita." Ajiyar zuciya ta sauke tana daukar wayarta ta fito tana fitowa Umma na fitowa daga parlo kasa sukayi da kansu saboda sam fuskar Umma babu fara'a a cikinta babu fuskar da ko sannu da gida suyi mata. daman koda sukaje gaidata da asuba haka fuskar take dan koda suka gaidata bata ansa ba gaba Umma tayi ta barsu tsaye kallon Zubaida tayi tana hawaye zatayi magana ta kulle bakinta tana girgiza kai taja hannunta suka fito,tsaye suka tadda Umma tana gaisawa dasu Dr Najib fuskarta sake sai murmushi take,cikin sanyin jiki suka iso wajen take Umma ta sauya cikin rawar murya suka hada baki wajen cewa.
"Good morning." Murmushi Dr Moha yayi yana cewa.. "Kun tashi lafiya."? Zubaida ce kawai tace." Alhamdulillah." Dr Najib ya bude ma Umma bayan mota da kanshi sai sunna kai yake k'asa dan kunyarta yake ji,cikin ladabi da kwantar da murya yace.."Ummarmu shiga." Murmushi Umma tayi tana cewa."Allah yayi maku albarka Najibullahi." Amin ya ansa ya koma mazaunin driva ya zauna yana danna ma Dr Moha horn,Zubaida ta koma gida tana masu a dawo lafiya sannan ita kuma Zulaihat ta shiga baya kusa da Umma.Dr Moha ya shiga suka dauki hanya,shuru motar ta dauka baka jin motsin komai sai kukan Zulaihat da take kuka kasa kasa,dukansu ba wanda baiji kukan nata ba. Amman suka yi banza da ita,Umma ce taji kukan ya isheta ta waigo ta kalleta tace.
"Idan baki kama bakinki ba kikayi man shuru wallahi Zulaihatu sai na zaneki,wai ban hanaki wannan kukan banzan ba?damai zamuji da rashin hankalin da kikayi ko kuma da wannan shirman kukan naki?ki fita ido na kulle ko dan kinga tun da kikayi abun nan ban maki komai ba shiyasa kike wannan tabarrar ko.?"
Girgiza kai tayi tana share hawayenta tace.."Umma dan Allah kiyi hakuri kibar hushi dani wallahi ba zan sake ba." Tsaki Umma tayi tana cewa.."ni ya zanyi dake Zulaihatu?da ace kuna jin maganata wallahi ko ance ku kalli namijin da baku sani ba kuyi mai magana ba zakuyi ba.daga ke har Zubaida kuwa,a matsayinki na babba kinyi wannan shashancin idan ita Zubaida tayi ace mata mai?ina maki kallon mai hankali da natsuwa ashe aikin banza ne."
Kuka ta sake rushewa dashi tace.."Allah Umma shine yazo ya taddani har inda nike ya ansheman littafi ba yanda banyi dashi ba a hakan ya bani ya hanani gashi kuma karatu nike." Cikin fushi Umma tace.."maiyasa baki bar mashi littafin ba kika anshi na Zubaida."?d'agowa tayi dan ta kalli Umma kacrab idonuwansu suka sark'e waje daya da sauri ta cire idonta cikin nashi tana share hawayenta tace.."Umma itama shi take karantawa,nasan nayi kuskure Amman dan Allah Umma ki yafeman wallahi ba zan iya jurar wannan fushin da kike dani ba,fushinki bala'i ne a wajena." har Umma ta bude baki zatayi magana Dr Moha ya rigata yana cewa.."Umma dan Allah kiyi hakuri yanda tace ba zata sake ba nasan ba zata sake ba din in shaa Allah." D'aga kai Umma tayi tana cewa."shikenan Muhammadu komai ya wuce sunci darajarka Amman da niyata nidasu munyi hannun riga."murmushi tayi tana fad'awa jikin Umma tace.."mungode Umma in shaa Allah bazamu sake ba."maida kallonta waje Dr Moha tace.. "Mungode Sir." Murmushi kawai yayi dai dai lokacin suka iso senate,Dr Najib da kanshi ya bude ma Umma mota ta fito sai sannu yake mata yayi gaba tana bayanshi itama Zulaihat bin bayasu tayi zuciyarta cika fall da mamakinshi yanda yake ma Umma abu kamar duka kenan.
A wani babban hall suka zauna a wajen akwai V.C da kuma D.VC sai registra da MSSN da Dr Najib bayan sun zauna Ameer din makarantar ya tashi ya bude taron da addua sannan ya fada maidu'in da ya tarasu a wajen. nan aka fara tautaunawa sosai take kuka saboda fadan da suke mata suna ce mata ai rashin tarbiyar ne ta aikata da rashin tunani.ba ita daya ba harta Umma tana jin zafin jefarta da Kalmar da suke ta rashin tarbiya.Amman ita ta jama kanta ai duk wanda ya sai rariya yasan zata dubda ruwa.
Sai da suka gama sannan Dr Najib ya ansa tunda ya fara magana wajen yayi shuru kowa shi yake saurara cikin natsuwa da fahimta yake ma Zulaihat magana duk da yafi kowa jin zafin abunda ya faru. amman bata bukatar fada damai zataji kowa fada yake mata ba inda zata dan ji sauki ,shiyasa ya sauko daga dokin fushin shi yayi mata fada mai hada da wa'azi sai da jikin kowa yayi lakwas a wajen ,sannan ya maida dubanshi wajen shugaban makaranta ya basu hakuri sosai sai da komai ya dawo dai dai akayi maganar Alkhamis anan VC yace ai sun kamashi kato dole a ansoma makaranta hakinta da mutuncinta saboda gaba idan aka barshi to gobe ma bashi daya zaizo ba zaizo da wasu ne suyi abunda yafi Wanda yayi daga farko,hakan yayi masu dadi kuwa bama kamar Zulaihat da taji zuciyarta ta danyi sanyi da jin irin hukuncin da za'ayi mashi.
Koda suka fito waya ya kira Moha ya fito suka wuce sai da suka kaisu gida,har zasu juya Umma tace.."ya kamata ku shiga kuci abinci ko Najibullahi kafin ku wuce."kasa yayi da kanshi yana sosa keya yace.."Umma mungode sosai amman da dai mun tafi." Girgiza kai Umma tayi tana cewa.."Bissimillanku." Ba yanda suka iya dan basu iya yima babba gardama ba suka bi bayansu suka shiga.
Da kallo yabi gidan dan Yau ne rana na farko da ya fara shiga cikin gidan. duk da kullun sai yazo kofar gidan yayi kamar awa biyu zuwa ukku yana kallonshi yana jin dadi,amman yau gashi Allah ya nufa ya shigo cikinshi ,ba wani babban gida bane gidane mai dauke da d'aki biyu ko wani daki da toilet sai kitchen da toilet din tsakar sai tsakar gida dai dai madaidaici ,kuma share yake babu wata kazanta ko kadan,parlo suka shiga Wanda yake dauke da kurya sai kuma daga gefen parlon room din su Zulaihat ne sai kitchen daga bangare na daban haka toilet ma.
Samu waje sukayi kasan carpet suka zauna ba yanda Umma batayi dasu ba akan su hau kan kujera suka k'i yarda sai dai kyalesu tayi ta shiga ciki,su Zulaihat ne suka kawo masu abinci da ruwa sai robobin lemu suka basu waje dan su sake..bayan sun fita suka dan zuba kadan suka ci abincin yayi masu dadi sosai dan kawai su duka biyun kusan halinsu daya sai dai daya yafi daya sakin fuska shine kawai banbancinsu,bayan sun gama Dr Moha yace.
"Umma mungode Allah ya kara girma.har zamu tafi Abba bai shigo ba." Murmushi tayi tana cewa.."Allah sarki ai an zama daya Muhammad." Dan shuru tayi tana kallonsu tana goge hawayen da zuka zubo mata sakamakon ambatar Abba da Moha yayi,rudewa sukayi kamar su yi Kuka wajen tambayarta lafiya?mai akayi mata?ina ke mata ciwo?girgiza masu kai tayi tana cewa.
"Muhammadu kace zaku tafi baku Abba ba ko."? Daga kai yayi yana matsawa kusa da kafafunta yace.." Eh hakane Umma amman dan Allah kiyi hakuri idan maganata ta bata maki banyita da wata manufa ba." Murmushi tayi tana share hawayenta tace.
"Shekara goma sha biyu kenan rabona da Abban Zubaida ai." Cikin mamaki da al'ajabi suka hada baki wajen cewa.."sha biyu Umma."?kallonsu tayi taga yanda suka shiga damuwa sosai sai ta sauke ajiyar zuciya tace.
"Kwarai kuwa." Dan gyara zama Najib yayi yana cewa.."Umma dan Allah kiyi hakuri karda kice mun wuce gona da iri.amman muna son ki gaya mana abunda ya rabaki da mijinki har na tsawo shekara sha biyu, Umma Shekara sha biyu ba nan bace." Murmushi Umma tayi tana cewa.."Najibullahi ko daya baku wuce gona da iri ba,na daukeku kamar yaran da na haifa da cikina.kuma ba komai bane dan kun tambayi jin abunda ya hadamu dan haka ku gyara zamanku zan gaya maku." Kasa magana sukayi sai ma zama suka gyara suna kallonta furzar da iskan bakinta mai zafi tayi tana cewa.
*WAIWAYE*
Sunana Hafsat Hamza Imam asilin mu yan jahar katsina ne a karamar hukumar kusada a wani kauye mai suna *GANGARA*,Gangara garin Fulani ne fulanin ma na asili mun taso cikin gata a wajen iyayenmu da yake biyu rak Allah ya basu a duniya,Yayana mai suna Aminu sai kuma ni Hafsat daga nan Allah bai kara ba iyayena haihuwa ba,suka cigaba da rainonmu cikin nuna kauna da kulawa. dan duk kauyen gangara ba Wanda ya kaimu gata da jindadi ina da shekara goma a duniya muka tashi daga gangara muka dawo birnin kano da zama a unguwar riyar lemu nan baba ya sama mana gida muna zaune sanadin dawowarmu birni mun tadda ana boko.anan Baba ya sakamu a makaranta muna karatun arabi da na zamani shi kuma Baba yana neman kudinshi ci da sha da sutura ba wanda muka rasa Alhamdullahi.
Muna rayuwa cikin tsarine kamar wasu yan asalin birni dan kuwa tarbiya dai bamu rasa ba kuma duk wani cigaba da Baba yaga ya shigo zai saka mu a ciki..idan kuwa bamu shiga ba to ya duba yaga akwai sabon Allah a cikinshi.. to shi wannan babu hannunshi a ciki, a kwana a tashi ba wuya a wajen Allah nida Yaya Aminu mun kammala karatun secondary sai Baba yace ni daga ita na tsaya aure zaiyi man.shi kuma Yaya sai ya cigaba anan BUK a inda yake karantar engineering ni kuma sai yace a cikin mane mana na fiddo d'aya Wanda na yarda dashi da kuma tarbiyarshi.anan na fiddo Mustapha aka saka mana ranar aure wata ukku.
Soyayya mai karfi mu kayi da Mustapha ba Wanda bai sanni da Mustapha ba..haka mukayi soyayyarmu danginshi sun sanni haka gidan mu harda yan gangara sunsan Mustapha... Akwana a tashi sai ga ranar da za'a daura mana aure da Mustapha tazo ranar juma'a a kofar family house dinmu dake a gangara anan aka daura auren akan sadaki naira dubu hamsim da dan marakin sa d'aya.
Tunda mukayi aure muke rayuwarmu cikin farinciki da soyayya mai tsanani da kuma shakuwa,munyi aure da wata shidda ciki ya baiyana jikina sai dai baiyi wata ukku ba cikin ya zube ,munji ba dadi amman muka dauki qaddararmu muka cigaba da rayuwarmu...Abu kamar wasa sai da na dauki ciki sau biyar a gidan Mustapha baya zama..wannan ya kawoman matsala a wajen mahaifiyarshi tace bata yarda ba.sai dai ya kara aure nan fa yace a'a ta bashi shekara daya za'a nemi magani idan maganin baiyi ba ya yarda ta zab'a mashi wanda tayi mata.
Nan ta yarda tace aje anemi maganin haka akaita neman magani shi ya nema haka gidanmu ma a nema..ba dai sauki sai wajen Allah,har akayi shekarar dai jiya i yau ciki yaki zama inaji ina gani Dada ta daura ma Mustapha aure da kanwarshi wato Jamila diyar yar'uwata. aka kawota da farko mun dan samu sabani nida Jamila tunda Mustapha ya kankareta mata warning akan yi man rashin kunyar da take sai ta natsu ta kama kanta.
Jamila tana da shekara daya zuwa ta biyu ta samu ciki haka akaita murna ana gayama yan'uwa da abokan arziki cikin ikon Allah da yarda shi cikin na cika watan haihuwarshi ta haifo shantalelen d'anta mai kama da ubanshi yaro yaci sunan Abdulganuyu.
Abdul ya taso cikin gata ba daga wajena ba ba daga wajen ubanshi ba haka muketa rainonshi cikin soyayya yana da shekara biyu ta sake haihuwa nan ma ta haiho mace taci suna Fatima. haka dai sai da Jamila tayi haihuwa shidda a gidan Mustapha banda ko daya kuma ina samun cikin baya zama,mamana kuma da yan uwana basu fasa nema man magani ba..Aminu ya gama karatunshi har ya dawo gida sai dai babu aiki yana dai zuwa kasuwa jiran shago a haka Allah ya hadashi da matarshi Zainab yar jahar Jigawa ya aura.
Muna jindadin zama da Zainab sosai duk da ita Zainab yar gidan mai hannu da shuni ce a jigawa,amman daga ita har danginta basu da wulakanta na kasa dasu.
Rayuwa ta fara juyaman baya a gidan Mustapha dan komai na gidan yana hannun Jamila .tun daga wajen ijiye abinci har da dakin baccinshi makullen duk suna hannunta idan kwanana yazo ita ke bude man ,abinci kuwa ban isa na aunoshi da kaina ba sai dai Jamila ta auna ta bani kuma na ansa nayi godiya.tunda ni ba wannan matsalar bace a gabana matsalata daya itace haihuwa...wulakanci da gori da cin mutunci da cin fuska ba wanda bani gani a wajen Mustapha da danginshi na dauke kai na mika lamarina a wajen Allah.,dan ko iyayena ban taba gaya masu ga halin da nike ciki ba..ana cikin wannan rayuwa Allah yayi ma Babanmu rasuwa munyi kuka har mungode Allah haka aka gama zaman makoki,Anan Yaya Aminu ya maido Mama gidan shi daman a gidan haya muke zaune..,nan aka cigaba da rayuwa Yaya Aminu aurenshi da shekara biyu matarshi Zainab ta haiho d'iya mace mai kama da babanta ranar da sakon haihuwar yazoman sai da nayi kuka dan dadi.
Ranar suna yarinya taci suna *ZULAIHATU* wato sunan mahaifiyarmu kenan,tunda aka haifi Zulaihat wani kuncin ya rage daga cikin zuciyata kusan kaso 50 daga cikin 100 sunan ban haifi Zulaihat bane kawai,amman komai nike ma yarinyar wajena take wuni bacci ke maidata a wajen uwarta ,haka muka kama rayuwa an haifi Zulaihat da wata shidda Allah yayi ma mahaifiyarmu rasuwa..,an kwanta da ita lafiya aka wayi gari bata nan nayi kuka har na gode Allah daga karshe dai na saka ma kaina dangana ba uwa ba uba bani da kowa sai Yaya Aminu shima haka bai da kowa sai ni ,sai muka hade kanmu muka zama tsinstiya madaurinki daya.
Zainab matar Yaya Aminu lafiya tak'i yau ciwo gobe ciwo haka dai aka tafi asibiti gwajin farko da akayi mata aka gano da tana dauke da wani cikin nan ma munyi murna.ni lokacin har na cire rai da haihuwa dan nafi shekara uku ko b'atan wata ban sake yi ba,da yake cikin yana bata wahala yasa na dawo da Zulaihat wajena muka cigaba da zamanmu.
Duk ina ankare da wulakancin da ake man a gidanMustpha ban nuna nadamu ba,ina dai rayuwa ta na baima Allah lamarina.fahimta da akayi ba zan tamka ba sai aka fara zalintar Zulaihat yarinyar da ko magana bata damu da yinta ba kominta silent yake.bata da fitina ko kadan sai dai idan suka zalunceta ta koma gefe tayi kuka,tun ina kauda kai har na kasa ina magana,idan kuma nayi magana ko na rama mata sai ace dan bansan zafin haihuwa ba shiyasa. na kanyi kuka na gode Allah.
Ganin zaman lafiya na neman gagarata na maida Zulaihat gidansu wajen iyayenta sai dai naje masu wuni ko suma suzo man da yake cikin Zainab ya dan tasa zai kai wata shidda zuwa bakwai.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau dadi gobe ba dadi sai dai hakuri har cikin Zainab ya isa haihuwa nan haihuwa tayi gardama har sai da aka yankata aka fiddo d'a namiji sai dai uwa babu lafiya... Binciken likitoci aka gano tana dauke da cencer mahaifa sai da aka cireta sannan lafiya ta samu aka dawo gida yaro yaci suna Hamza.
Muna kiran Hamza da suna Daddy ,Daddy yarone mai shiga rai ga kyau da Allah ya wadatashi dashi ,bai da rigimar banza sabanin Mamana da kullun take cikin kukan banza sai ya zama Daddy ne babba itace karama dan idan tana kukan shi yake lailashinta duk da ko magana bai ida iyawa ba a lokacin.bai wuce shekara daya a ta biyu yake ita kuma Zulaihat tana da shekara uku tana neman shiga ta hudu ma.
Watarana ina zaune kawai na shirya na tafi gidan Yaya Aminu dan inason ganin su Mamana. koda naje gidan Mamana na tadda tasa uwar a gaba sai kuka take anyi anyi tayi shuru taki har Zainab tasaka mata ido. tana ta hidimarta shi kuma Daddy yana kwance yana bacci,tambayarta nayi tun yaushe yake baccin?tace man zaiyi awa biyu yana gama shan sweet ya kwanta nace baccin ya isa haka ya kama ta a tadashi.
Ashe rai yayi halinshi ba jijigawar da bamuyi mashi ba cikin rudewa uwar ta dauke shi tayi waje dashi tana watsa mashi ruwa nan ma bai motsa ba haka muka hakura muka kira babbanshi muka gaya mashi halin da ake ciki akazo aka kai shi gidanshi na gaiskiya.
Jamamin mutuwar yaron ya jefeni bani da aiki sai ciwo ganin ba sauki sai wajen Allah na tafi asibiti anan ake gayaman ina da ciki har na tsawon wata takwas nayi murna harda kuka kuwa...koda na gayama Mustapha shima yayi murna dan farincikinshi har bai boyu ba haka na karasa rainon cikina Daddy nada wata biyu da rasuwa na haifi y'ata mace mai kama dani a asibiti na haifeta koda muka dawo gida yarinya taci suna *ZUBAIDA* sunan kakar Mustapha kenan.
Haka nida Mustapha muka cigaba da rainon Zubaida duk da yaiyenta su Abdul suna zaluntarta sai dai na kauda ido dan basan fitina da tashin hankali sam, da Zubaida ta girma ta kai shekara hudu a duniya sai ta fara rama fada da kanta dan bata kyale duk wanda ya tabata lokacin Zulaihat tana da shekara shidda a duniya,amman Zubaida ke rama mata fada dan ita Zulaihat sam bata san rigima da tashin hankali ,duk da Zulaihat ta girmi Zubaida amman komai tare ake masu dan Zubaida tana da garin jiki tsawone bata dashi sosai kamar Zulaihat, hatta makaranta tare Yaya Aminu ya sakasu komai tare yake masu nima idan na samu kudi inayi masu dinki iri daya da dai abunda baifi karfina ba dan ina Sana'a kuma ina samu Alhamdulillahi.
Bayan wasu shekaru a lokacin Zubaida na da shekara takwas itama kuma Zulaihat tana da shekara goma tafiya ta kama Yaya Aminu zaije sokoto interview din wani aiki har sun shirya suka biyo ta gidana yi man sallama. Zulaihat na ganin Zubaida sai tace bata binsu tana wajena ba yanda ba'ayi da ita ba.ta bisu taki harda kukan ta. ba dan sunso ba suka barta suka tafi ita kuma ta cigaba da wasanta da Zubaida daman wasan ta gani ya dauke mata hankali taki bin iyayen nata sokoto..cikin dare muna zaune sai karatu nike koya masu aka kira wayata sai naga number Yaya Aminu daman na kirasu har sau biyu basu dauka ina dauka nace nayi fushi inata kira ba'a dauka ba sai akace man bashi bane hatsarin mota sukayi yanzun haka suna teaching hospital sokoto dan haka ana bukatar ganinmu gobe duk yanda naso a gaya man a wani hali suke anki andai ce suna lafiya na dai zo.
Haka na kama kuka Mustapha harda Jamila sun kewayeni sai hakuri suke bani tun da asuba muka dauki hanyar sokoto dani da Mustapha da Zulaihat muka barma Jamila Zubaida koda muka isa asibiti muka kira waya a emergency akace muzo muna zuwa na tadda Yayana cikin halin rai ko mutuwa nan na fasa ihu ina na bani na lalace Yaya dan Allah karda ka mutu ka barni kasan bani da kowa kaine uwata Yaya kaine ubana
Kallona Yaya Aminu yayi ya maida kallonshi wajen Zulaihat hawaye na zubowa a fuskarshi a hankali yace mutuwa rigar kowa ce Hafsat duk mai rai sai ya mutu ya bar duniya ita duniya gidan arone ga amanar Zulaihat nan na bar maki ki tuna bata da kowa sai ke da Zubaida... Wani sabon kukan na fashe dashi ina cewa in shaa Allah zaka tashi ka cigaba da rainon Zulaihat har ka aurar da ita kai da aunty Zainab... Girgiza man kai yayi yace ..Hafsat ai tuni Zainab rai yayi halinshi nima ta Allah nike jira karda ki yada zumuncin Allah Hafsat ki rike Zulaihat da amana kamar yanda zaki rike Zubaida ki sakata tayi ilimi mai zurfi wanda al'umma zasuyi alfahari da ita ina fatan aurene kawai zai rabaku....daga ni har Zulaihat din kuka muke da yake yarinyar a lokacin tasan maiye mutuwa dan tana da shekara goma a duniya kuka nike ina rike da hannunshi itama Zulaihat tana rike da gudun hannunshi ta daura kanta saman gadon da yake kwance tana kuka...muna cikin haka Allah ya anshi abunshi nan sabon tashin hankali ya barke dan suma na dunga yi a asibitin sai da nasha ledar ruwa biyar sannan Mustapha ya bada kudi aka bamu gawarsu Yaya Aminu da matarshi Zainab muka jiyo dasu kano.
Bayan rasuwarsu da wata biyar Mustapha yace shi sam bai yarda da zaman Zulaihat a gidanshi ba sai dai na kaita jigawa wajen dangin uwarta amman bata zaman mashi gida...ba yanda banyi dashi ba akan ya barta ta zauna ba sai yayi mata komai ba ni zanyi mata komai amman yace sai fa ta bar mashi gida..ganin da gaske Mustapha yake sai nima nace ban yarda ba...banga wanda ya isa ya rabani da marainiyar Allah ba nan akaita fada nidai na tsaya akan bakata sai Mustapha yace na zab'a zaman aure dashi ko kuma zama da Zulaihat? Ni kuma nace zama da Zulaihat anan ne yayi man saki biyu na kwashe kayana na dawo nan gidan da zama wato gidan Yaya Aminu na kwashe kayan matarshi na saida na sama Zulaihat kudin a account kudin suna nan ajiye ko biyar ban taba ba ,ban kuma bar mashi Zubaida ba da ita na taho muka cigaba da rayuwarmu ina sana'ata ba abunda ban masu har kawo yau kunji dalilin rabuwata da mijina.
*AMATULLAH DATA SERVICES*
*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700
*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500
9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000
VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank
*** for call or whatsapp
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*****
*****